Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro (Ta Nazari)  |  Nuwamba 2016

Sun Fito Daga Duhu

Sun Fito Daga Duhu

“[Jehobah] ya kiraye ku daga cikin duhu zuwa cikin haskensa mai-ban al’ajabi.”1 BIT. 2:9.

WAƘOƘI: 116102

1. Ka bayyana abin da ya faru sa’ad da aka halaka Urushalima.

A SHEKARA ta 607 kafin haihuwar Kristi, Sarki Nebukadnezzar na biyu da rundunarsa sun kai wa birnin Urushalima hari. Littafi Mai Tsarki ya faɗa irin kisan da aka yi a wurin sa’ad da ya ce: ‘[Nebuchadnezzar] ya karkashe samarinsu da takobi a cikin wurinsu mai-tsarki, ba ya kuwa ji tausayin saurayi ko budurwa, ko tsoho, ko mai-furfura ba. . . . Ya ƙone gidan Allah, ya rurrushe ganuwar Urushalima, ya ƙone dukan fādodinta da wuta, ya lalatar da dukan kayanta masu-kyau.’2 Laba. 36:17, 19.

2. Wane gargaɗi ne game da halakar Urushalima Jehobah ya ba da, kuma mene ne zai faru da Yahudawa?

2 Bai kamata mutanen da suke Urushalima su yi mamaki cewa an halaka birnin ba. Domin shekaru da yawa kafin wannan lokacin, annabawan Allah sun yi wa Yahudawa gargaɗi cewa za su zama bayi a Babila idan suka ci gaba da ƙin bin Dokar Allah. Ƙari ga haka, an gaya musu cewa za a kashe Yahudawa da yawa, kuma waɗanda ba su mutu ba za su yi zaman bauta a Babila. (Irm. 15:2) Wane irin rayuwa ce suka yi a Babila? Shin abin da ya faru a lokacin ya faru a zamaninmu ne? Yaushe ne hakan ya faru?

 SA’AD DA SUKE ZAMAN BAUTA

3. Ta yaya bautar da Isra’ilawa suka yi a Babila ta bambanta da wadda suka yi a Masar?

3 Abin da annabawan suka faɗa ya faru da gaske. Ta wurin bakin Irmiya, Jehobah ya gaya wa waɗanda za su yi zaman bauta cewa su amince da yanayinsu kuma su yi iya ƙoƙarinsu su ji daɗin rayuwa a wajen. Ya ce: Ku “gina wa kanku gidaje [a Babila], ku zauna a cikinsu: ku dasa gonaki, ku ci amfaninsu: Ku biɗi lafiyar birni inda na sa a kai ku bauta, ku yi wa Ubangiji addu’a dominta: gama a cikin nata lafiya ku za ku sami naku.” (Irm. 29:5, 7) Waɗanda suka bi gargaɗin Allah sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum a Babila. Waɗanda suka kai Yahudawa bauta sun ba su damar ci gaba da yin harkokinsu. Suna da ‘yancin zuwa ko’ina a ƙasar. A zamanin dā ƙasar Babila ce cibiyar kasuwanci, kuma rubuce-rubucen da aka tono sun nuna cewa Yahudawa da yawa sun koyi yin kasuwanci a wajen, kuma wasu sun zama ƙwararrun maƙera. Ƙari ga haka, wasu Yahudawa sun zama masu arziki. Bautar da suka yi a Babila ba kamar wanda suka yi ƙarnuka da suka shige a ƙasar Masar ba.Karanta Fitowa 2:23-25.

4. Ban da Isra’ilawan da suka yi tawaye, su wane ne suka yi zaman bauta a Babila, kuma me ya sa ba za su iya bin kome da Dokar Allah ta ce su yi ba?

4 Ko da yake an biya bukatun Yahudawan da suke zaman bauta a Babila, amma ta yaya za su bauta wa Jehobah? An riga an halaka haikalin Jehobah da bagadinsa, kuma firistoci ba sa yin hidimominsu kuma. Duk da haka, a cikin waɗanda suka je zaman bauta a ƙasar, da akwai bayin Allah masu aminci kuma sun sha wahala tare da sauran mutanen. Amma sun yi iya ƙoƙarinsu su bi Dokar Allah. Alal misali, Daniel da abokansa guda uku masu suna Shadrach da Meshach da Abednego sun ƙi cin abincin da aka hana Yahudawa su ci. Kuma Daniel ya ci gaba da yin addu’a ga Allah a kai a kai. (Dan. 1:8; 6:10) Tun da yake Yahudawa suna zaman bauta a ƙarƙashin al’ummar da ba sa bauta wa Allah, zai yi wa masu aminci a cikin su wuya su yi kome da Dokar ta ce su yi.

5. Wane alkawari ne Jehobah ya yi wa mutanensa, kuma me ya sa hakan yake da ban mamaki?

5 Shin Isra’ilawa za su sake bauta wa Allah kuma a hanyar da ta dace? A lokacin, kamar hakan ba zai yiwu ba, domin mutanen Babila ba sa taɓa barin bayi su sami ‘yanci. Amma, Jehobah ya yi alkawari cewa mutanensa za su sami ‘yanci, kuma hakan ya faru. Duk abin da Allah ya faɗa zai faru.Isha. 55:11.

KIRISTOCI SUN TAƁA ZAMAN BAUTA KUWA?

6, 7. Me ya sa ya dace mu daidaita yadda muka fahimci zaman bauta a Babila Babba na zamani?

6 Shin Kiristoci sun taɓa zaman bauta kamar yadda Isra’ilawa suka yi a Babila? Mujallar Hasumiyar Tsaro ta yi shekaru tana bayyana cewa bayin Allah a zamaninmu sun soma bauta a shekara ta 1918 kuma sun sami ‘yanci daga zaman bauta da suke yi a shekara ta 1919. Amma a wannan talifin da kuma na gaba, za mu ga dalilin da ya sa ya dace mu sake bincika wannan batun.

7 Ka yi tunani game da wannan: Babila Babba tana wakiltar dukan addinan ƙarya. Saboda haka, idan mutanen Allah sun zama bayinta a shekara ta 1918, hakan yana nufin cewa suna bin koyarwar addinin ƙarya a wannan lokacin.  Amma, tarihi ya nuna cewa shekaru da yawa kafin a soma Yaƙin Duniya na ɗaya, bayin Allah shafaffu sun soma janyewa daga Babila Babba. Ko da yake an tsananta wa shafaffu a lokacin yaƙin duniya na ɗaya, gwamnatoci ne ainihi suka tsananta musu ba Babila Babba ba. Saboda haka, mutanen Jehobah ba su yi zaman bauta a Babila Babba ba a shekara ta 1918.

A WANE LOKACI NE BAYIN ALLAH SUKA YI ZAMAN BAUTA?

8. Ka bayyana yadda aka ɓata koyarwar da ke cikin Kalmar Allah. (Ka duba hoton da ke shafi na 21.)

8 A ranar Fentakos ta shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu, ruhu mai tsarki ya sauko kan dubban Yahudawa da baƙin da suka zama Kiristoci. Waɗannan Kiristocin sun zama ‘zaɓaɓen iri, zuriyar firist ba-sarauci, al’umma mai-tsarki, jama’a abin mulki na Allah kansa.’ (Karanta 1 Bitrus 2:9, 10.) Manzannin sun ci gaba da kula da ikilisiyoyin mutanen Allah har suka mutu. Amma, bayan mutuwar manzannin, sai wasu maza suka soma koyarwar ƙarya domin “su janye masu bi bayansu.” (A. M. 20:30; 2 Tas. 2:6-8) Ƙari ga haka, da yawa cikinsu maza ne masu hakki a cikin ikilisiyoyi, wato su masu kula ne. Sun kafa rukunin limamai, ko da yake Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa: “Ku duka kuwa ‘yan’uwa ne.” (Mat. 23:8) Waɗannan mutanen suna son bin koyarwar Aristotle da Plato kuma suka soma koyar da waɗannan ra’ayin maimakon gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah.

9. Ka bayyana yadda gwamnatin Roma ta goyi bayan Kiristoci da suka yi ridda, kuma mene ne sakamakon hakan?

9 A shekara ta 313 bayan haihuwar Yesu, Sarki Constantine ne yake sarautar Roma kuma ya sa aka soma bin koyarwar ‘yan ridda a ƙasar. Bayan hakan, sai Coci suka soma cuɗanya da gwamnatin Roma. Alal misali, sarki Constantine ya yi taro da shugabanan addinai, kuma ana kiran wannan taron Council of Nicaea. Bayan wannan taron, sarkin ya kori wani firist mai suna Arius daga ƙasar don ya ƙi ya amince cewa Yesu ne Allah. Ƙari ga haka, a shekara ta 379 zuwa 395 bayan haihuwar Yesu, Theodosius na ɗaya ya zama sarkin Roma kuma Cocin Katolika ya zama ainihin addinin da ake bi a ƙasar Roma. Masanan tarihi sun ce Romawa sun zama Kiristoci a ƙarni na huɗu. Amma gaskiyar ita ce a wannan lokacin, Kiristoci da suka ridda sun amince da koyarwar ƙarya, saboda haka sun riga sun zama mambobin Babila Babba. Duk da haka, da akwai wasu Kiristoci shafaffu masu aminci. Suna kama da alkamar da Yesu ya yi magana a kai, kuma sun yi iya ƙoƙarinsu don su bauta wa Allah, amma ba wanda yake sauraron abin da suke faɗa. (Karanta Matta 13:24, 25, 37-39.) Babu shakka, da gaske sun yi zaman bauta a Babila Babba!

10. Me ya sa mutane suka soma ƙin koyarwar coci?

10 Ɗarurruwan shekaru bayan haihuwar Kristi, mutane da yawa suna karanta Littafi Mai Tsarki a yaren Girka ko kuma Latin. Suna iya kwatanta koyarwar Kalmar Allah da koyarwar coci. Sa’ad da wasu suka lura cewa coci suna koyarwar ƙarya, sai suka ƙi bin waɗannan koyarwar. Amma gaya wa mutane ra’ayinsu a fili yana da haɗari sosai saboda ana iya kashe su don hakan.

11. Ta yaya limamai suka soma hana mutane karanta Littafi Mai Tsarki?

 11 Da shigewar lokaci, yawancin mutane ba su iya yaren Girka da Latin ba, kuma shugabanan addinai sun ƙi a fassara Kalmar Allah zuwa wasu harsuna da mutane suka iya. Saboda haka, limamai da wasu masu ilimi ne kawai suke iya karanta Littafi Mai Tsarki, kuma wasu a cikinsu ba su iya karatu ko kuma rubutu sosai ba. Ƙari ga haka, za a hukunta duk wani da ya ƙi amincewa da koyarwar coci. Kiristoci shafaffu masu aminci suna taro a ƙananan rukuni, kuma wasu ba sa yin taron gaba ɗaya. Kamar Yahudawa da suka je bauta a Babila, shafaffu “zuriyar firist ba-sarauci” ba su iya tsara yadda za su riƙa bauta wa Allah ba. Babu shakka, Babila Babba tana matsa wa mutanen sosai!

KIRISTOCI SUN SOMA KOYAN GASKIYA

12, 13. Waɗanne abubuwa biyu ne suka sa mutane suka soma samun ‘yanci daga Babila Babba? Ka ba da bayani.

12 Shin Kiristoci na gaskiya za su taɓa samun ‘yancin bauta wa Allah yadda ya dace? Ƙwarai kuwa! Abubuwa biyu masu muhimmanci sun faru da suka sa aka kasance da begen samun wannan ‘yancin. Na farko ya faru a shekara ta 1450 sa’ad da aka ƙera na’urar buga littattafai da ake juyawa da hannu. Kafin a ƙera wannan na’urar, ana rubuta Littafi Mai Tsarki da hannu kuma hakan ba shi da sauƙi. Littafi Mai Tsarki yana da tsada sosai kuma ba a cika samunsa a cikin kasuwa. Ƙari ga haka, yakan ɗauki watanni goma kafin wanda ya iya rubutu sosai ya gama Littafi Mai Tsarki guda ɗaya. Kuma saboda marubuta suna yin amfani da fatan dabbobi,  hakan ya sa kayan rubutu suke da tsada sosai. Amma, mutum zai iya buga shafuffukan littattafai guda 1,300 a kowace rana ta yin amfani da na’urar buga littattafai da kuma takardu.

Ƙera na’urar buga littattafai da kuma mafassaran Littafi Mai Tsarki masu gaba gaɗi sun sa aka kasance da begen samun ‘yanci daga Babila (Ka duba sakin layi na 12, 13)

13 Na biyu shi ne yadda wasu maza masu ƙarfin zuciya a farkon ƙarni na 16 suka tsai da shawarar fassara Kalmar Allah zuwa harsunan da mutane suka iya. Mafassara da yawa sun yi wannan aikin ko da sun san cewa za a iya kashe su don yin hakan. Limaman sun yi fushi sosai kuma sun ji tsoro. Domin idan mutane suka karanta Littafi Mai Tsarki a yarensu, za su soma tambayoyi kamar: A ina ne a cikin Kalmar Allah aka ambata gidan azaba? A ina ne a ce a riƙa biyan limamai kafin su yi wa mutum jana’iza? Kuma a ina ne aka ambata cewa a naɗa paparuma da wasu manyan limamai? Shugabanan addinai sun yi fushi sosai sa’ad da mutane suka yi musu tambaya, kuma an kashe mutanen da suka ƙi koyarwarsu da ke bisa ga koyarwar Aristotle da Plato, wato mutanen da suka yi rayuwa kafin a haifi Yesu Kristi. Sun yi hakan don su hana mutane karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin tambayoyi. Kuma sun yi nasara. Amma wasu masu gaba gaɗi sun ƙi barin Babila Babba ta shawo kansu don sun koyi gaskiya da ke cikin Kalmar Allah, kuma suna so su ci gaba da koyon abubuwa. Hakan ya nuna cewa an soma samun ‘yanci daga addinin ƙarya.

14. (a) Mene ne waɗanda suke son nazarin Littafi Mai Tsarki suka yi a shekara ta 1870? (b) Ka bayyana yadda Ɗan’uwa Russell ya koyi gaskiya.

14 Mutane da yawa da suke son su koyi gaskiya sun gudu zuwa ƙasashen da za su samu ‘yancin nazarin Littafi Mai Tsarki. Suna so su karanta da yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma tattauna da juna ba tare da wani ya riƙa gaya musu abin da za su yi ba. A ƙasar Amirka ne Charles Taze Russell da kuma abokansa suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki a shekara ta 1870. Da farko, Ɗan’uwa Russell yana so ya san su wane ne suke koyar da gaskiya a cikin addinan. Sai ya soma bincika koyarwar addinai da yawa da kuma koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ba da daɗewa ba, sai ya ga cewa babu wani a cikinsu da ke bin abin da Kalmar Allah ta ce. Ƙari ga haka, ya yi magana da shugabanan coci da yawa da fatan cewa za su amince da koyarwar da shi da abokansa suka binciko daga Littafi Mai Tsarki kuma su koya wa mabiyansu. Amma limaman ba sa son yin hakan. Hakan ya sa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka ga cewa ba za su iya bauta wa Allah ba tare da waɗanda suke cikin Babila Babba.Karanta 2 Korantiyawa 6:14.

15. (a) A wane lokaci ne Kiristoci suka soma bin addinin ƙarya? (b) Waɗanne tambayoyi ne za a tattauna a talifi na gaba?

15 A wannan talifin, mun koyi cewa Kiristoci na gaskiya sun soma bin addinin ƙarya bayan da manzannin suka mutu. Amma, muna bukatar mu san amsoshin tambayoyin nan: Ta yaya muka san cewa sun samu ‘yanci daga Babila Babba shekaru da yawa kafin 1914? Da gaske ne cewa Jehobah ya yi fushi da bayinsa domin sun daina wa’azi a lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya? Shin a lokacin wasu ‘yan’uwa sun ƙi bauta wa Jehobah kuma suka rasa alherinsa ne? A ƙarshe, idan Kiristoci sun bi addinin ƙarya daga ƙarni na biyu bayan haihuwar Yesu, a wane lokaci ne suka samu ‘yanci? Waɗannan tambayoyi ne masu muhimmanci sosai, kuma za a ba da amsoshinsu a talifi na gaba.