“Kada fa ka ji tsoro, gama ina tare da kai, kada ka damu, gama ni ne Allahnka; Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka.”​—ISHA. 41:10.

WAƘA TA 7 Jehobah Ne Ƙarfinmu

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) Ta yaya saƙon da ke Ishaya 41:10 ya taimaki Yoshiko? (b) Su waye ne za su amfana daga wannan saƙon da Jehobah ya sa a rubuta?

AN GAYA wa wata amintacciyar ’yar’uwa mai suna Yoshiko wani labari marar daɗi. Likita ta gaya mata cewa za ta mutu bayan ’yan watanni. Yaya ta ji? Yoshiko ta tuna da wata aya a Littafi Mai Tsarki da ta fi so, wato Ishaya 41:10. (Karanta.) Sai ta gaya wa likitar cewa ba ta tsoro domin Jehobah yana riƙe da hannunta. * Saƙo mai ban ƙarfafa da ke wannan ayar ya taimaka wa ’yar’uwarmu ta dogara ga Jehobah sosai. Wannan ayar za ta taimaka mana mu natsu sa’ad da muke fuskantar matsaloli masu tsanani. Don mu fahimci yadda wannan ayar za ta taimaka mana, bari mu fara bincika dalilin da ya sa Allah ya ba Ishaya wannan saƙon.

2 Da farko, Jehobah ya sa Ishaya ya rubuta waɗannan kalami don ya ƙarfafa Yahudawa da za su je zaman bauta a Babila. Jehobah ya sa a adana wannan saƙon ba don Yahudawa kaɗai ba, amma don dukan bayinsa. (Isha. 40:8; Rom. 15:4) A yau, muna rayuwa a ‘kwanakin ƙarshe da za a sha wahala sosai.’ Saboda haka, a yau muka fi bukatar ƙarfafa da ke littafin Ishaya.​—2 Tim. 3:1.

3. (a) Waɗanne alkawura ne ke Ishaya 41:10? (b) Me ya sa muke bukatar waɗannan alkawuran?

3 A wannan talifin, za mu mai da hankali ga alkawuran Jehobah da ke rubuce a Ishaya 41:10 da za su taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu: (1) Jehobah zai kasance  tare da mu, (2) shi ne Allahnmu, kuma (3) zai taimaka mana. Muna bukatar wannan tabbacin * domin kamar Yoshiko, muna fuskantar matsaloli a rayuwa. Ban da haka, munanan abubuwan da ke faruwa a duniya suna shafan mu. Gwamnatoci masu iko suna tsananta ma wasu a cikinmu. Bari mu tattauna waɗannan alkawura uku ɗaya-bayan-ɗaya.

“INA TARE DA KAI”

4. (a) Wane alkawari ne za mu fara tattaunawa? (Ka duba ƙarin bayani.) (b) A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya gaya mana yadda yake ji game da mu? (c) Ta yaya abin da Allah ya ce ya shafe ka?

4 Jehobah ya fara ƙarfafa mu da wannan kalami: “Kada fa ka ji tsoro, gama ina tare da kai.” * Jehobah ya nuna cewa yana tare da mu ta wurin mai da mana hankali sosai da kuma nuna mana ƙauna. Ka lura da yadda ya furta ƙaunarsa da yadda yake ji game da mu. Ya ce: ‘Kana da daraja a idanuna, ina girmama ka, ina kuma ƙaunarka.’ (Isa. 43:4) Babu abin da zai sa Jehobah ya daina ƙaunar bayinsa kuma ba zai taɓa yashe mu ba. (Isha. 54:10) Yadda Jehobah yake ƙaunar mu da kuma yin abota da mu yana ƙarfafa mu sosai. Zai kāre mu yadda ya kāre Abram, wato Ibrahim abokinsa. Jehobah ya gaya masa cewa: Abram, “kada ka ji tsoro, ni garkuwa ne gare ka.”​—Far. 15:1.

Jehobah zai taimaka mana mu jimre duk matsalolin da muke fuskanta ko da suna kama da koguna ko kuma wuta (Ka duba sakin layi na 5-6) *

5-6. (a) Ta yaya muka san cewa Jehobah yana so ya taimaka mana sa’ad da muke fuskantar matsaloli? (b) Wane darasi ne za mu iya koya daga Yoshiko?

5 Mun san cewa Jehobah yana so ya taimaka mana sa’ad da muke fuskantar matsaloli domin ya yi wa mutanensa alkawari cewa: ‘Sa’ad da ka bi ta ruwa mai zurfi, ina tare da kai, ko ka bi ta tsakiyar koguna, ba za su kwashe ka ba. Ko ka bi ta cikin wuta, ba za ta ƙone ka ba, harshen wuta kuma ba zai cinye ka ba.’ (Isha. 43:2) Mene ne waɗannan kalmomi suke nufi?

6 Jehobah bai yi alkawari cewa zai kawar da ƙalubalen da muke fuskanta ba. Amma ba zai bar matsaloli masu kama da “koguna” su kwashe mu ba ko kuma gwaji  masu kama da “wuta” su kawo mana lahani na dindindin ba. Allah ya yi mana alkawari cewa zai kasance tare da mu kuma ya taimaka mana mu jimre da dukan waɗannan matsalolin. Mene ne Jehobah zai yi? Zai sa mu kasance da kwanciyar rai don mu riƙe amincinmu ko da za mu mutu. (Isha. 41:13) Abin da ya faru da Yoshiko da aka ambata ɗazu ke nan. ’Yarta ta ce: “Yadda mamarmu ta natsu ya burge mu sosai. Mun ga cewa Jehobah ya sa ta kasance da kwanciyar rai. Har zuwa ranar da mamarmu ta rasu, ta ci gaba da yin wa’azi ga masu aiki a asibiti da majiyata game da Jehobah da kuma alkawuransa.” Mene ne muka koya daga Yoshiko? Idan muka amince da wannan alkawarin da Allah ya yi cewa yana “tare da” mu, za mu kasance da gaba gaɗi kuma mu jimre da matsaloli.

“NI NE ALLAHNKA”

7-8. (a) Wane tabbaci na biyu ne za mu tattauna, kuma mene ne yake nufi? (b) Me ya sa Jehobah ya gaya wa Yahudawa da suke zaman bauta cewa: ‘Kada ku damu’? (c) Waɗanne kalmomi da ke Ishaya 46:​3, 4 ne suka ƙarfafa mutanen Allah?

7 Jehobah ya sake ƙarfafa mu ta wajen yi mana wannan alkawarin da Ishaya ya rubuta cewa: “Kada ka damu, gama ni ne Allahnka.” Mene ne wannan furuci yake nufi? A yaren da aka rubuta littafin Ishaya, kalmar nan “damu” tana nufin “mutum ya riƙa kallon baya a kowane lokaci domin yana jin tsoro cewa wani abu zai faru da shi ko kuma wani zai kawo masa hari.”

8 Me ya sa Jehobah ya gaya wa Yahudawa da za su je zaman bauta a Babila cewa kada su “damu”? Domin ya san cewa mazaunan ƙasar za su ji tsoro. Me zai sa su ji tsoro? Sojojin Mediya da Farisa za su kai wa Babila hari a kusan ƙarshen shekara 70 da Yahudawa za su yi a Babila. Jehobah zai yi amfani da waɗannan sojojin don ya ’yantar da mutanensa daga Babila. (Isha. 41:​2-4) Mene ne Babiloniyawa da mutanen sauran al’ummai suka yi sa’ad da suka ga cewa magabtansu sun kusan kawo musu hari? Sun yi ƙoƙari su kasance da ƙarfin zuciya kuma suka gaya wa juna: Ku “yi ƙarfin hali.” Ban da haka, sun ƙara ƙera gumaka don suna ganin waɗannan allolin ne za su kāre su. (Isha. 41:​5-7) Amma Jehobah ya sanyaya zuciyar Yahudawa da suke Babila cewa: “Ya kai Isra’ila bawana [ba kamar maƙwabtanku ba] . . . Kada ka damu, gama ni ne Allahnka.” (Isha. 41:​8-10) Ku lura cewa Jehobah ya ce: ‘Ni ne Allahnka.’ Ta wannan furucin, Jehobah yana taimaka wa bayinsa su daina damuwa domin har ila, shi ne Allahnsu kuma su mutanensa ne. Ya gaya musu: ‘Zan ɗauki nauyinku, ni zan cece ku.’ Babu shakka, waɗannan kalmomin sun ƙarfafa Yahudawa da suke zaman bauta.​—Karanta Ishaya 46:​3, 4.

9-10. Me ya sa bai kamata mu riƙa damuwa ba? Ka ba da misali.

9 Mutane suna damuwa yanzu fiye da dā domin yanayin duniya yana daɗa taɓarɓarewa. Hakika, waɗannan matsalolin suna shafan mu, amma ba ma bukatar mu riƙa jin tsoro. Jehobah yana gaya mana cewa: ‘Ni ne Allahnku.’ Me ya sa wannan furucin zai taimaka mana mu kasance da kwanciyar rai?

10 Ku yi la’akari da wannan misalin: A ce fasinjoji biyu, Salisu da Ali suna cikin babban bas kuma suka kai hanya mai gargada sosai. Yayin da motar take fama da hanyar, sai direban ya ce: “Ku zauna da kyau. Za mu ɗan jima kafin mu wuce  wurin nan.” Sai hankalin Salisu ya tashi. Amma direban ya daɗa cewa: “Ku kwantar da hankalinku.” A wannan lokacin, sai Salisu ya soma shakka ya ce, “Yaya za mu kwantar da hankalinmu a wannan yanayin?” Amma, ya lura cewa Ali bai damu ba ko kaɗan. Sai Salisu ya tambaye shi: “Me ya sa ba ka damu ba?” Ali ya yi murmushi ya ce: “Domin na san wannan direban sosai. Mahaifina ne!” Ƙari ga haka, Ali ya ce: “Bari in gaya maka game da mahaifina. Na tabbata cewa idan ka san cewa ya ƙware sosai, kai ma hankalinka zai kwanta.”

11. Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga kwatanci na fasinjoji biyu?

11 Waɗanne darussa ne wannan kwatancin ya koya mana? Kamar Ali, muna da kwanciyar rai domin mun san Jehobah sosai. Mun san cewa zai taimaka mana mu jimre sa’ad da muke fuskantar matsaloli masu wuya a wannan kwanaki na ƙarshe. (Isha. 35:4) Domin mun dogara ga Jehobah, mun kwantar da hankalinmu yayin da mutane a duniya suke jin tsoro. (Isha. 30:15) Muna bin misalin Ali idan muka gaya wa mutane dalilin da zai sa su dogara ga Allah. Hakan zai sa su ma su tabbata cewa Jehobah zai tallafa musu a duk yanayin da suke ciki.

“ZAN SA KA YI ƘARFI, IN KUMA TAIMAKE KA”

12. (a) Wane tabbaci na uku ne za mu tattauna? (b) Mene ne furucin nan ‘hannun’ Jehobah yake tuna mana?

12 Ka yi la’akari da tabbaci na uku da Ishaya ya rubuta: “Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka.” Ishaya ya riga ya kwatanta yadda Jehobah zai ƙarfafa mutanensa, ya ce: ‘Yahweh yana zuwa cikin iko, hannunsa mai ƙarfi yana mulki.’ (Isha. 40:10) Sau da yawa, ana amfani da kalmar nan ‘hannu’ a Littafi Mai Tsarki sa’ad da ake magana game da iko. Saboda haka, furucin nan cewa “hannunsa . . .  yana mulki” yana tuna mana cewa Jehobah Sarki ne mai ƙarfi sosai. Ya yi amfani da ƙarfinsa a dā don ya tallafa wa bayinsa kuma ya kāre su. A yau, Jehobah yana ƙarfafa mutanen da ke dogara gare shi kuma yana kāre su.​—M. Sha. 1:​30, 31; Isha. 43:10.

Babu kayan yaƙin da zai hana Jehobah kāre bayinsa (Ka duba sakin layi na 12-16) *

13. (a) A wane lokaci ne musamman Jehobah yake cika alkawarinsa cewa zai ƙarfafa mu? (b) Wane alkawari ne ke ƙarfafa mu da kuma sa mu gaba gaɗi?

13 Jehobah yana cika alkawarinsa cewa “zan sa ka yi ƙarfi” musamman ma sa’ad da magabta suke tsananta mana. A wasu ɓangarorin duniya a yau, magabtanmu suna ƙoƙari su hana mu wa’azi ko kuma su saka taƙunƙumi a aikinmu. Duk da haka, ba ma yawan damuwa. Jehobah ya tabbatar mana da cewa zai ƙarfafa mu kuma ya sa mu kasance da gaba gaɗi. Ya yi mana alkawari cewa: “Babu kayan yaƙin da aka ƙera domin a yaƙe ki wanda zai yi nasara.” (Isha. 54:17) Wannan furucin ya tabbatar mana da abubuwa uku masu muhimmanci.

14. Me ya sa ba ma mamaki cewa magabtan Allah suna tsananta mana?

14 Na farko, ya kamata mu san cewa za a tsane mu tun da yake mu mabiyan Kristi ne. (Mat. 10:22) Yesu ya annabta cewa za a tsananta wa almajiransa sosai a wannan kwanaki na ƙarshe. (Mat. 24:9; Yoh. 15:20) Na biyu, Ishaya ya annabta cewa magabtanmu za su tsane mu, kuma za su yi hakan ta hanyoyi dabam-dabam. Hakan ya ƙunshi yin ƙarya game da mu ko kuma tsananta mana sosai. (Mat. 5:11) Jehobah ba zai hana magabtanmu tsananta mana ba. (Afis. 6:12; R. Yar. 12:17) Amma ba ma bukatar mu riƙa jin tsoro. Me ya sa?

15-16. (a) Wane abu na uku ne ya kamata mu tuna, kuma ta yaya Ishaya 25:​4, 5 ya nuna hakan? (b) Ta yaya Ishaya 41:​11, 12 ya kwatanta sakamakon masu fushi da mu?

15 Ka yi la’akari da abu na uku da ya kamata  mu tuna. Jehobah ya ce “babu kayan yaƙin” da aka ƙera domin mu da “zai yi nasara.” Kamar yadda bango ke kāre mu daga ruwan sama da iska mai ƙarfi, haka ne Jehobah yake kāre mu daga makaman mugaye. (Karanta Ishaya 25:​4, 5.) Magabtanmu ba za su taɓa iya kawo mana illa na dindindin ba.​—Isha. 65:17.

16 Jehobah ya kuma ƙarfafa mu ta wurin bayyana mana abin da zai faru da “masu fushi” da mu. (Karanta Ishaya 41:​11, 12.) Ko da magabtanmu suna tsananta mana sosai, sakamakon zai zama cewa dukansu “za su mutu su ɓace.”

YADDA ZA MU ƘARA DOGARA GA JEHOBAH

Za mu ƙara dogara ga Jehobah ta wurin karanta game da shi a kai a kai a cikin Littafi Mai Tsarki (Ka duba sakin layi na 17-18) *

17-18. (a) Ta yaya karanta Littafi Mai Tsarki zai sa mu ƙara dogara ga Allahnmu? Ka ba da misali. (b) Ta yaya yin bimbini game da jigon shekara ta 2019 zai taimaka mana?

17 Muna ƙara dogara ga Jehobah ta wajen yin ƙoƙari mu san game da shi sosai. Ƙari ga haka, karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini ne kaɗai za su taimaka mana mu san shi sosai. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labaran yadda Jehobah ya kāre mutanensa a dā. Waɗannan labaran sun sa mu kasance da tabbaci cewa zai riƙa kula da mu a yau.

18 Ka yi la’akari da kwatancin da Ishaya ya yi amfani da shi don ya nuna yadda Jehobah yake kāre mu. Ya ce Jehobah yana kama da makiyayi kuma bayinsa tumaki ne. Ishaya ya ce Jehobah “yana tara ’yan tumakin a hannuwansa, ya rungume su a ƙirjinsa.” (Isha. 40:11) Idan muka san cewa Jehobah ya riƙe mu da hannunsa mai iko, hakan yana kwantar mana da hankali. Don ya taimaka mana mu kwantar da hankalinmu duk da matsalolin da muke fuskanta, bawan nan mai aminci da mai hikima ya zaɓi furucin da ke Ishaya 41:10 ya zama jigon shekara ta 2019 cewa, ‘Kada ka damu, domin ni ne Allahnka.’ Mu riƙa bimbini a kan kalmomin nan masu ƙayatarwa. Za su ƙarfafa mu yayin da muke fuskantar matsaloli a nan gaba.

WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka

^ sakin layi na 5 A jigon shekara ta 2019, an ba da dalilai uku da za su taimaka mana mu kasance da kwanciyar rai a lokacin da munanan abubuwa suke faruwa a duniya ko kuma sa’ad da muke fuskantar matsaloli. A wannan talifin, za mu tattauna waɗannan dalilan kuma za su taimaka mana mu rage yin alhini. Ƙari ga haka, za su sa mu dogara ga Jehobah sosai. Ku riƙa yin bimbini a kan jigon. Ku yi ƙoƙari ku haddace shi. Zai ƙarfafa ku don matsalolin da za ku fuskanta a nan gaba.

^ sakin layi na 3 MA’ANAR WASU KALMOMI: Tabbaci yana nufin alkawarin da aka yi cewa babu shakka wani abu zai faru. Tabbacin da Jehobah ya bayar za su taimake mu mu rage yin alhini game da matsalolin da za mu iya fuskanta.

^ sakin layi na 4 A Ishaya 41:​10, 13 da 14, an ƙarfafa mu sau uku cewa kada mu ji tsoro. A ayoyin nan, an yi amfani da kalmar nan “Ni,” wato Jehobah sau da yawa. Me ya sa Jehobah ya hure Ishaya ya yi amfani da kalmar nan “Ni” a kai a kai? Hakan ya nuna cewa idan muka dogara ga Jehobah, ba za mu riƙa jin tsoro ba.

^ sakin layi na 52 BAYANI A KAN HOTUNA: Membobin iyali suna fuskantar gwaji a wurin aiki, suna fama da rashin lafiya, suna fuskantar matsala sa’ad da suke wa’azi da kuma a makaranta.

^ sakin layi na 54 BAYANI A KAN HOTUNA: ’Yan sanda sun shigo wani gida da ’yan’uwa suke taro don su kama su, amma ’yan’uwan ba su ji tsoro ba.

^ sakin layi na 56 BAYANI A KAN HOTUNA: Yin Ibada ta Iyali a kai a kai na ƙarfafa mu mu jimre.