JEHOBAH ya hure manzo Bulus ya rubuta game da halaye tara da ruhu mai tsarki yake taimaka mana mu kasance da su. (Gal. 5:​22, 23) An kira duka waɗannan halayen ‘’yar Ruhu.’ * Kuma suna cikin “sabon” hali da ya kamata Kiristoci su kasance da shi. (Kol. 3:10) Kamar yadda itace yakan yi ’ya’ya idan ya sami isashen ruwa, haka ma yake da mutane, idan suna da ruhu mai tsarki, za su riƙa nuna waɗannan halayen.​—Zab. 1:​1-3.

Ɗaya daga cikin halayen ’yar ruhu da Bulus ya ambata da farko shi ne ƙauna. Ta yaya ƙauna take da muhimmanci? Bulus ya ce idan bai nuna ƙauna ba, shi ba “komi” ba ne. (1 Kor. 13:2) Amma mene ne ƙauna kuma ta yaya za mu kasance da wannan halin kuma mu riƙa nuna ta?

YADDA AKE NUNA ƘAUNA

Littafi Mai Tsarki ya nuna mana yadda ya kamata mutum mai nuna ƙauna zai riƙa yin abubuwa da kuma ra’ayinsa ko da yake yana da wuya a iya bayyana abin da kalmar nan ƙauna take nufi. Alal misali, mutumin da yake nuna ƙauna yana ‘yawan haƙuri da nasiha.’ Ban da haka ma, ƙauna “tana murna da gaskiya; tana jimrewa da abu duka, tana gaskata abu duka, tana kafa bege ga abu duka, tana daurewa da abu duka.” Wannan mutumin yana ƙaunar mutane, yana kula da su kuma za a iya tabbata da shi. Amma mutumin da ba ya ƙauna zai iya zama mai kishi da fahariya da halin banza da son kai da ƙin gafarta wa mutane. Halin da muke so mu kasance da shi ba kamar waɗannan ba domin ƙauna “ba ta biɗa ma kanta” kawai.​—1 Kor. 13:​4-8.

JEHOBAH DA YESU SUN KAFA MANA MISALIN NUNA ƘAUNA

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ƙauna ne.” Babu shakka, Jehobah ne ya soma nuna ƙauna. (1 Yoh. 4:8) Yadda yake yin abubuwa da halittunsa sun tabbatar da hakan. Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar mutane sosai, sa’ad da ya aiko da Yesu duniya don ya sha wahala kuma ya mutu domin mu. Manzo Bulus ya ce: “Inda aka bayyana ƙaunar Allah gare mu ke nan, Allah ya aike Ɗansa haifaffensa kaɗai cikin duniya, domin mu rayu ta wurinsa. Nan akwai ƙauna, ba cewa mu ne muka yi ƙaunar Allah ba, amma shi ne ya ƙaunace mu, ya aike Ɗansa kuma ya biya hakin zunubanmu.” (1 Yoh. 4:​9, 10) Saboda ƙaunar da Allah ya yi mana ne ya sa zai iya gafarta mana zunubanmu kuma mu zama da bege kuma mu sami rai na har abada.

Yesu ya nuna yana ƙaunar mutane ta wurin yin abin da Allah ya gaya masa ya yi. Manzo Bulus ya rubuta: “[Yesu] ya ce, Ga ni na zo garin in aika nufinka. . . . Bisa ga wannan nufi an tsarkake mu ta wurin miƙa jikin Yesu Kristi so ɗaya ɗungum.” (Ibran. 10:​9, 10) Babu wani ɗan Adam da zai iya nuna mana irin wannan ƙaunar. Yesu ya ce: “Ba wanda yake da ƙauna wadda ta fi gaban wannan, wato mutum ya ba da ransa domin abokansa.” (Yoh. 15:13) Shin mutane za su iya yin koyi da ƙaunar da Yesu da kuma Jehobah suka nuna kuwa? Hakika, za su iya! Bari mu tattauna yadda za mu iya yin hakan.

 KU CI GABA DA NUNA “ƘAUNA”

Bulus ya yi mana gargaɗi cewa: “Ku zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu; ku yi tafiya cikin ƙauna, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunace ku, ya ba da kansa kuma domin ku.” (Afis. 5:​1, 2) Muna “tafiya cikin ƙauna” ko ci gaba da nuna ƙauna idan muka kasance da wannan halin a duk fannin rayuwarmu. Muna nuna wannan halin ta wurin yadda muke yin abubuwa ba ta abin da muke faɗa kawai ba. Yohanna ya ce: ‘’Ya’ya ƙanƙanana, kada mu yi ƙauna da baki ko kuwa da harshe; amma da aiki da gaskiya kuma.’ (1 Yoh. 3:18) Alal misali, muna wa mutane ‘bishara ta mulki’ domin muna ƙaunar Jehobah da kuma mutane. (Mat. 24:14; Luk. 10:27) Idan muna da haƙuri da kirki kuma muna gafarta wa mutane, muna nuna ƙauna. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa: “Kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku, haka nan kuma sai ku yi.”​—Kol. 3:13.

Idan muka shawarci wasu ko kuma ja musu kunne, hakan ba ya nufin cewa ba ma ƙaunarsu. Alal misali, idan yaro yana kuka, wasu iyayen sukan lallashe shi ta wurin ba shi duk abin da yake so. Amma duk mutumin da ke son yaronsa sosai zai ɗauki matakin da ya dace don ya kwaɓe shi. Haka ma yake da Allah, ko da yake shi ƙauna ne amma Littafi Mai Tsarki ya ce wanda Allah yake “ƙauna shi yake horo.” (Ibran. 12:6) Saboda haka, muna ƙaunar yaranmu idan muka yi musu horon da ya dace da kuma a lokacin da suke bukatar hakan. (Mis. 3:​11, 12) Amma idan muna yin hakan ya kamata mu tuna cewa mu masu zunubi ne kuma mukan yi kuskure. A gaskiya, dukanmu muna da wuraren da ya kamata mu daɗa ƙwazo idan ya zo ga nuna ƙauna. Ta yaya za mu iya yin hakan? Bari mu tattauna hanyoyi uku da za su taimaka mana.

TA YAYA ZA MU ZAMA MASU ƘAUNA?

Na farko, ka roƙi Allah ya ba ka ruhunsa da zai taimaka maka ka kasance da ƙauna. Yesu ya ce Jehobah yana ba da “ruhu Mai-tsarki ga waɗanda suke roƙonsa.” (Luk. 11:13) Idan muka yi addu’a don a ba mu ruhu mai tsarki kuma muka yi ƙoƙari mu “yi tafiya bisa ga ruhu,” za mu riƙa nuna ƙauna sosai. (Gal. 5:16) Alal misali, idan kai dattijo ne a ikilisiya, za ka iya roƙan ruhu mai tsarki ya taimaka maka ka ba da shawara a hanyar da ta dace. Idan kana da yara, za ka iya roƙon Jehobah ya ba ka ruhu mai tsarki ya taimaka maka ka hori yaranka da ƙauna ba da fushi ba.

Na biyu, ka yi tunanin yadda Yesu ya nuna ƙauna sa’ad da ake wulaƙanta shi. (1 Bit. 2:​21, 23) Za mu iya koyan darasi daga misalin Kristi sa’ad da wani ya yi mana laifi ko kuma lokacin da aka mana rashin adalci. A irin wannan yanayin, tambayar da ya kamata mu yi wa kanmu ita ce, ‘Da a ce Yesu ne, me zai yi?’ Wata ’yar’uwa mai suna Leigh ta ce yin tunanin a kan wannan tambayar kafin ta ɗauki mataki ya taimaka mata sosai. Ta ce: “Akwai wani lokaci da wata da muke aiki tare ta aika wa sauran abokan aikinmu saƙo cewa ban iya aiki ba. Abin ya dame ni sosai. Amma sai na tambayi kaina, ‘Ta yaya zan yi koyi da Yesu sa’ad da nake sha’ani da wannan matar?’ Bayan da na yi tunani a kan irin matakin da Yesu zai ɗauka da a ce shi ne, sai na tsai da shawara cewa zan yafe mata. Bayan wani lokaci, sai na ji cewa matar nan tana fama da wani ciwo kuma tana baƙin ciki sosai. Sai na gane cewa wataƙila ta rubuta abin ba da niyyar ɓata mini rai ba, amma yanayin da take ciki ne ya sa ta yi hakan. Yin bimbini a kan misalin da Yesu ya kafa sa’ad da yake fushi ya taimaka min kada in yi fushi da abokiyar aikina, amma in ƙaunace ta.” A gaskiya, idan muka bi misalin Yesu, za mu riƙa nuna ƙauna.

Na uku, ka koyi yadda za ka riƙa nuna ƙauna ba tare da son kai ba don wannan halin ne yake sa mutane su gane Kiristoci na gaske. (Yoh. 13:​34, 35) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu yi koyi da Yesu ta wajen nuna “wannan hali.” Da ya zo duniya, “ya wofinta kansa da ya ɗauki surar bawa” a madadin mu “har mutuwa.” (Filib. 2:​5-8) Idan muka yi koyi da irin ƙaunar da Yesu ya yi, za mu kasance da ra’ayin  Kristi kuma hakan zai sa mu yi sha’ani da mutane ba tare da son kai ba. Wane ƙarin sakamako kuma ake samuwa idan aka nuna ƙauna?

NUNA ƘAUNA YANA KAWO SAKAMAKO MAI KYAU

Za mu sami albarka sosai idan muna nuna ƙauna. Ka yi la’akari da misalai guda biyu:

Ta yaya muke amfana idan muna nuna ƙauna?

  • ’YAN’UWANMU A FAƊIN DUNIYA: Da yake muna ƙaunar juna sosai, muna ta tabbaci cewa kowace ikilisiya da muka je a faɗin duniya, ’yan’uwan da ke wurin za su karɓe mu da hannu bibbiyu. Yadda ’yan’uwanmu ‘da ke faɗin duniya’ suke ƙaunarmu albarka ce sosai, ko ba haka ba? (1 Bit. 5:9) Shin ban da ƙungiyar Jehobah, akwai wurin da za mu ga mutane suna ƙaunar juna sosai?

  • SALAMA: Idan muna ‘haƙuri da juna cikin ƙauna’ hakan zai taimaka mana mu kasance da “salama” da juna. (Afis. 4:​2, 3) Muna ganin wannan haɗin kai da salama sa’ad da muka je manyan taro da taron ikilisiya. Kana ganin irin wannan haɗin kan a wani wuri ban da ƙungiyar Jehobah? (Zab. 119:165; Isha. 54:13) Idan muna ƙoƙari mu yi zaman lafiya da mutane, hakan yana nuna cewa muna ƙaunarsu kuma Jehobah ma yana farin ciki.​—Zab. 133:​1-3; Mat. 5:9.

ƘAUNA TANA DA BAN ƘARFAFA

Bulus ya ce: “Ƙauna kuwa takan inganta” mu. (1 Kor. 8:​1, Littafi Mai Tsarki) Ta yaya ƙauna take hakan? A sura ta sha uku ta wasiƙar da Bulus ya rubuta wa ’yan’uwa a Koranti ya bayyana yadda ƙauna take inganta ko ƙarfafa mu. Idan mutum yana da ƙauna, yana tunanin yadda halinsa zai iya shafan wasu. (1 Kor. 10:24; 13:5) Ban da haka ma, idan mutum yana da ƙauna, yana la’akari da wasu, yana tausayinsu, yana musu nasiha kuma ya ƙarfafa iyalai kuma hakan yana sa a kasance da haɗin kai a ikilisiya.​—Kol. 3:14.

Akwai hanyoyi da yawa da za mu riƙa ƙaunar mutane, amma ƙaunar da muke yi wa Allah ce ta fi muhimmanci da ban ƙarfafa. Me ya sa? Domin wannan ƙaunar tana sa mu zama da haɗin kai. Mutane daga dukan kabilu da harsuna da ƙasashe suna bauta wa Jehobah “da zuciya ɗaya.” (Zaf. 3:9) Bari dukanmu mu tsai da shawarar nuna irin wannan hali na ’yar ruhu a harkokinmu na yau da kullum.

^ sakin layi na 2 Wannan ne talifi na farko cikin jerin talifofi guda tara da za mu wallafa da za a tattauna ’ya’yan ruhu ɗaya bayan ɗaya.