“Ku ɗaura wa jikinku dukan kayan kāriya yaƙi wanda Allah ya bayar domin ku iya tsayawa ku yi gāba da dabarun Shaiɗan.”​—AFIS. 6:11.

WAƘOƘI: 79, 140

1, 2. (a) Me ya sa matasa suke yin nasara a yaƙin da suke yi da Shaiɗan da kuma aljanu? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Mene ne za mu tattauna?

MANZO BULUS ya ce Kiristoci suna kamar sojan da ke bakin dāga. Amma ba da mutane muke yaƙi ba, da Shaiɗan ne da kuma aljanu. Shaiɗan da aljanunsa sun daɗe suna yaƙi kuma sun ƙware sosai. Sanin hakan yana iya sa mu ji kamar ba za mu iya yin nasara ba, musamman ma idan mu matasa ne. Amma matasa za su iya yin nasara a kan waɗannan maƙiyan kuwa? Hakika, matasa za su iya yin nasara kuma suna yin hakan. Me ya sa? Domin suna samun ƙarfi daga wurin “Ubangiji.” Amma ba hakan ne kaɗai yake taimaka musu ba. Wani abu kuma da ke taimaka musu shi ne, ‘ɗaura wa jikinsu dukan kayan kāriya na yaƙi wanda Allah ke bayarwa.’​—Karanta Afisawa 6:​10-12.

2 Wataƙila a lokacin da Bulus yake ba da kwatanci nan, yana tunanin irin kayan yaƙin da sojojin ƙasar Roma suke sakawa. (A. M. 28:16) Bari mu tattauna abin da ya sa wannan kwatanci ya dace sosai. Yayin da muke hakan, ka yi la’akari da abin da wasu matasa suka ce game da ƙalubalen da suka fuskanta da kuma  yadda suka amfana ta wurin saka kayan kāriya wanda Allah yake bayarwa.

Ka Saka Dukan Kayan Kāriya na Yaki Kuwa?

“GASKIYA TA ZAMA ƊAMARARKU”

3, 4. Ta yaya gaskiyar da ke Kalmar Allah take kamar ɗamarar sojan Roma?

3 Karanta Afisawa 6:14. Ɗamarar da sojojin Roma ke ɗaurawa tana ɗauke da ƙarfen da ke kāre ƙugunsu. An ƙera wannan ɗamarar ne a hanyar da za ta taimaka wa sojan don kada ya ji nauyin rigar ƙarfe ta yaƙi da ya saka. Ban da haka, wasu ɗamarar suna ɗauke da ƙaramin sashe da sojan zai iya saka takobinsa. Idan sojan ya sha ɗamara da kyau, hakan zai ba shi gaba gaɗin yin yaƙi.

4 Hakazalika, gaskiyar da muke koya daga Kalmar Allah tana kāre mu daga koyarwar ƙarya da za ta iya ɓata dangantakarmu da Allah. (Yoh. 8:​31, 32; 1 Yoh. 4:1) Kuma idan muka ci gaba da ƙaunar gaskiyar, hakan zai sa ya yi mana sauƙi mu saka ‘rigar ƙarfe ta yaƙi,’ wato bin ƙa’idodin Jehobah. (Zab. 111:​7, 8; 1 Yoh. 5:3) Ƙari ga haka, idan muka fahimci Kalmar Allah sosai, hakan zai taimaka mana mu iya kāre abin da muka yi imani da shi.​—1 Bit. 3:15.

5. Me ya sa muke bukatar mu riƙa faɗin gaskiya a koyaushe?

5 Idan muka sha ɗamara sosai da gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, za mu sa rayuwarmu ta jitu da wannan gaskiyar kuma za mu riƙa faɗin gaskiya a koyaushe. Me ya sa bai kamata mu riƙa yin ƙarya ba? Domin ƙarya tana ɗaya daga cikin abubuwan da Shaiɗan yake amfani da su sosai. Ƙarya tana ɓata sunan mutumin da ke yin ta, da kuma wanda ke amincewa da ita. (Yoh. 8:44) Don haka, duk da cewa mu ajizai ne, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu guji yin ƙarya. (Afis. 4:25) Daina yin ƙarya ba shi da sauƙi. Wata ’yar shekara 18 mai suna Abigail, ta ce: “Faɗin gaskiya ba shi da sauƙi, musamman ma a lokacin da yin ƙarya zai cece ka daga wani mawuyacin yanayi.” To, me ya sa take ƙoƙarin faɗin gaskiya a koyaushe? Ta ƙara da cewa: “Idan na faɗi gaskiya, zuciyata ba za ta riƙa damu na ba. Ƙari ga haka, iyayena da kuma abokaina za su riƙa amincewa da ni.” Wata ’yar shekara 23 mai suna Victoria, ta ce: “Idan ka faɗi gaskiya kuma ka tsaya a kan abin da ka yi imani da shi, hakan zai iya sa a riƙa zaluntar ka. Amma za ka amfana sosai domin za ka kasance da gaba gaɗi, za ka kusaci Jehobah kuma mutanen da ke ƙaunar ka za su riƙa daraja ka.” Babu shakka, hakan ya nuna mana cewa barin ‘gaskiya ta zama ɗamara’ a gare mu a koyaushe yana da muhimmanci sosai.

Gaskiya ta zama ɗamara (Ka duba sakin layi na 3-5)

“ADALCI YA ZAMA RIGAR ƘARFENKU”

6, 7. Me ya sa aka kwatanta adalci da rigar ƙarfe ta yaƙi?

6 Ana yin wani irin rigar yaƙi da sojojin Roma suke sakawa a ƙarni na farko da ƙarfuna da aka lanƙwasa. Ana lanƙwasa ƙarfunan yadda za su yi daidai da kirjin sojan, sai a haɗa da maɗaurin fata don a riƙa ɗaura rigar da shi. Bayan haka, sai a saka ƙarfuna a kafaɗarsa kuma a haɗa shi da maɗaurin fatar. Irin wannan rigar ba ta barin soja ya yi tafiya a sake, kuma yana bukatar ya riƙa dubawa a kai a kai ko maɗaurin ya kwance. Ƙari ga haka, rigar tana hana takobi ko kuma kibiya ta yi masa rauni a zuciya ko kuma a wasu gaɓoɓin jikinsa.

7 Babu shakka, wannan kwatanci ne mai kyau na yadda bin ƙa’idodin Jehobah yake kāre mu daga abubuwan da za su iya ɓata dangantakarmu da Jehobah. (K. Mag. 4:23) Hakika, soja ba zai so ya canja rigar ƙarfe na yaƙi da wanda ba na ƙarfe ba. Mu ma ba za mu so mu canja ƙa’idodin Jehobah game da abin da ya dace da namu ƙa’idodin ba. Me ya sa? Domin ba za mu iya kāre zuciyarmu ba. (K. Mag. 3:​5, 6) A maimakon haka, ya kamata mu riƙa bincika  a kai a kai ko har ila, ‘rigar ƙarfe ta yaƙi’ da muka saka tana kāre zuciyarmu.

8. Me ya sa bin ƙa’idodin Jehobah yake da amfani?

8 Shin a wasu lokuta kana ji kamar ƙa’idodin Jehobah suna hana ka sakewa, ko suna hana ka yin abubuwan da kake son ka yi? Wani ɗan shekara 21 mai suna Daniel, ya ce: “Malaman makarantarmu da kuma abokan makarantarmu sukan yi mini ba’a domin ina bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Hakan ya ɗan sa na kasa kasancewa da gaba gaɗi kuma ya sa ni baƙin ciki sosai.” Amma yaya yake ji yanzu? Ya ce: “Da shigewar lokaci, na ga amfanin bin ƙa’idodin Jehobah. Wasu a cikin ‘abokaina’ sun soma shan ƙwaya, wasu kuma suka daina zuwa makaranta. Abin taƙaici ne ganin yadda rayuwarsu ta zama. Hakika Jehobah yana kāre mu sosai.” Wata ’yar shekara 15 mai suna Madison, ta ce: “Bin ƙa’idodin Jehobah, maimakon yin abin da abokaina suke so bai yi mini sauƙi ba.” Mene ne ya taimaka mata? Ta ce: “Na tuna cewa ni Mashaidiyar Jehobah ce kuma Shaiɗan ne yake jarraba ni. Kuma a duk lokacin da na yi nasara a kan jarrabawarsa, ina farin ciki sosai.”

Rigar ƙarfe ta adalci (Ka duba sakin layi na 6-8)

‘LABARI MAI DAƊI NA SALAMA YA ZAMA KAMAR TAKALMA A ƘAFAFUNKU’

9-11. (a) Wane irin takalmi na alama ne Kiristoci suke sakawa? (b) Mene ne zai taimaka mana mu ji daɗin yin wa’azi?

9 Karanta Afisawa 6:15. Duk sojan Roma da bai saka takalminsa ba, bai yi shirin zuwa yaƙi ba. Kuma da fata guda uku da aka haɗa su tare ne ake yin takalman sojojin Roma domin takalmin ya yi ƙarfi sosai. Ban da haka ma, an yi shi yadda sojan zai jin daɗin tafiya idan ya saka takalmin. Don haka, sojan yana iya yin tafiya da kyau ba tare da zamewa ba.

10 Hakika, takalmin sojojin Roma yana taimaka musu su yi nasara a yaƙi. Hakazalika, takalmi na alama da muke sakawa yana taimaka mana mu yaɗa bishara ta salama. (Isha. 52:7; Rom. 10:15) Duk da haka, a wasu lokuta muna bukatar gaba gaɗin yin wa’azi. Wani ɗan shekara 20 mai suna Roberto, ya ce: “Ina jin tsoron yi wa abokan ajinmu wa’azi. Ban san abin da ya sa ba, amma yanzu ina farin cikin yi wa tsarana wa’azi.”

11 Matasa da yawa sun lura cewa yana musu sauƙi su yi wa’azi idan sun yi shiri sosai. Wane irin shiri ne ya kamata ka yi? Wata ’yar shekara 16 mai suna Julia, ta ce: “Ina saka littattafai a jakar makaranta, kuma ina sauraran ’yan ajinmu yayin da suke bayyana abin da suka yi imani da shi. Yin hakan yana taimaka mini in san abin da zai taimaka musu. Idan na yi shiri sosai, nakan gaya musu abin da zai amfane su.” Wata ’yar shekara 23 mai suna Maria, ta ce: “Idan kana nuna alheri kuma kana sauraran abin da mutane ke faɗa, hakan zai sa ka fahimci abin da suke fama da shi. Ina karanta dukan talifofin da aka wallafa game da matasa. Hakan yana taimaka mini ina sami abin da zan nuna musu a Littafi Mai Tsarki ko kuma a dandalin jw.org da zai iya taimaka musu.” Kamar yadda kalaman nan suka nuna, yin shiri yana kamar saka “takalmin” da ya dace da ƙafarka sosai.

Ƙafafun da ke a shirye (Ka duba sakin layi na 9-11)

“BANGASKIYA TA ZAMA GARKUWARKU”

12, 13. Waɗanne ‘kibiyoyi na wuta’ ne Shaiɗan yake amfani da su?

12 Karanta Afisawa 6:16. Sojojin Roma suna riƙe ‘garkuwar’ da take rufe su daga kafaɗa har zuwa gwiwa. Dalilin shi ne don ta kāre su daga takobi da kibiya da kuma mashi.

13 Wasu cikin ‘kibiyoyi na wuta’ da Shaiɗan yake amfani da su don ya yaudari mutane su ne ƙarya game da Jehobah. Shaiɗan yana cewa Jehobah bai damu da mu  ba kuma ba ya ƙaunar mu. Wata ’yar shekara 19 mai suna Aida, ta ce: “A dā, nakan ji kamar ba zan iya kusantar Jehobah ba kuma ba ya son in zama abokiyarsa.” Me take yi idan ta soma jin hakan? Ta ce: “Taron ikilisiya yana taimaka mini in ƙarfafa bangaskiyata sosai. Nakan halarci taro ba tare da yin kalami ba, a gani na babu wanda yake son jin abin da zan ce. Amma yanzu, ina shiri sosai kafin in halarci taro, kuma ina yin kalami sau biyu ko uku. Yin hakan bai da sauƙi, amma ina farin ciki sosai idan na yi hakan. Ban da haka ma, ’yan’uwa suna ƙarfafa ni sosai. Bayan na halarci taro, nakan ga cewa Jehobah yana ƙauna ta sosai.”

14. Wane darasi ne muka koya daga labarin Aida?

14 Mun koyi darasi mai kyau daga labarin Aida. Garkuwar sojoji ba ta canjawa, amma bangaskiyarmu takan ƙaru ko kuma ta ragu. Mu ne za mu iya sa bangaskiyarmu ta ƙaru ko kuma ta ragu. (Mat. 14:31; 2 Tas. 1:3) Saboda haka, yana da muhimmanci mu riƙa ƙarfafa bangaskiyarmu!

Garkuwar bangaskiya (Ka duba sakin layi na 12-14)

“HULAR KWANO, WATO CETO”

15, 16. Ta yaya bege yake kamar hular kwano?

15 Karanta Afisawa 6:17. Ana ƙera hular kwanon da sojan Roma yake sakawa don ta riƙa kāre kansa da wuyansa da kuma fuskarsa. Wasu hular kwano suna da wurin da soja zai iya riƙe hular a hannu.

16 Kamar yadda hular kwano take kāre ƙwaƙwalwar soja, haka ma begenmu na “samun ceto” yake kāre tunaninmu. (1 Tas. 5:8; K. Mag. 3:21) Bege yana taimaka  mana mu mai da hankali ga alkawuran Jehobah kuma yana sa kada mu yi sanyin gwiwa sa’ad da muke fuskantar matsaloli. (Zab. 27:​1, 14; A. M. 24:15) Amma idan muna so “hular kwano,” wato begenmu ya taimaka mana sosai, wajibi ne mu saka ta a kanmu, kada mu riƙe ta a hannu.

17, 18. (a) Ta yaya Shaiɗan yake raunana begenmu? (b) Ta yaya za mu tabbatar da cewa Shaiɗan bai yaudare mu ba?

17 Ta yaya Shaiɗan yake raunana begenmu? Ka yi la’akari da abin da ya yi wa Yesu. Shaiɗan ya san cewa Yesu ne zai zama sarkin Mulkin Allah. Amma dole ne Yesu ya jira har sai lokacin da Jehobah ya ƙayyade. Kafin wannan lokacin, Yesu zai sha wahala kuma ya mutu. Don haka, Shaiɗan ya ba Yesu damar yin sarauta a lokacin. Shaiɗan ya gaya wa Yesu cewa idan Yesu ya yi masa sujada, zai ba shi dukan mulkokin duniya nan da nan. (Luk. 4:​5-7) Hakazalika, Shaiɗan ya san cewa Jehobah ya yi mana alkawarin yin rayuwa a aljanna. Amma muna bukatar mu jira, kuma wataƙila za mu fuskanci matsaloli da yawa yayin da muke jira. Shi ya sa Shaiɗan yake ba mu damar jin daɗin rayuwa yanzu. Yana son mu sa biɗan abin duniya a kan gaba a rayuwarmu, maimakon Mulkin Allah.​—Mat. 6:​31-33.

18 Matasa da yawa suna tsayayya da Shaiɗan. Alal misali, wata ’yar shekara 20 mai suna Karina, ta ce: “Na san cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai iya magance matsalolin da muke fuskanta.” Ta yaya begen da take da shi ya taimaka mata? Ta ce: “Begen yin rayuwa a aljanna ya taimaka mini in san cewa kayan duniyar Shaiɗan ba zai dawwama ba.” Ta daɗa cewa: “Ba na ƙoƙari in mai da hankali ga neman arziki a wannan duniyar. Maimakon hakan, ina yin amfani da lokacina da kuma kuzarina don in bauta wa Jehobah.”

Hular kwano ta samun ceto (Ka duba sakin layi na 15-18)

“TAKOBIN RUHU, WATO KALMAR ALLAH”

19, 20. Ta yaya za mu ƙware sosai a yin amfani da Kalmar Allah?

19 A lokacin da Bulus ya rubuta wasiƙarsa, takobin da sojojin Roma suke amfani da shi ya kai wajen tsawon inci 20. Kuma sojojin Roma sun ƙware a yin yaƙi da takobi don suna koyan yin amfani da shi a kowace rana.

20 Bulus ya ce Kalmar Allah tana kamar takobi kuma Jehobah ne ya ba mu ita. Amma muna bukatar mu koyi yin amfani da ita sosai sa’ad da muke kāre abin da muka yi imani da shi, ko kuma sa’ad da muke son mu daidaita tunaninmu. (2 Kor. 10:​4, 5; 2 Tim. 2:15) Ta yaya za ka ƙware a yin amfani da ita? Wani ɗan shekara 21 mai suna Sebastian, ya ce: “Ina rubuta aya guda daga kowace sura da na karanta a cikin Littafi Mai Tsarki. A yanzu haka, ina rubuta ayoyin da na fi so. Hakan yana taimaka mini in san ra’ayin Jehobah.” Daniel da aka ambata ɗazu ya ce: “Sa’ad da nake karanta Littafi Mai Tsarki, ina mai da hankali ga ayoyin da nake gani za su taimaka wa mutane sa’ad da nake wa’azi. Na lura cewa mutane suna saurarawa idan sun ga cewa kana son Littafi Mai Tsarki sosai, kuma kana yin iya ƙoƙarinka don ka taimaka musu.”

Takobin ruhu (Ka duba sakin layi na 19-20)

21. Me ya sa ba ma bukatar mu ji tsoron Shaiɗan da kuma aljanunsa?

21 Kamar yadda muka koya daga misalan matasan da aka ambata a wannan talifin, ba ma bukatar mu riƙa jin tsoron Shaiɗan da aljanunsa. Gaskiya ne cewa suna da ƙarfi amma ba su fi Jehobah ƙarfi ba. Kuma ba za su rayu har abada ba. Nan ba da daɗewa ba sa’ad da Yesu ya soma sarauta, za a jefa su cikin rami marar matuƙa inda ba za su iya yin kome ba. Bayan haka, za a halaka su. (R. Yar. 20:​1-3, 7-10) Mun san maƙiyinmu da dabarunsa da kuma abin da yake son ya cim ma. Amma da taimakon Jehobah, za mu yi tsayayya da shi!