“Za ku ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye.”​—MAL. 3:​18, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 127, 101

1, 2. Wane ƙalubale ne bayin Allah suke fuskanta a yau? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

MA’AIKATAN kiwon lafiya da yawa suna kula da mutanen da ke fama da cututtukan da za a iya kamuwa da su. Suna wannan aikin domin suna so su taimaka wa mutanen. Duk da haka, suna bukatar su kāre kansu don kada su kamu da cutar da suke neman su warkar. Hakazalika, yawancinmu muna cuɗanya da mutanen da ke da munanan halaye kuma hakan ƙalubale ne sosai a gare mu.

2 A wannan kwanaki na ƙarshe da muke rayuwa a ciki, lokaci ne da halayen mutane sun lalace sosai. A wasiƙa ta biyu da Manzo Bulus ya rubuta wa Timotawus, ya bayyana halayen da mugayen mutane za su kasance da su. Ya ce za a fi kasancewa da halayen a kwanaki na ƙarshe. (Karanta 2 Timotawus 3:​1-5, 13.) Ko da yake za mu iya yin mamaki idan muka ga mutane suna nuna waɗannan halayen, amma idan ba mu yi hankali ba, za mu iya kamuwa da su. (Mis. 13:20) A wannan talifin, za mu tattauna yadda waɗannan mugayen halayen suka bambanta da halayen da bayin Allah za su kasance da su. Za mu kuma tattauna yadda za mu kāre kanmu daga kamuwa da  waɗannan halayen yayin da muke taimaka wa mutane su zama bayin Jehobah.

3. Su waye ne suke nuna halayen da aka ambata a 2 Timotawus 3:​2-5?

3 Manzo Bulus ya ce abubuwa za su yi wuya sosai a “cikin kwanaki na ƙarshe.” Bayan haka, sai ya faɗi munanan halaye guda 19 da mutane za su kasance da su a lokacin. Waɗannan halayen kusan ɗaya ne da waɗanda ke littafin Romawa 1:​29-31. Amma akwai wasu halayen da Bulus ya ambata a wasiƙarsa ga Timotawus da a ayoyin ne kaɗai aka ambata a Nassosin Helenanci na Kirista. Bulus ya soma ambata halayen da furucin nan “gama mutane za su zama . . . ” Furucin nan “mutane” yana nufin cewa maza da mata ne suke da halayen. Amma ba kowa ne ke da halayen ba. Halayen Kiristoci sun bambanta sosai da waɗannan.​—Karanta Malakai 3:18.

YADDA MUKE ƊAUKAN KANMU

4. Yaya za ka kwatanta masu girman kai?

4 Bayan Bulus ya faɗa cewa mutane za su zama masu son kansu da kuma kuɗi, ya ƙara da cewa za su zama masu ruba, masu girman kai da kuma masu kumbura. Waɗannan halaye ne da mutane suke nunawa saboda matsayinsu ko iyawarsu ko kuma siffarsu. Irin mutanen nan suna so a riƙa sha’awarsu da kuma bauta musu. Ga abin da wani malami ya ce game da masu girman kai: “Suna gina bagadi a cikin zuciyarsu kuma suna bauta wa kansu a bagadin.” Wasu sun ce girman kai yana da ƙyama sosai har masu girman kai ma sun tsani mutanen da ke hakan.

5. Ta yaya wasu bayin Allah suka yi girman kai?

5 Jehobah ya tsani masu girman kai. Ƙari ga haka, ya tsani masu “kallon reni.” (Mis. 6:​16, 17, Juyi Mai Fitar da Ma’ana) Girman kai yana hana mutane kusantar Allah. (Zab. 10:4) Shaiɗan ne uban masu girman kai. (1 Tim. 3:6) Amma har wasu bayin Jehobah ma sun kamu da wannan halin kuma hakan abin baƙin ciki ne sosai. Ɗaya daga cikinsu shi ne sarki Uzziah na Yahudiya. Uzziah ya yi shekaru da yawa yana bauta wa Jehobah. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce sa’ad da “ya yi ƙarfi, zuciyarsa ta habaka, ya kuwa jawo halakarsa, ya saɓi Ubangiji, Allahnsa; har ya shiga cikin haikalin Ubangiji garin shi ƙona turare a bisa bagadin turare.” Sarki Hezekiya ma ya yi girman kai amma ya canja daga baya.​—2 Laba. 26:16; 32:​25, 26.

6. Me Dauda yake da shi da zai iya sa shi girman kai, amma me ya sa bai yi hakan ba?

6 Wasu mutane suna girman kai domin suna da kyau sosai ko farin jini ko ƙarfi ko babban matsayin ko kuma sun iya waƙa. Sarki Dauda yana da abubuwan nan duka, amma, ya kasance da sauƙin kai muddar ransa. Bayan Dauda ya kashe Goliyat, an ba shi ’yar sarki Saul ya aura. Amma Dauda ya ce: “Wane ni, me ke gareni kuma, mene ne gidan ubana kuma cikin Isra’ila da zan zama surukin sarki?” (1 Sam. 18:18) Mene ne ya taimaka wa Dauda ya kasance da sauƙin kai? Allah ne ya sa Dauda ya sami halaye masu kyau da iyawa da kuma arziki. Kuma ‘ƙasƙantar da kai,’ ko kuma sauƙin kai da Allah ya nuna ne ya sa ya lura da Dauda har ya albarkace shi. (Zab. 113:​5-8) Dauda ya san cewa Jehobah ne ya ba shi dukan abubuwan da yake da shi.​—Ka gwada 1 Korintiyawa 4:7.

7. Me zai taimaka mana mu nuna sauƙin kai?

7 Bayin Allah a yau suna da sauƙin kai kamar Dauda. Mun san cewa Jehobah Mafi girma a sama da ƙasa yana da sauƙin kai kuma hakan na da ban sha’awa. (Zab. 18:35) Muna la’akari sosai a kan  shawarar nan: “Ku yafa zuciya ta tausayi, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa.” (Kol. 3:12) Mun kuma san cewa ƙauna “ba ta yin fahariya, ba ta yin kumbura.” (1 Kor. 13:4) Idan muna da sauƙin kai, hakan zai iya sa mutane su soma bauta wa Jehobah. Kamar yadda hali mai kyau na mace zai iya sa mijinta ya soma bauta wa Allah, hakan ma kasancewa da sauƙin kai zai iya sa wasu su soma bauta wa Allah.​—1 Bit. 3:1.

YADDA MUKE BI DA MUTANE

8. (a) Ta yaya mutane a yau suke ɗaukan yin biyayya ga iyaye? (b) Mene ne Nassosi suka shawarci yara su riƙa yi?

8 Bulus ya bayyana yadda mutanen da ke rayuwa a kwanaki na ƙarshe za su riƙa bi da juna. Ya ce a kwanaki na ƙarshe, yara za su zama marasa-bin iyaye. Ko da yake ana yawan ɗaukaka hakan a littattafai da fina-finai da kuma shirye-shiryen talabijin, amma rashin biyayya ga iyaye yana ɓata gamin iyali wanda shi ne tushen al’umma. ʼYan Adam sun daɗe da sanin wannan gaskiyar. Alal misali, a ƙasar Helas a zamanin dā, idan wani ya bugi iyayensa, ana janye ’yancinsa gabaki ɗaya. Romawa kuma sun kafa doka cewa duk wanda ya bugi mahaifinsa ya yi laifin mai tsanani kamar kisa. Nassosin Ibrananci da kuma Nassosin Helenanci na Kirista sun shawarci yara su riƙa yin biyayya ga iyayensu.​—Fit. 20:12; Afis. 6:​1-3.

9. Mene ne zai iya taimaka wa yara su yi biyayya ga iyayensu?

9 Yara za su iya kāre kansu daga munanan halaye ta wajen yin la’akari da abin da iyayensu suka yi musu. Idan mun fahimci cewa Allah wanda shi ne Ubanmu yana so mu riƙa biyayya, hakan zai taimaka mana mu riƙa biyayya. Idan yara ba sa yin baƙar magana game da iyayensu, hakan zai sa wasu yara su bi misalinsu. Hakika, idan iyaye ba sa ƙaunar yaransu, zai yi wuya yaran su yi musu biyayya da zuciya ɗaya. Amma idan yaro ya lura cewa iyayensa na ƙaunarsa da gaske, hakan zai motsa shi ya yi abubuwan da za su faranta musu rai ko da yin hakan na da wuya. Wani mai suna Austin ya ce: “Sa’ad da na ƙarya dokokin iyayena, ba na son su yi mini horo, amma suna gaya mini dalilan da ya sa suka kafa dokokin kuma suna hakan da fara’a. Hakan ya taimaka mini in riƙa yin biyayya. Na gane sarai cewa suna ƙauna ta kuma haka ya sa ina son yi musu biyayya.”

10, 11. (a) Waɗanne munanan halaye ne za su nuna cewa mutane ba sa ƙaunar wasu? (b) Ka bayyana irin ƙaunar da Kiristoci na gaskiya za su riƙa ma wasu.

10 Bulus ya ambata wasu munanan halayen da suka nuna cewa mutane ba sa ƙaunar juna. Shi ya sa aka ambata marasa-godiya bayan “marasa-bin iyaye,” domin hakan yana kwatanta halayen mutanen da ba sa daraja alherin da wasu suka nuna musu. Ƙari ga haka, mutane za su zama marasa-tsarki. Za su zama masu-baƙar zuciya, wato su ƙi sasantawa da wani da ya yi musu laifi. Za su kuma zama masu-zagi da masu-cin amana, mutanen da za su riƙa zagin Allah da kuma wasu. Bugu da ƙari, mutane za su zama masu-tsegumi, wato mutanen da za su riƙa yaɗa labaran da za su ɓata sunan wasu. *

11 Bayin Jehobah a yau suna ƙaunar mutane sosai kuma hakan ya bambanta su da mugayen mutanen da suka cika ko’ina. Sun daɗe suna nuna wannan halin. Yesu ya ce dokar da ta fi wadda ta ce mu riƙa ƙaunar mutane, wato a·ga’pe  girma, ita ce mu riƙa ƙaunar Allah. (Mat. 22:​38, 39) Ya kuma ce yadda Kiristoci suke ƙaunar juna ne zai sa a san cewa su bayin Allah ne. (Karanta Yohanna 13:​34, 35.) Ƙari ga haka, Kiristoci na gaskiya za su riƙa ƙaunar maƙiyansu.​—Mat. 5:​43, 44.

12. Ta yaya Yesu ya nuna ƙauna ga mutane?

12 Yesu ya ƙaunaci mutane sosai. Ya je birane dabam-dabam yana wa mutane wa’azi game da Mulkin Allah. Ya warkar da makafi da guragu da kutare da kurame, kuma ya ta da matattu. (Luk. 7:22) Ƙari ga haka, ya mutu domin mutane su sami rai ko da yake da yawa cikinsu sun tsane shi. Yesu nuna ƙauna sosai kamar Ubansa. Hakazalika, Shaidun Jehobah a faɗin duniya suna nuna ƙauna ga mutane.

13. Ta yaya ƙaunar da muke nuna ma wasu zai taimaka musu su bauta wa Jehobah?

13 Idan muka nuna ƙauna ga mutane, hakan zai iya motsa su su bauta wa Jehobah. Alal misali, wani mutum a ƙasar Thailand ya halarci taron yanki, kuma yadda ʼyan’uwa suke nuna ƙauna ga juna ya ratsa zuciyarsa. Da ya koma gida, sai ya ce Shaidun Jehobah su riƙa nazari da shi sau biyu a mako. Ya yi wa dukan danginsa wa’azi, kuma wata shida bayan taron, an ba shi karatun Littafi Mai Tsarki a Majami’ar Mulki. Idan muna so mu san ko muna nuna ƙauna ga wasu, zai dace mu yi wa kanmu waɗannan tambayoyin: ‘Ina yin iya ƙoƙarina wajen taimaka wa dangina da mutane a ikilisiya da kuma a yankinmu? Ina ɗaukan mutane yadda Jehobah yake ɗaukansu?’

KERKECI DA ƊAN RAGO

14, 15. Waɗanne halaye irin na dabbobi ne mutane da yawa suke da shi a yau, amma ta yaya wasu suka yi canji?

14 Akwai wasu halaye kuma da mutane suke nunawa a wannan zamanin da ya kamata mu guje musu. Alal misali, mutane da yawa marasa-son nagarta ne, ko kuma “masu ƙin nagarta” in ji wasu juyin Littafi Mai Tsarki. Irin mutanen nan marasa-kamewa ne da masu-zafin hali. Wasu za su zama masu-taurin kai, wato za su riƙa  ɗaukan mataki ba tare da sun yi tunani sosai a kai ba.

15 Mutane da yawa da suke da halayen dabbobi a dā sun yi canji. An annabta irin waɗannan canje-canjen a cikin Littafi Mai Tsarki. (Karanta Ishaya 11:​6, 7.) Annabcin ya ce namomin daji kamar su kerkeci da zakuna, za su zauna lafiya da dabbobi kamar su ɗan rago da ɗan maraƙi. Me zai taimaka musu su zauna da juna cikin lumana? Littafi Mai Tsarki ya ce domin “duniya za ta cika da sanin Ubangiji, kamar yadda ruwaye suke rufe teku.” (Isha. 11:9) Dabbobi ba sa koya game da Jehobah. Saboda haka, wannan annabcin yana cika a kan ʼyan Adam a alamance domin suna canja halayensu.

Bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki yana gyara rayuwar mutane! (Ka duba sakin layi na 16)

16. Ta yaya Littafi Mai Tsarki yake taimaka wa mutane su yi canje-canje?

16 Akwai mutane da yawa a dā da suke da ban-tsoro kamar zakuna, amma a yau suna zaman lafiya da mutane. Za ku iya karanta labaransu a cikin talifofin nan “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” a jw.org/ha. Mutanen da suke bauta wa Jehobah a yau ba sa kamar mutanen da suke riƙe da surar ibada, amma sun musunci ikonta. Irin mutanen nan suna yi kamar suna bauta wa Allah, amma halayensu na nuna cewa hakan ƙarya ne. Akasin haka, mutane masu zafin hali a dā sun “yafa sabon mutum, wanda an halitta shi bisa ga Allah cikin adalci da tsarkin gaskiya.” (Afis. 4:​23, 24) Yayin da mutane suke koya game da Allah, suna gani cewa suna bukatar su bi ƙa’idodinsa a rayuwarsu. Hakan na motsa su su yi canje-canje a imaninsu da ayyukansu da kuma halayensu. Yin waɗannan canje-canjen ba wasan yara ba ne. Amma ruhu mai tsarki zai taimaka wa mutanen da suke so su yi nufin Allah su yi hakan.

“DAGA WAJEN WAƊANNAN KUMA SAI KA BIJIRE”

17. Me zai taimaka mana don kada mu kamu da munanan halaye?

17 A yau, ba shi da wuya sosai a ga bambanci tsakanin masu bauta wa Allah da kuma waɗanda ba sa bauta masa. Ya kamata mu da ke bauta wa Allah mu yi hankali don kada mu kamu da halayen mugayen mutane. Shi ya sa ya kamata mu bijire, wato mu nisanta kanmu daga halayen da aka ambata a littafin 2 Timotawus 3:​2-5. Ko da yake ba zai yiwu mu nisanta kanmu gabaki ɗaya daga mugayen mutane ba. Wasu cikinsu abokan aikinmu ne ko abokan makaranta ko kuma maƙwabtanmu. Amma za mu iya nisanta kanmu daga kamuwa da irin tunaninsu da kuma munanan halayensu. Me zai taimaka mana mu yi hakan? Ƙarfafa abotarmu da Jehobah ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki da yin tarayya da mutanen da suka duƙufa su riƙa bauta wa Jehobah ne zai taimaka mana.

18. Ta yaya furucinmu da halayenmu za su iya taimaka ma wasu su soma bauta wa Jehobah?

18 Ya kamata mu taimaka wa mutane su san Jehobah. Ka riƙa neman zarafin yi musu wa’azi kuma ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka faɗi abin da zai ratsa zuciyarsu. Mu riƙa sa mutane su san cewa mu Shaidun Jehobah ne. Idan muna yin haka, halayenmu masu kyau za su ɗaukaka Allah ba kanmu ba. Jehobah ya koya mana mu riƙa ƙin “rashin bin Allah da mugayen sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi zamanmu a duniyan nan da natsuwa, da adalci, da kuma bin Allah.” (Tit. 2:​11-14, LMT) Idan muna yin abubuwan da suka dace, wasu za su lura da hakan kuma za su iya ce mana: “Za mu tafi tare da ku, gama mun ji labari Allah yana tare da ku.”​—Zak. 8:23.

^ sakin layi na 10 A Helenanci, furucin nan “mai-tsegumi” ko “mai zargi” di·aʹbo·los ne, kuma Shaiɗan ne ake kira da wannan sunan a cikin Littafi Mai Tsarki don yana ɓata sunan Allah.