“Waɗanda ke bisa tabi’ar ruhu [suna ƙwallafa ransu ga], al’amuran ruhu.”​—ROM. 8:5.

WAƘOƘI: 5752

1, 2. Ta yaya Kiristoci shafaffu za su amfana daga bincika littafin Romawa sura 8?

A LOKACIN tuna da mutuwar Yesu wataƙila ka karanta littafin Romawa 8:​15-17. Wannan littafin ya bayyana yadda shafaffun Kiristoci suka san cewa su shafaffu ne, saboda ruhu mai tsarki ya tabbatar musu da hakan. Ƙari ga haka, ayar farko ta wannan surar ta bayyana cewa su na “Kristi Yesu” ne. Shin littafin Romawa sura 8 yana magana ne kawai game da shafaffu? Ko kuma yana magana har da waɗanda za su yi rayuwa a duniyar nan?

2 Wannan surar ta yi magana ne game da shafaffu. Sun zama “na Ruhu” a matsayin masu ‘jiran ɗayanci, watau, fansar jikinsu.’ (Rom. 8:23) Hakika, za su zama ‘ya’yan Allah kuma za su yi rayuwa a sama. Hakan ya yiwu domin bayan baftismarsu, Allah ya yi amfani da fansar Yesu domin ya yafe musu zunubansu, kuma ya sa su kasance adalai a matsayin ‘ya’yansa.​—Rom. 3:​23-26; 4:25; 8:30.

3. Me ya sa muka ce Kiristoci masu begen rayuwa a duniya har abada za su amfana daga littafin Romawa sura 8?

3 Duk da haka, waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya za su iya amfana daga littafin Romawa sura 8 saboda Allah yana  ganin su adalai ne. Abin da Bulus ya rubuta a surorin baya sun tabbatar mana da hakan. A sura ta 4 Bulus ya yi magana game da Ibrahim. Wannan mutum mai bangaskiya ya yi rayuwa kafin Jehobah ya kafa wa Isra’ila doka kuma kafin Yesu ya zo ya mutu domin zunubanmu. Duk da haka, Jehobah ya lura da bangaskiyar Ibrahim kuma ya kira shi mai adalci. (Karanta Romawa 4:​20-22.) Haka ma a yau, Jehobah zai iya kiran Kiristoci masu aminci da suke da begen rayuwa har abada a duniya adalai. Saboda haka, su ma za su amfana daga umurnin da ke littafin Romawa sura 8.

4. Wace tambaya ce karanta littafin Romawa 8:21 zai sa mu yi?

4 Mun sami tabbaci a littafin Romawa sura 8:21 cewa sabuwar duniya za ta zo. Wannan ayar ta tabbatar mana cewa, ‘halitta da kanta za ta tsira daga bautar ɓacewa zuwa cikin ‘yancin darajar ‘ya’yan Allah.’ Yanzu tambayar ita ce, shin za mu kasance a wurin kuma mu sami wannan ladan? Kana da tabbacin hakan kuwa? Littafin Romawa sura 8 ta ba da wata shawara da za ta taimaka maka ka yi hakan.

ƘWALLAFA RAI GA “AL’AMURAN JIKI”

5. Wane batu mai muhimmanci ne Bulus ya bayyana a littafin Romawa 8:​4-13?

5 Karanta Romawa 8:​4-13. Littafin Romawa sura 8 ya nuna bambanci da ke tsakanin waɗanda suka ƙwallafa ransu ga ‘al’amuran jiki’ da kuma waɗanda suka ƙwallafa ransu ga ‘al’amuran ruhu.’ Wasu za su iya yin tunani cewa wannan bambancin tsakanin waɗanda suka san Jehobah ne da kuma waɗanda ba su san shi ba ko kuma Kiristoci da waɗanda ba Kiristoci ba. Amma Bulus ya rubuta wasiƙarsa ga ‘waɗanda ke cikin Roma, ƙaunatattun Allah kirayayyu su zama tsarkaka.’ (Rom. 1:⁠7) Saboda haka, Bulus yana nuna bambanci da ke tsakanin Kiristocin da suke ƙwallafa ransu ga al’amuran jiki da kuma waɗanda suke ƙwallafa ransu ga al’amuran ruhu. Mene ne bambancin?

6, 7. (a) A waɗanne hanyoyi ne aka yi amfani da kalmar nan “jiki” a Littafi Mai Tsarki? (b) A wace hanya ce Bulus ya yi amfani da kalmar nan “jiki” a littafin Romawa 8:​4-13?

6 Bari mu tattauna abin da Bulus yake nufi sa’ad da ya ambata kalmar nan “jiki.” An yi amfani da kalmar nan “jiki” a cikin Littafi Mai Tsarki a hanyoyi da yawa. A wasu lokuta, yana nufin jikin mutum  na zahiri. (Rom. 2:28; 1 Kor. 15:​39, 50) Kuma yana iya nufin dangantaka. Yesu ya fito ne daga “zuriyar Dauda ga zancen jiki” kuma Bulus ya ɗauki Yahudawa a matsayin ‘’yan’uwansa na kabila’ ko kuma na zahiri.​—Rom. 1:3; 9:3.

7 Abin da Bulus ya rubuta a sura ta 7 ya bayyana mana abin da “jiki” da aka ambata a Romawa 8:​4-13 yake nufi. Ya bayyana alaƙar da ke tsakanin yin rayuwa ga “al’amuran jiki” da kuma “sha’awoyi na zunubi” da mutane ‘suke aikatawa cikin gaɓaɓuwansu.’ (Rom. 7:⁠5) Hakan ya sa mun san cewa waɗanda suka ƙwallafa ransu ga “al’amuran jiki” su ne waɗanda Bulus ya ce suna mai da hankali ga abubuwan jiki. Yana magana ne game da mutane ajizai da suke bin sha’awoyin zunubi, wato suna yin abin da suka ga dama.

8. Me ya sa gargaɗin da aka yi wa shafaffu game da yin rayuwa bisa ga “al’amuran jiki” ya dace?

8 Amma za ka iya yin tunani a kan dalilin da ya sa Bulus ya nanata wa Kiristoci shafaffu hadarin da ke tattare da yin rayuwa bisa ga “al’amuran jiki.” Shin a yau irin wannan hadarin zai iya shafan Kiristocin da Allah ya ɗauke su a matsayin abokansa? Abin takaici shi ne Kirista zai iya soma yin irin wannan rayuwar. Alal misali, Bulus ya rubuta cewa wasu daga cikin ‘yan’uwan da ke Roma suna yi wa “cikinsu” bauta. Abin da Bulus yake nufi shi ne, abubuwan da suka saka a gaba kawai su ne, zina da abinci da dai wasu abubuwan shaƙatawa. (Rom. 16:​17, 18; Filib. 3:​18, 19; Yahu. 4, 8, 12) Kuma ka tuna cewa a Koranti akwai wani ɗan’uwa da ya auri “matar ubansa.” (1 Kor. 5:⁠1) Wannan dalilin ne ya sa Allah ya hure Bulus ya gargaɗi Kiristoci game da yin rayuwa bisa ga “al’amuran jiki.”​—Rom. 8:​5, 6.

9. Gargaɗin Bulus da ke Romawa 8:6 bai shafi waɗanne irin mutane ba?

9 Wannan gargaɗin ya shafe mu a yau. Kirista da ya daɗe yana bauta wa Allah zai iya soma ƙwallafa ransa ga al’amuran jiki. Amma wannan gargaɗin bai shafi Kiristan da a wasu lokuta yakan yi tunani game da abinci ko aiki ko nishaɗi ko kuma soyayya ba. Bayin Allah sukan tuna waɗannan abubuwan a wasu lokuta. Yesu ma ya ciyar da wasu kuma ya ci abinci ya kuma yi nishaɗi. Ƙari ga haka, Bulus ya rubuta cewa jima’i yana da muhimmanci tsakanin ma’aurata kaɗai.

Shin hirar da kake yi yana nuna cewa ka ƙwallafa ranka ga al’amuran ruhu ko na jiki? (Ka duba sakin layi na 10, 11)

10. Mene ne furucin nan yin rayuwa bisa ga “al’amuran jiki” da ke Romawa 8:​5, 6, yake nufi?

 10 Mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya ambaci yin rayuwa bisa ga “al’amuran jiki”? Kalmar Helenancin da Bulus ya yi amfani da ita tana nufin “sa rai ga wani abu da yin ƙwazo sosai don a sami abin.” Wani masani ya ce furucin da ke Romawa 8:5 da ya ambaci yin rayuwa bisa ga al’amuran jiki ya shafi waɗanda suke yawan magana game da sha’awoyin jiki kuma abin da suka saka a gaba ke nan. Sun bar sha’awoyinsu suna yin mulki a kansu.

11. Waɗanne abubuwa ne za mu iya ƙwallafa ranmu a kai?

11 Yadda Kiristocin da ke Roma suka bincika kansu don su san abubuwan da suka ƙwallafa ransu a kai ya dace. Wataƙila waɗannan Kiristocin sun ƙwallafa ransu ga “al’amuran jiki” ne, ko ba haka ba? Saboda haka, yana da muhimmanci mu ma mu bincika kanmu don mu ga ko mun ƙwallafa ranmu ga abubuwa na jiki. Mene ne muka fi mai da hankali a kai kuma ta yaya furucinmu zai nuna hakan? Mene ne muka saka a gaba? Wasu sun gano cewa abin da suka fi mai da hankali a kai shi ne shan giya iri iri da gyara gidansu da sayan kaya da ake yayi da tara dukiya da yin tafiye-tafiye da dai sauransu. Biɗan waɗannan abubuwan ba laifi ba ne, hanyar jin daɗin rayuwa ce. Alal misali, akwai lokacin da Yesu ya juya ruwa ya zama ruwan anab ko giya kuma Bulus ma ya gaya wa Timotawus ya sha “ruwan anab” kaɗan. (1 Tim. 5:23; Yoh. 2:​3-11) Shin Bulus da Yesu sun ƙwallafa ransu ga giya ne, suna hirarsa a kowane lokaci? Shin sun mai da hankali ga sha’awoyinsu? A’a. Mu kuma fa, me muke yawan hirarsa?

12, 13. Me ya sa abin da muka ƙwallafa ranmu a kai batu ne mai muhimmanci?

12 Zai dace mu bincika kanmu. Me ya sa? Bulus ya ce: Ƙwallafa rai ga ‘jiki mutuwa ce.’ (Rom. 8:⁠6) Hakan ba batun wasa ba ne don zai iya sa mutum ya ɓata dangantakarsa da Allah yanzu kuma ya kasa samun rai na har abada a nan gaba. Amma Bulus ba ya nufin cewa idan mutum ya soma ƙwallafa ransa ga abubuwa na jiki ba zai iya canjawa ba. Mutumin da aka yi maganarsa a Koranti da ya bi sha’awoyin “jiki” har sai da aka yi masa yankan zumunci kafin ya gyara halinsa kuma aka dawo da shi. Abin da ya taimaka masa shi ne ya daina bin sha’awoyin jiki kuma ya soma yin abin da ya dace.​—2 Kor. 2:​6-8.

13 Da yake wannan mutumin ya canja halinsa, Kirista ma a yau zai iya canja halinsa musanmman ma wanda bai bi sha’awoyin jiki kamar na wannan mutumin Koranti ba. Babu shakka, gargaɗin da Bulus ya ba da game da sakamakon ƙwallafa rai ga “al’amuran jiki” zai taimaka mana mu yi duk wani canji da muke bukatar yi.

ƘWALLAFA RAI GA “AL’AMURAN RUHU”

14, 15. (a) Mene ne manzo Bulus ya ƙarfafa mu mu riƙa mai da hankali a kai? (b) Mene ne ƙwallafa rai ga “al’amuran ruhu” ba ya nufi?

14 Bayan da manzo Bulus ya gargaɗe mu kada mu ƙwallafa rai ga “al’amuran jiki,” sai ya tabbatar mana da cewa: “Himmantuwar [ko ƙwallafa rai ga al’amuran] ruhu rai ne da lafiya.” Ladan da za mu samu rai ne da salama. Ta yaya za mu sami wannan ladan?

15 Ƙwallafa rai ga “al’amuran ruhu” ba ya nufin cewa mutum ba zai riƙa tunanin wasu abubuwa ba. Kuma ba ya nufin cewa mutum zai riƙa yin hirar Littafi Mai Tsarki da ƙaunar da yake wa Allah da kuma begen da yake da shi a nan gaba kawai. Mu yi la’akari da Bulus da wasu a ƙarni na  farko, sun yi rayuwa da mutane suka saba yi. Suna cin abinci kuma suna shan ruwan anab. Da yawa daga cikinsu sun yi aure kuma sun ji daɗin zama da iyalansu, ban da haka ma, sun ji daɗin aikin da suka yi don su biya bukatunsu.​—Mar. 6:3; 1 Tas. 2:9.

16. Ko da yake Bulus ya yi wasu ayyuka, amma mene ne ya saka a gaba?

16 Duk da haka, bayin Allah ba su bar waɗannan abubuwan su zama tamkar abin da suka saka a gaba ba. Bayan da Littafi Mai Tsarki ya ce Bulus yana yin tanti don ya sami abin biyan bukata, ya gaya mana abubuwan da ya saka a kan gaba. Mene ne ke nan? Yana wa’azi kullum kuma yana koyar da mutane. (Karanta Ayyukan Manzanni 18:​2-4; 20:​20, 21, 34, 35.) Shi ya sa ya ƙarfafa Kiristocin da ke Roma su riƙa yin waɗannan ayyukan. Babu shakka, Bulus ya ƙwallafa ransa ga yin ayyukan ibada. Kiristoci da ke Roma suna bukatar su yi koyi da Bulus.​—Rom. 15:​15, 16.

17. Wane lada za mu samu idan muka saka “al’amuran ruhu” a kan gaba?

17 Wane lada za mu samu idan muka saka ayyukan ibada a kan gaba? Littafin Romawa 8:6 ya ba mu amsar, ya ce: Ƙwallafa rai ga “ruhu rai ne da lafiya.” Hakan yana nufin muna bukatar mu bari ruhu mai tsarki ya riƙa yi mana ja-gora kuma mu riƙa yin tunanin da ya jitu da ƙa’idodin Jehobah. Za mu kasance da tabbacin cewa idan muka bar “ruhu” mai tsarki ya riƙa yi mana ja-gora, za mu yi rayuwa mai ma’ana yanzu, kuma a nan gaba za mu sami rai na har abada a nan duniyar ko kuma a sama.

18. Ta yaya muke samun salama sa’ad da muka ƙwallafa rai ga “al’amuran ruhu”?

18 Muna da tabbaci cewa idan muka ƙwallafa ranmu ga “al’amuran ruhu” za mu sami salama. Bari mu bincika hakan. Mutane da yawa suna son su sami salama ko kwanciyar hankali, amma abin baƙin ciki shi ne mutane kaɗan ne suke samun hakan. Duk da haka, muna moran salama da kwanciyar hankali. Kuma abin da yake taimaka mana mu yi hakan shi ne yin ƙokari mu kasance da salama a iyalinmu da kuma ikilisiya. Mun fahimci cewa dukanmu a ikilisiya ajizai ne, saboda haka, a wasu lokuta mukan samu saɓani da juna. Amma idan hakan ya faru, zai dace mu bi shawarar Yesu cewa, ka ‘sulhunta da ɗan’uwanka.’ (Mat. 5:24) Yin hakan zai kasance mana da sauƙi idan muka tuna cewa ‘yan’uwanmu ma suna bauta wa “Allah na salama.”​—Rom. 15:33; 16:⁠20.

19. Wace irin salama ce kuma za mu more?

19 Akwai wata irin salama da babu makamancinta. Idan muka ƙwallafa rai ga “al’amuran ruhu” za mu kasance da salama da mahaliccinmu. Ishaya ya yi wani furucin da zai iya amfanarmu a yau. Ya ce: “Za ka [Jehobah] riƙe shi cikin cikakkiyar salama, shi wanda hankalinsa yana kafe bisa gareka; saboda yana dogara gareka.”​—Isha. 26:3; karanta Romawa 5:1.

20. Me ya sa muke bukatar mu nuna godiya don umurnin da yake littafin Romawa sura 8?

20 Babu shakka, ko da muna da begen yin rayuwa har abada a sama ko kuma a duniya, muna bukatar mu nuna godiya saboda umurnin da ke littafin Romawa sura 8. Muna farin ciki saboda ƙarfafa da muka samu cewa kada mu ƙwallafa ranmu ga “al’amuran jiki.” Amma mu riƙa rayuwar da ta jitu da ƙa’idar nan da ta ce, idan muka ƙwallafa ranmu ga “al’amuran ruhu” za mu sami rai da kuma salama. Ladan da za mu samu idan muka yi hakan shi ne rai na har abada. Manzo Bulus ya ce: “Hakkin zunubi mutuwa ne; amma kyautar Allah rai na har abada ce cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.”​—Rom. 6:23.