Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro (Ta Nazari)  |  Janairu 2016

Ka Nuna Godiya ga Allah Saboda “Kyautarsa Wadda Ta Fi Gaban Magana”

Ka Nuna Godiya ga Allah Saboda “Kyautarsa Wadda Ta Fi Gaban Magana”

“Godiya ga Allah domin kyautarsa wadda ta fi gaban magana.”2 KORINTIYAWA 9:15.

WAƘOƘI: 121, 63

1, 2. (a) Mece ce ‘kyautar [Allah] wadda ta fi gaban magana’ ta ƙunsa? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?

JEHOBAH ya ba mu kyauta mafi kyau sa’ad da ya aiko da Ɗansa Yesu ƙaunatacce, ya zo duniya! (Yohanna 3:16; 1 Yohanna 4:9, 10) Manzo Bulus ya kira ta ‘kyauta wadda ta fi gaban magana.’ (2 Korintiyawa 9:15) Me ya sa Bulus ya yi amfani da wannan furucin?

2 Bulus ya san cewa hadayar da Yesu ya yi za ta sa Allah ya cika dukan alkawura da ya yi. (Karanta 2 Korintiyawa 1:20.) Hakan yana nufin cewa kyautar Allah wadda ta fi gaban magana ta ƙunshi hadayar da Yesu ya bayar da dukan nagarta da kuma ƙauna da Jehobah yake nuna mana. Ba za a iya kwatanta amfanin wannan kyautar a hanyar da za mu iya fahimta sosai ba. Yaya ya kamata mu ji game da wannan kyauta ta musamman? Ta yaya wannan kyautar za ta sa mu kasance a shirye don taron Tuna Mutuwar Yesu a ranar Laraba, 23 ga Maris, 2016?

 KYAUTA TA MUSAMMAN DA ALLAH YA BA MU

3, 4. (a) Yaya kake ji sa’ad da wani ya ba ka kyauta? (b) Ta yaya babban alheri da wani ya yi maka zai iya canja rayuwarka?

3 Muna farin ciki sosai idan wani ya ba mu kyauta. Amma wasu kyauta suna da tamani sosai don sukan yi tasiri sosai a rayuwarmu. Alal misali, a ce ka yi wani laifi kuma za a yi maka hukuncin kisa don hakan. Amma, farat ɗaya, wani da ba ka sani ba ya ce a hukunta shi a madadinka. Yana a shirye ya mutu domin ka! Ta yaya wannan alheri na musamman zai sa ka ji?

4 Irin wannan alheri na musamman zai sa ka yi gyara a rayuwarka. Wataƙila hakan zai motsa ka ka ƙara nuna wa mutane karimci da ƙauna kuma ka gafarta wa kowanne mutum da ya yi maka laifi. A dukan rayuwarka, za ka riƙa nuna godiya don hadaya da aka yi maka.

5. Ta yaya kyautar hadaya da Allah ya bayar ta fi kowace kyauta tamani?

5 Kyautar hadaya da Allah ya ba mu ta fi kyautar da aka ambata a wannan misalin. (1 Bitrus 3:18) Ka yi tunanin wannan: Dukanmu mun gaji zunubi daga Adamu, kuma hukuncin zunubi shi ne mutuwa. (Romawa 5:12) Ƙauna ce ta sa Jehobah ya aiko da Yesu zuwa duniya don ya mutu a madadin ‘yan Adam, wato “ya ɗanɗana mutuwa sabili da kowane mutum.” (Ibraniyawa 2:9) Ban da wannan akwai wasu amfani da za mu samu daga hadayar da Yesu ya ba da! Za ta sa a kawo ƙarshen mutuwa. (Ishaya 25:7, 8; 1 Korintiyawa 15:22, 26) Dukan waɗanda suka ba da gaskiya ga Yesu za su yi zaman lafiya kuma su yi farin ciki har abada, wasu a cikinsu za su yi sarauta a matsayin sarakuna da Kristi a sama ko kuma talakawan Mulkin Allah a duniya. (Romawa 6:23; Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10) Wane albarka ne wannan alherin da Jehobah ya yi mana zai sa mu samu?

6. (a) Waɗanne abubuwa ne da za mu samu saboda alherin Jehobah kake marmarinsa? (b) Ka ambata abubuwa uku da kyautar Allah za ta motsa mu mu yi.

6 Alherin da Allah zai yi mana ta ƙunshi sa duniya ta zama aljanna da warkar da masu ciwo da kuma ta da matattu daga mutuwa. (Ishaya 33:24; 35:5, 6; Yohanna 5:28, 29) Muna ƙaunar Jehobah da kuma Ɗansa ƙaunatacce don sun ba mu wannan kyautar “wadda ta fi gaban magana.” Mene ne wannan kyautar za ta motsa mu mu yi? Za ta motsa mu (1) mu yi koyi da Yesu Kristi sosai, (2) mu ƙaunaci ‘yan’uwanmu, da kuma (3) gafarta wa mutane da dukan zuciyarmu.

“ƘAUNAR KRISTI” TANA MOTSA MU MU YI KOYI DA SHI

7, 8. Ta yaya ya kamata mu ji game da ƙaunar da Kristi ya nuna mana, mene ne hakan zai motsa mu mu yi?

7 Da farko ya kamata hakan ya motsa mu yi amfani da rayuwarmu don mu ɗaukaka Yesu. Manzo Bulus ya ce: “Ƙaunar Kristi” tana motsa mu mu yi koyi da shi. (Karanta 2 Korintiyawa 5:14, 15.) Bulus ya san cewa idan muka amince da ƙaunar Yesu, hakan zai motsa mu mu ƙaunaci da kuma ɗaukaka Yesu. Hakika, idan muka fahimci abin da Jehobah ya yi mana da kyau, ƙaunarsa za ta motsa mu yi rayuwa a hanyar da ke girmama Yesu. Ta yaya za mu yi hakan?

8 Ƙaunar Jehobah za ta motsa mu mu yi koyi da misalin Yesu, wato mu bi sawunsa sosai. (1 Bitrus 2:21; 1 Yohanna 2:6) Idan muka yi biyayya da Allah da kuma Kristi, muna nuna cewa muna ƙaunarsu sosai.  Yesu ya ce: “Wanda yake da dokokina, yana kuwa kiyaye su, shi ne yana ƙaunata: wanda yana ƙaunata kuma za ya zama ƙaunatacen Ubana, ni ma zan ƙaunace shi, in bayyana kaina gareshi kuma.”Yohanna 14:21; 1 Yohanna 5:3.

9. Wane irin matsi ne muke fuskanta?

9 A wannan lokacin Tuna da Mutuwar Yesu, yana da kyau mu yi bimbini a kan yadda muke amfani da rayuwarmu. Saboda haka, ka tambayi kanka: ‘A waɗanne wurare ne nake yin koyi da Yesu? A waɗanne wurare ne nake bukata na yi gyara?’ Yana da muhimmanci mu yi wa kanmu waɗannan tambayoyin domin mutanen duniya suna so mu yi irin rayuwa da suke yi. (Romawa 12:2) Idan ba mu mai da hankali ba, za su matsa mana mu soma yin koyi da malaman duniya da shahararrun ‘yan wasa da kuma zakarun wasanni. (Kolosiyawa 2:8; 1 Yohanna 2:15-17) Ta yaya za ka yi tsayayya da wannan matsin?

10. Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi wa kanmu a lokacin Tuna Mutuwar Yesu, kuma mene ne amsoshin za su motsa mu mu yi? (Ka duba hoton da ke shafi na 9.)

10 Yana da kyau mu keɓe lokaci don mu duba tufafin da muke sakawa da fina-finai da kaɗe-kaɗe da kuma abin da ke cikin kwamfutarmu da wayar selula ko kuma kwamfutar hannu a lokacin Tuna Mutuwar Yesu. Ka tambayi kanka: ‘Zan ji kunya ne idan Yesu yana nan kuma ya ga rigar da na saka?’ (Karanta 1 Timotawus 2:9, 10.) ‘Shin rigar da na saka za ta nuna cewa ni mai bin Kristi ne? Shin Yesu zai so ya kalli fina-finai da nake kallo? Shin zai saurari kiɗa da nake ji? Idan Yesu ya ari wayata ko kuma kwamfutar hannuna, shin zan ji kunya don abin da zai gani a ciki? Shin zai yi mini wuya in bayyana wa Yesu dalilin da ya sa nake jin daɗin wasannin bidiyo da nake yi?’ Ƙaunar da muke wa Jehobah za ta motsa mu mu kawar da dukan abin da bai dace Kirista ya yi amfani da shi ba, ko da mun sayi abin da tsada sosai. (Ayyukan Manzanni 19:19, 20) Mun yi alkawari za mu yi amfani da rayuwarmu don mu ɗaukaka Kristi sa’ad da muka keɓe kanmu ga Jehobah. Saboda haka, bai kamata mu kasance da kome da zai sa ya yi mana wuya mu yi koyi da Yesu ba.Matta 5:29, 30; Filibiyawa 4:8.

11. (a) Ta yaya yadda muke ƙaunar Jehobah da Yesu take motsa mu mu yi wa’azi? (b) Ta yaya ƙauna take motsa mu mu taimaka wa mutane a cikin ikilisiya?

11 Ƙaunarmu ga Yesu za ta motsa mu mu yi wa’azi da kuma koyar da mutane da ƙwazo. (Matta 28:19, 20; Luka 4:43) A lokacin Tuna Mutuwar Yesu, shin za ka shirya ayyukanka don ka yi hidimar majagaba na ɗan lokaci kuma ka ba da awoyi 30 ko 50 a yin wa’azi? Wani ɗan’uwa mai shekara 84, da matarsa ta rasu yana ganin ba zai iya yin majagaba ba don ya tsufa kuma yana rashin lafiya. Amma majagaba da suke yankinsa suna son su taimaka masa. Sun yi masa tanadin mota kuma suka zaɓi yankin da ya dace da zai yi wa’azi a ciki. Hakan ya sa ɗan’uwan ya cim ma burinsa na samun awoyi 30. Shin za ka iya taimaka wa wani a ikilisiyarku ya yi hidimar majagaba na ɗan lokaci a watan Maris ko Afrilu? Hakika ba kowa ba ne zai iya yin hidimar majagaba, amma za mu iya yin amfani da lokacinmu da kuzarinmu don mu ƙara hidimarmu ga Jehobah. Kamar Bulus, idan muka yi hakan, za mu nuna cewa ƙaunar Yesu ce take motsa mu. Wane abu ne ƙauna ga Allah za ta ƙara motsa mu mu yi?

 WAJIBI NE MU ƘAUNACI JUNA

12. Mene ne ƙaunar Allah take motsa mu mu yi?

12 Na biyu, ya kamata ƙaunarmu ga Allah ta motsa mu mu ƙaunaci ‘yan’uwanmu. Manzo Yohanna ya ce: “Masoya, idan Allah ya ƙaunace mu haka nan, ya kamata mu kuma mu yi ƙaunar junanmu.” (1 Yohanna 4:7-11) Saboda haka, idan muka fahimci abin da ƙaunar Allah take nufi sosai, muna bukatar mu ƙaunaci ‘yan’uwanmu. (1 Yohanna 3:16) Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunarsu?

13. Wane misali ne Yesu ya ƙafa don yana ƙaunar mutane?

13 Misalin da Yesu ya kafa ya nuna mana yadda za mu ƙaunaci wasu. Sa’ad da yake duniya, ya taimaka wa mutane, musamman ma masu tawali’u. Ya warkar da masu ciwo da guragu da makafi da kurame da kuma bebe. (Matta 11:4, 5) Ba kamar shugabanan addinai ba, Yesu ya ji daɗin koyar da mutane da suke son su san game da Allah. (Yohanna 7:49) Ya ƙaunaci masu tawali’u kuma ya yi ƙoƙari sosai don ya taimaka musu.Matta 20:28.

Shin za ka iya taimaka wa tsofaffi a hidima? (Ka duba sakin layi na 14)

14. Mene ne za ka yi don ka nuna kana ƙaunar ‘yan’uwanka?

14 A lokacin Tuna Mutuwar Yesu, yana da kyau ka yi tunanin yadda za ka taimaka wa ‘yan’uwa da ke cikin ikilisiyarku, musamman ma tsofaffi. Shin za ka iya kai musu ziyara? Za ka iya dafa musu abinci da taimaka musu da aikace-aikacen gida da kuma kai su taro ko kuma ka gayyace su su fita wa’azi tare da kai? (Karanta Luka 14:12-14.) Bari ƙaunar Allah ta motsa ka ka riƙa ƙaunar ‘yan’uwanka!

MU RIƘA GAFARTA WA ‘YAN’UWANMU

15. Mene ne ya zama wajibi mu sani?

15 Na uku, ƙaunar Jehobah tana motsa mu mu gafarta wa ‘yan’uwanmu. Dukanmu mun gāji zunubi da mutuwa daga Adamu, saboda haka ba wanda zai ce “Ba na bukatar fansa.” Har bawan Allah mai aminci sosai ma yana bukatar fansa. An gafarta wa kowannenmu bashi mai yawa! Me ya sa yake da muhimmanci mu san da hakan? Amsar tana cikin wani kwatanci da Yesu ya ba da.

16, 17. (a) Mene ne ya kamata mu koya daga kwatancin da Yesu ya bayar game da wani sarki da kuma bayinsa? (b) Bayan mun yi bimbini a kan kwatancin Yesu, mene ne ka kuɗiri niyyar yi?

16 Yesu ya ba da kwatancin wani sarki da ya yafe wa bawansa bashin dinari miliyan 60. Amma, daga baya wannan bawan bai gafarta wa bawa ɗan’uwansa da yake bin sa bashin dinari 100 kawai ba. Ya kamata wannan bawan ya ji tausayin ɗayan bawan kamar yadda sarki ya ji tausayinsa. Sarkin ya yi fushi sosai sa’ad da ya ji labarin cewa bawan bai gafarta wa abokin bautarsa ɗan bashin nan ba. Sai ya ce: “Kai mugun bawa ne! Na yafe maka duk bashin nan saboda ka roƙe ni, ashe, bai kyautu kai ma ka ji tausayin abokin bautarka, kamar yadda na ji tausayinka ba?” (Mat. 18:23-35, Littafi Mai Tsarki.) Kamar wannan sarkin, Jehobah  ya gafarta mana bashi mai yawa sosai. Mene ne ya kamata ƙaunar Jehobah da jin kansa su motsa mu mu yi?

17 Yayin da muke shirin Tuna Mutuwar Yesu, ya kamata mu tambayi kanmu: ‘Wani ɗan’uwa ya ɓata mini rai ne? Shin yana mini wuya na gafarta masa?’ Idan haka ne, ya kamata mu yi koyi da Jehobah “mai-hanzarin gafartawa” a wannan lokacin Tuna Mutuwar Yesu. (Nehemiya 9:17; Zabura 86:5) Idan muna godiya don jin kan da Jehobah ya yi mana, za mu nuna wa mutane jin kai kuma mu gafarta musu da dukan zuciyarmu. Idan ba ma ƙaunar ‘yan’uwanmu da kuma gafarta musu, Jehobah ba zai ƙaunace mu ba kuma ba zai gafarta mana ba. (Matta 6:14, 15) Idan muka gafarta wa mutane, hakan ba ya nufin cewa ba su ɓata mana rai ba, amma zai taimake mu mu yi farin ciki a nan gaba.

18. Ta yaya ƙaunar Allah ta taimaka wa wata ‘yar’uwa ta riƙa haƙuri da wata ‘yar’uwarta Kirista?

18 Ba shi da sauƙi mu jimre da ajizancin ‘yan’uwanmu. (Karanta Afisawa 4:32; Kolosiyawa 3:13, 14.) Wata ‘yar’uwa mai suna Lily ta yi hakan. [1] (Ka duba ƙarin bayani.) Ta taimaka wa wata gwauruwa mai suna Carol. Alal misali, tana tuƙa Carol zuwa duk inda za ta je kuma ta taimaka mata da wasu sayayya. Ƙari ga haka ta yi mata wasu abubuwa da yawa. A kowane lokaci, Carol tana zargin Lily duk da cewa tana taimaka mata sosai, kuma a wasu lokatai ba shi da sauƙi ta taimaka wa Carol. Duk da haka, Lily ta mai da hankali ga halayen Carol masu kyau kuma ta taimaka mata sosai har Carol ta soma rashin lafiya mai tsanani kuma ta rasu. Duk da cewa ba shi sauƙi ta taimaki Carol, Lily ta ce game da ita: “Ina ɗokin ganin Carol sa’ad da ta tashi daga mutuwa. Ina son in san ta sa’ad da ta zama kamila.” Hakika, ƙaunar Allah za ta motsa mu mu jimre da ‘yan’uwanmu kuma mu saurari lokacin da ajizanci ba zai ƙara kasancewa ba.

19. Mene ne kyautar Allah “wadda ta fi gaban magana” za ta motsa ka ka yi?

19 Hakika, Jehobah ya ba mu kyauta “wadda ta fi gaban magana.” Bari mu riƙa nuna godiya don hakan! A lokacin Tuna Mutuwar Yesu yana da kyau mu yi bimbini a kan dukan abubuwa da Jehobah da Yesu suka yi mana. Hakika, Jehobah da Yesu suna ƙaunar mu sosai. Saboda haka, bari mu yi koyi da Yesu sosai don mu ƙaunaci ‘yan’uwanmu kuma mu gafarta musu da dukan zuciyarmu.

^ [1] (sakin layi na 18) An canja wasu sunaye a wannan talifin.