Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Shin Wa’azin da Kake Yi Yana Kamar Raba Ne?

Shin Wa’azin da Kake Yi Yana Kamar Raba Ne?

WA’AZIN da muke yi yana da muhimmanci kuma yana amfanar mutane. Amma ba duka mutanen da muke yi musu wa’azi ne suke fahimtar hakan ba. Ko da yake suna son su ji abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa, ba sa ganin yana da muhimmanci mu yi nazarin Kalmar Allah da su.

Alal misali, Gavin yana halartan taro a Majami’ar Mulki, amma ba ya son a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Gavin ya ce bai san Littafi Mai Tsarki sosai ba kuma ba ya son mutane su san hakan. Ba ya son a ce ya soma bin wani addini don yana ganin hakan yaudara ce. Shin kana ganin taimaka wa Gavin ya kasance da sauƙi ne? Ka yi tunanin yadda koyarwar Littafi Mai Tsarki zai iya ratsa zuciyar mutum. Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa cewa: “Zancena ya yi tururi kamar raɓa; kamar yayyafi bisa yabanya.” (Kubawar Shari’a 31:19, 30; 32:2) Bari mu koyi wasu abubuwa game da raɓa kuma mu ga yadda hidimarmu take da alaƙa da raɓa don hakan zai sa mu ƙware sa’ad da muke taimaka wa “dukan mutane.”1 Timotawus 2:3, 4.

 TA YAYA WA’AZIN DA MUKE YI ZAI IYA ZAMA KAMAR RAƁA?

Raɓa tana sauka a hankali. Raɓa tana somawa ne da danshi a iska kuma daga baya ta zama ruwa kuma ta soma ɗiga. Ta yaya furucin Jehobah “ya yi tururi kamar raɓa”? Ya bi da mutanensa a hankali kuma ya nuna musu ƙauna sa’ad da yake yi musu magana. Idan muka nuna wa mutane cewa ra’ayinsu yana da muhimmanci, muna yin koyi da Musa. Muna taimaka musu su yi tunani a kan wani batu kuma su yanke shawara da kansu. Sa’ad da muka nuna cewa muna ƙaunar mutane yayin da muke yi musu wa’azi, za su so su saurari abin da muke faɗa kuma hakan zai sa su saurare mu.

Raɓa tana wartsakarwa. Wa’azin da muke yi zai kasance da daɗin ji idan muka yi tunanin hanyoyi dabam-dabam da za mu iya taimaka wa mutane su koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Wani ɗan’uwa mai suna Chris, ya gaya wa Gavin cewa yana so ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi, amma bai tilasta masa ba. A maimakon haka, ya nemi hanyoyi dabam-dabam don ya sa Gavin ya ji daɗin tattaunawa game da Littafi Mai Tsarki. Chris ya gaya wa Gavin cewa akwai wani batu mai muhimmanci da aka bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki kuma idan ya san wannan batun, hakan zai taimaka masa ya ƙara fahimtar abubuwan da ake tattaunawa a taronmu. Bayan haka, sai Chris ya bayyana cewa annabcin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ne ya tabbatar masa cewa Allah ne ya hure Littafi Mai Tsarki. A sakamakon haka, sun tattauna yadda annabce-annabce da yawa suka cika. Wannan tattaunawar da suka yi ya faranta ran Gavin, kuma ya amince a soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.

Raɓa tana rayarwa. A lokacin rani a ƙasar Isra’ila, ana yin watanni da dama babu ruwan sama. Idan babu raɓa, ba za a sami danshi ba. Saboda haka, tsire-tsire za su soma bushewa kuma suna mutuwa. Jehobah ya annabta cewa zamaninmu zai zama kamar lokacin fari ko kuma rashin ruwa, mutane za su yi ƙishi, amma ba na ruwa ba, don “jin maganar Ubangiji.” (Amos 8:11) Ya annabta cewa shafaffu za su zama “kamar rāɓa daga wajen Ubangiji” yayin da suke wa’azin bishara ta Mulki tare da “waɗansu tumaki.” (Mikah 5:7; Yohanna 10:16) Jehobah zai ba da rai ga waɗanda suke son jin wa’azi kuma suka amince da wa’azin da muke yi. Shin muna ɗaukan wannan wa’azin da muhimmanci kuwa?

Raɓa albarka ce daga Jehobah. (Kubawar Shari’a 33:13) Wa’azin bishara da muke yi zai iya zama albarka ga waɗanda suka saurare mu. Nazarin Littafi Mai Tsarki da aka yi da Gavin ya zama albarka a gare shi don hakan ya taimaka masa ya sami amsoshin dukan tambayoyin da suke ci masa tuwo a ƙwarya. Ya sami ci gaba a nazarin da yake yi kuma ya yi baftisma. Yanzu yana yin wa’azin bishara ta Mulkin Allah tare da matarsa, Joyce.

Shaidun Jehobah suna wa’azin bisharar Mulki a ko’ina a duniya

KA DARAJA HIDIMARKA

Idan muka kwatanta aikin bishara da muke yi da raɓa, hakan zai sa mu fahimci cewa ƙoƙarin da kowannenmu yake yi a wa’azin bishara yana da muhimmanci sosai. Ta yaya? Raɓa da ke ɗiga a wani wuri ba za ta cim ma wani abin kirki ba, amma idan ana raɓa gama gari, ko’ina zai yi danshi. Hakazalika, za mu iya tunani cewa abin da kowanenmu yake yi a wa’azi bai taka kara ya karya ba. Amma ka yi la’akari da wannan: Wa’azin da miliyoyin Shaidun Jehobah suke yi, yana sa mutane ‘ko’ina a duniya’ su ji wa’azin bishara. (Matta 24:14, Littafi Mai Tsarki) Idan muka sa hidimarmu ta zama albarka ga mutane, wa’azin bishara da muke yi zai zama kamar raɓa mai sauka a hankali, zai wartsakar da su kuma zai sa su rayu!