“Ku haifar da halin rayuwa mai kyau wadda za ta nuna cewa ku almajiraina ne, kamar itacen da ya haifi ’ya’ya masu kyau, gama wannan ne yake ɗaukaka Ubana.”​—YOH. 15:8.

WAƘOƘI: 53, 60

1, 2. (a) Kafin Yesu ya mutu, wane batu ne ya tattauna da mabiyansa? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa tuna dalilan da suka sa muke wa’azi? (c) Mene ne za mu tattauna?

A DARE na ƙarshe kafin Yesu ya mutu, ya tattauna da mabiyansa sosai, kuma ya tabbatar musu da cewa yana ƙaunar su. Ban da haka ma, ya ba da kwatancin itacen inabi da muka tattauna a talifin da ya gabata. Yesu ya yi amfani da kwatancin wajen ƙarfafa mabiyansa su ci gaba da ba “ ’ya’ya masu kyau.”​—Yoh. 15:8.

2 Amma, Yesu bai gaya wa mabiyansa abin da suke bukatar su yi kaɗai ba. Ya gaya musu dalilan da suka sa suke bukatar su yi wa’azi. Me ya sa yake da muhimmanci mu tattauna dalilan? Yin hakan zai taimaka mana mu fahimci cewa idan muna tunawa da dalilin da ya sa muke wa’azi, hakan zai ba mu ƙarfin gwiwa. Ƙari ga haka, zai motsa mu mu ci gaba da jimrewa yayin da muke yi wa “dukan al’umma” wa’azi. (Mat. 24:​13, 14) Yanzu, bari mu tattauna dalilai huɗu da suka sa muke wa’azi. Ban da haka ma, za mu tattauna halaye huɗu da za su taimaka mana mu jimre sa’ad da muke ba da amfani.

 MUNA ƊAUKAKA JEHOBAH

3. (a) Wane dalili na yin wa’azi ne aka ambata a littafin Yohanna 15:8? (b) Mene ne ’ya’yan inabi a kwatancin Yesu suke wakilta, kuma me ya sa kwatancin ya dace?

3 Dalili mafi muhimmanci da ya sa muke wa’azi shi ne don mu ɗaukaka Jehobah kuma mu tsarkake sunansa a gaban mutane. (Karanta Yohanna 15:​1, 8.) A kwatancin itacen inabi, Yesu ya ce Jehobah ne manomin da ya shuka itacen. Ban da haka ma, Yesu ya ce shi ne itacen inabin, mabiyansa kuma rassan itacen. (Yoh. 15:5) ’Ya’yan inabin kuma suna wakiltar amfanin da mabiyan Yesu suke bayarwa ko kuma wa’azi da suke yi. Yesu ya gaya wa manzanninsa cewa za su ɗaukaka Ubansa idan suka ci gaba da ba da ’ya’ya. Kamar yadda itacen inabin da ya yi ’ya’ya masu kyau yake sa manomin farin ciki, haka mu ma muke ɗaukaka Jehobah ko kuma tsarkake sunansa idan muna iya ƙoƙarinmu a yin wa’azi game da Mulkinsa.​—Mat. 25:​20-23.

4. (a) A waɗanne hanyoyi ne muke tsarkake sunan Allah? (b) Yaya kake ji don gatan da kake da shi na tsarkake sunan Allah?

4 Sunan Allah yana da tsarki sosai. Ba za mu iya tsarkake shi fiye da yadda yake ba. Don haka, ta yaya wa’azinmu yake tsarkake sunan Allah? Ka yi la’akari da abin da annabi Ishaya ya ce: “Yahweh Mai Runduna, . . . Mai Tsarki ne.” (Isha. 8:13) Muna tsarkake sunan Allah idan muka ɗauki sunan da muhimmanci fiye da kowane suna kuma muka taimaka wa mutane su san cewa sunan na da tsarki. (Mat. 6:9) Alal misali, idan muka yi wa’azi game da halayen Jehobah da kuma nufinsa ga ’yan Adam, muna wanke sunansa daga zargi da kuma ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan. (Far. 3:​1-5) Ban da haka, muna tsarkake sunan Allah idan muka ƙoƙarta wajen taimaka wa mutane a yankinmu su san cewa Jehobah ne kaɗai ya cancanci ya “karɓi ɗaukaka, da girma, da iko.” (R. Yar. 4:11) Wata mai suna Rune da ta yi shekara 16 tana hidimar majagaba, ta ce: “Ina godiya don gatan da nake da shi na yin wa’azi game da Mahaliccin sama da ƙasa. Hakan yana ƙarfafa ni in ci gaba da wa’azi.”

MUNA ƘAUNAR JEHOBAH DA KUMA ƊANSA

5. (a) Wane dalilin yin wa’azi ne aka ambata a littafin Yohanna 15:​9, 10? (b) Ta yaya Yesu ya nuna wa mabiyansa cewa suna bukatar jimrewa?

5 Karanta Yohanna 15:​9, 10. Ƙaunarmu ga Jehobah da kuma Yesu ne ya sa muke yin wa’azi game da Mulkin Allah. (Mar. 12:30; Yoh. 14:15) Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa su ‘zauna cikin ƙaunarsa.’ Me ya sa Yesu ya faɗi hakan? Domin ya san cewa mabiyansa za su bukaci su riƙa jimrewa a bautarsu ga Jehobah. Don haka, Yesu ya yi amfani da kalmar nan “zauna” a littafin Yohanna 15:​4-10 don ya taimaka wa mabiyansa su fahimci cewa za su bukaci su riƙa jimrewa a bautarsu ga Jehobah.

6. Ta yaya muke nuna cewa muna son mu zauna cikin ƙaunar Kristi?

6 Ta yaya za mu nuna cewa muna son mu zauna cikin ƙaunar Kristi kuma muna so ya amince da mu? Za mu yi hakan ta wajen yin biyayya ga Yesu. Yesu ya ce mu yi abin da shi ma da kansa ya yi. Ya ce: “Kamar yadda ni na bi umarnin Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunar da yake mini.” (Yoh. 15:16) Ta yin hakan, Yesu ya kafa mana misali mai kyau.​—Yoh. 13:15.

7. Wane alaƙa ne ke tsakanin biyayya da ƙauna?

7 Don Yesu ya taimaka wa almajiransa su san cewa akwai alaƙa tsakanin biyayya da kuma ƙauna, ya ce: “Duk wanda ya san umarnaina, yana binsu kuma, shi ne yake  ƙaunata.” (Yoh. 14:21) Umurnin da Yesu ya bayar na Ubansa ne. Don haka, idan muka yi wa Yesu biyayya kuma muka yi wa’azi, muna nuna cewa muna ƙaunar Jehobah. (Mat. 17:5; Yoh. 8:28) Idan muka nuna wa Jehobah da Yesu cewa muna ƙaunar su, su ma za su riƙa ƙaunar mu.

MUNA YI WA MUTANE GARGAƊI

8, 9. (a) Wane dalili ne kuma muke da shi na yin wa’azi? (b) Me ya sa abin da Jehobah ya ce a littafin Ezekiyel 3:​18, 19 da kuma 18:23 suke motsa mu mu yi wa’azi?

8 Muna da wasu dalilai na ci gaba da yin wa’azi. Muna yin wa’azi don mu yi wa mutane gargaɗi. A Littafi Mai Tsarki, an kira Nuhu ‘mai wa’azi.’ (Karanta 2 Bitrus 2:5.) Kafin a yi ambaliyar ruwa a zamanin Nuhu, babu shakka, Nuhu ya yi wa mutane wa’azi cewa za a halaka mugaye. Me ya sa muka ce haka? Ka yi la’akari da abin da Yesu ya ce: ‘Kamar a lokacin nan kafin babbar ambaliyar ruwan, ana ci, ana sha, maza suna aure, ana ba da mata ga aure, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgin. Kafin su san abin da ake ciki, babbar ambaliyar ta zo ta kwashe su duka. Haka kuwa dawowar Ɗan Mutum za ta kasance.’ (Mat. 24:​38, 39) Nuhu ya ci gaba da yin aikin da Jehobah ya ba shi na yi wa mutane gargaɗi, duk da cewa mutanen ba su saurare shi ba.

9 A yau, muna yin wa’azi game da Mulkin Allah don mu taimaka wa mutane su sami damar koya game da nufin Allah ga ’yan Adam. Kamar Jehobah, mu ma muna son mutane su saurari saƙon don su “rayu” har abada. (Ezek. 18:23) Idan muka yi wa’azi gida-gida da kuma a inda akwai jama’a, muna yi wa mutane da yawa gargaɗi cewa nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai halaka mugaye.​—Ezek. 3:​18, 19; Dan. 2:44; R. Yar. 14:​6, 7.

MUNA ƘAUNAR MAƘWABTANMU

10. (a) Wane dalilin yin wa’azi ne aka ambata a littafin Matta 22:39? (b) Ka faɗi yadda Bulus da Sila suka taimaka wa wani mai gadin kurkuku a Filibi.

10 Ga wani dalili mai muhimmanci kuma da ya sa muke wa’azi: Muna yin wa’azi domin muna ƙaunar maƙwabtanmu. (Mat. 22:39) Ƙaunar nan ce take sa mu ci gaba da yin wa’azi don mun san cewa mutane suna iya canja ra’ayinsu game da wa’azinmu idan yanayinsu ya canja. Ka yi la’akari da abin da manzo Bulus da kuma abokin wa’azinsa Sila suka fuskanta. ’Yan adawa sun saka su cikin kurkuku a birnin Filibi. Amma da tsakar dare, sai aka yi girgizar ƙasa da ta sa ƙofofin kurkukun suka buɗe. Mai gadin ya kusan kashe kansa domin yana tsoro cewa fursunonin sun gudu. Amma Bulus ya kira shi da babbar murya, ya ce: “Kada ka yi wa kanka ciwo!” Sai mai gadin ya yi tambaya ya ce: “Me zan yi in sami ceto?” Su kuma suka ce masa: “Ka gaskata da Ubangiji Yesu” za ka sami ceto.​—A. M. 16:​25-34.

Ƙaunarmu ga Jehobah da Yesu da kuma maƙwabtanmu ne ke sa mu yin wa’azi (Ka duba sakin layi na 5, 10)

11, 12. (a) Mene ne labarin mai gadin kurkuku ya koya mana game da wa’azinmu? (b) Me ya sa muke son mu ci gaba da yin wa’azi?

11 Mene ne labarin mai gadin kurkukun ya koya mana game da yin wa’azi? Ka lura cewa mai gadin ya canja ra’ayinsa ne bayan da girgizar ƙasa ta auku. Hakazalika,  wasu mutanen da ba sa sauraran wa’azinmu suna iya canja ra’ayinsu kuma su nemi taimako idan yanayinsu ya canja. Alal misali, wasu a yankinmu suna iya rasa aikin da suka daɗe suna yi kuma hakan yana iya sa su baƙin ciki. Wasu kuma suna iya baƙin ciki idan aurensu ya mutu. Ƙari ga haka, wasu suna iya yin baƙin ciki sosai idan suka ji cewa suna da wani ciwo mai tsanani ko kuma idan wani nasu ya rasu. Idan irin waɗannan abubuwan suka faru, mutanen suna iya yin tambayoyin da a dā ba sa yi. Wataƙila ma suna iya yin wannan tambayar, ‘Mene ne zan yi don in sami ceto?’ Kuma idan muka haɗu da su, suna iya so su saurari wa’azinmu a ƙaro na farko a rayuwarsu.

12 Don haka, idan muka ci gaba da yin wa’azi da aminci, za mu ta’azantar da mutane a lokacin da suke bukatar hakan. (Isha. 61:1) Wata mai suna Charlotte da ta yi shekara 38 tana hidimar majagaba ta ce: “A yau, mutane da yawa suna cikin duhu kuma suna bukatar su ji wa’azi game da Mulkin Allah.” Wata kuma mai suna Eva da ta yi shekara 34 tana hidimar majagaba, ta ce: “A yau mutane da yawa ba sa jin daɗin rayuwa, kuma ina so in taimaka musu sosai. Abin da ya sa nake wa’azi ke nan.” Babu shakka, ƙauna ga maƙwabtanmu ma ya sa muna wa’azi!

HALAYEN DA KE TAIMAKA MANA MU JIMRE

13, 14. (a) Wane hali ne aka ambata a Yohanna 15:11? (b) Ta yaya za mu yi murna kamar Yesu? (c) Ta yaya yin murna yake taimaka mana a wa’azinmu?

13 A daren Yesu na ƙarshe kafin a kashe shi, ya gaya wa mabiyansa halaye da yawa da za su taimaka musu su jimre sa’ad da suke ba da amfani. Waɗanne halaye ke nan, kuma yaya za mu amfana daga halayen?

14 Yin murna. Shin yin wa’azi yana da wuya ne? A’a. Bayan Yesu ya ba da kwatancin itacen inabi, ya ce masu wa’azin Mulki za su yi murna. (Karanta Yohanna 15:11.) Hakika, ya tabbatar mana da cewa za mu riƙa murna kamar shi. Ta yaya? Kamar yadda aka ambata ɗazu, Yesu ya ce shi ne itacen inabi kuma almajiransa ne rassan. Itacen na tallafa wa rassan. Muddin ba a yanke rassan daga itacen ba, za su ci gaba da samun ruwa da wasu sinadarai daga itacen. Hakazalika, muddin mun kasance tare da Kristi ta wurin bin sawunsa, za mu yi farin ciki kamar yadda yake yi don yana yin nufin Ubansa. (Yoh. 4:34; 17:13; 1 Bit. 2:21) Wata mai suna Ana da ta yi fiye da shekara 40 tana hidimar majagaba, ta ce: “Murnar da nake yi bayan na yi wa’azi tana ƙarfafa ni in ci gaba a hidimata ga Jehobah.” Hakika, yin farin ciki yana ƙarfafa mu mu ci gaba da yin wa’azi a yankunan da yawancin mutane ba sa saurarar mu.​—Mat. 5:​10-12.

15. (a) Wane hali ne littafin Yohanna 14:27 ya ambata? (b) Me ya sa salama take taimaka mana mu ci gaba da yin wa’azi?

15 Kasancewa da salama. (Karanta Yohanna 14:27.) A daren Yesu na ƙarshe kafin a kashe shi, ya gaya wa manzanninsa cewa: “Salamata nake ba ku.” Ta yaya salamar Yesu take taimaka mana mu ba da amfani? Idan muna wa’azi, mun san cewa muna faranta ran Jehobah. Sanin cewa muna faranta ran Jehobah yana sa mu kasance da salama. Kasancewa da salama yana sa mu ci gaba da yin wa’azi. (Zab. 149:4; Rom. 5:​3, 4; Kol. 3:15) Wani mai suna Alfredo da ya yi shekara 45 a hidima ta cikakken lokaci ya ce: “Yin wa’azi yana sa in gaji, amma yana sa in sami gamsuwa kuma rayuwata ta kasance da ma’ana.” Hakika, muna godiya sosai don kwanciyar rai da muke da shi!

16. (a) Wane hali ne aka ambata a littafin Yohanna 15:15? (b) Me zai taimaki manzannin Yesu su ci gaba da zama abokansa?

 16 Zama abokan Yesu. Bayan Yesu ya gaya wa almajiransa cewa yana son su riƙa farin ciki, ya bayyana musu dalilin da ya sa suke bukatar su nuna ƙaunar da ba ta son kai. (Yoh. 15:​11-13) Bayan haka, sai ya ce: “Ina ce da ku abokai.” Hakika, zama abokan Yesu babban gata ne sosai! Mene ne manzannin suke bukatar su yi don su ci gaba da zama abokan Yesu? Suna bukatar su ci gaba da ba da “ ’ya’ya.” (Karanta Yohanna 15:​14-16.) Shekaru biyu kafin wannan lokacin, Yesu ya umurci manzanninsa cewa: “Yayin da kuke tafiya, ku yi ta yi musu wa’azi cewa, ‘Mulkin sama ya yi kusa.’ ” (Mat. 10:7) Don haka, a dare na ƙarshe kafin Yesu ya mutu, ya ƙarfafa su cewa su ci gaba da jimrewa yayin da suke aikin da ya ba su. (Mat. 24:13; Mar. 3:14) Babu shakka, Yesu ya san cewa aikin ba zai yi musu sauƙi ba, amma za su yi nasara kuma su ci gaba da zama abokansa. Me zai taimaka musu? Wata kyauta ce da ya ba su.

17, 18. (a) Wace kyauta ce aka ambata a littafin Yohanna 15:16? (b) Ta yaya wannan kyautar za ta taimaka wa mabiyan Yesu? (c) Waɗanne kyaututtuka ne suke ƙarfafa mu a yau?

17 Amsa addu’o’inmu. Yesu ya ce: “Uba zai ba ku dukan abin da kuka roƙa a cikin sunana.” (Yoh. 15:16) Hakika, wannan alkawarin ya ƙarfafa manzannin Yesu sosai! * Manzannin Yesu ba su fahimci yadda wannan alkawarin zai cika ba da yake Yesu ya kusan mutuwa. Amma Jehobah zai ci gaba da taimaka musu ta wajen amsa addu’o’insu. Ƙari ga haka, zai taimaka musu su ci gaba da yin wa’azi game da Mulkinsa. Bayan Yesu ya mutu, manzannin sun roƙi Jehobah ya ba su ƙarfin zuciya kuma Jehobah ya amsa addu’o’insu.​—A. M. 4:​29, 31.

Muna da tabbaci cewa Jehobah yana amsa addu’o’inmu kuma yana taimaka mana (Ka duba sakin layi na 18)

18 Haka ma a yau, idan muka ci gaba da jimrewa a yin wa’azi, za mu zama abokan Yesu. Ban da haka ma, za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai amsa addu’o’inmu. Zai kuma taimaka mana mu magance duk matsalolin da muke fuskanta yayin da muke wa’azi game da Mulkinsa. (Filib. 4:13) Muna godiya sosai cewa Jehobah yana amsa addu’armu kuma muna abokantaka da Yesu! Waɗannan kyaututtukan suna ƙarfafa mu mu ci gaba da ba da amfani.​—Yaƙ. 1:17.

19. (a) Me ya sa muke ci gaba da yin wa’azi? (b) Mene ne ke taimaka mana mu yi aikin da Allah ya ba mu?

19 Kamar yadda muka tattauna a wannan talifin, muna yin wa’azi don mu ɗaukaka Jehobah, mu tsarkake sunansa kuma mu nuna cewa muna ƙaunar shi da kuma Yesu. Ƙari ga haka, muna yi wa mutane gargaɗi da kuma nuna wa maƙwabtanmu ƙauna. Ban da haka, yin murna da kasancewa da salama da zama abokan Yesu da kuma addu’o’inmu da Jehobah yake amsawa suna ƙarfafa mu mu ci gaba da yin aikin da Jehobah ya ba mu. Jehobah yana farin ciki sosai idan muka ci gaba “da ba da amfani” da dukan zuciyarmu!

^ sakin layi na 17 Yayin da Yesu yake tattauna da manzanninsa, ya tabbatar musu sau da yawa cewa Jehobah zai amsa addu’arsu.​—Yoh. 14:13; 15:​7, 16; 16:23.