A ƘARSHEN watan Nuwamba na shekara ta 1932 a babban birnin Meziko wurin da mutane fiye da miliyan ɗaya suke zama, ya yi wajen sati ɗaya yanzu da aka saka danjar ba da hannu. Amma akwai wani abin da ya fi sa mutanen farin ciki. ’Yan rahoto da kamaransu sun je tashar jirgin ƙasa suna jiran wani babban baƙo ya iso ƙasar. Wane ne wannan mutumin? Joseph F. Rutherford ne wanda a lokacin shi ne shugaban Watch Tower Society. Shaidun Jehobah da suke zama a wurin ma sun zo don su marabce ɗan’uwa Rutherford zuwa babban taro na kwana uku da za a yi a ƙasar.

Mujallar Golden Age ta ce: “Babu shakka, a tarihi za a riƙa tuna wannan babban taron a matsayin wani abu mai muhimmanci da aka yi” don a yaɗa bishara a ƙasar Meziko. Amma mene ne ya sa wannan taron yake da muhimmanci haka, tun da wajen mutane 150 ne kawai suka halarci taron?

Kafin taron nan, ba dukan mutane ba ne a Meziko suka ji wa’azin Mulkin Allah. Tun daga shekara ta 1919, ana yin ƙananan taro amma bayan wasu shekaru ikilisiyoyin sun ragu. Ana ganin abubuwa za su gyaru da aka kafa ofishin Shaidun Jehobah a babban birnin Meziko a shekara ta 1929, sai dai akwai wasu ƙalubalen. An umurci majagaba cewa su daina yin kasuwanci sa’ad da suke yin wa’azi, wannan umurnin ya ba ma wani majagaba haushi, don haka ya daina bauta wa Jehobah kuma ya je ya kafa na sa cocin. Ban da haka ma, wani da yake kula da ofishin a lokacin ya yi wasu abubuwan da ba su dace ba, kuma aka kwace matsayinsa. Don wannan yanayin Shaidun da ke Meziko suna bukatar ƙarfafa.

A lokacin da ɗan’uwa Rutherford ya kai musu ziyara ya ba da jawabin da ya ƙarfafa ’yan’uwan, ya ba da jawabai guda biyu a taron da kuma guda biyar a tashar rediyo. Wannan shi ne lokaci na farko da ’yan’uwan suka yi amfani da rediyo don su yi wa’azi a dukan Meziko. Bayan taron, an naɗa sabon mai kula da ofishin Shaidun Jehobah don ya riƙa tsara ayyukan da za su yi. Yanzu Shaidun sun samu ƙarfin gwiwan ci gaba da yin wa’azi kuma Jehobah ya albarkace su.

Babban taron shekara ta 1941 a babban birnin Meziko

A shekara ta gaba an yi taro guda biyu a ƙasar, ɗaya a birnin Veracruz ɗaya kuma a babban birnin Meziko. An samu sakamako mai kyau don sun saka ƙwazo a yin wa’azi. A shekara ta 1931 Shaidun Jehobah guda 82 akwai a ƙasar. Amma bayan shekara goma Shaidun sun ƙaru sosai! Mutane 1,000 ne suka zo babban birnin Meziko don su halarci babban taro mai jigo “Free Nation” da aka yi a shekara ta 1941.

“YADDA AKA MAMAYE TITUNA”

A shekara ta 1943, Shaidun Jehobah sun sanar da mutane cewa za a yi babban taro mai jigo “Free Nation” a birane guda 12 a ƙasar Meziko. * Kuma sun yi  hakan ta wajen rataye fosta guda biyu gaba da baya a jikinsu. Tun daga shekara ta 1936 Shaidun Jehobah suna sanar da mutane cewa za su yi babban taro.

Mujallar shekara ta 1944 da ya nuna fostar da Shaidu suka rataye suna sanar da mutane game da babban taro da za su yi a birnin Meziko

Jaridar La Nación ta bayyana yadda Shaidun Jehobah suka fita don su gayyato mutane, ta ce: “A ranar farko na taron, an umurci Shaidun su gayyaci wasu mutane don su halarci taron. Kuma a rana ta biyu, mutanen da suka halarci taron sun fi na dā yawa.” Wannan gayyatar da Shaidun suka yi ya sa limaman cocin Katolika suka soma yi wa Shaidun Jehobah hamayya. Ban da haka ma, an sake faɗa a jaridar cewa: “Mutanen birnin duka sun ga Shaidun . . . da fosta a rataye a jikinsu suna sanar da mutane cewa suna da babban taro.” A jaridar an saka hotunan ’yan’uwa a kan titin Meziko da fosta a jikinsu. Kuma a ƙarƙashin hoton an rubuta: “Yadda aka mamaye tituna.”

“GADAJEN SUN FI ƘASA LAUSHI DA ƊIMI”

Kafin yawancin Shaidun Jehobah su halarci babban taro da ake yi a Meziko a dā, suna bukatar su yi sadaukarwa sosai. ’Yan’uwa da yawa sun zo daga ƙauyukan da ba su da hanyar mota kuma jirgin ƙasa ba ya zuwa wurin. Shi ya sa ’yan’uwa a wata ikilisiya suka rubuto cewa: “Babu wani jirgin ƙasa da yake zuwa inda muke.” Saboda irin wannan yanayin, ’yan’uwa da yawa sun yi tafiya a kan jaki ko kuma da ƙafa na kwanaki da yawa kafin su iso tashar jirgin ƙasar da zai kai su birnin da za a yi taron.

Yawancin Shaidun talakawa ne, kuma samun kuɗin tafiya kawai zuwa babban taro yana yi musu wuya. Da suka iso birnin, Shaidu da yawa sun zauna a gidajen wasu ’yan’uwa da ke wurin kuma sun marabce su da hannu bibbiyu. Wasu kuma sun kwana a Majami’ar Mulki. Akwai wani lokacin da mutane 90 suka kwana a ofishin Shaidun Jehobah da ke wurin, a wurin an ba su “kwalayen littattafai guda 20 don su kwana a kai.” An faɗa a Yearbook cewa ’yan’uwan sun ji daɗi har ma suka ce “gadajen sun fi ƙasa laushi da ɗimi.”

Shaidun sun yi farin ciki sosai don sun haɗu da ’yan’uwa da yawa kuma hakan ya sa sun gane cewa sadaukarwa da suka yi ba a banza ba. A yau, Shaidun Jehobah kusan miliyan ɗaya da ke wurin suna da irin wannan ra’ayin. * Wani rahoton ofishin Shaidun Jehobah na shekara ta 1949 a Meziko, ya yi magana game da ’yan’uwa da ke wurin kuma ya ce: “Duk da cewa rayuwa ba ya musu sauƙi, hakan bai sa sun daina kasancewa da ƙwazo a bautarsu ga Jehobah ba, saboda kowane babban taro muka yi, jigon ne za su riƙa magana a kai, kuma abin da ’yan’uwa suke yawan tambaya shi ne yaushe za mu yi wani babban taro kuma?” Haka ma yake a yau.​—Daga tarihinmu a Amirka ta Tsakiya.

^ sakin layi na 9 Kamar yadda Yearbook na shekara ta 1944 ya ce wannan taron ya sa mutane suka san Shaidun Jehobah sosai a Meziko.

^ sakin layi na 14 A Meziko mutane guda 2,262,646 ne suka halarci Taron Tuna da Mutuwa Yesu na shekara ta 2016.