Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro (Ta Nazari)  |  Maris 2016

Yara da Matasa, Kun Yi Shirin Yin Baftisma Kuwa?

Yara da Matasa, Kun Yi Shirin Yin Baftisma Kuwa?

“Wane ne a cikinku, kadan yana so ya gina soro, ba shi kan fara zaunawa tukuna, ya yi lissafin tamanin gini, ko yana da abin da za ya gama shi?”LUKA 14:28.

WAƘOƘI: 120, 64

An rubuta wannan talifi da na gaba don yara da matasa da suke son su yi baftisma

1, 2. (a) Mene ne yake sa mutanen Allah farin ciki a yau? (b) Ta yaya iyaye Kirista da dattawa za su taimaka wa matasa su fahimci abin da yin baftisma yake nufi?

WANI dattijo ya gaya wa wani mai shela ɗan shekara 12 mai suna Christopher cewa: “Na san ka tun kana jariri, kuma na yi farin ciki da na ji cewa kana son ka yi baftisma. Amma barin in tambaye ka, ‘Me ya sa kake son ka yi baftisma?’” Wannan dattijo yana da dalilai masu kyau na yin wannan tambaya. Muna farin cikin ganin cewa ana yi wa dubban matasa baftisma a kowace shekara. (Mai-Wa’azi 12:1) Amma ya kamata iyaye Kiristoci da dattawa su tabbata cewa matasan ne da kansu suka tsai da shawara cewa za su yi baftisma. Ƙari ga haka, ya kamata su fahimci abin da yin hakan yake nufi.

2 A cikin Littafi Mai Tsarki, mun koya cewa idan mutum ya  keɓe kansa kuma ya yi baftisma, hakan yana nufi cewa ya soma wani sabon salon rayuwa a matsayinsa na Kirista. Jehobah zai albarkace shi sosai don bin wannan salon rayuwa amma zai fuskanci hamayya daga wurin Shaiɗan. (Misalai 10:22; 1 Bitrus 5:8) Saboda haka, ya kamata iyaye su koya wa yaransu sosai abin da yake nufi mutum ya zama almajirin Kristi. Ƙari ga haka, ya kamata dattawa su taimaka wa matasan da iyayensu ba Shaidun Jehobah ba ne su fahimci abin da yake nufi mutum ya keɓe kansa kuma ya yi baftisma. (Karanta Luka 14:27-30.) Kamar yadda mutum zai yi shiri sosai kafin ya kammala aikin gina gida, wajibi ne matasa su yi shiri kafin su yi baftisma don hakan zai taimaka musu su bauta wa Jehobah da aminci “har ƙarshe.” (Matta 24:13, Littafi Mai Tsarki) Mene ne zai taimaka wa matasa su ƙudura niyya su bauta wa Jehobah har abada? Bari mu gani.

3. (a) Mene ne kalmomin Yesu da Bitrus suka koya mana game da muhimmancin yin baftisma? (Matta 28:19, 20; 1 Bitrus 3:21) (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna, kuma me ya sa?

3 Shin kai matashi ne da yake son ya yi baftisma? Idan haka ne, ka kafa maƙasudi mafi kyau! Gata ne mai girma mutum ya zama Mashaidin Jehobah da ya yi baftisma. Ƙari ga haka, wajibi ne Kirista ya yi baftisma kuma wannan matakin yana da muhimmanci ga waɗanda suke so su tsira a lokacin ƙunci mai girma. (Matta 28:19, 20; 1 Bitrus 3:21) Sa’ad da ka yi baftisma, ka yi alkawari cewa za ka bauta wa Jehobah har abada. Babu shakka, kana son ka cika wannan alkawarin, saboda haka, tambayoyi na gaba za su taimaka maka ka ga ko ka yi shirin yin baftisma: (1) Shin na manyanta in tsai da wannan shawara? (2) Shin ina son in tsai da wannan shawara da kai na? (3) Shin na fahimci abin da yake nufi mutum ya keɓe kansa ga Jehobah? Bari mu tattauna waɗannan tambayoyin.

A WANE LOKACI NE YA KAMATA KA YI BAFTISMA?

4, 5. (a) Me ya sa ya kamata ba manya kaɗai ne ya kamata su baftisma ba? (b) Mene ne yake nufi mutum ya manyanta?

4 Littafi Mai Tsarki bai ce sai waɗanda suka yi girma ne za su yi baftisma ko kuma sai mutum ya kai wasu shekaru kafin ya yi baftisma ba. Misalai 20:11 ya ce: ‘Ayyukan da saurayi [yaro NW ] ke yi su ke bayyana yadda yake, kana iya sani ko shi amintacce ne, mai nagarta’ (LMT). Saboda haka, ko yaro ma zai iya fahimtar abin da yake nufi mutum ya yi abin da ya dace kuma ya keɓe kansa ga Mahaliccinsa. Yin baftisma mataki ne mai muhimmanci da ya kamata matashi da ya nuna cewa ya manyanta ya  ɗauka, kuma ya keɓe kansa ga Jehobah.Misalai 20:7.

5 Mene ne yake nufi cewa mutum ya manyanta? Ba ta shekaru ko kuma ta girman jiki ne ake sanin cewa mutum ya manyanta ba. Littafi Mai Tsarki ya ce mutane da suka manyanta sun koyar da ‘hankalinsu’ don su san bambanci tsakanin nagarta da mugunta. (Ibraniyawa 5:14) Mutumin da ya manyanta ya san abin da ya dace kuma ya ƙudura a zuciyarsa cewa zai yi hakan. Saboda haka, zai yi wuya a rinjaye shi ya aikata mugunta. Ƙari ga haka, ba zai bukaci wani ya riƙa gaya masa a kowane lokaci ya yi abin da ya dace ba. Ya kamata mu tabbata cewa matashin da ya yi baftisma zai yi abin da ya dace ko da iyayensa ko kuma wasu da suka manyanta ba sa tare da shi.—Gwada Filibbiyawa 2:12.

6, 7. (a) Ka kwatanta ƙalubale da Daniyel ya fuskanta sa’ad da yake Babila. (b) Ta yaya Daniyel ya nuna cewa ya manyanta?

6 Shin wani matashi zai iya nuna irin wannan manyantar kuwa? Ka yi la’akari da misalin Daniyel. Wataƙila bai kai shekara 20 ba sa’ad da aka ɗauke shi daga iyayensa kuma aka kai shi Babila. Farat ɗaya, Daniyel ya zauna a tsakanin mutanen da ba sa bin umurnin Allah. Amma, bari mu ƙara bincika yanayin Daniyel sosai. An ba shi wani gata na musamman a Babila. Yana cikin matasa kalilan da aka zaɓa su riƙa yi wa sarki hidima. (Daniyel 1:3-5, 13) Kamar dai matsayin da Daniyel yake da shi a Babila ya wuce wanda zai taɓa samu a Isra’ila.

7 Amma, wane mataki ne Daniyel ya ɗauka? Shin ya bar mutanen Babila su canja ra’ayinsa ne ko kuma su raunana  bangaskiyarsa? Ko kaɗan! Littafi Mai Tsarki ya ce sa’ad da Daniyel yake Babila, ya ƙudura ‘a zuciyarsa ba za ya ɓāta kansa’ ba, kuma ya ce zai guji duk abin da yake da alaƙa da bautar ƙarya. (Daniyel 1:8) Hakan ya nuna cewa ya manyanta sosai!

Matashin da ya manyanta ba ya nuna cewa yana da dangantaka mai kyau da Allah a Majami’ar Mulki, alhali a makaranta, yana yin wasu abubuwan da mutanen duniya suke yi (Ka duba sakin layi na 8)

8. Mene ne za ka iya koya daga misalin Daniyel?

8 Mene ne za ka iya koya daga misalin Daniyel? Matashin da ya manyanta zai nace a kan abin ya yi imani shi ko a yanayi mai wuya. Ba ya kamar hawainiya da ke canja kalarsa don ya ɓad da kamanninsa. Ba zai nuna cewa yana da dangantaka mai kyau da Allah a Majami’ar Mulki, alhali a makaranta, yana rayuwa kamar waɗanda ba sa bauta wa Jehobah ba. A maimakon haka, zai kasance da aminci sa’ad da yake fuskantar gwaji.Karanta Afisawa 4:14, 15.

Matashin da ya manyanta zai nace a kan abin ya yi imani da shi ko a yanayi mai wuya

9, 10. (a) Ta yaya matashi zai amfana ta yin tunani game da matakin da ya ɗauka sa’ad da ya fuskanci gwaji? (b) Mene ne yin baftisma yake nufi?

9 Hakika, dukan mu ajizai ne. Matasa da kuma manyan sukan yi kuskure a wani lokaci. (Mai-Wa’azi 7:20) Amma idan kana so ka yi baftisma, zai yi kyau ka bincika ko ka ƙudura aniya za ka yi biyayya ga umurnin Jehobah. Ka tambayi kanka, ‘Shin na daɗe ina yi wa Jehobah biyayya?’ Ka yi tunanin abin da ka yi a lokacin da ka fuskanci gwaji ga bangaskiyarka. Shin ka ɗauki matakin da ya dace? Kamar Daniyel, shin wani ya ƙarfafa ka ka yi amfani da iyawarka a duniyar Shaiɗan? Idan hakan gwaji ne a gare ka, shin ka fahimci nufin Jehobah a gare ka?—Afisawa 5:17.

10 Me ya sa yake da muhimmanci mu san amsoshin waɗannan tambayoyin? Domin za su taimaka maka ka ga cewa baftisma wani abu ne mai muhimmanci sosai. Baftisma yana nuna wa mutane cewa ka yi alkawari mai muhimmanci ga Jehobah. Ka yi masa alkawari cewa za ka ƙaunace shi kuma ka bauta masa har abada da dukan zuciyarka. (Markus 12:30) Ya kamata duk wanda ya yi baftisma ya ƙuduri niyyar cika alkawarinsa ga Jehobah.Karanta Mai-Wa’azi 5:4, 5.

ME YA SA KAKE SO KA YI BAFTISMA?

11, 12. (a) Wane tabbaci ne wanda yake son ya yi baftisma zai kasance da shi? (b) Mene ne zai taimaka maka ka kasance da ra’ayin da ya dace game da yin baftisma?

11 Littafi Mai Tsarki ya ce dukan mutanen Jehobah, har da matasa za su bauta masa “da yardan rai.” (Zabura 110:3) Saboda haka, mutumin da yake so ya yi baftisma yana bukatar ya tabbata cewa shi ne da kansa yake son ya yanke wannan shawarar. Wannan zai sa ka bincika abin da kake so sosai, musamman idan iyayenka Shaidun Jehobah ne.

12 Mai yiwuwa, sa’ad da kake girma ka ga mutane da yawa suna yin baftisma, wataƙila har da wasu cikin abokanka da ‘yan’uwanka. Amma, ka mai da hankali don kada ka soma ganin cewa wajibi ne ka yi baftisma don kana gani cewa  shekarunka sun kai ko kuma domin wasu suna yin baftisma. Ta yaya za ka tabbata cewa ka kasance da ra’ayin Jehobah a batun yin baftisma? Ka yi tunani sosai game da abin da ya sa baftisma yake da muhimmanci. Za ka samu dalilai da yawa masu kyau a wannan talifin da kuma na gaba.

13. Ta yaya za ka san ko shawarar yin baftisma ya fito daga zuciyarka?

13 Yin tunani a kan yadda kake yin addu’a zai taimaka maka ka san ko shawarar da tsai da na yin baftisma ya fito daga zuciyarka. Shin kana addu’a a kai a kai ga Jehobah kuwa? Sa’ad da kake addu’a, kana ambata ainihin batutuwa da suke damunka? Amsoshin waɗannan tambayoyin nan za su nuna ko ka ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah. (Zabura 25:4) A yawancin lokaci, Jehobah yana amsa addu’o’inmu a cikin Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, wata hanya da za ka san ko kana so ka kusaci Jehobah kuma ka bauta masa daga zuciyarka ita ce ta wurin bincika tsarin yin nazari da kake bi. (Joshua 1:8) Ka tambayi kanka: ‘Shin ina nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai? Ina yin kalami sa’ad da muke ibada ta iyali da son zuciyata?’ Amsoshin waɗannan tambayoyin za su taimaka maka ka ga ko kai ne da kanka kake son ka yi baftisma.

MENE NE KEƁE KAI GA JEHOBAH YAKE NUFI?

14. Ka faɗi bambancin keɓe kanka ga Jehobah da kuma yin baftisma.

14 Wasu matasa ba su san bambancin keɓe kai ga Jehobah da yin baftisma ba. Wasu suna iya cewa sun riga sun keɓe kansu ga Jehobah amma ba su yi shirin yin baftisma ba. Amma, shin hakan zai yiwu da gaske? Keɓe kai yana nufin yin addu’a don bayyana wa Jehobah cewa ka ɗauki alkawarin bauta masa har abada. Amma yin baftisma yana nuna wa mutane cewa ka riga ka keɓe kanka ga Jehobah. Saboda haka, kafin ka yi baftisma, kana bukatar ka fahimci abin da keɓe kanka ga Allah yake nufi.

15. Mene ne keɓe kai ga Jehobah yake nufi?

15 Sa’ad da ka keɓe kanka ga Jehobah, ka gaya masa cewa daga lokacin ka ba da kanka gare shi don ka yi nufinsa. Ka yi alkawari cewa za ka ba wa bautarsa fifiko a rayuwarka. (Matta 16:24) Irin wannan alkawarin da ka yi wa Allah yana da muhimmanci sosai! (Matta 5:33) To, ta yaya za ka nuna cewa ka ba da kanka ga Jehobah kuma ka yi watsi da muradinka da son ranka don ka bi ja-gorar Jehobah a dukan abubuwan da kake yi?Romawa 14:8.

16, 17. (a) Ka ba da misalin abin da yake nufin ka ƙi kanka. (b) Wane alkawari ne mutumin da ya keɓe kansa ga Jehobah ya yi?

16 Alal misali, a ce wani abokinka yana so ya ba ka kyautar mota. Ya miƙa maka takardun motar kuma ya ce: “Na ba ka wannan motar kyauta.” Amma, sai ya ce: “Zan riƙe maƙullin motar, kuma ni ne zan riƙa tuƙa motar ba kai ba.” Shin kana gani ya ba ka kyautar motar da zuciya ɗaya kuwa? Wani irin kallo ne za ka yi wa wannan abokinka da ya ba ka kyautar mota?

17 Sa’ad da wani ya keɓe kansa ga Jehobah, ya gaya wa Allah: “Na ba ka rai na. Ni naka ne.” Jehobah zai bukaci mutumin ya cika alkawarinsa. Amma idan mutumin ya soma rashin biyayya ga Jehobah  ta wurin fita zance da wadda ba ta bauta wa Allah ko ya karɓi aikin da ke hana shi fita wa’azin bishara da halartan taron ikilisiya a kai a kai. Wannan mutumin ba ya cika alkawarin da ya yi wa Jehobah. Hakan yana kamar ba wa mutum kyautar mota ne kuma ka hana shi maƙullin. Sa’ad da muka keɓe kanmu ga Jehobah, mun gaya masa, “Rayuwata tana hannunka, ba hannuna ba.” Saboda haka, za mu riƙa yin abin da Jehobah yake so ko a yanayi mai wuya. Bari mu yi koyi da Yesu sa’ad da ya ce: “Na sauko daga sama, ba domin in yi nufin kaina ba, amma nufin wanda ya aiko ni.”—Yohanna 6:38.

Yin baftisma mataki ne mai muhimmanci kuma babban gata ne

18, 19. (a) Ta yaya furucin Rose da Christopher ya nuna cewa yin baftisma gata ne da ke kawo albarka sosai? (b) Yaya kake ji game da gatan yin baftisma?

18 Hakika, yin baftisma mataki ne mai muhimmanci sosai. Babban gata ne ka keɓe kanka ga Jehobah kuma ka yi baftisma. Matasan da suke ƙaunar Jehobah kuma sun fahimci abin da keɓe kansu yake nufi ba sa jinkirin yin hakan da kuma yin baftisma. Ba sa yin da-na-sani game da shawara da suka yanke. Wata yarinya mai suna Rose da ta yi baftisma ta ce: “Ina ƙaunar Jehobah, kuma bauta masa ne ya fi sa ni farin ciki. A dukan shawarwarin da na yanke, babu wanda na taɓa kasance tabbaci a kai kamar na yin baftisma.”

19 Christopher da muka ambata ɗazu a farkon wannan talifin kuma fa? Yaya yake ji game da shawarar da ya yanke na yin baftisma sa’ad da yake ɗan shekara sha biyu? Ya ce ya yi farin ciki sosai cewa ya tsai da wannan shawarar. Ya soma hidimar majagaba na kullum sa’ad da yake ɗan shekara 17, kuma ya zama bawa mai hidima sa’ad da yake shekara 18. Yanzu yana hidima a Bethel. Ya ce: “Shawarar yin baftisma da na yi yana da kyau sosai. Ina amfani da rayuwata don na yi aiki mai gamsarwa ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa.” Idan kana so ka yi baftisma, ta yaya za ka yi shirin yin hakan? Talifi na gaba zai ba da amsar wannan tambayar.