Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

‘Aikin Kuwa da Girma’

‘Aikin Kuwa da Girma’

LOKACI ya yi da za a yi wata babban taro mai muhimmanci a Urushalima. Sarki Dauda ya tattara dukan hakiman Isra’ila da shugabanni da dukan jarumai. Kuma sun ji daɗin sanarwar da aka yi. Jehobah ya ba wa Sulemanu, ɗan Dauda izinin yin wani babban ginin da za a keɓe don bauta wa Allah na gaskiya. Sarkin Isra’ila ne aka hure ya san yadda tsarin ginin zai kasance, kuma ya gaya wa Sulemanu yadda zai yi ginin. Dauda ya ce, “aiki kuwa da girma: gama haikalin ba domin mutum ba ne, amma domin Ubangiji Allah ne.”1 Laba. 28:1, 2, 6, 11, 12; 29:1.

Bayan haka, Dauda ya yi tambaya cewa: “Wanene fa za ya bayar da yardan rai, shi cika hannunsa yau ga Ubangiji?” (1 Laba. 29:5) Da a ce kana wurin, mene ne za ka yi? Za ka so ka taimaka don a yi wannan aiki mai girma? Nan da nan Isra’ilawan suka ɗauki mataki. Kuma “suka yi murna, da shi ke sun bayar da yardan ransu, da sahihiyar zuciya suka yi baiko ga Ubangiji da yardan rai.”1 Laba. 29:9.

Ƙarnuka bayan haka, Jehobah ya kafa wani abin da ya fi haikalin nan muhimmanci. Jehobah ya kafa haikali na alama, shiri ne da ya yi don ‘yan Adam su kusace shi bisa fansar Yesu. (Ibran. 9:11, 12) Ta yaya Jehobah yake taimaka wa mutane su sulhunta da shi a yau? Yana yin hakan ta wa’azi da muke yi. (Mat. 28:19, 20) Saboda wannan aikin, kowace shekara miliyoyin mutane suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma da yawa suna yin baftisma. Ƙari ga haka, ana kafa ikilisiyoyi da yawa.

Saboda irin wannan ci gaba, ana bukatar a daɗa buga littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki, da gina Majami’un Mulki da kula da su, kuma ana bukatar wajen da za a riƙa yin manyan taro. Shin ka yarda cewa wa’azin da muke yi, aiki ne mai muhimmanci kuma ana samun ci gaba sosai?Mat. 24:14.

Ƙaunar da muke wa Allah da maƙwabtanmu da kuma sanin muhimmancin wa’azi su ne suke sa mutanen Allah suke ba da gudummawa da yardan rai. Abin farin ciki ne mu riƙa ‘girmama Ubangiji da wadatarmu,’ kuma mu ga yadda ake amfani da shi da kyau don a yi aikin da ya fi muhimmanci a duk tarihin ‘yan Adam!Mis. 3:9.