Me ya sa Shaidun Jehobah suke zana manzo Bulus a matsayin mai sanƙo ko kuma marar suma sosai?

Hotunan Bulus da ke littattafanmu zane-zane ne da suke wakiltar yadda wataƙila kamaninsa yake. Kuma ba a zana su bisa ga bayanai da masana suka gano ba.

Amma, da akwai wasu bayanai game da yadda wataƙila kamanin Bulus yake. Alal misali, a mujallar Zion’s Watch Tower [Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona] ta 1 ga Maris, 1902, an yi ƙaulin wani da ya ce: “Game da kamanin Bulus: . . . A littafin nan ‘Acts of Paul and Thecla,’ da aka rubuta shekara 150 bayan mutuwar Yesu, an bayyana yadda kamanin Bulus yake kuma za a iya gaskata da wannan bayanin. A kwatancin, an bayyana kamanin Bulus a matsayin ‘mutum mai ƙaramin jiki, mai sanƙo kuma ƙafafunsa ba miƙaƙƙu ba ne sosai. Ban da haka, an ce girarsa suna taɓa juna kuma yana da dogon hanci.’”

Littafin Oxford Dictionary of the Christian Church (bugun 1997) ya yi magana game da littafin ‘Acts of Paul and Thecla’ cewa: “Zai yiwu abin da littafin nan ya faɗa ya yi daidai da tarihi.” Littafin nan ‘Acts of Paul and Thecla,’ littafi ne da ake darajawa sosai a ƙarnuka da suka shige, kuma an tabbatar da hakan ne don an sami kofi 80 a yaren Girka, har ma a wasu yaruka. Don haka, zane-zanenmu sun jitu da kwatancen da wasu suka yi game da kamanin manzo Bulus.

Ka tuna cewa da akwai abubuwan da suka fi sanin yadda kamanin Bulus yake muhimmanci. A lokacin da Bulus yake hidimarsa, wasu ’yan sūka sun ce “ainin jikinsa rarrauna ne, bakinsa kuwa ba wani abu ba ne.” (2 Kor. 10:10) Amma kada mu manta cewa ta hanyar mu’ujiza ce Yesu ya sa Bulus ya zama Kirista. Muna ma iya yin tunani a kan abubuwan da Bulus ya cim ma a matsayinsa na ‘zaɓaɓe [ga Kristi wanda], zai ɗauki sunana [Yesu] gaban al’ummai.’ (A. M. 9:​3-5, 15; 22:​6-8) Ƙari ga haka, ka yi tunanin yadda muke amfana daga littattafan Littafi Mai Tsarki da Jehobah ya hure Bulus ya rubuta.

Bulus bai yi fahariya don abubuwan da ya cim ma kafin ya zama Kirista ba, kuma bai bayyana yadda kamanin yake ba. (A. M. 26:​4, 5; Filib. 3:​4-6) Ya ce: “Ni autan manzanni ne, ni da ban isa a ce da ni manzo” ba. (1 Kor. 15:9) Bayan haka, ya sake cewa: “Ni, wanda na zama koma bayan baya cikin tsarkaka duka, a gare ni aka ba da wannan alheri, in yi wa’azin wadatar Kristi wurin al’ummai, wadata wadda ta fi ƙarfin a biɗa.” (Afis. 3:8) Babu shakka, wannan saƙon ya fi sanin yadda kamanin Bulus yake muhimmanci.