Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Mayu 2016

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 27 ga Yuni, zuwa 31ga Yuli, 2016.

Ku Sasanta Matsalolinku Cikin Kauna

Wane buri ne ya kamata ka kasance da shi? Ka nuna cewa kai ne mai gaskiya, ka nuna wa mutumin cewa shi ne mai laifi, ko kuma wani abu dabam?

‘Ku Tafi . . . , Ku Almajirtar da Dukan Al’ummai’

Amsoshin tambayoyi hudu ya nuna wadanda suke cika annabcin Yesu a yau.

Yaya Kake Tsai da Shawarwari?

Mene ne ya kamata ka yi idan kana so ka yanke shawara a batun da Littafi Mai Tsarki bai ba da takamaiman doka ba?

Kana Barin Littafi Mai Tsarki Ya Kyautata Halayenka Har Ila?

Wani Mashaidi ya daina yin caca, shan taba, shan giya da kwaya don ya cancanci yin baftisma, amma ya ga cewa yana da wani hali da ke da wuyan canjawa.

Kana Amfana Daga Dukan Abubuwan da Jehobah Yake Tanadinsu Kuwa?

Mene ne zai iya hana mu amfana daga dukan abubuwa da Jehobah yake tanadinsu?

DAGA TARIHINMU

“Wanda Aka Danka wa Aikin”

Wani abin da ya faru a shekara ta 1919 ya sa an soma wani aikin da ya shafi duniya baki daya.

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Mene ne zai iya taimaka wa Kiristoci su san ko ya dace su ba wa ma’aikatan gwamnati kyauta ko kuma kudin goro? Ta yaya ’yan’uwa a cikin ikilisiya za su nuna farin cikinsu sa’ad da aka sanar cewa an dawo da wanda aka yi masa yankan zumunci? Mene ne zai iya sa ruwan tafkin Baitasda da ke Urushalima ya yi “motsi”?