“Ka tuna da ni yanzu, ya Ubangiji, ina roƙonka, da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci, da zuciya ɗaya.”2 SAR. 20:3, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 52, 65

1-3. Mene ne bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu ta ƙunsa? Ka bayyana.

TUN da yake mu ajizai ne, mukan yi kuskure. Amma Jehobah ba ya yi mana “gwargwadon zunubanmu,” idan muka tuba kuma muka nemi gafara daga gare shi ta wajen hadayar Yesu. (Zab. 103:10) Duk da haka, kamar yadda Dauda ya gaya wa Sulemanu, kafin Jehobah ya karɓi ibadarmu, muna bukatar mu bauta masa da dukan zuciyarmu. (1 Laba. 28:9) Amma a matsayinmu na ajizai ta yaya za mu iya yin hakan?

2 Abin da zai iya taimaka mana mu yi hakan shi ne yin la’akari da yadda rayuwar Sarki Asa ta bambanta da ta Sarki Amaziah. Dukansu sarakunan Yahuda ne kuma sun yi abin da Jehobah yake so, amma Asa ya yi hakan da dukan zuciyarsa. (2 Laba. 15:16, 17; 25:1, 2; Mis. 17:3) Ko da yake dukansu ajizai ne, kuma sun yi kuskure. Amma Asa bai daina bin Jehobah ba, ya bauta wa Allah da dukan zuciyarsa. (1 Laba. 28:9) Amaziah kuma bai bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsa ba. Sa’ad da yi nasara a kan maƙiyansa, sai ya dawo da allolinsu kuma ya soma bauta musu.2 Laba. 25:11-16.

 3 Kafin mutum ya bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsa, wajibi ne sai ya ƙaunaci Jehobah sosai kuma ya bauta masa har ƙarshen ransa. A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “zuciya” a wasu lokuta tana nufin ainihin halin mutum. Kuma ya ƙunshi abin da muke tunaninsa da abin da muke so da abin da za mu so mu yi da rayuwarmu da kuma dalilin da ya sa muke yin abubuwa. Saboda haka, ko da yake mu ajizai ne, za mu iya bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu. Muna bauta masa domin muna son mu yi hakan, ba don ya tilasta mana mu yi hakan ba.2 Laba. 19:9.

4. Mene ne za mu bincika?

4 Don mu fahimci abin da ake nufin da bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu, bari mu duba rayuwar Asa da kuma ta wasu sarakunan Yahuda da suka bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya, waɗannan su ne Jehoshafat da Hezekiya da kuma Josiah. Dukan su huɗun sun yi kuskure, amma Jehobah ya amince da su. Me ya sa Jehobah ya ɗauke su a matsayin waɗanda suka bauta masa da dukan zuciyarsu?

ASA YA BAUTA WA JEHOBAH DA DUKAN ZUCIYARSA

5. Wane mataki ne Asa ya ɗauka?

5 Bayan an raba masarautar Isra’ila da ta Yahuda, Asa shi ne sarki na uku da ya yi sarauta a Yahuda. Ya kawar da bautar gumaka, bayan haka, sai ya kori mazan da suke karuwanci a haikali daga daularsa gabaki ɗaya. Ƙari ga haka, ya cire kakarsa Maacah a matsayin sarauniya, domin ta yi wata sifar gunki mai-ƙazamta. (1 Ki. 15:11-13) Ban da haka ma, Asa ya umurci mutanensa su “biɗi Ubangiji . . . su kiyaye shari’a da umurni.” Asa ya yi iya ƙoƙarinsa don ya sa mutanensa su bauta wa Jehobah.2 Laba. 14:4.

6. Mene ne Asa ya yi sa’ad da Habashawa suka kawo masa hari?

6 Jehobah ya yi wa Yahudawa albarka kuma sun sami kwanciyar hankali. Bayan haka, Zerah Bahabashe ya zo da sojoji guda 1,000,000 da kuma karusa guda 300 don ya yaƙi Yahuda. (2 Laba. 14:1, 6, 9, 10) Mene ne Asa ya yi da ya ga hakan? Ya dogara ga Jehobah sosai kuma ya kasance da gaba gaɗi. (Karanta 2 Labarbaru 14:11.) Allah ya amsa addu’ar Asa kuma ya sa ya yi nasara a kan sojojin Habasha. (2 Laba. 14:12, 13) Jehobah ya ba wa sarakuna da ma ba su da aminci nasara a kan maƙiyansu don ya nuna cewa shi ne Allah na gaskiya. (1 Sar. 20:13, 26-30) Asa ya dogara ga Jehobah, kuma Jehobah ya amsa addu’arsa. Amma akwai lokacin da Asa ya yi kuskure sosai. Alal misali, ya nemi taimakon sarkin Assuriya maimakon ya nemi taimakon Jehobah. (1 Sar. 15:16-22) Duk da haka, Jehobah ya ce Asa ya bauta masa da dukan zuciyarsa a duk “kwanakin ransa.” Ta yaya za mu iya yin koyi da Asa?1 Sar. 15:14.

7, 8. Ta yaya za ka yi koyi da Asa a ibadarka ga Jehobah?

7 Dukanmu za mu iya bincika zuciyarmu don mu san ko muna bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. Ka tambayi kanka, ‘Shin ina shirye in yi abin da Jehobah yake so, in kāre bauta ta gaskiya kuma in kāre bayin Jehobah daga wani abin da zai iya ɓata dangantakarsu da shi?’ Ka yi tunanin irin gaba gaɗin da Asa ya kasance da shi kafin ya yi abin da ya yi wa Maacah wadda “sarauniya” ce a ƙasar! Babu shakka, wataƙila ba ka taɓa ganin wani da ya yi irin abin da ta yi ba, amma wani yanayi zai iya tasowa da ya kamata ka  nuna irin gaba gaɗin Asa. Alal misali, idan ɗan’uwanka ko kuma abokinka ya yi zunubi kuma ya ƙi tuba, har aka yi masa yankan zumunci, me za ka yi? Shin za ka ɗau matakin daina yin tarayya da shi ne? Mene ne zuciyarka za ta sa ka yi?

8 Kamar Asa za ka iya nuna cewa kana bauta wa Jehobah da dukan zuciyarka idan ka dogara da shi sa’ad da kake fuskantar tsanantawa sosai har da waɗanda kake gani ba za ka iya shawo kansu ba. Zai yiwu a riƙa zolayarka a makaranta don kai Mashaidin Jehobah ne, ko kuma abokan aikinka suna iya yi maka dariya don ka ɗauki hutu don ibada, ko don ba ka yawan karɓan ƙarin aiki bayan an tashi. A irin wannan yanayin ka yi wa Allah addu’a kamar yadda Asa ya yi. Kuma ka dogara ga Jehobah ka ci gaba da yin abin da ya dace. Ƙari ga haka, ka tuna cewa kamar yadda Allah ya ƙarfafa Asa kuma ya taimake shi, kai ma zai yi maka hakan.

9. Sa’ad da muke wa’azi, ta yaya za mu nuna cewa muna bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu?

9 Bayin Allah ba sa tunanin kansu kawai. Asa ya sa mutane sun soma bauta wa Jehobah. Mu ma muna taimaka wa mutane su zo su “biɗi Ubangiji.” Babu shakka, Jehobah yana farin ciki sa’ad da ya ga muna koya wa maƙwabtanmu da sauran mutane game da shi. Kuma muna yin hakan don muna ƙaunarsa kuma muna so mutane su sami rai na har abada!

JEHOSHAPHAT YA BIƊI JEHOBAH

10, 11. Ta yaya za ka iya yin koyi da Jehoshaphat?

10 Jehoshaphat “ya yi tafiya cikin hanyar Asa ubansa.” (2 Laba. 20:31, 32) Ta yaya ya yi hakan? Kamar mahaifinsa, Jehoshaphat ya ƙarfafa mutanensa su biɗi Jehobah. Ya yi hakan, sa’ad da ya shirya a riƙa koyar da mutane ta wajen yin amfani da “litafin shari’ar Ubangiji.” (2 Laba. 17:7-10) Ƙari ga haka, ya je biranen da suke arewacin Isra’ila har zuwa wurin mutanen da ke tuddan Ifraimu, don ya “dawo da su wurin Ubangiji.” (2 Laba. 19:4) Jehoshaphat sarki ne “wanda ya biɗi Ubangiji da dukan zuciyarsa.”2 Laba. 22:9.

11 A yau, Jehobah yana so mutane a dukan duniya su san shi. Kuma dukanmu za mu iya taimaka wajen yin hakan. Shin burinka ne kowane wata ka riƙa koya wa mutane Kalmar Allah don su bauta masa? Idan kana wa’azi da ƙwazo, za ka iya soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Shin kana yin addu’a game da yin hakan? Shin za ka iya yin amfani da lokacinka don yin hakan? Kamar yadda Jehoshaphat ya je biranen Ifraimu don ya taimaka wa mutane su komo ga yin bauta ta gaskiya, mu ma za mu iya taimaka wa waɗanda suka yi sanyin gwiwa. Ƙari ga haka, dattawan ikilisiya suna kai ziyara don su taimaka wa waɗanda aka yi wa yankan zumunci amma daga baya suka tuba.

12, 13. (a) Sa’ad da Jehoshaphat yake fuskantar mawuyacin yanayi, mene ne ya yi? (b) Me ya sa ya kamata mu yi koyi da Jehoshaphat?

12 Ko da yake sojoji masu yawa sun kawo wa Yahuda hari, Jehoshaphat ya dogara ga Jehobah kamar mahaifinsa. (Karanta 2 Labarbaru 20:2-4.) Jehoshaphat ya ji tsoro, amma “ya sa zuciyarsa ga neman Ubangiji.” Sa’ad da yake addu’a, ya gaya wa Jehobah cewa mutanensa ba su da “wani ƙarfi wurin wannan babban taron” kuma ba su san abin da za su yi ba. Ya dogara ga Jehobah sosai  kuma ya ce: “Idanunmu suna gareka.”2 Laba. 20:12.

13 Kamar Jehoshaphat mukan sami kanmu a wani irin yanayin da ba za mu san abin da za mu yi ba, har ma mu riƙa jin tsoro. (2 Kor. 4:8, 9) Amma ka tuna cewa Jehoshaphat ya gaya wa Jehobah cewa shi da mutanensa ba su san abin da za su yi ba. (2 Laba. 20:5) Magidanta za su iya yin koyi da Jehoshaphat ta wajen neman ja-gorar Jehobah sa’ad da suke fuskantar wata matsala. Kada ka ji kunyar barin iyalinka su ji abubuwan da kake roƙon Jehobah. Me ya sa? Hakan zai sa su ga cewa ka dogara ga Jehobah. Kuma kamar yadda Allah ya taimaka wa Jehoshaphat, zai taimaka maka.

HEZEKIYA YA CI GABA DA YIN ABIN DA YA DACE

14, 15. Ta yaya Hezekiya ya nuna cewa ya dogara ga Jehobah da dukan zuciyarsa?

14 Hezekiya wani sarki ne da ya “manne wa Ubangiji” ko da yake mahaifinsa bai kafa masa misali mai kyau ba, domin ya bauta wa gumaka. Amma Hezekiya “ya kawar da masujadai, ya kakkarya su umudai, ya farfashe maciji na jan ƙarfe, wanda Musa ya ƙera,” domin ‘ya’yan Isra’ila sun soma bauta wa gunki. Hezekiya ya dogara ga Jehobah kuma ya ci gaba da ‘kiyaye umurnansa waɗanda Ubangiji ya umurta wa Musa.’2 Sar. 18:1-6.

15 Har ma a lokacin da Assuriyawa waɗanda suke da ƙarfi sosai suka zo su yaƙi Yahuda da kuma Urushalima, Hezekiya ya dogara ga Jehobah da dukan zuciyarsa. Ƙari ga haka, Sennacherib, Sarkin Assuriya ya faɗi abubuwa marar daɗi game da Jehobah kuma ya nemi Hezekiya ya miƙa wuya. Amma Hezekiya ya dogara ga Jehobah kuma ya nemi taimakonsa. (Karanta Ishaya 37:15-20.) Allah ya amsa addu’arsa kuma ya tura mala’ika ɗaya da ya kashe Assuriyawa guda 185,000.Isha. 37:36, 37.

16, 17. Ta yaya za ka yi koyi da Hezekiya a bautarka ga Jehobah?

16 Daga baya, Hezekiya ya soma rashin lafiya sosai har ya kusan mutuwa. Sai ya roƙi Jehobah ya tuna da yadda ya yi masa biyayya. (Karanta 2 Sarakuna 20:1-3.) Jehobah ya amsa addu’arsa kuma ya warkar da shi. Amma, Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mun fahimci cewa ba ma rayuwa a lokacin da Jehobah zai yi mu’ujiza don ya warkar da mu ko ya daɗa mana tsawon rayuwa. Duk da haka, kamar yadda Hezekiya ya yi, dukanmu za mu iya yin addu’a ga Jehobah kuma mu gaya masa cewa: “Ka tuna yanzu yadda na yi tafiya a gabanka da gaskiya.” Shin ka yarda cewa Jehobah zai iya taimaka maka har a lokacin da kake rashin lafiya?Zab. 41:3.

17 Ta yaya za mu bi misalin Hezekiya? Za mu yi hakan ta wurin daina yin abin da zai ɓata dangantakarmu da Jehobah kuma ya hana mu mai da hankali ga ibadarmu. Saboda haka, bai kamata mu yi koyi da mutanen duniya da suke yin amfani da shafuffukan sada zumunta suna ɗaukaka mutane kamar gumaka ba. Hakika, wasu Kiristoci suna jin daɗin yin amfani da hanyar nan don su riƙa tattaunawa da iyalinsu ko kuma abokansu. Amma mutane da yawa a duniya suna amfani da kafofin sada zumunta don su yi tarayya da maza da mata da ba su sani ba, ko kuma su riƙa ɓata lokaci suna kallon hotuna ko kuma karanta labaran mutane. Za mu iya zama masu fahariya saboda mutane da yawa suna son hotunan da muka saka a irin waɗannan wuraren,  ko kuma mu soma jin haushi domin wasu sun daina kallon hotunanmu. Maimakon hakan, mu yi koyi da manzo Bulus ko Akila da Biriskilla. Shin sun ɓata lokacinsu ne suna bin wasu ko suna ƙoƙarin sanin kome game da su duk da cewa ba sa bauta wa Jehobah? Littafi Mai Tsarki ya ce Bulus “ya taƙure da magana.” Akila da Biriskilla kuma sun yi amfani da lokacinsu don su koya wa mutane “tafarkin Allah sosai.” (A. M. 18:4, 5, 26) Za mu iya tambayar kanmu, ‘Shin ina ɗaukaka mutane da kuma ɓata lokaci wajen yin abin da ba shi da muhimmanci?’Karanta Afisawa 5:15, 16.

JOSIAH YA BI DOKOKIN JEHOBAH

18, 19. Ta wace hanya ce za ka yi koyi da Josiah?

18 Jikan Hezekiya, wato Sarki Josiah ya bi dokokin Jehobah da “dukan zuciyarsa.” (2 Laba. 34:31) A lokacin da yake matashi, Josiah “ya soma neman Allah na ubansa Dawuda,” kuma a lokacin da ya kai shekara ashirin ya soma kawar da dukan gumakan da ke Yahuda. (Karanta 2 Labarbaru 34:1-3.) Josiah ya saka ƙwazo a yin abin da Jehobah yake so fiye da sarakunan Yahuda da yawa. Sa’ad da aka gano littafin da ke ɗauke da Dokokin da Allah ya ba da ta hannun Musa kuma aka karanta wa Josiah, hakan ya sa ya ga cewa yana bukatar ya ƙara ƙwazo a yin abin da Jehobah yake so. Kuma ya ƙarfafa wasu ma su bauta wa Jehobah. Abin da ya yi ya sa mutanen “ba su rabu da bin Ubangiji” ba dukan kwanakin rayuwar Josiah.2 Laba. 34:27, 33.

19 Matasa suna bukatar su soma bin Jehobah tun suna ƙanana kamar yadda Josiah ya yi. Wataƙila bayan Sarki Manasseh ya tuba, ya koya wa Josiah cewa Jehobah mai jin kai ne. Matasa, kuna bukata ku kusaci tsofaffi da suke iyalinku da kuma ikilisiyarku don ku koyi yadda Jehobah ya kula da su. Ƙari ga haka, ku tuna cewa karatun Littafi Mai Tsarki ne ya taɓa zuciyar Josiah kuma ya sa shi ya yi ƙwazo a bautarsa ga Jehobah. Karanta Littafi Mai Tsarki zai sa ku kasance da ƙwazo a bautarku ga Jehobah. Ban da haka, karanta Littafi Mai Tsarki zai taimaka muku ku yi farin ciki kuma ku ci gaba da ƙarfafa dangantakarku da Jehobah. Hakan zai taimaka ma wasu ma su san shi. (Karanta 2 Labarbaru 34:18, 19.) Kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka ka fahimci hanyoyin da za ka inganta ibadarka ga Jehobah kamar yadda Josiah ya yi.

KA BAUTA WA JEHOBAH DA DUKAN ZUCIYARKA!

20, 21. (a) Mene ne sarakuna huɗun suka yi? (b) Mene ne za mu bincika a talifi na gaba?

20 Shin nazarin yadda sarakuna huɗun nan suka bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsu ya amfane ka? Sun sa ƙwazo sosai a hidimarsu ga Jehobah kuma sun ci gaba da bauta masa. Ƙari ga haka, sun yi hakan har a lokacin da maƙiyansu suke so su kawo musu hari. Amma mafi muhimmanci, sun bauta wa Jehobah domin suna ƙaunarsa.

21 Ko da yake sarakuna huɗun nan sun yi kuskure, Jehobah ya amince da su. Ya ga abin da yake zuciyarsu kuma ya san cewa suna ƙaunarsa da gaske. Mu ma ajizai ne kuma muna kuskure, amma Jehobah zai yi farin ciki idan ya ga cewa muna bauta masa da dukan zuciyarmu. A talifi na gaba za mu bincika abin da muka koya daga kurakuren waɗannan sarakunan.