“Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda yake koya maka zuwa amfaninka, wanda yana bishe ka ta hanyar da za ka bi.”—ISHA. 48:17.

WAƘOƘI: 117, 114

1, 2. (a) Yaya Shaidun Jehobah suke ɗaukan Littafi Mai Tsarki? (b) Wane sashe ne ka fi so a cikin Littafi Mai Tsarki?

SHAIDUN JEHOBAH suna son karanta Littafi Mai Tsarki sosai don yana ɗauke da shawarwari masu amfani. Ƙari ga haka, yana ƙarfafa mu kuma yana sa mu kasance da bege. (Rom. 15:4) Ba mu ɗauki Littafi Mai Tsarki a matsayin labarin da ’yan Adam suka rubuta ba, amma ainihi yadda yake, wato “maganar Allah.”—1 Tas. 2:13.

2 Babu shakka, dukan mu muna da nassin da muka fi so a cikin Littafi Mai Tsarki. Wasu suna jin daɗin karanta littattafan Matta da Markus da Luka da kuma Yohanna saboda sun bayyana halayen Jehobah ta wurin Ɗansa. (Yoh. 14:9) Wasu kuma suna son karanta sashen Littafi Mai Tsarki da ke ɗauke da annabci kamar Ru’ya ta Yohanna wanda ya yi magana game da “al’amura da za su faru ba da daɗewa ba.” (R. Yoh. 1:1) Amma babu wani a cikin mu da zai ce ba ya jin daɗin karanta Zabura ko kuma shawarwarin da ke littafin Misalai. Hakika, Littafi Mai Tsarki yana da amfani ga dukan mutane.

3, 4. (a) Yaya muke ji game da littattafanmu? (b) Waɗanne littattafai ne ake wallafawa don rukunin mutane na musamman?

3 Muna son Littafi Mai Tsarki da kuma Littattafanmu da suke  bayyana Littafi Mai Tsarki. Alal misali, muna ji daɗin karanta littattafai da ƙasidu da mujallu da kuma wasu littattafan da muke samu daga ƙungiyar Jehobah. Mun san cewa Jehobah ne yake tanadar mana da waɗannan littattafan don mu kasance a faɗake, mu kusace shi kuma mu kasance “sahihai cikin bangaskiya.”—Tit. 2:2.

4 Ban da littattafan da aka wallafa don Shaidun Jehobah, ƙungiyar Jehobah tana wallafa wasu littattafai don matasa da kuma iyaye. Yawancin littattafan da aka buga ko kuma aka saka a dandalinmu, an wallafa su ne don jama’a. Waɗannan tanadodin suna tuna mana cewa Jehobah ya cika alkawarin da ya yi cewa “za ya yi wa dukan al’ummai biki na abinci mai-mai.”—Isha. 25:6.

5. Wane tabbaci muke da shi cewa Jehobah yana farin ciki da mu?

5 Hakika, yawancin mu za su so su sami ƙarin lokaci don karanta Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan da ƙungiyar Jehobah take wallafawa. Muna da tabbaci cewa Jehobah yana farin ciki saboda ƙoƙarin da muke yi don mu nemi ‘zarafin’ karanta da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai. (Afis. 5:15, 16) Ko da yake ba za mu iya mai da hankali ga dukan tanadodin da ake yi mana ba. Amma idan ba mu yi hankali ba, za mu iya faɗa cikin wani haɗari. Mene ne wannan haɗarin?

6. Mene ne zai iya hana mu moran wasu abubuwan da ƙungiyar Jehobah take tanadarwa?

6 Da akwai matsala idan muka soma tunani cewa wani littafi da aka wallafa ba zai amfane ne mu ba. Alal misali, idan ka karanta wani sashe a cikin Littafi Mai Tsarki kuma ka ɗauka cewa ba zai amfane ka ba fa? Ko kuma idan abin da aka wallafa a cikin wani littafi bai shafe mu ba fa? Shin kana karanta littafin da sauri ne ko kuma ba ka karantawa gaba ɗaya? Idan muna yin hakan, ba za mu amfana daga darasin da ke ciki ba. Ta yaya za mu guji yin hakan? Ya kamata mu tuna cewa Allah shi ne yake tanadar mana da dukan abubuwan nan. Ta wurin annabi Ishaya, Allah ya ce: “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda yake koya maka zuwa amfaninka.” (Isha. 48:17) Za mu tattauna wasu shawarwari uku da za su taimaka mana mu ji daɗin karanta Littafi Mai Tsarki da kuma wasu abubuwan da ake tanadar mana.

YADDA ZA KA AMFANA DAGA KARATUN LITTAFI MAI TSARKI

7. Me ya sa muke bukatar mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki da niyyar koyan darasi?

7 Ka karanta da niyyar koyan wani darasi. Littafi Mai Tsarki ya ce ‘Kowane nassi hurarre daga wurin Allah, mai-amfani.’ (2 Tim. 3:16) An rubuta wasu sassa na Littafi Mai Tsarki musamman don wani mutum ko kuma wani rukuni. Shi ya sa ya kamata mu karanta nassosi da niyyar koyan darasi. Wani ɗan’uwa ya ce: “Sa’ad da na karanta Littafi Mai Tsarki, ina ƙoƙarin in tuna cewa da akwai darussa da yawa da zan iya koya daga ciki. Hakan ya taimaka mini in koyi darussa da yawa.” Kafin mu karanta Littafi Mai Tsarki, ya kamata mu yi addu’a ga Jehobah don ya ba mu hikima da kuma basira don mu koyi darussan da yake so mu koya.—Ezra 7:10; karanta Yaƙub 1:5.

Karatun Littafi Mai Tsarki da kake yi yana amfanar ka sosai kuwa? (Ka duba sakin layi na 7)

8, 9. (a) Waɗanne tambayoyi ne za mu yi wa kanmu sa’ad da muke karanta Littafi Mai Tsarki? (b) Mene ne umurnin da aka bayar don dattawa suke koya mana game da Jehobah?

8 Ka yi tambayoyi. Yayin da kake karanta Littafi Mai Tsarki, ka ɗan dakata kuma ka yi wa kanka waɗannan tambayoyin: ‘Mene ne wannan wajen yake koya min game da Jehobah? Ta yaya zan iya yin amfani da wannan darasin a rayuwata? Ta yaya zan iya yin amfani da wannan umurnin don in taimaka wa wasu?’ Idan muka yi bimbini a kan waɗannan tambayoyin, za  mu ji daɗin karatun Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ka yi la’akari da umurnin da aka bayar game da halin da ya kamata dattawa su kasance da shi. (Karanta 1 Timotawus 3:2-7.) Tun da yawancin mu ba dattawa ba ne, muna iya tunani cewa wannan sashen ba zai amfane mu ba. Amma idan muka yi la’akari da waɗannan tambayoyi na gaba, za mu ga cewa za mu iya amfana a hanyoyi da yawa daga umurnin.

9 Mene ne wannan wajen yake koya min game da Jehobah? Ta wajen ba da wannan umurnin, Jehobah ya nuna cewa wajibi ne waɗanda aka ba wa hakkin kula da ikilisiya su bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, suna bukata su kafa misali mai kyau don za su ba da lissafi a kan yadda suka bi da ’yan’uwa a cikin ikilisiya waɗanda Jehobah “ya sayi da jinin” Ɗansa. (A. M. 20:28) Jehobah yana son dattawa su kula da mu sosai. (Isha. 32:1, 2) Waɗannan ƙa’idodin suna tuna mana cewa Jehobah yana ƙaunar mu sosai.

10, 11. (a) Sa’ad da muke karanta ƙa’idodi game da dattawa, ta yaya za mu iya yin amfani da su a rayuwarmu? (b) Ta yaya za mu iya yin amfani da wannan umurnin don mu taimaka wa wasu?

10 Ta yaya zan iya yin amfani da wannan darasin a rayuwata? A wasu lokatai, wanda aka naɗa a ikilisiya yana bukata ya yi amfani da waɗannan ƙa’idodin wajen bincika kansa don ya ga inda zai iya yin gyara. Ɗan’uwan da yake da “burin aikin kula da ikilisiya” yana bukata ya mai da hankali ga waɗannan ƙa’idodin kuma ya yi iya ƙoƙarinsa don ya bi ƙa’idodin. (1 Tim. 3:1, Littafi Mai Tsarki) Ban da haka, kowane Kirista zai iya koyan darasi daga waɗannan ƙa’idodin da aka lissafa a cikin ayoyin domin sun ƙunshi abubuwan da Jehobah yake bukata daga dukan Kiristoci. Alal misali, dukan mu muna bukata mu kasance da sanin yakamata da kuma natsuwa. (Filib. 4:5; 1 Bit. 4:7) Yayin da dattawa suke kafa “gurbi . . . ga garken,” za mu iya bin misalinsu kuma mu “yi koyi da bangaskiyarsu.”—1 Bit. 5:3; Ibran. 13:7.

11 Ta yaya zan iya yin amfani da wannan umurnin don in taimaka wa wasu? Za mu iya yin amfani da waɗannan ƙa’idodin don mu taimaka wa waɗanda suke son saƙonmu da kuma waɗanda muke yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su don su san cewa dattawanmu sun bambanta da limaman Kiristendom. Ƙari ga haka, sa’ad da muke karanta waɗannan ƙa’idodin, za mu iya tunawa da ƙoƙarin da dattawa suke yi a madadinmu.  Yin bimbini a kan hakan zai sa mu ƙara “girmama masu fama da aiki” a cikin mu. (1 Tas. 5:12, LMT) Dattawa za su yi farin ciki sosai idan muka nuna cewa muna daraja su don aikin da suke yi.—Ibran. 13:17.

12, 13. (a) Wane bincike ne za mu iya yi da littattafan bincike da muke da su? (b) Ka ba da misalin da ya nuna cewa za mu iya koyan darussa da dama idan muka binciko wasu bayanai game da wani sashe na Littafi Mai Tsarki.

12 Ka yi bincike. Ta wajen yin amfani da littattafan bincike, za mu iya samun bayanai game da waɗannan tambayoyin:

  • Wane ne ya rubuta wannan sashe na Littafi Mai Tsarki?

  • A ina ne kuma yaushe aka rubuta shi?

  • Waɗanne muhimman abubuwa ne suka faru a lokacin da aka rubuta wannan sashe na Littafi Mai Tsarki?

Irin waɗannan bayanan za su taimaka mana mu koyi darussa da yawa.

13 Alal misali, ka yi la’akari da abin da aka rubuta a Ezekiyel 14:13, 14 cewa: “Sa’anda wata ƙasa ta yi mani zunubi ta wurin laifin da take yi mani, na kuwa miƙa hannuna a kanta, na karya mata abinci, abin tokare rai, na aike mata da yunwa, na datse mata mutum da dabba; ko da a ce waɗannan mutum uku, Nuhu, Daniel, da Ayuba suna ciki, rayukansu kaɗai za su ceta ta wurin adalcinsu, in ji Ubangiji Yahweh.” Idan muka yi bincike, za mu gano cewa an rubuta wannan sashe na Littafi Mai Tsarki a shekara ta 612 kafin haihuwar Yesu. A lokacin, Nuhu da Ayuba sun riga sun mutu da daɗewa, amma Allah bai manta da amincinsu ba. Daniyel yana raye a lokacin kuma wataƙila shekarunsa tsakanin 17 zuwa 23 ne. Amma Jehobah ya ce shi mai adalci ne kamar Nuhu da Ayuba. Shin wane darasi ne za mu iya koya daga waɗannan ayoyin? Jehobah yana lura da dukan masu bauta masa da aminci kuma suna da daraja a gabansa, hakan ya haɗa da matasa.—Zab. 148:12-14.

KA YI AMFANI DA LITTATTAFAI DABAM-DABAM

14. Ta yaya littattafai da ake wallafawa don matasa suke taimaka musu, kuma ta yaya za su amfani wasu mutane? (Ka duba hoton da ke shafi na 23.)

14 Mun koyi cewa za mu iya koyan darussa daga dukan sassan Littafi Mai Tsarki. Hakazalika, za mu iya koyan darussa daga dukan abubuwan da ƙungiyar Jehobah take wallafawa. Ka yi la’akari da wasu misalai. Littattafan da aka buga don matasa. An buga littattafai da yawa don matasa a shekarun baya bayan nan. [1] An buga wasu don ya taimaka musu su sha kan matsi a makaranta ko kuma ƙalubalen da suke fuskanta yayin da suke girma. Ta yaya dukanmu za mu amfana idan muka karanta waɗannan littattafan? Za mu tuna da ƙalubalen da matasanmu masu aminci suke fuskanta. Hakan zai sa mu san yadda za mu iya taimakonsu da kuma ƙarfafa su.

15. Me ya sa ya kamata Kiristoci da suka manyanta su riƙa karanta littattafan da aka wallafa don matasa?

15 Ba matasa ba ne kawai suke fuskantar matsaloli da aka ambata a cikin littattafai da aka wallafa domin matasa ba. Dukanmu muna bukata mu bayyana bangaskiyarmu, mu kame kanmu, mu guji matsi daga tsara kuma mu guji tarayya da kuma nishaɗin da za su ɓata dangantakarmu da Jehobah. An buga littattafai game da waɗannan batutuwan da kuma wasu don matasa. Shin ya kamata mu ɗauka cewa Kirista da ya manyanta ya fi ƙarfin ya karanta littattafan da aka wallafa don matasa ne? A’a! Gaskiya ne cewa an tsara waɗannan littattafan a yadda matasa za su ji daɗin karantawa, amma bayanan da ke ciki suna ɗauke da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su iya amfanar dukanmu.

16. Mene ne kuma Littafi Mai Tsarki yake taimaka wa matasa su yi?

 16 Ƙari ga haka, littattafan da aka wallafa don matasa yana taimaka musu su ƙarfafa bangaskiyarsu kuma su kusaci Jehobah. (Karanta Mai-Wa’azi 12:1, 13.) Har ila Kiristoci da suka manyanta za su amfana daga littattafan. Alal misali, a mujallar Awake! na Afrilu 2009, an saka wani talifi mai jigo: “Young People Ask . . . How Can I Make Bible Reading Enjoyable?” A cikin talifin, an tattauna hanyoyi dabam-dabam da za a iya jin daɗin karatun Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, akwai wani shafi mai akwati da za a iya yankewa kuma a saka a cikin Littafi Mai Tsarki don ya taimaka wajen karatu. Shin Kiristoci da suka manyanta sun amfana daga wannan talifin kuwa? Wata ’yar’uwa wadda matar aure ce da kuma mahaifiya ta ce: “A dā, ba na jin daɗin karatun Littafi Mai Tsarki.” Amma daɗa cewa: “Na bi shawarwarin da aka ba da a cikin wannan talifin, kuma ina amfani da shafin da na yanke daga cikin talifin. Yanzu ina marmarin karanta Littafi Mai Tsarki. Hakan ya sa na fahimci yadda littattafan ko kuma sassa dabam-dabam na Littafi Mai Tsarki suka jitu suka zama jigo ɗaya kamar wani hoto mai kyan gani. Ban taɓa jin daɗin karatun Littafi Mai Tsarki kamar haka ba.”

17, 18. Ta yaya za mu amfana idan muka karanta abubuwan da aka wallafa don jama’a? Ka ba da misali.

17 Abubuwan da ake wallafawa don jama’a. Tun shekara ta 2008, muna jin daɗin Hasumiyar Tsaro na Nazari da ake wallafawa don Shaidun Jehobah. Amma za mu iya amfana daga mujallunmu da ake wallafawa don jama’a kuwa? Ka yi la’akari da wani kwatanci. A ce kana cikin Majami’ar Mulki sai ka lura cewa wani mutumin da ka gayyata zuwa taro ya zo kafin a soma jawabi ga jama’a. Babu shakka za ka yi farin ciki. Yayin da ɗan’uwan yake ba da jawabinsa, wataƙila za ka riƙa tunani game da mutumin. Yayin da kake sauraro, za ka riƙa tunanin yadda jawabin zai amfani wannan mutumin da ka gayyata. Saboda haka, jawabin zai ratsa zuciyarka kuma za ka ƙara fahimtar batun da aka yi jawabi a kai.

18 Za mu iya samun kanmu a cikin irin wannan yanayin sa’ad da muka karanta wani talifin da aka wallafa don jama’a. Alal misali, an tattauna wasu batutuwan Littafi Mai Tsarki a cikin Hasumiyar Tsaro na wa’azi a yadda mutumin da ba Mashaidin Jehobah ba zai iya fahimta. Ƙari ga haka, ana wallafa irin waɗannan talifofi a dandalin jw.org/ha, a ƙarƙashin sassa kamar “An Amsa Tambayoyin Littafi Mai Tsarki” da kuma “Tambayoyin da Ake Yawan Yi.” Sa’ad da muka karanta waɗannan batutuwan, muna ƙara fahimtar gaskiyar Littafi Mai Tsarki, kuma yana taimaka mana mu ƙara sanin wasu hanyoyin da za mu iya bayyana abin da muka yi imani da shi sa’ad da muka fita wa’azi. Hakazalika, idan muna karanta Awake! a kai a kai, muna samun ƙarin dalilai na gaskata cewa akwai Allah kuma hakan yana taimaka mana mu kāre imaninmu.—Karanta 1 Bitrus 3:15.

19. Ta yaya za mu iya nuna godiya ga Jehobah saboda abubuwan da yake tanadar mana?

19 Hakika, Jehobah ya yi mana tanadi da yawa don mu ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da shi. (Mat. 5:3) Bari mu ci gaba da yin amfani da dukan waɗannan abubuwan da yake tanadar mana. Idan muka yi hakan, muna nuna godiyarmu ga Wanda yake koyar da mu don mu amfani kanmu.—Isha. 48:17.

^ [1] (sakin layi na 14) Waɗannan littattafan sun haɗa da Questions Young People Ask—Answers That Work, Volume 1 da Volume 2, da kuma jerin “Tambayoyin Matasa” da ake wallafawa a dandalinmu na jw.org/ha.