Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Su Wa Suke Yi wa Mutanen Allah Ja-gora a Yau?

Su Wa Suke Yi wa Mutanen Allah Ja-gora a Yau?

“Ku tuna da waɗanda suke shugabannanku.”IBRAN. 13:7.

WAƘOƘI: 125, 43

1, 2. Wane tunani ne manzanni suka yi bayan da Yesu ya koma sama?

MANZANNIN Yesu suna tsaye a Dutsen Zaitun, suna kallon sama sa’ad da ubangijinsu da abokinsu ya hau sama kuma gajimare suka rufe shi. (A. M. 1:9, 10) Yesu ya yi shekaru biyu yana koyar da su da ƙarfafa su da kuma yi musu ja-gora. Amma yanzu ya tafi sama. Me za su yi?

2 Kafin wannan lokaci, Yesu ya umurci mabiyansa cewa: “Za ku zama shaiduna kuma cikin Urushalima da cikin dukan Yahudiya da Samariya, har kuma iyakan duniya.” (A. M. 1:8) Ta yaya za su kammala aikin nan? Yesu ya tabbatar musu cewa ruhu mai tsarki zai taimaka musu. (A. M. 1:5) Duk da haka, yin wa’azi a dukan duniya yana bukatar ja-gora da kuma tsari. Jehobah ya yi amfani da mutane a zamanin dā wajen tsara da kuma ja-gorar mutanensa. Duk da haka, manzannin sun yi tunani, ‘Shin Jehobah zai naɗa sabon shugaba ne?’

3. (a) Wace shawara mai muhimmanci ce manzannin suka yanke bayan da Yesu ya koma sama? (b) Me za mu tattauna a wannan talifin?

3 Kusan makonni biyu bayan haka, almajiran Yesu sun bincika  Kalmar Allah, suka yi addu’a don Allah ya ja-gorance su kuma suka zaɓi Matiyas ya ɗauki matsayin Yahuda Iskariyoti. (A. M. 1:15-26) Me ya sa wannan zaɓin da suka yi yake da muhimmanci a gare su da kuma Jehobah? Don sun ga cewa Matiyas zai yi aiki mai muhimmanci a tsarin Allah. * Yesu ya zaɓi almajiransa ba don su riƙa wa’azi tare da shi kawai ba, amma don su yi wani aiki mai muhimmanci na taimaka wa mutanen Allah. Wane aiki ne kuma ta yaya Jehobah ya yi amfani da Yesu don ya taimaka musu? Wane tsari ne mutanen Allah suke bi a yau da ya yi kama da wanda Yesu ya kafa? Kuma ta yaya za mu ‘tuna da waɗanda suke shugabannanci’ a tsakaninmu, musamman ma waɗanda suke cikin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima”?Ibran. 13:7; Mat. 24:45.

YESU YANA WA HUKUMAR DA KE KULA DA ƘUNGIYAR JEHOBAH JA-GORA

4. Wane aiki ne manzanni da wasu dattawa a Urushalima suka yi a ƙarni na farko?

4 Manzannin sun soma ja-gorar ikilisiyar Kirista tun daga Fentakos 33 a zamaninmu. A wani lokaci, “Bitrus, tare da goma sha ɗayan nan a tsaye” suka koya wa mutane da yawa Kalmar Allah, wato Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba. (A. M. 2:14, 15) Kuma yawancinsu sun zama Kiristoci. Bayan haka, waɗannan sabbin Kiristoci sun “lizima a cikin koyarwar manzanni.” (A. M. 2:42) Manzannin ne suke tsara yadda za a yi amfani da kuɗaɗe a ikilisiyar Allah a lokacin. (A. M. 4:34, 35) Suna koyar da mutanen Allah kuma suka ce: “Za mu lizima kullayaumi ga addu’a da hidimar kalmar.” (A. M. 6:4) Kuma sun zaɓi ƙwararrun Kiristoci don su riƙa wa’azi a sababbin yankuna. (A. M. 8:14, 15) Bayan wani lokaci, sai wasu dattawa shafaffu suka soma taimaka wa manzannin wajen yanke shawarwari a ikilisiya. Da yake su suke ja-gora, su ne suke gaya wa ikilisiyoyi abin da ya kamata su yi.A. M. 15:2.

5, 6. (a) Ta yaya ruhu mai tsarki ya taimaka wa hukumar da ta kula da ikilisiyar Kirista a dā? (Ka duba hoton da ke shafi na 23.) (b) Ta yaya mala’iku suka taimaka wa hukumar a dā? (c) Ta yaya Kalmar Allah ta ja-goranci hukumar a dā?

5 Kiristoci a ƙarni na farko sun tabbata cewa Jehobah ne yake wa rukunin da ke kula da ikilisiya a lokacin ja-gora, amma yana amfani ne da Shugabansu Yesu Kristi. Ta yaya suka tabbatar da haka? Da farko, ruhu mai tsarki ya taimaka ma wannan rukunin. (Yoh. 16:13) An ba wa dukan shafaffun Kiristoci ruhu mai tsarki, musamman ma manzanni da wasu dattawa na Urushalima don su yi ja-gora. Alal misali, a shekara ta 49 a zamaninmu, ruhu mai tsarki ya taimaka wa rukunin da ke kula da ikilisiya wajen yanke shawara game da yin kaciya. Ikilisiyar ta bi wannan ja-gora kuma “suka ƙarfafa cikin imani, yawansu yana ƙaruwa kowace rana.” (A. M. 16:4, 5) Wasiƙar ta nuna cewa hukumar da ke kula da ikilisiyar tana da bangaskiya da kuma ƙauna.A. M. 15:11, 25-29; Gal. 5:22, 23.

6 Na biyu, mala’iku sun taimaka wa hukumar da ke kula da ikilisiyar. Kafin Karniliyus, Ba-al’umme marar kaciya ya yi baftisma, mala’ika ya ja-gorance shi ya kirawo manzo Bitrus don ya taimaka masa. Bayan da Bitrus ya yi wa Karniliyus da danginsa wa’azi, sai aka ba su ruhu mai tsarki ko da yake ba su yi kaciya ba. Wannan abin da ya faru ya sa manzanni da wasu ‘yan’uwa sun fahimci nufin Allah kuma suka yarda marasa kaciya su yi ibada tare da su a ikilisiyar Kirista. (A. M. 11:13-18) Ƙari ga haka, mala’iku sun taimaka wajen faɗaɗa wa’azin da hukumar da ke kula da ikilisiyar ta yi.  (A. M. 5:19, 20) Na uku, Kalmar Allah ta ja-goranci hukumar da ke kula da ikilisiyar. Wannan rukunin dattawa sun yi amfani da Kalmar Allah wajen yin ja-gora da kuma tsai da wasu shawarwari da suka shafi ikilisiyar.A. M. 1:20-22; 15:15-20.

7. Me ya sa za mu ce Yesu ne ya ja-goranci Kiristoci a ƙarni na farko?

7 Ko da yake rukuni da ke kula da ikilisiyar suna da iko bisa ikilisiyar, sun fahimci cewa Yesu ne Shugabansu. Manzo Bulus ya ce: Kristi “ya kuma ba da waɗansu su zama manzanni.” Kuma ya ƙara da cewa bari “mu yi girma cikin abu duka zuwa cikinsa, wanda shi ne kai, wato Kristi.” (Afis. 4:11, 15) Maimakon su riƙa kiran kansu da sunan wani manzo, sai aka fara kiransu ‘masu bin Kristi.’ (A. M. 11:26) A gaskiya, Bulus ya san muhimmancin ‘kiyaye koyarwa’ ko bin umurnin da manzanni da kuma wasu da suke ja-gora suka bayar. Duk da haka, ya daɗa da cewa: “Amma ina so ku sani, kan kowane namiji [har da kowane dattijo da ke cikin hukumar da ke kula da ƙungiyar Jehobah] Kristi ne; . . . kan Kristi kuma Allah ne.” (1 Kor. 11:2, 3) Babu shakka, Jehobah ne ya naɗa Yesu Kristi ya riƙa ja-gorar ikilisiya.

“WANNAN BA AIKIN ƊAN ADAM BA NE”

8, 9. Wane aiki na musamman ne Ɗan’uwa Russell ya yi?

8 A shekara ta 1870, ɗan’uwa Charles Taze Russell da wasu abokansa sun yi ƙoƙari su soma bauta wa Allah bisa ga koyarwar Littafi Mai Tsarki. Za su bukaci su taimaka wa mutane da suke harsuna dabam-dabam. Saboda haka, aka yi rajistan Zion’s Watch Tower Tract Society a shekara ta 1884, kuma Ɗan’uwa Russell ne shugaban. * Ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki sosai kuma bai ji tsoron gaya wa mutane cewa koyarwar coci kamar su Allah-Uku-Cikin ɗaya da kuma koyarwa cewa kurwa ba ta mutuwa ba su jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba. Ya fahimci cewa ba za a ga lokacin da Kristi zai dawo a zahiri ba da kuma cewa “zamanan Al’ummai” za su cika a shekara ta 1914. (Luk. 21:24) Ɗan’uwa Russell ya yi amfani da lokacinsa da ƙarfinsa da kuma kuɗinsa don ya koya wa mutane waɗannan abubuwan. A bayyane yake cewa Jehobah da Yesu sun yi amfani da Ɗan’uwa Russell don su ja-goranci ikilisiya a wannan lokaci mai muhimmanci a tarihi.

9 Ɗan’uwa Russell ba ya son mutane su ɗaukaka shi. A shekara ta 1896, ya rubuta cewa: “Ba ma son mutane su ɗaukaka mu ko kuma abubuwan da muke wallafawa, kuma ba ma son a ba mu laƙabi na musamman. Ƙari ga haka, ba ma son wani mutum ko rukuni ya ba wa kansa sunanmu.” Daga baya ya ce: “Wannan ba aikin ɗan Adam ba ne.”

10. (a) A wane lokaci ne Yesu ya naɗa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima”? (b) Ka bayyana yadda aka nuna cewa Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta bambanta da Watch Tower Society.

10 Bayan shekara uku da Ɗan’uwa Russell ya rasu a shekara ta 1919, Yesu ya naɗa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” Me ya sa? Don ya riƙa ba ‘yan gidansa “abincinsu a lotonsa.” (Mat. 24:45) A wannan lokacin, wani ƙaramin rukuni na ‘yan’uwa shafaffu da suke hidima a hedkwatarmu da ke Brooklyn, New York ne ke tanadin koyarwar Littafi Mai Tsarki ga mabiyan Yesu. An soma amfani da furucin nan “governing body” wato hukumar da ke kula da ayyukan Shaidun Jehobah a littattafanmu na Turanci bayan shekara ta 1940. A lokacin, an ɗauka cewa wannan hukumar ce darektocin Watch Tower Bible and Tract  Society. Amma a shekara ta 1971, an bayyana cewa Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta bambanta da darektocin Watch Tower Society. Darektocin ne ke ba da umurni idan ya zo ga batun bin dokokin gwamnati. Tun daga lokacin, ana barin ‘yan’uwa shafaffu da ba darektocin Watch Tower Society ba su zama mambobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. A cikin ‘yan shekaru da suka shige, an naɗa ‘yan’uwa maza da suka manyanta, daga cikin “waɗansu tumaki” su zama darektocin Watch Tower Society da kuma wasu hukumomin da mutanen Allah suke amfani da su. Hakan ya ba Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah damar mai da hankali ga koyar da Kalmar Allah da kuma yin ja-gora. (Yoh. 10:16; A. M. 6:4) A cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli 2013, an bayyana cewa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ƙaramin rukunin ‘yan’uwa maza ne kuma su ne ake kira Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah.

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah a shekara ta 1950 zuwa 1959

11. Ta yaya Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah take tsai da shawara?

11 Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana tsai da shawarwari masu muhimmanci a matsayin rukuni. Ta yaya suke yin hakan? Membobin suna yin taro a kowane mako, hakan yana sa su riƙa tattaunawa da kyau kuma su kasance da haɗin kai. (Mis. 20:18) Babu wani a cikinsu da yake ganin ya fi sauran muhimmanci, shi ya sa a kowace shekara suna canja wanda yake ja-gora a taron. (1 Bit. 5:1) Kwamitoci shida na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ma suna bin wannan tsarin. Babu memban da ke ganin shi ne shugaban ‘yan’uwansa. Dukansu ‘yan ‘gidan’ Yesu ne da ake koya musu Kalmar Allah kuma suna bin ja-gorar bawan nan mai aminci.

Tun da aka naɗa bawan nan a 1919, su suke tanadar da abubuwan da ke ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah har wa yau (Ka duba sakin layi na 10, 11)

“WANE NE FA BAWAN NAN MAI-AMINCI MAI-HIKIMA?”

12. Da yake ba a hure Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ba kuma su ajizai ne, waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi?

12 Jehobah ba ya sauko wa Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah wahayi, kuma su ajizai ne. Saboda haka, a wasu lokuta za su iya yin kuskure sa’ad da suke bayyana wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki ko kuma a yadda suke ja-gorar mutanen Allah. Hakika, littafin nan Watch Tower Publications Index na Turanci yana ɗauke da jigon nan “Beliefs Clarified,” da ya nuna wasu koyarwa da aka ba da ƙarin haske a kansu tun daga 1870. Babu shakka, Yesu bai gaya mana cewa bawansa mai aminci ba zai yi kuskure sa’ad da yake tanadar da abincin da zai ƙarfafa dangantakarmu da Allah ba. Don haka, ta yaya za mu sami amsar tambayar da Yesu ya yi cewa: “Wane ne fa bawan nan mai-aminci, mai-hikima?” (Mat. 24:45) Wane tabbaci muke da shi cewa wannan Hukumar ne ke tanadar da abinci da yake ƙarfafa dangantakarmu da Allah? Bari mu tattauna abubuwa guda uku da suka taimaka wa hukumar a ƙarni na farko.

13. Ta yaya ruhu mai tsarki yake taimaka wa Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu?

13 Tabbaci cewa suna da ruhu mai tsarki. Ruhu mai tsarki yana taimaka wa Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah su fahimci wasu koyarwa da ba a fahimce su ba a dā. Alal misali, ka yi tunani a kan jigon nan “Beliefs Clarified” da aka ambata a sakin layi na 12. Babu shakka, ba za a yaba wa wani ɗan Adam don fahimtar waɗannan koyarwa “zurfafa na Allah” ba. (Karanta 1 Korintiyawa 2:10.) Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta yi ƙaulin manzo Bulus wanda ya ce: “Su ne kuwa muke sanarwa ta maganar da ba hikimar ɗan adam ce ta koyar ba, sai dai wadda Ruhu ya koyar, muna  bayyana al’amura masu ruhu ga waɗanda suke na ruhu.” (1 Kor. 2:13, Littafi Mai Tsarki) Bayan shekaru da yawa da addinai suke koyarwar ƙarya kuma mutane suna cikin duhu, me ya sa muke ƙara fahimtar koyarwa da yawa tun daga shekara ta 1919? Babu shakka, ruhu mai tsarki ne ya taimaka wa hukumar, ko ba haka ba?

14. Bisa ga Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7, ta yaya mala’iku suke taimaka wa bayin Allah a yau?

14 Tabbaci cewa mala’iku suna taimaka musu. Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah suna jan aiki wajen kula da wa’azin da Shaidu sama da miliyan takwas suke yi a faɗin duniya. Me ya sa ake yin nasara a wannan hidimar? Wani cikin dalilan shi ne mala’iku suna taimakawa a wa’azin da muke yi. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7.) Labarai da yawa sun nuna cewa sa’ad da wasu ‘yan’uwa suka je wa’azi, sun haɗu da wasu da suke yin addu’a don Allah ya aiko da wani bawansa! * Hakika, nasara da muke yi a wa’azi da kuma koyar da mutane duk da tsanantawa da ake mana ya nuna cewa mala’iku ne suke ja-gora a hidimar.

15. Ta yaya Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta bambanta da shugabannin wasu addinai? Ka ba da misali.

15 Suna dogara ga Kalmar Allah. (Karanta Yohanna 17:17.) Ka yi la’akari da abin da ya faru a shekara ta 1973. Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuni ta wannan shekarar ta yi tambayar nan: “Shin zai yiwu waɗanda ba su daina shan taba ba su cancanci yin baftisma?” Amsar da aka bayar ita ce: “Nassi  ya nuna cewa ba su cancanci yin baftisma ba.” Bayan da ya ambata wasu Nassosi da yawa, Hasumiyar Tsaron ta nuna dalilin da ya sa za a iya yi ma wanda bai daina shan taba ba yankan zumunci. (1 Kor. 5:7; 2 Kor. 7:1) Hasumiyar Tsaron ta ƙara da cewa: “Wannan ba ra’ayin ‘yan Adam ba ne amma na Allah ne wanda yake nuna mana nufinsa a cikin Kalmarsa.” Shin akwai wasu addinai da suke dogara ga Kalmar Allah ko da yin hakan ba zai kasance da sauƙi ga mabiyansu ba? Wani littafin Amirka na kwana kwanan nan da ya yi magana game da addini ya ce: “Shugabanan addinan Kirista suna canja koyarwarsu kusan kullum don ya jitu da ra’ayoyinsu da na membobinsu.” Idan Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana dogara ga Kalmar Allah don ja-gora, hakika, Allah ne yake yi musu ja-gora, ko ba haka ba?

‘KU TUNA DA WAƊANDA SUKE SHUGABANCI’

16. Ta wace hanya ce za mu iya tuna da Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu?

16 Karanta Ibraniyawa 13:7. Kalmar nan “tuna” tana iya nufin “ambata.” Saboda haka, hanya ɗaya da muke “tuna da waɗanda suke shugabannanci” ita ce ambata Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu sa’ad da muke yin addu’a don Jehobah ya riƙa taimaka musu. (Afis. 6:18) Ya kamata mu riƙa tuna da hakkinsu na koyar da mu Kalmar Allah da yin ja-gora a wa’azin da muke yi a faɗin duniya da kuma tsara yadda ya kamata mu yi amfani da kuɗaɗe. Babu shakka, suna son mu riƙa yin addu’a a madadinsu don Jehobah ya riƙa taimaka musu.

17, 18. (a) Ta yaya muke haɗa hannu da Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu? (b) Ta yaya muke taimaka wa bawan nan mai aminci da kuma Yesu?

17 Babu shakka, tuna da Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ba a baki kawai ake yi ba, ya kamata mu bi ja-gorar da suke mana. Hukumar tana ba da umurni ta littattafan da muke amfani da su a taron ikilisiya da manyan taro da kuma taron yanki. Ban da haka ma, suna naɗa masu kula da da’ira, masu kula da da’ira kuma su naɗa dattawa a ikilisiya. Masu kula da da’ira da dattawa suna tuna da Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta wurin bin ja-gora da suke yi musu. Dukanmu muna yin biyayya ga Shugabanmu Yesu ta bin umurninsa da na mutanen da yake amfani da su.Ibran. 13:17.

18 Wata hanya kuma da muke tuna da Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ita ce ta yin ƙwazo a wa’azin da muke yi. Manzo Bulus ya ƙarfafa Kiristoci su yi koyi da bangaskiyar waɗanda suke ja-gora a ikilisiya. Bawan nan mai aminci yana ƙwazo sosai don faɗaɗa wa’azin da ake yi a faɗin duniya. Shin kana cikin wasu tumaki da suke haɗa hannu da shafaffu wajen yin wannan aikin? Babu shakka, za ku yi farin ciki sa’ad da Yesu ya ce: “Da shi ke kuka yi wannan ga guda ɗaya a cikin waɗannan ‘yan’uwana, ko waɗannan mafiya ƙanƙanta, ni kuka yi wa.”Mat. 25:34-40.

19. Me ya sa ka ƙuduri aniya ka yi biyayya da shugabanmu Yesu?

19 Sa’ad da Yesu ya koma sama, bai yi watsi da mabiyansa ba. (Mat. 28:20) Ya san cewa ruhu mai tsarki da mala’iku da kuma Kalmar Allah sun taimaka masa sa’ad da yake hidima a nan duniya. Shi ya sa yake taimaka wa bawan nan mai aminci a yau. A matsayin shafaffun Kiristoci, bawan nan yana ‘bin Ɗan rago inda ya tafi duka.’ (R. Yoh. 14:4) Idan mun bi umurnin da suke ba mu, muna bin umurnin Yesu ke nan. Nan ba da daɗewa ba, zai ja-gorance mu zuwa aljanna inda za mu rayu har abada. (R. Yoh. 7:14-17) Babu wani shugaba cikin ‘yan Adam da zai iya yi mana irin wannan alkawarin!

^ sakin layi na 3 Yana yiwuwa Jehobah ya shirya ya sami manzanni 12 da za su zama tushe “goma sha biyu” na Sabuwar Urushalima. (R. Yoh. 21:14) Shi ya sa ba a bukatar a naɗa wani sabon manzon da zai cika gurbin manzon da ya gama hidimarsa a duniya da aminci.

^ sakin layi na 8 Tun daga shekara ta 1955, an san wannan ƙungiyar da sunan Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania.

^ sakin layi na 14 Ka duba shafuffuka na 58-59 a littafin nan “Bearing Thorough Witness” About God’s Kingdom.