Me ya sa abin da Matta da Luka suka rubuta game da rayuwar Yesu ya bambanta?

Abin da Matta ya rubuta game da haihuwar Yesu da kuma rayuwarsa na farko ya bambanta da wanda Luka ya rubuta. Hakan ya faru ne domin kowannensu ya ba da labarin Linjilar bisa ga abin da ya mai da wa hankali da abubuwan da ya sani a rayuwa.

Littafin Matta ya mai da hankali ne ga abubuwan da suka shafi Yusufu. Ya faɗi yadda Yusufu ya ji a lokacin da Maryamu take da juna biyu da kuma mafarkin da ya yi sa’ad da wani mala’ika ya bayyana masa yanayin da kuma yadda ya amince da bayanin da aka masa. (Mat. 1:​19-25) Ƙari ga haka, Matta ya ba da labarin mafarkin da Yusufu ya yi sa’ad da mala’ikan ya umurce shi ya ƙaura zuwa ƙasar Masar da iyalinsa. Ban da haka ma, Matta ya faɗi mafarkin da Yusufu ya yi sa’ad da mala’ikan ya ce masa ya koma ƙasar Isra’ila, da kuma yadda ya zauna a Nazarat da iyalinsa. (Mat. 2:​13, 14, 19-23) A surori na farko da ke littafin Linjilar Matta a asalin rubutu na Littafi Mai Tsarki, marubucin ya ambata sunan Yusufu sau takwas amma na Maryamu sau huɗu.

Amma Linjilar Luka ta mai da hankali ga labarin Maryamu. Kuma a labarin ya ambata yadda mala’ika Jibra’ilu ya kai wa Maryamu ziyara da kuma ziyarar da Maryamu ta kai wa ’yar’uwarta mai suna Alisabatu har da kalaman da Maryamu ta yi don ta yabi Jehobah. (Luk. 1:​26-56) Ban da haka ma, Luka ya ambata abin da Siman ya faɗa wa Maryamu game da yadda Yesu zai sha wahala a nan gaba. A labarin ziyarar haikali da Yesu da iyayensa suka yi a lokacin da yake ɗan shekara 12, Luka ya ambata abin da Maryamu ta faɗa amma bai ambata na Yusufu ba. Ban da haka, Luka ya faɗa cewa abubuwan da suka faru sun shafi Maryamu sosai. (Luk. 2:​19, 34, 35, 48, 51) A surori biyu na farko a Linjilar Luka, an ambata sunan Maryamu sau goma sha biyu, amma na Yusufu sau uku kawai. Hakan ya nuna mana cewa Matta ya mai da hankali ga abubuwan da Yusufu ya yi amma Luka kuma ya fi mai da hankali ga abubuwan da Maryamu ta yi.

Ban da haka ma, yadda suka lissafa zuriyar Yesu ya bambanta. Matta ya soma lissafa kakannin Yusufu don ya nuna cewa ɗan riƙon Yusufu wato Yesu shi ne ya cancanci ya gāji sarautar Dauda. Me ya sa? Dalilin shi ne Yusufu zuriyar Sarki Dauda ne, don ya fito daga zuriyar Sulemanu ɗan Dauda. (Mat. 1:​6, 16) Amma Luka ya lissafa zuriyar Maryamu don ya nuna cewa har ila Yesu ne ya cancanta ya gāji sarautar Dauda bisa “ga zancen jiki.” (Rom. 1:3) Me ya sa? Dalilin shi ne Maryamu zuriyar Sarki Dauda ne, don ta fito daga wurin ɗan Dauda mai suna Nathan. (Luk. 3:31) Amma me ya sa Luka bai lissafa Maryamu a matsayin ’yar Hali ba, tun da shi ne mahaifinta? Dalilin shi ne ana yin lissafin zuriyar mutane ta wurin mazan ne ba ta wurin matan ba. Don haka, lissafa Yusufu a matsayin ɗan Hali da Luka ya yi ya nuna cewa Yusufu surukin Hali ne.​—Luk. 3:23.

Lissafin zuriyar Yesu da Matta da Luka suka yi ya nuna cewa Yesu shi ne Almasihun da aka annabta cewa zai zo. Ƙari ga haka, an san wannan labarin sosai don har Farisawa da Sadukiyawa ma ba su iya musanta ƙirgen ba. Kuma a yau, ƙirgen zuriyar Yesu da Matta da Luka suka yi yana cikin abubuwan da suke taimaka mana mu kasance da bangaskiya kuma mu gaskata cewa Allah zai cika dukan alkawuran da ya yi.