KA YI tunanin ranar da ta fi muhimmanci a rayuwarka. Ranar auren ka ne? Ko ranar da aka haifi ɗanka na fari? Ko kuma ranar da ka yi baftisma ne? Hakika, ranar da aka yi maka baftisma za ta iya kasancewa rana mafi muhimmanci da kuma farin ciki a rayuwarka. A wannan ranar, ‘yan’uwan maza da mata sun yi farin ciki sosai yayin da suka ga yadda ka bayyana ƙaunarka ga Allah da dukan zuciyarka, da ranka, da azancinka da kuma ƙarfinka!​—⁠Markus 12:⁠30.

Babu shakka, tun ranar da aka yi maka baftisma, abubuwa da yawa da suka faru a bautar ka ga Jehobah sun sa ka farin ciki sosai. Amma waɗansu masu shela yanzu sun daina yin farin ciki a bautar su ga Jehobah. Me ya sa hakan ya faru? Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki?

DALILIN DA YA SA WASU SUN DAINA YIN FARIN CIKI

Wa’azin bishara ta Mulki yana sa mu farin ciki sosai. Me ya sa? Domin Jehobah ya yi alkawari cewa, nan ba da daɗewa ba, Mulkinsa zai halaka wannan mugun zamani kuma ya kawo aljanna a duniya. Zafaniya 1:14 ta ce: “Babbar ranar Ubangiji ta kusa, kurkusa ce, tana kuwa gaggabta ƙwarai, watau muryar ranar Ubangiji; ƙaƙarfan mutum yana kuka mai-zafi a cikinta.” Idan muna gani cewa ƙarshen zai daɗe kafin ya zo, hakan zai iya sa mu daina kasancewa da farin ciki kamar yadda muka yi a dā. A sakamako, za mu iya yin sanyin gwiwa a hidimarmu ga Allah.​—⁠Misalai 13:⁠12.

Idan muna cuɗanya da ‘yan’uwanmu maza da mata, hakan zai ƙarfafa mu mu ci gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki. Mai yiwuwa halayen kirki na mutanen Jehobah ne ya sa muka soma bauta ta gaskiya kuma ya sa muna yin hidimarmu da farin ciki. (1 Bitrus 2:12) Amma, mene ne zai iya faruwa idan aka yi wa wasu ‘yan’uwa horo don sun ƙi bin ƙa’idodin Allah? Hakan zai iya sa wasu a cikin ikilisiya su yi sanyin gwiwa kuma su daina yin farin ciki.

Abin duniya zai iya sa mu daina jin daɗin bautarmu ga Jehobah. Ta yaya? Tsarin kasuwanci da talla da ake yi a wannan duniyar zai iya sa mu soma sayan abubuwan da ba ma bukata. Yesu ya ce: “Ba wanda ke da iko shi bauta wa ubangiji biyu: gama ko shi ƙi ɗayan, shi ƙaunaci ɗayan: ko kuwa shi lizimci ɗayan, shi rena ɗayan. Ba ku da iko ku bauta wa Allah da dukiya ba.” (Matta 6:24) Idan muna biɗan abin duniya, ba za mu iya bauta wa Jehobah da farin ciki ba.

ABUBUWAN DA KE SA MU FARIN CIKI A BAUTAR JEHOBAH

Ga waɗanda suke ƙaunar Jehobah, bauta masa ba jan aiki ba ne. (1 Yohanna 5:⁠3) Ka tuna cewa Yesu ya ce, “Ku zo gareni, dukanku da kuke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗaukar wa kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai-sauƙi ce,  kayana kuma mara-nauyi.” (Matta 11:​28-30) Rayuwa a matsayin Kirista na gaskiya tana sa kwanciyar hankali da kuma farin ciki. Babu shakka, muna da dalilai masu kyau na yin farin ciki a hidimar Jehobah. Bari mu tattauna guda uku daga cikinsu.​—⁠Habakkuk 3:⁠18.

Muna bauta wa Mahaliccinmu, Allah mai farin ciki. (Ayyukan Manzanni 17:28; 1 Timotawus 1:11) Jehobah ne mahalicci kuma shi ya ba mu rai. Saboda haka, bari mu ci gaba da bauta masa da farin ciki, ko da shakaru da yawa sun wuce sa’ad da muka yi baftisma.

Héctor ya ci gaba da farin ciki ta wajen tuna da begensa na Mulki da kuma kasancewa da ƙwazo a hidimarsa ga Jehobah

Ka yi la’akari da wani ɗan’uwa mai suna Héctor, wanda ya yi shekaru 40 yana hidimar mai-kula mai-ziyara. Har lokacin da ya “tsufa” ma ya ci gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki. (Zabura 92:​12-14) Ko da yake rashin lafiyar matarsa ya hana shi yin wasu abubuwa a hidimar Jehobah, Héctor ya ci gaba da kasancewa da farin ciki. Ya ce: “Matata tana rashin lafiya kuma da sannu a hankali yanayinta yana daɗa muni, hakan ya sa ni baƙin ciki. Ƙari ga haka, kula da ita bai da sauƙi. Amma wannan yanayin bai hana ni bauta wa Allah da farin ciki ba. Jehobah ne ya ba ni rai kuma ya halicci ‘yan Adam da manufa, shi ya sa nake ƙaunarsa kuma ina bauta masa da dukan zuciyata. Ina yin ƙoƙarin kasancewa da ƙwazo a wa’azi, kuma nakan yi bimbini a kan abubuwan da Mulkin Allah zai kawo don in ci gaba da yin farin ciki.”

Jehobah ya yi tanadin fansa, hakan yana sa mu farin ciki a rayuwa. Littafi Mai Tsarki ya ce, ‘Allah yana ƙaunar duniya har ya ba da Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana ba da gaskiya gare shi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.’ (Yohanna 3:16) Hakika, Allah zai gafarta mana zunubanmu, kuma za mu iya samun rai na har abada idan muka nuna bangaskiyarmu ga kyautar fansa da Allah ya yi mana. Wannan kyakkyawan dalili ne na yin godiya kuma hakan yana motsa mu mu bauta wa Jehobah da farin ciki.

Jesús ya sauƙaƙa rayuwarsa, kuma ya bauta wa Jehobah da farin ciki shekaru da yawa

Wani ɗan’uwa da ya zauna a Meziko mai suna Jesús, ya ce: “Ina son aikina sosai, a wani lokaci, nakan yi aiki dabam-dabam sau biyar ko da yin hakan ba wajibi ba ne. Amma ina yin hakan ne don kuɗin da nake samu. Sa’ad da na soma koya game da Jehobah da kuma yadda ya ba da ɗansa don fansar ‘yan Adam, sai na ƙudiri niyyar bauta masa. Na ba da kaina ga Jehobah kuma na yi baftisma. Sai na yi murabus bayan na yi shekara 28 ina yi wa kamfanin aiki kuma na soma hidima ta cikakken lokaci.” Yadda Jesús ya soma bauta wa Jehobah da farin ciki ke nan.

Muna rayuwa bisa ɗabi’u masu kyau kuma hakan yana sa mu farin ciki. Za ka iya tuna yadda rayuwarka take kafin ka soma bauta wa Jehobah? Manzo Bulus ya gaya wa Kiristoci da ke Roma cewa  su “bayi ne na zunubi a dā” amma yanzu su “bayi ne ga adalci.” Domin suna yin rayuwa bisa kyawawan ɗabi’u, suna da begen yin rayuwa har abada. (Romawa 6:​17-22) Mu ma muna bin ƙa’idodin Jehobah, shi ya sa ba ma fuskantar matsalolin da ke tattare da yin lalata ko kuma rashin imani. Hakika, hakan abin farin ciki ne!

“Shekaru da na fi farin ciki a rayuwata sune waɗanda na yi ina bauta wa Jehobah.”​—⁠Jaime

Ka yi la’akari da wani mai suna Jaime, wanda bai gaskata cewa akwai Allah ba. Ƙari ga haka, shi ɗan dambe ne mai ra’ayin bayyanau. Jaime ya fara halartan taron Shaidun Jehobah kuma yadda suke ƙaunar juna ya motsa shi sosai. Don ya bar salon rayuwarsa na dā, Jaime ya roƙi Jehobah ya taimaka masa ya gaskata da shi. Jaime ya ce: “A hankali sai na fahimci cewa Uba mai ƙauna yana wanzuwa kuma shi Allah ne mai jin ƙai. Bin ƙa’idodi masu kyau na Jehobah ya kāre ni sosai. Dā a ce ban canja halina ba, da wataƙila an kashe ni kamar abokanai na na dā masu dambe. Shekaru da na fi farin ciki a rayuwata sune waɗanda na yi ina bauta wa Jehobah.”

KADA KA KASALA!

Yaya ya kamata mu ji yayin da muke jiran ƙarshen wannan muguwar duniyar? Ka tuna cewa muna yin nufin Allah, kuma muna sauraron yin rayuwa har abada a nan gaba. Saboda haka, “kada mu yi kasala kuma cikin aikin nagarta: gama in lokaci ya yi za mu girbe, in ba mu yi suwu ba.” (Galatiyawa 6:​8, 9) Da taimakon Jehobah, bari mu ci gaba da jurewa, muna yin aikin tuƙuru don mu kasance da halayen da muke bukata don mu tsira a lokacin “babban tsanani,” kuma mu ci gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki.​—⁠Ru’ya ta Yohanna 7:​9, 13, 14; Yaƙub 1:​2-4.

Muna da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace mu idan muka jure, domin ya san aikin da muke yi. Ƙari ga haka, ya san cewa muna ƙaunarsa kuma muna kāre sunansa. Idan muka ci gaba da bauta masa da farin ciki, za mu zama kamar marubuci Dauda, wanda ya ce: “Na sa Ubangiji a gabana kullum: Da shi ke yana ga hannun damana ba zan jijigu ba. Domin wannan zuciyata ta yi fari, darajata tana murna; jikina kuma za shi zauna a natse.”​—⁠Zabura 16:​8, 9.