Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro (Ta Nazari)  |  fabrairu 2016

 TARIHI

Jehobah Ya Sa Na Yi Nasara a Hidimarsa

Jehobah Ya Sa Na Yi Nasara a Hidimarsa

Na gaya wa hafsan cewa an taɓa jefa ni a kurkuku don na ƙi shiga soja. Na tambaye shi, “Za ka sake saka ni a kurkuku ne?” Karo na biyu ke nan da aka umurce ni in shiga soja a ƙasar Amirka.

AN HAIFE ni a shekara ta 1926, a birnin Crooksville, a jihar Ohio da ke ƙasar Amirka. Iyayenmu ba masu ibada ba ne amma sun ƙarfafa mu mu riƙa zuwa coci. Mu takwas ne iyayenmu suka haifa. Ina zuwa wani cocin da ake kira Methodist. Sa’ad da nake shekara 14, faston cocin ya ba ni kyauta don na yi shekara ban fasa zuwa coci ranar Lahadi ko sau ɗaya ba.

Margaret Walker (‘yar’uwa ta biyu daga hannu hagu) ce ta taimaka min na koya game da Jehobah

A wannan lokacin, wata maƙwabciyarmu mai suna Margaret Walker ta soma ziyarar mahaifiyata kuma ta yi mata wa’azi daga Littafi Mai Tsarki. Ita Mashaidiyar Jehobah ce. Wata rana sai na zauna tare da su sa’ad da suke nazarin amma mahaifiyata ta ce in fita waje domin tana ganin zan dame su. Amma na yi iya ƙoƙarina don na saurari abin da suke cewa. Bayan wani lokaci, sai Margaret ta tambaye ni, “Ka san sunan Allah kuwa?” Na ce, “Ai kowa ya san cewa Allah ne sunansa.” Sai ta ce, “Ka je ka duba Zabura 83:18 a Littafi Mai Tsarki.” Sa’ad da na duba, sai na ga cewa sunan Allah Jehobah ne. Na fita a guje na je wurin abokaina na gaya musu, “Idan kun je gida yau da dare ku duba Zabura 83:18 a Littafi Mai Tsarki ku ga sunan Allah.” Ta haka ne na soma yin wa’azi.

Na yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma na yi baftisma a shekara ta 1941. Jim kaɗan bayan haka, sai aka ce in soma gudanar da nazarin littafi na ikilisiya. Na ƙarfafa mahaifiyata da ‘yan’uwana su zo taron kuma suka soma halarta. Amma mahaifina bai so hakan ba.

HAMAYYA DAGA WURIN MAHAIFINA

An ƙara ba ni ayyuka a cikin ikilisiya kuma na karɓi littattafai da yawa da Shaidun Jehobah suka buga. Wata rana, mahaifina ya nuna min littattafaina sai ya ce: “Ka ga waɗannan abubuwan? Ba na son su a gidan nan kuma ka bar gidana.” Na bar gidanmu kuma na soma zama a birnin Zanesville, wani gari da bai da nisa daga inda iyayena suke a jihar Ohio. Amma nakan je gida don na ƙarfafa mahaifiyarta da ‘yan’uwana.

Mahaifina ya yi ƙoƙarin hana mahaifiyata zuwa taro. A wani lokaci, idan za ta je taro, zai biyo ta a  guje kuma ya ja ta cikin gida. Amma mahaifiyata za ta gudu ta bi ta wata ƙofa kuma ta je taron. Na gaya wa mahaifiyata: “Kar ki damu, zai gaji da bin ki.” Da shigewar lokaci, sai ya ƙyale ta ta riƙa zuwa taro.

Sa’ad da aka soma gudanar da Makarantar Hidima ta Allah a shekara ta 1943, na fara ba da jawabi a matsayin ɗalibi a ikilisiyarmu. Shawarwarin da nake samu a makarantar ya sa na ƙware.

BATUN SHIGA SOJA A LOKACIN YAƘI

A lokacin Yaƙin Duniya na Biyu a shekara ta 1944, an umurce ni na shiga soja. Na je inda ake ɗaukan soja a Fort Hayes a birnin Columbus a jihar Ohio. Na yi wasu gwaje-gwaje kuma na cika wani fom. Na gaya wa hafsoshin cewa ba zan shiga soja ba. Sai suka bar ni in tafi gida. Amma bayan ‘yan kwanaki, sai wani hafsa ya zo gidana ya ce, “Corwin Robison, an ba ni izinin kama ka.”

Bayan sati biyu, mun je kotu kuma alƙalin ya ce: “In ta ni ne zan yi maka ɗaurin rai da rai. Kana da wani bayani ne?” Sai na ce: “Ya Mai Girma mai shari’a, zan so a ɗauke ni a matsayin mai wa’azi. Ina wa’azi gida-gida kuma na yi wa mutane da yawa wa’azi game da Mulkin Allah.” Sai alƙalin ya gaya wa rukunin alƙalai guda goma sha biyu da suke wajen cewa: “Ba ku zo nan don ku yanke shawarar ko wannan mutumin mai wa’azi ne ko a’a ba. Ku zo nan ne don ku gaya mana ko ya yarda ya shiga aikin soja ko a’a.” A cikin minti 30, rukunin alƙalan suka yanke hukunci cewa ina da laifi. Sai aka yi min hukuncin shekara biyar a kurkuku a birnin Ashland da ke jihar Kentucky.

JEHOBAH YA KĀRE NI A CIKIN KURKUKU

Na yi sati biyu na farko a kurkuku da ke babban birnin Columbus a jihar Ohio. A rana ta farko, ban fita waje ba. Na yi addu’a ga Jehobah cewa: “Ba zan yin shekara biyar a kurkuku ba. Ban san na yi ba.”

Washegari, masu gaɗi sun bar ni na fita waje. Sai na je wajen wani ɗan fursuna. Shi wani ƙato ne mai tsayi. Sai muka tsaya muna kallo daga taga. Sai ya tambaye ni, “Me kake yi a nan gajere?” Sai na ce, “Ni Mashaidin Jehobah ne.” Ya ce, “Da gaske? To me kake yi a nan?” Sai na ce, “Shaidun Jehobah ba sa zuwa yaƙi kuma ba sa kisa.” Ya ce, “Sun saka ka a kurkuku domin ka ƙi yin kisa. Amma sai su saka wasu a kurkuku don sun yi kisa. Shin hakan ya dace kuwa?” Sai na ce, “A’a, hakan bai dace ba.”

Sai ya ce, “Na yi shekara 15 a wani kurkuku. A wajen na karanta wasu littattafanku.” Da na ji haka, sai na yi addu’a kuma na ce, “Jehobah ka sa wannan mutumin ya taimaka min.” Sai wannan ɗan fursuna mai suna Paul ya ce: “Idan waɗannan mutanen suka tsokane ka, ka yi gaya min kawai. Zan yi maganinsu.” Saboda haka, ban samu wata matsala da fursunoni 50 da ke wannan bangaren kurkukun ba.

Ina ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah da aka saka su a cikin kurkuku a birnin Ashland da ke jihar Kentucky saboda sun ƙi su saka hannu a yaƙi

Hafsoshin sun kai ni wani kurkuku da ke birnin Ashland. A wajen ne na haɗu da wasu ‘yan’uwa da  suka manyanta. Sun taimaka min da kuma wasu ‘yan’uwa mu kusaci Jehobah sosai. Suna gaya mana ayoyin Littafi Mai Tsarki da za mu karanta kowane mako kuma muna shirya tambayoyi da amsoshi don taron da muke kira Taron Nazarin Littafi Mai Tsarki. Muna zama a cikin wani babban ɗakin da ke da gadaje da yawa kusa da bango. Akwai wani ɗan’uwa da yake tsara mana yanki da za mu yi wa’azi. Zai gaya mini: “Robison, kai ne za ka yi wa waɗanda aka ba wa wannan gadon da wancan gadon wa’azi. Nan ne yankin ka. Ka tabbata cewa ka yi musu wa’azi kafin su tafi.” Ta hakan ne muka yi wa’azi da tsari a kurkuku.

ABUBUWAN DA SUKA FARU BAYAN NA FITO DAGA KURKUKU

Bayan Yaƙin Duniya Na Biyu a shekara ta 1945, na zauna a cikin kurkuku na ɗan lokaci. Na damu da mahaifiyata da kuma ‘yan’uwana domin mahaifina ya taɓa gaya min, “Idan na iya na kore ka daga gidan nan to sauran ba za su gagare ni ba.” Bayan da aka sake ni na yi mamaki cewa mutane bakwai a cikin gidanmu suna zuwa taro kuma wata ‘yar’uwata ta yi baftisma duk da tsanantawar da suka fuskanta daga mahaifina.

Ina wa’azi tare da Demetrius Papageorge, wani ɗan’uwa ne shafaffe da ya fara bauta wa Jehobah a shekara ta 1913

Sa’ad da yaƙi ya ɓarke tsakanin Koriya ta Kudu da ta Arewa a shekara 1950, an sake gaya min in je inda ake ɗaukan soja wato Fort Hayes don in shiga aikin soja. Bayan an yi min gwaji, sai hafsan ya ce, “Ka ci jarabawar sosai.” Sai na ce, “Hakan yana da kyau amma ba zan shiga soja ba.” Sai na yi ƙaulin 2 Timotawus 2:3 kuma na ce, “Ni mayaƙin Kristi ne.” Sai hafsan ya yi shiru na wani lokaci sa’an nan ya ce, “Ka tafi.”

Ba da daɗewa ba, na halarci taro don masu son yin hidima a Bethel a babban taro da aka yi a birnin Cincinnati a jihar Ohio. Ɗan’uwa Milton Henschel ya gaya mana cewa ana bukatar ‘yan’uwa maza masu ƙwazo a Bethel. Don haka, sai na cika fom ɗin kuma aka gayyaci ni. A watan August a shekara ta 1954 ne na soma hidima a Brooklyn, kuma tun daga lokacin ban daina yin hidima a Bethel ba.

A Bethel, na yi aiki sosai. Shekaru da yawa na yi aiki a wurin na’urorin tafasa ruwa da ke maɗaba’a da kuma inda aka gina ofisoshi. Ƙari ga haka, na yi aikin makaniki da maƙulli da kuma a Majami’un Taro da ke birnin New York.

Ina aiki a wurin na’urorin tafasa ruwa a inda aka gina ofisoshi a Bethel da ke Brooklyn

Ina son tsarin ayyuka da ake yi a Bethel kamar ibada ta safiya da nazarin Hasumiyar Tsaro na iyali da kuma yin wa’azi da ikilisiyar da nake halartar taro. Hakika, abin da ya kamata iyalan Shaidun Jehobah su riƙa yi a kai a kai ke nan. Idan iyaye da yara suna tattauna nassosin yini tare, suna yin ibada ta iyali a kai a kai, suna saka hakan a ayyukan taron ikilisiya  kuma suna yin wa’azin bishara da ƙwazo, hakan zai sa kowa a iyalin ya kusaci Jehobah sosai.

Ina da abokai da yawa a Bethel da kuma a ikilisiya. Wasu a cikin su shafaffu ne kuma sun je sama. Wasu ba shafaffu ba ne. Amma dukan bayin Jehobah ajizai ne har da waɗanda suke hidima a Bethel. Idan ina da wata matsala da wani ɗan’uwa, ina iya ƙoƙarina in ga cewa mun sasanta. Ina tunanin littafin Matta 5:23, 24 da kuma yadda za mu iya sasanta matsalar da ke tsakaninmu. Ba shi da sauƙi a ce “Yi haƙuri,” amma ta hakan ne za a iya sasanta matsaloli da yawa.

ALBARKAR DA NA SAMU A HIDIMAR DA NA YI

Yanzu, ba shi da sauƙi in yi wa’azi gida-gida don na tsufa. Amma hakan bai sa na karaya ba. Na koyi yaren Mandarin na mutanen Caina kuma ina jin daɗin yi wa ‘yan Caina wa’azi a gefen titi sosai. A wasu lokatai da safe, ina ba da mujallu 30 ko 40 ga mutane.

Ina wa’azi ga mutanen Caina a Brooklyn da ke New York

Na taɓa yi wa wata magana game da Littafi Mai Tsarki a Caina! Wata rana, wata yarinya mai kirki ta yi min murmushi kuma ta nuna min ‘ya’yan itatuwa da take sayarwa. Na yi mata murmushi kuma na ba ta mujallar Hasumiyar Tsaro da Awake! a yaren Caina. Ta karɓa kuma ta ce sunanta Katie. Bayan haka, Katie tana zuwa wuri na kuma ta yi min magana a duk lokacin da ta gan ni. Na koya mata sunayen wasu ‘ya’yan itatuwa da kayan lambu a Turanci kuma tana maimaita kalmomin bayan na faɗa mata. Ƙari ga haka, na bayyana mata wasu abubuwa game da Littafi Mai Tsarki kuma ta karɓi littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Amma bayan wasu makonni, ban ƙara ganin ta ba.

Bayan wasu watanni, na ba wa wata yarinya da take talla mujallu kuma ta karɓa. Mako na gaba, sai ta ba ni waya kuma ta ce, “Ka yi magana da wata a Caina.” Sai na ce, “Ni ban san kowa a Caina ba.” Amma ta nace, saboda haka sai na karɓi wayar kuma na ce, “Sannu, sunana Robison.” Sai na ji muryar wata ta ce, “Robby, Katie ce. Ina Caina yanzu.” Sai na ce, “Caina?” Katie ta amsa ta ce, “Ƙwarai kuwa. Robby, wadda ta ba ka wayar ‘yar’uwata ce. Ka koya mini abubuwa masu kyau da yawa. Don Allah ka koya mata yadda ka koya mini.” Sai na ce, “Katie, zan yi iya ƙoƙarina. Na gode sosai da kika gaya mini inda kike.” Ba da daɗewa ba, na yi magana ta ƙarshe da ‘yar’uwar Katie. Ina fata cewa a duk inda ‘yan mata nan biyu suke yanzu, za su ci gaba da koya game da Jehobah.

Na yi shekara 73 ina bauta wa Jehobah kuma ina farin ciki cewa ya taimaka min ban je yaƙi ba kuma na kasance da aminci sa’ad da nake kurkuku. Ƙari ga haka, ‘yan’uwana sun gaya mini cewa yadda na ci gaba da bauta wa Jehobah duk da tsanantawa da mahaifinmu ya yi mini ya ƙarfafa su sosai. Daga baya, mahaifiyata da kuma ‘yan’uwana maza da mata guda shida sun yi baftisma. Mahaifina ya daina tsananta mana kuma ya halarci wasu taronmu kafin ya mutu.

Idan nufin Allah ne, za a ta da ‘yan gidanmu da kuma abokaina daga mutuwa kuma za su yi rayuwa a sabuwar duniya. Za mu yi farin ciki sosai yayin da muke bauta wa Jehobah tare da waɗanda muke ƙauna har abada! *—Ka duba ƙarin bayani.

^ sakin layi na 32 Sa’ad da ake shirya wannan talifin, Corwin Robison ya rasu kuma ya kasance da aminci ga Jehobah har mutuwarsa.