Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro (Ta Nazari)  |  Afrilu 2017

Mene ne Mulkin Allah Zai Kawar?

Mene ne Mulkin Allah Zai Kawar?

‘Duniya ma tana wucewa, duk da sha’awarta: amma wanda ya aika nufin Allah zai zauna har abada.’1 YOH. 2:17.

WAƘOƘI: 134, 24

1, 2. (a) A wace hanya ce wannan muguwar duniya take kama da mugun mutumin da ake so a kashe? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Yaya waɗanda suke sama da duniya za su ji bayan an halaka wannan muguwar duniya?

KA YI tunanin wannan yanayin. An fito da wani mugun mutum daga fursuna da aka yanke masa hukuncin kisa, kuma ana kai shi wurin da za a bindige shi. Ko da yake mutumin yana da koshin lafiya, an riga an yanke masa hukuncin kisa kuma ba abin da zai iya hana a kashe shi.

2 Wannan muguwar duniyar da muke ciki tana kama da wannan mugun da ake son a kashe, don an kusa a halaka ta. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duniya ma tana wucewa.” (1 Yoh. 2:17) Jehobah ya riga ya tsai da shawara cewa zai halaka wannan duniyar ba da daɗewa ba, kuma babu shakka zai halaka ta. Amma da akwai bambanci tsakanin wannan kwatancin da yadda ƙarshen duniya zai kasance. Wasu mutane suna iya ganin cewa hukuncin da aka yi ma mugun mutumin nan bai dace ba kuma su soma zanga-zanga da fatan cewa ba za a kashe shi ba. Amma, Jehobah ba ya kuskure a shari’arsa, kuma shawarar da ya tsai da cewa zai halaka wannan duniyar ya dace. (K. Sha. 32:4) Ba za a ɓata lokaci wajen halaka wannan  duniyar ba. Bayan haka, kowa da ke sama da duniya zai fahimci cewa hukuncin da Jehobah ya yanke daidai ne. Mutane ba za su sha wahala ba!

3.Waɗanne abubuwa huɗu da Mulkin Allah zai kawar za mu bincika?

3 Mene ne wannan “duniya” da ke “wucewa” ta ƙunsa? Ta ƙunshi ayyuka marasa kyau na yau da kullum da mutane suke yi. Shin hakan labari ne mai daɗi? Ƙwarai kuwa, domin yana cikin ‘bishara ta Mulki’ da muke gaya wa mutane. (Mat. 24:14) Za mu bincika abubuwa huɗu da Mulkin Allah zai kawar. Waɗannan sun ƙunshi, mugayen mutane da mugayen ƙungiyoyi da ayyuka marar kyau da kuma abubuwan da ba su dace ba. A kowannensu, za mu bincika (1) yadda waɗannan abubuwan suke shafan mu a yau, (2) abin da Jehobah zai yi game da su, da kuma (3) yadda zai sauya su da abubuwa masu kyau.

MUGAYEN MUTANE

4. A waɗanne hanyoyi ne mugayen mutane suke shafanmu a yau?

4 Ta yaya mugayen mutane suke shafanmu a yau? Bayan da manzo Bulus ya annabta cewa a kwanaki na ƙarshe ‘mugayen zamanu za su zo,’ ya rubuta cewa: ‘Mugayen mutane da [“masu ruɗu,” New World Translation] za su daɗa mugunta gaba gaba.’ (2 Tim. 3:1-5, 13) Waɗannan abubuwa suna faruwa a yau? Hakika, domin da yawa daga cikinmu mun sha wahala a hannun mazalunta da masu nuna wariyar da masu ƙiyayya. Wasu a cikinsu ba sa ɓoye mugayen ayyukan da suke yi, wasu kuma suna yi kamar suna taimaka wa mutane, amma da gaske mugaye ne. Ko da a ce ba mu taɓa faɗawa a hannun mugaye ba, duk da haka, halayensu suna shafan mu domin muna baƙin ciki sosai sa’ad da muka ji yadda suke zaluntar yara da tsofaffi da wasu da ba su da masu taimako. Waɗannan mugayen mutane suna yin abubuwa kamar dabbobi ko kuma aljannu. (Yaƙ. 3:15) Abin farin ciki shi ne Kalmar Jehobah ta sa mu kasance da bege.

5. (a) Wane zarafi ne har ila mugaye suke da shi? (b) Mene ne zai faru da waɗanda suka ƙi su tuba?

5 Mene ne Jehobah zai yi? A yanzu, Jehobah yana ba mugayen mutane damar su canja halinsu. (Isha. 55:7) Ko da yake ba da daɗewa ba, Allah zai halaka duka tsarin da Shaiɗan yake amfani da shi, bai yi wa mugayen mutane shari’a ba tukun. Amma a lokacin ƙunci mai girma, mene ne zai faru da waɗanda suka ƙi su tuba kuma suka ci gaba da bin tsarin da Shaidan yake amfani da shi? Jehobah ya yi alkawari cewa zai kawar da dukan mugayen mutane daga duniya. (Karanta Zabura 37:10.) Mugaye suna iya ganin cewa sun tsira don suna ɓoye abubuwan da suke yi, kuma sau da yawa ba a hukunta su. (Ayu. 21:7, 9) Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idanun [Allah] suna duban tafarkun mutane, Yana kuwa ganin dukan hanyoyinsa. Babu wani duhu, ko inuwar mutuwa, inda masu-aika mugunta za su ɓuya.” (Ayu. 34:21, 22) Babu wani mugun da zai ruɗi Jehobah, don yana ganin kome da mugaye suke yi. Bayan yaƙin Armageddon, za mu nemi mugaye amma ba za mu ƙara ganinsu ba!Zab. 37:12-15.

6. Su waye ne za su kasance a duniya sa’ad da aka kawar da mugayen mutane, kuma me ya sa wannan labari ne mai daɗi?

6 Su wane ne za su kasance a duniya sa’ad da aka halaka mugayen mutane? Jehobah ya yi alkawari cewa: “Masu-tawali’u za su gāji ƙasar; za su faranta  zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.” Daga baya kuma ya ce: “Masu-adalci za su gāji ƙasar, su zauna a cikinta har abada.” (Zab. 37:11, 29) Su waye ne “masu-tawali’u” da “masu-adalci”? Masu tawali’u su ne waɗanda suka amince da koyarwar Jehobah kuma suke yi masa biyayya. Masu adalci kuma su ne waɗanda suke son yin abin da ya dace a gaban Jehobah. A wannan duniyar, mugaye sun fi masu adalci yawa. Amma a sabuwar duniya, masu adalci ne kaɗai za su kasance a wannan duniya kuma su mai da ita aljanna.

MUGAYEN ƘUNGIYOYI

7. Ta yaya mugayen ƙungiyoyi suke sa mu sha wahala a yau?

7 Ta yaya mugayen ƙungiyoyi suke sa mu sha wahala a yau? Ƙungiyoyi ne suke jawo yawancin muguntar da ake yi a wannan duniyar ba mutane ba ne. Ƙungiyoyin addinai suna ruɗin mutane da yawa. Alal misali, suna ƙarya game da Allah kuma sun ce ba za a iya dogara da Littafi Mai Tsarki ba, kuma ba sa gaya mutane gaskiya game da abin da zai faru da duniya da kuma ‘yan Adam a nan gaba ba. Mugayen ƙungiyoyi ne suke jawo yaƙe-yaƙe da tashin hankali tsakanin ƙabilu da kuma zaluntar talakawa da waɗanda ba su da masu taimako. Gwamnatocin da suke cin hanci da rashawa suna daɗa zama masu arziki da iko da kuma son kai. Wasu ƙungiyoyi masu haɗama kuma suna gurɓata mahalli, suna ɓata arzikin ƙasa kuma suna wulaƙanta mutane don su sa wasu su yi arziki yayin da miliyoyi suke fama da talauci. Hakika, mugayen ƙungiyoyi ne suke haddasa yawancin matsalolin da mutane suke fuskanta a yau.

8. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce zai faru da ƙungiyoyin da mutane suke ganin suna da ƙarfi sosai?

8 Mene ne Jehobah zai yi? Za a soma ƙunci mai girma sa’ad da rukunin siyasa suka kai wa dukan addinan ƙarya hari. Kuma Littafi Mai Tsarki ya kira waɗannan ƙungiyoyin addinan ƙarya ƙaruwa, wato Babila Babba. (R. Yoh. 17:1, 2, 16; 18:1-4) Za a halaka waɗannan ƙungiyoyin addinan ƙarya gabaki ɗaya. Mene ne zai faru da sauran mugayen ƙungiyoyin? Littafi Mai Tsarki ya kwatanta su da tuddai da yankunan da ke kusa da teku da kuma mutanen da suke ganin ba abin da zai iya same su. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 6:14.) Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za a halaka gwamnatoci da dukan ƙungiyoyin da ba sa goyon bayan Mulkin Allah. Wannan ne zai zama sashe na ƙarshe na ƙunci mai girma. (Irm. 25:31-33) Bayan hakan, mugayen ƙungiyoyi ba za su ƙara kasancewa ba.

9. Me ya sa muke da tabbaci cewa za a tsara duniya da kyau?

9 Da me Jehobah zai sauya mugayen ƙungiyoyi? Bayan yaƙin Armageddon, akwai ƙungiyar da za ta rage a duniya? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bisa ga alkawarinsa, muna sauraron sababbin sammai da sabuwar duniya, inda adalci yake zaune.” (2 Bit. 3:13) Tsofaffin sammai da duniya suna nufin mugayen gwamnatoci da kuma mutanen da ke ƙarƙashinsu. Mene ne zai sauya su bayan an kawar da su? Furucin nan “sababbin sammai da sabuwar duniya” yana nufin cewa za a kafa sabuwar gwamnati da sabuwar duniya kuma wannan gwamnatin ce za ta yi sarauta bisa sabuwar duniya. Yesu sarkin wannan gwamnati zai yi koyi da Jehobah, Allah mai tsara abubuwa da kyau. (1 Kor. 14:33, NW ) Saboda haka, za a  tsara “sabuwar duniya” da kyau. Mutane masu adalci ne za su kula da harkokin duniyar. (Zab. 45:16) Yesu da abokan sarautarsa 144,000 ne za su yi wa mutane ja-gora. A lokacin, ƙungiya ɗaya ce mai haɗin kai da ba ta rashawa za ta sauya dukan mugayen ƙungiyoyi da ke wannan duniyar!

AYYUKAN DA BA SU DACE BA

10. Waɗanne irin ayyuka marasa kyau ne suka fi yawa a inda kake zama, kuma ta yaya hakan yake shafanka da iyalinku?

10 Ta yaya ayyukan da ba su dace ba suke shafanmu a yau? Muna zama a duniyar da lalata da rashin gaskiya da mugunta suka zama ruwan dare gama gari. Masu shirya fina-finai da abubuwan nishaɗi suna sa mutane suka riƙa tunanin cewa yin irin waɗannan abubuwa yana da kyau. Ƙari ga haka, suna sa mutane su riƙa taƙa ƙa’idodin Jehobah a kan abubuwan da suka dace da waɗanda ba su dace ba. (Isha. 5:20) Ya kamata iyaye musamman su yi iya ƙoƙarinsu don su kāre kansu da yaransu daga irin waɗannan abubuwan. Hakika, ya kamata dukan Kiristoci na gaskiya su yi aiki tuƙuru don su kāre dangantakarsu da Jehobah a wannan duniyar da ba ta daraja ƙa’idodin Allah.

11. Mene ne muka koya daga hukuncin da Jehobah ya yi wa Saduma da kuma Gwamarata?

11 Mene ne Jehobah zai yi game da ayyukan da ba su dace ba? Ka yi la’akari da abin da Jehobah ya yi wa biranen Gwamarata da Saduma don mugayen abubuwan da suka yi. (Karanta 2 Bitrus 2:6-8.) Lutu mutumi ne mai adalci, amma shi da iyalinsa sun sha wahala sosai domin mugayen abubuwan da mutane suke yi a biranen. Jehobah ya halaka dukan waɗannan wuraren don ya kawar da mugayen abubuwan da ake yi a wurin. Ƙari ga haka, yana son abin da ya yi ya zama “abin nuni ga” mugaye. Kamar yadda Jehobah ya kawar da mugayen ayyuka a lokacin, haka zai kawar da mugayen abubuwan da ake yi a yau sa’ad da ya kawo ƙarshen wannan zamanin.

12. Waɗanne ayyuka ne za ka so ka yi a lokacin da aka kawar da wannan zamanin?

12 Mene ne za su sauya ayyukan da ba su dace ba? A sabuwar duniya, za mu yi ayyuka da yawa da za su sa mu farin ciki. Alal misali, za mu mai da wannan duniyar ta zama aljanna kuma mu gina wa kanmu da abokanmu gidaje masu kyau. Ƙari ga haka, za mu marabci miliyoyin mutane da za a ta da su daga mutuwa kuma mu koya musu game da Jehobah da dukan abubuwan da ya yi wa ‘yan Adam. (Isha. 65:21, 22; A. M. 24:15) A wannan lokacin, za mu shagala da ayyukan da za su sa mu farin ciki kuma mu yabi Jehobah!

MUMMUNAN YANAYI

13. Mene ne tawayen da Shaiɗan da Adamu da kuma Hauwa’u suka yi ya jawo?

13 Ta yaya mummunan yanayi yake shafanmu a yau? Mugayen mutane da ƙungiyoyi da kuma ayyuka marasa kyau da ake yi suna jefa mutane cikin mawuyacin hali. Ƙari ga haka, yaƙi da talauci da wariyar launin fata da rashin lafiya da kuma mutuwa na shafan dukan mutane. Muna cikin wannan mummunan yanayin ne domin Shaiɗan da Adamu da Hauwa’u sun yi wa Jehobah tawaye. Tawayen da suka yi ya shafi dukan mutane.

14. Mene ne Jehobah zai yi game da mummunan yanayi da muke ciki a yau? Ka ba da misali.

14 Mene ne Jehobah zai yi game da mummunan yanayin da muke ciki a yau? Ka yi la’akari da wasu cikin abubuwan da ya ce zai kawar. Ya yi alkawari zai kawar da  yaƙe-yaƙe. (Karanta Zabura 46:8, 9.) Zai kawar da rashin lafiya. (Isha. 33:24) Zai haɗiye mutuwa har abada! (Isha. 25:8) Zai cire talauci. (Zab. 72:12-16) Ƙari ga haka, Jehobah zai kawar da dukan mummunan yanayi da suke wahalar da mu a yau. Ban da haka ma, zai kawar da mugun tasirin Shaiɗan da aljannunsa.—Afis. 2:2.

Ka yi tunanin yadda duniya za ta kasance idan babu yaƙi da rashin lafiya da kuma mutuwa! (Ka duba sakin layi na 15)

15. Waɗanne abubuwa ne za a kawar bayan yaƙin Armageddon?

15 Ka yi tunanin yadda wannan duniyar za ta kasance idan ba a yaƙi da rashin lafiya ko kuma mutuwa. Babu sojoji da makamai kuma ba za a yi bikin tunawa da waɗanda suka mutu ba. Ba za mu bukaci asibitoci da likitoci da nas-nas da ɗakin ajiye gawawwaki da makabarta ko kuma masu ɗaukan gawa ba. Ƙari ga haka, za a kawar da mugunta, ba za mu bukaci ‘yan sanda ba da ƙungiyoyin tsaro, kuma ba za mu saka ƙararrawa a gidajenmu ba. Wataƙila ba za mu riƙa kulle ƙofofinmu da makulli ba. Za a kawar da dukan waɗannan mummunan yanayi da ke sa mu damuwa.

16, 17. (a) Yaya waɗanda suka tsira daga yaƙin Armageddon za su ji? Ka ba da misali. (b) Ta yaya za mu kasance da tabbaci cewa za mu ci gaba da rayuwa bayan an kawar da wannan duniyar?

16 Wane irin rayuwa za mu yi bayan an kawar da mummunan yanayi? Ba za mu iya kwatanta irin jin daɗin da za mu yi a sabuwar duniya ba. Me ya sa? Don shan wahalar ya zama jininmu. Alal misali, mutane da suke zaune kusa da tashar jirgin ƙasa sun saba da ƙarar jirgi har abin baya daminsu. Haka ma, mutanen da suke zaune kusa da inda ake zubar da shara sun saba da warinsa. Amma mutane ba za su ƙara shan wahala ba sa’ad da Jehobah ya kawar da dukan mummunan yanayi daga wannan duniyar!

17 Me zai sauya matsalolin da muke fuskanta a yau? Zabura 37:11 ta ce: “Za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.” Waɗannan kalmomin suna da ban ƙarfafa, don irin yanayin da Jehobah yake so mu kasance a ciki ke nan. Saboda haka, ka yi iya ƙoƙarinka don ka kusanci Jehobah kuma kada ka daina tarayya da ƙungiyarsa a waɗannan mawuyacin kwanaki na ƙarshe. Abubuwa masu kyau da kake bege za su faru a nan gaba suna da tamani sosai, don haka, zai dace ka riƙa tunani sosai a kan su kuma ka tabbatar wa kanka cewa hakan zai faru da gaske. Ban da haka, ka yi wa mutane wa’azi game da begen da kake da shi. (1 Tim. 4:15, 16; 1 Bit. 3:15) Idan ka yi hakan, za ka kasance da tabbaci cewa ba za a halaka wannan muguwar duniyar tare da kai ba. Maimakon haka, za ka yi rayuwa har abada cikin farin ciki!