“Ya Allahnmu, muna gode maka, muna yabon sunanka mai-daraja.”​—1 LABA. 29:13.

WAƘOƘI: 80, 50

1, 2. Ta yaya Jehobah yake nuna mana alheri?

JEHOBAH mai alheri ne sosai. Kuma shi ya ba mu kome da muke da shi. Shi ya yi zinariya da azurfa da kuma dukan abubuwa masu tamani da ke duniya, kuma yana yin amfani da su don ya taimaka mana mu rayu. (Zab. 104:​13-15; Hag. 2:8) A Littafi Mai Tsarki, akwai labarai da yawa na yadda Jehobah ya yi amfani da abubuwan nan ta hanyar mu’ujiza don ya taimaka wa mutanensa.

2 Alal misali, sa’ad da Isra’ilawa suka yi shekara 40 a jeji, Jehobah ya ciyar da su da manna kuma ya ba su ruwan sha. (Fit. 16:35) Hakan ya sa “ba su rasa komi ba.” (Neh. 9:​20, 21) Ban da haka ma, ya sa annabi Elisha ya yi mu’ujiza don kada mān wata gwauruwa ya ƙare. Wannan kyauta da Jehobah ya yi mata ya taimaka mata ta biya bashin da ake bin ta kuma ta sami abin da ita da ɗanta za su riƙa ci. (2 Sar. 4:​1-7) Jehobah ya taimaka wa Yesu ya ciyar da mutane kuma ya tanadar da kuɗi ta hanyar mu’ujiza.​—Mat. 15:​35-38; 17:27.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Jehobah zai iya yin amfani da duk wani abin da yake so don  ya taimaka wa halittunsa a duniya. Amma ya ba bayinsa damar yin amfani da wadatarsu don su tallafa wa ƙungiyarsa. (Fit. 36:​3-7; karanta Misalai 3:9.) Me ya sa Jehobah yake so mu riƙa ba da gudummawar wadatarmu? Ta yaya bayin Allah a dā suka tallafa wa wakilan Jehobah? Ta yaya ƙungiyar Jehobah take yin amfani da gudummawar da ake bayarwa a yau? Za a amsa waɗannan tambayoyin a wannan talifin.

ME YA SA MUKE BA JEHOBAH KYAUTA?

4. Idan muka ba da gudummawa don aikin Jehobah, mene ne hakan yake nunawa?

4 Muna ba Jehobah kyauta domin muna ƙaunar sa kuma muna so mu nuna masa godiya. Muna farin ciki sosai sa’ad da muka yi tunanin duk abubuwan da Jehobah ya yi mana. A lokacin da Sarki Dauda yake bayyana abubuwan da ake bukata don a gina haikali, ya ce kome da muke da shi Jehobah ne ya ba mu kuma duk wani abu da muka ba Jehobah, shi ya ba mu.​—Karanta 1 Labarbaru 29:​11-14.

5. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna mana cewa ba da gudummawa yana da muhimmanci a bautarmu?

5 Muna ba Jehobah gudummawa domin yin hakan ma wata hanya ce ta bauta masa. Manzo Yohanna ya ga wahayi game da bayin Jehobah a sama suna cewa: “Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.” (R. Yoh. 4:11) Babu shakka, Jehobah ya cancanci mu ɗaukaka shi kuma mu daraja shi ta wurin ba da gudummawar wadatarmu. Jehobah ya sa Musa ya umurci Isra’ilawa cewa su yi idi sau uku a shekara. Kuma tun da yin hakan ibada ce ga Jehobah, an umurci Isra’ilawa cewa kada “su bayyana a gaban Ubangiji hannu wofi.” (K. Sha. 16:16) Haka ma a yau, ba da gudummawa don bautar Jehobah yana da muhimmanci sosai. Domin ta yin hakan ne muke tallafa wa ƙungiyar Jehobah na duniya.

6. Me ya sa yake da kyau mu riƙa ba da kyauta? (Ka duba hoton da ke shafi na 17.)

6 Yana da kyau mu zama masu bayarwa ba masu karɓa kawai ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bawan da aka lallashe shi tun yana yaro, a ƙarshe zai ɗauki kansa shi ɗa ne,” wato ba zai nuna godiya ba. (Mis. 29:​21, Juyi Mai Fitar da Ma’ana) Ka yi tunanin yaron da ya saya wa iyayensa kyauta daga ɗan kuɗin da suke ba shi. Babu shakka iyayen za su yi farin ciki sosai don abin da yaron ya yi! Ko kuma ka yi tunanin wani matashi da wataƙila yake hidimar majagaba kuma yana zama da iyayensa, amma yana tallafa musu ta wurin ba su kuɗi don su sayi wasu abubuwa. Ko da yake iyayen ba su sa rai cewa yaron zai yi hakan ba, amma za su karɓi kyautar don zai nuna cewa yaron ya daraja abin da suka yi masa. Hakazalika, Jehobah ma ya san cewa yana da kyau mu riƙa ba da kyauta.

YADDA BAYIN ALLAH SUKA BA DA GUDUMMAWA A DĀ

7, 8. Ta yaya bayin Jehobah a dā suka kafa misalin ba da kyauta don (a) wani gini da za a yi? (b) su tallafa wa aikin Jehobah?

7 A Littafi Mai Tsarki, mun koyi cewa bayin Allah sun ba da gudummawa sosai don tallafa wa aikinsa. A wasu lokuta suna ba da gudummawa don wani aikin da za a yi. Alal misali, kamar yadda Sarki Dauda ya yi sa’ad da ake so a gina haikali, Musa ma ya ƙarfafa Isra’ilawa su ba da gudummawa don a gina mazauni. (Fit. 35:5; 1 Laba. 29:​5-9) A zamanin Sarki Jehoash, firistoci sun yi amfani da kuɗin da aka ba da gudummawa don su yi wasu gyare-gyare a gidan Jehobah. (2 Sar. 12:​4, 5) Ban da haka ma, da aka gaya wa Kiristoci a ƙarni na farko cewa  wasu na fama da yunwa, ‘kowane mutum gwargwadon abin da ya iya, suka ƙudurta su aika gudummawa ga ’yan’uwa da ke zaune cikin Yahudiya.’​—A. M. 11:​27-30.

8 A lokacin, bayin Jehobah sun ba da gudummawar kuɗi don su tallafa ma waɗanda suke yin ja-goranci. Alal misali, a dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa, Lawiyawa ba sa samun gādo kamar sauran ƙabilu. A maimakon haka, Isra’ilawa ne suke ba su zakka kuma hakan ne ya taimaka wa Lawiyawan su mai da hankali ga aikin da suke yi a mazauni. (Lit. Lis. 18:21) Yesu da manzaninsa ma sun amfana daga alherin da matan da suka “yi musu hidima daga cikin dukiyarsu” suka nuna musu.​—Luk. 8:​1-3.

9. A waɗanne hanyoyi ne aka ba da gudummawa a zamanin dā?

9 Babu shakka, ana ba da gudummawa a hanyoyi dabam-dabam. A lokacin da Isra’ilawa suke jeji kuma suke so su ba da gudummawa don gina mazauni, wataƙila sun ba da abubuwan da suka kawo daga ƙasar Masar. (Fit. 3:​21, 22; 35:​22-24) A ƙarni na farko, wasu Kiristoci sun sayar da dukiyarsu kamar su filaye ko gidaje kuma suka kawo wa manzannin Yesu kuɗin. Manzannin kuma suka raba kuɗin ga mabukata. (A. M. 4:​34, 35) Wasu kuma sun ƙayyade gudummawar da za su riƙa bayarwa a kai a kai don su tallafa wa aikin. (1 Kor. 16:2) Don haka, masu arziki da talakawa duk sun tallafa wa aikin da aka yi.​—Luk. 21:​1-4.

YADDA MUKE BA DA GUDUMMAWA A YAU

10, 11. (a) Ta yaya za mu yi koyi da bayin Allah na zamanin dā? (b) Yaya tallafa wa ƙungiyar Jehobah take sa ka ji?

10 A yau, za a iya ƙarfafa mu mu ba da gudummawa don wani aikin da ake so a yi. Alal misali, wataƙila ikilisiyarku tana bukatar Majami’ar Mulki ko ana so a yi wasu gyare-gyare ko ana son a yi gyara a ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasarku. Ban da haka ma, wataƙila muna bukatar ba da gudummawan don babban taro ko kuma taimaka ma wasu ’yan’uwa da bala’i ta same su. Ƙari ga haka, muna ba da gudummawa don tallafa wa waɗanda suke yin aiki a hedkwatarmu da kuma wasu ofisoshinmu da ke ƙasashe dabam-dabam. Kuma ana yin amfani da gudummawar da muke bayarwa don a tallafa wa ’yan’uwan da suke yin wa’azi a wata ƙasa da majagaba na musamman da kuma masu kula da da’ira. Har ila, wataƙila ikilisiyarku ta yi alkawari cewa za ku riƙa tura kuɗi don tallafa wa aikin gina Majami’un Manyan Taro da kuma Majami’un Mulki don ’yan’uwa a dukan faɗin duniya su amfana.

11 Dukan mu za mu iya tallafa wa aikin da Jehobah yake son a yi a wannan kwanaki na ƙarshe. Yawancin masu ba da gudummawa ba sa son a san cewa su ne suka yi hakan. A duk lokacin da muke ba da gudummawar kuɗi a akwatunan da ke Majami’ar Mulki ko a dandalin jw.org, ba ma barin wasu su san yawan kuɗin da muka bayar. A wasu lokuta, muna iya jin kamar kyauta da muka bayar ya yi kaɗan. Amma a yau, yawancin gudummawar da muke samu daga ʼyan’uwa ne da ba su da kuɗi sosai, ba daga ʼyan’uwa ƙalilan da suke da kuɗi sosai ba. ’Yan’uwanmu, har da waɗanda ba su da arziki, suna kamar Makidoniyawa da suke cikin ‘talauci’ sosai, amma sun roƙa a ba su gatan ba da kyauta kuma suka yi hakan da zuciya ɗaya.​—2 Kor. 8:​1-4.

12. Ta yaya ƙungiyar Jehobah take yin iya ƙoƙarinta don a yi amfani da gudummawar da mutane suke bayarwa yadda ya dace?

12 Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana mai da hankali sosai ga yadda take amfani da gudummawar da ake bayarwa. (Mat. 24:45) Kuma ana tsara yadda za a yi amfani da dukan  gudummawar da mutane suke bayarwa. (Luk. 14:28) A zamanin dā, waɗanda suke adana kuɗin da aka keɓe don Ubangiji suna mai da hankali don su ga cewa an yi amfani da gudummawar don ayyukan ibada kaɗai. Alal misali, Ezra ya koma Urushalima da gudummawar zinariya da azurfa da kuma wasu abubuwan da sarkin Fasiya ya bayar kuma waɗannan abubuwan a yau sun kai dala miliyan ɗari. Ezra ya san cewa kuɗin, gudummawa ne ga Jehobah. Don haka, sa’ad da suke komawa ƙasarsu ta hanyoyi masu haɗari, ya yi iya ƙoƙarinsa don ya kāre kuɗin. (Ezra 8:​24-34) Manzo Bulus ma ya karɓi gudummawar kayan agaji da aka bayar don ’yan’uwan da ke Yahudiya. Kuma ya mai da hankali sosai don ya tabbatar da cewa waɗanda za su kai kayan sun yi “tattalin al’amuran da ke na kirki, ba gaban Ubangiji kaɗai ba, amma gaban mutane kuma.” (Karanta 2 Korintiyawa 8:​18-21.) Ƙungiyar Jehobah a yau tana bin misalin Ezra da Bulus ta wajen yin amfani da gudummawar da ake bayarwa a hanyar da ta dace.

13. Ta yaya ya kamata mu ɗauki canje-canje da ake yi a ƙungiyar Jehobah?

13 Iyalai suna iya canja salon rayuwarsu don kada su riƙa kashe fiye da kuɗin da suke samu. Ko kuma wataƙila su nemi hanyoyin sauƙaƙa rayuwarsu don su ƙara ƙwazo a hidimarsu ga Jehobah. Haka ma ƙungiyar Jehobah take yi a yau. A cikin ’yan shekaru da suka shige, an yi wasu ayyuka sosai. Kuma hakan a wasu lokuta ya sa an kashe kuɗi fiye da gudummawar da ake samu. Saboda haka, ƙungiyar Jehobah tana neman hanyoyin rage kuɗin da ake kashewa, kuma ta sauƙaƙa aikin don a iya yin ayyuka da yawa da suka shafi bautar Jehobah.

YADDA AKE AMFANI DA GUDUMMAWARKU

Gudummawarka tana taimaka wajen tallafa wa aikin da ake yi a faɗin duniya (See paragraph 7)

14-16. (a) Mene ne ake cim ma da gudummawarku? (b) Kuma ta yaya ka amfana daga waɗannan abubuwan?

14 Mutane da yawa da suka daɗe suna bauta wa Jehobah sun ce ba su taɓa ganin lokaci kamar yanzu ba. Me ya sa? Don muna da abubuwa da yawa da za su sa mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah sosai fiye da dā. Alal misali, a cikin ’yan shekaru da suka shige, mun soma amfani da dandalin jw.org da kuma Tashar JW. Ban da haka ma, an fassara New World Translation of the Holy Scriptures zuwa yaruka da yawa. Ƙari ga haka, a shekara ta 2014 da 2015, an yi Taron Ƙasashe mai jigo “Ku Riƙa Biɗan Mulkin Allah Farko!” a filayen wasa mafi girma a birane 14 a faɗin duniya. Kuma waɗanda suka halarci taron nan sun yi farin ciki sosai.

 15 Mutane da yawa suna nuna godiyarsu don yadda suke amfana daga abubuwan da ƙungiyar Jehobah take tanadarwa. Alal misali, wasu ma’aurata da suke hidima a wata ƙasa a Asiya sun rubuto game da Tashar JW. Sun ce: “Muna yin hidima a wani ƙaramin birni. Saboda haka, a wasu lokuta mukan ji kamar ba mu da yawa. Amma da zarar mun kalli shirye-shiryen da ake yi a Tashar JW, hakan na tuna mana cewa muna da ’yan’uwa da yawa a faɗin duniya. ’Yan’uwa suna farin ciki don Tashar JW, kuma muna yawan jin yadda wasu suke faɗan hakan bayan sun gama kallon shirin a kowane wata. Shirin yana sa su kusaci mambobin Hukumar da ke Kula da Ayyukanmu. Kuma yanzu, alfaharin da suke yi cewa suna cikin ƙungiyar Jehobah ya fi na dā.”

16 A dukan duniya, ana shirin gina ko kuma yin wasu gyare-gyare a Majami’un Mulki kusan 2,500. Sa’ad da wata ikilisiya a ƙasar Honduras suka soma yin amfani da Majami’ar Mulki da aka gina musu, ’yan’uwan sun ce: “Muna farin ciki sosai cewa muna cikin ƙungiyar Jehobah kuma muna moran dangantaka da ’yan’uwa a faɗin duniya. Haka ne ya taimaka mana mu sami Majami’ar Mulki a yankinmu.” Kamar waɗannan ’yan’uwa, mutane da yawa suna nuna godiyarsu bayan sun karɓi Littafi Mai Tsarki ko kuma wasu littattafai da aka fassara a yarensu. Wasu kuma suna yin hakan bayan an taimaka musu da kayan agaji ko kuma sun ga sakamakon da ake samu don yin wa’azi da amalanke da kuma tebura a yankinsu.

17. Ta yaya muka san cewa Jehobah yana goyon bayan ƙungiyarsa a yau?

17 Mutane da yawa da ba sa bauta wa Jehobah ba za su fahimci yadda muke yin amfani da gudummawa da ake bayarwa don waɗannan ayyukan ba. Bayan shugaban wani babban kamfani ya je zagaya a wurin da ake buga littattafanmu, ya yi mamaki da ya ji cewa da gudummawa ake tallafa wa dukan aikin kuma ba a taɓa yin taro don neman kuɗin yin aikin ba. Ya ce bai yarda cewa gudummawa kaɗai muke amfani da ita wajen yin waɗannan ayyukan ba. Hakika, mun san cewa muna yin aikin ne don Jehobah yana goyon bayanmu.​—Ayu. 42:2.

ALBARKAR BA DA GUDUMMAWA

18. (a) Waɗanne albarka ne za mu samu idan muka ba da gudummawa don tallafa wa Mulkin Allah? (b) Kuma ta yaya za mu koya wa yara da kuma sababbi yin hakan?

18 Jehobah yana daraja mu sosai shi ya sa ya ba mu gatan tallafa wa aikinsa a yau. Ban da haka ma, ya ba mu tabbacin cewa zai yi mana albarka idan muka goyi bayan mulkinsa. (Mal. 3:10) Jehobah ya yi mana alkawarin cewa wanda yake ba da kyauta da zuciya ɗaya zai sami albarka. (Karanta Misalai 11:​24, 25.) Ban da haka ma, ba da kyauta yana sa mu farin ciki don Littafi Mai Tsarki ya ce, “bayarwa ta fi karɓa albarka,” wato sa farin ciki. (A. M. 20:35) Ta furucinmu da kuma misalinmu mai kyau, za mu iya taimaka wa yara da kuma sababbi su koyi ba da gudummawa domin yin hakan yana kawo albarka sosai.

19. Ta yaya wannan talifin ya ƙarfafa ka?

19 Jehobah ne ya ba mu kome da muke da shi. Kuma idan muka ba da gudummawa, hakan zai nuna cewa muna ƙaunar sa kuma muna godiya don abin da yake yi mana. (1 Laba. 29:17) A lokacin da Isra’ilawa suke ba da gudummawa don gina haikali, sun “yi murna, da shi ke sun bayar da yardan ransu, da sahihiyar zuciya suka yi baiko ga Ubangiji da yardan rai.” (1 Laba. 29:9) Bari mu ma mu ci gaba da yin farin ciki da kuma samun gamsuwa yayin da muke ba Jehobah kyauta daga abubuwan da ya ba mu.