Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Ku Nisanta Kanku Daga Harkokin Wannan Duniyar da Babu Hadin Kai

Ku Nisanta Kanku Daga Harkokin Wannan Duniyar da Babu Hadin Kai

“Ku ba . . . Allah kuma abin da ke na Allah.”MATTA 22:21.

WAƘOƘI: 33 137

1. Ta yaya za mu yi biyayya ga Allah da kuma gwamnatocin ‘yan Adam?

LITTAI MAI TSARKI ya ce mu riƙa yi wa gwamnatocin ‘yan Adam biyayya. Kuma ya ce wajibi ne mu riƙa yin biyayya ga Allah a kowane lokaci. (Ayyukan Manzanni 5:29; Titus 3:1) Ta yaya za mu iya yin hakan? Yesu ya bayyana wata ƙa’ida da za ta taimaka mana mu san wanda ya kamata mu yi masa biyayya. Ya ce “Ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar; Allah kuma abin da ke na Allah.” [1] (Ka duba ƙarin bayani.) (Matta 22:21) Muna ba “Kaisar abin da ke na Kaisar” sa’ad da muka bi dokokin gwamnati kuma muka daraja ma’aikatan gwamnati. Ƙari ga haka, ya kamata mu riƙa biyan haraji. (Romawa 13:7) Amma sa’ad da gwamnati ta bukace mu mu yi abin da Allah ya haramta, ba ma yarda, duk da haka za mu bayyana musu hakan cikin ladabi.

2. Ta yaya za mu nuna cewa ba ma saka hannu a harkokin siyasa na wannan duniya?

2 Hanya ɗaya da muke ba “Allah . . . abin da ke na Allah” ita ce ta ƙin goyon bayan wani batun siyasa na wannan duniya. Ba ma saka baki a waɗannan batutuwa. (Ishaya 2:4) Ba ma gāba da gwamnatocin ‘yan Adam tun da yake Jehobah ne ya ƙyale su su  riƙa yin sarauta. Ƙari ga haka, ba ma saka hannu a ayyukan da ke nuna kishin ƙasa. (Romawa 13:1, 2) Ba ma goyon bayan canji a gwamnatoci kuma ba ma rinjayar ‘yan siyasa. Ba ma jefa ƙuri’a kuma ba ma harkar siyasa.

3. Me ya sa ya zama wajibi ne mu guji saka hannu a harkokin siyasa da yaƙe-yaƙe da makamantansu?

3 Da akwai dalilai da yawa da suka sa Allah ya gaya mana mu zama ‘yan ba ruwanmu a wannan duniya. Dalili na farko shi ne cewa muna yin koyi da Yesu, wanda yake “ba na duniya ba ne.” Bai saka hannu a siyasa ko kuma yaƙe-yaƙe na wannan duniya ba. (Yohanna 6:15; 17:16) Wani dalili kuma shi ne cewa muna goyon bayan Mulkin Allah. Sa’ad da muke wa’azi cewa Mulkin Allah ne kawai zai magance dukan matsalolin ‘yan Adam, muna yin hakan da zuciya ɗaya da yake ba ma goyon bayan gwamnatocin ‘yan Adam. Addinan ƙarya suna goyon bayan siyasa, kuma hakan yana raba mutane. Amma domin ba ma saka hannu a harkokin siyasa, muna da haɗin kai da ‘yan’uwanmu da ke faɗin duniya.1 Bitrus 2:17.

4. (a) Ta yaya muka san cewa nisanta kanmu daga harkokin siyasa da yaƙi zai daɗa kasancewa da wuya? (b) Me ya sa ya kamata mu yi shiri yanzu don mu guji saka hannu a harkokin siyasa?

4 Wataƙila muna zama a ƙasar da ba a ce lallai sai mun saka hannu a siyasa ba. Amma yayin da muke kusatowa da ƙarshen zamanin Shaiɗan, zai daɗa wuya mu yi zaman ‘yan ba ruwanmu da siyasa. Mutane a yau marasa cika alkawari ne kuma suna da “taurin kai.” Ƙari ga haka, rashin haɗin kai tsakanin mutane zai daɗa ƙaruwa. (2 Timotawus 3:3, 4) Canje-canje na siyasa da aka yi farat ɗaya ya shafi wasu cikin ‘yan’uwanmu a ƙasarsu. Shi ya sa muke bukatar mu kasance a shirye yanzu don mu guji saka hannu a harkokin siyasa ko da yin hakan yana da wuya. Bari mu tattauna abubuwa huɗu da za su taimaka mana mu kasance a shirye.

KA ƊAUKI GWAMNATOCI ‘YAN ADAM YADDA JEHOBAH YAKE ƊAUKANSU

5. Ta yaya Jehobah yake ɗaukan gwamnatocin ‘yan Adam?

5 Wani abu da za mu iya yi don mu yi shiri yanzu mu kasance ‘yan ba ruwanmu shi ne mu ɗauki gwamnatocin ‘yan Adam yadda Jehobah yake ɗaukansu. Sa’ad da Jehobah ya halicci ‘yan Adam, bai ba su ikon sarautar kansu ba. (Irmiya 10:23) A gaban Jehobah, dukan ‘yan Adam iyali ɗaya ne. Amma, gwamnatocin ‘yan Adam suna raba mutane ta wajen yin da’awa cewa ƙasarsu ta fi wasu ƙasashe kyau. Ko da yake wasu gwamnatoci suna taimaka wa talakawansu, babu gwamnatin da za ta iya magance dukan matsaloli. Ƙari ga haka, Allah ya kafa Mulkinsa a shekara ta 1914 kuma gwamnatocin ‘yan Adam suna gāba da Mulkin Allah. Ba da daɗewa ba, wannan Mulkin zai kawar da dukan gwamnatocin ‘yan Adam.Karanta Zabura 2:2, 7-9.

Ka kasance a shirye yanzu don ka guji saka hannu a siyasa har ma a mawuyancin yanayi

6. Ta yaya ya kamata mu bi da masu mulki a gwamnatocin ‘yan Adam?

6 Allah ya ƙyale gwamnatocin ‘yan Adam su yi sarauta domin su sa ‘yan Adam su yi zaman lafiya daidai gwargwado. Hakan yana taimaka mana mu yi wa’azin bishara game da Mulkin Allah. (Romawa 13:3, 4) Ƙari ga  haka, Allah ya gaya mana mu riƙa yin addu’a a madadin masu iko domin mu bauta masa cikin kwanciyar hankali. (1 Timotawus 2:1, 2) Idan an yi mana rashin adalci, muna iya neman taimakon waɗanda suke da iko a gwamnati don su taimaka mana. Abin da Bulus ya yi ke nan. (Ayyukan Manzanni 25:11) Ko da yake Littafi Mai Tsarki ya ce Shaiɗan ne yake ja-gorar gwamnatocin ‘yan Adam, bai ambata ba cewa shi ne yake ja-gorar kowane ma’aikacin gwamnati ba. (Luka 4:5, 6) Saboda haka, bai kamata mu sa wani ya soma tunani cewa Iblis ne yake ja-gorar wani ma’aikacin gwamnati ba. Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya ce kada mu zagi mutane.Titus 3:1, 2.

7. Wane ra’ayi ne za mu guji kasancewa da shi?

7 Idan muna biyayya ga Allah, ba za mu goyi bayan wani ɗan siyasa ko kuma jami’in siyasa ba, ko da a ce za mu amfana daga ra’ayinsu. A wani lokaci, hakan ba zai kasance da sauƙi ba. Alal misali, a ce mutane sun yi tawaye da wata gwamnatin da ta haddasa wahala wa mutane, har ma da Shaidun Jehobah. Hakika, ba za ka bi su sa’ad da suke tawaye ba, amma shin za ka soma yin tunani cewa matakin da ‘yan tawayen suka ɗauka yana da kyau kuma ka riƙa yi musu fata cewa su yi nasara? (Afisawa 2:2) Idan muna so mu kasance ‘yan ban ruwanmu da harkokin siyasa, ya kamata mu guji yin tunani cewa wani rukunin siyasa ya fi wani kyau. Ya kamata furucinmu da ayyukanmu su nuna cewa ba ma goyon baya wani rukunin siyasa.

KA KASANCE ‘MAI AZANCI’ DA KUMA MARAR LAIFI

8. Sa’ad da yake mana wuya mu guji saka hannu a siyasa da yaƙi, ta yaya za mu zama “masu azanci” da kuma marasa laifi?

8 Wata hanya kuma da za mu kasance ‘yan ba ruwanmu da harkokin siyasa ita ce mu zama “masu-azanci . . . kamar macizai, marasa-ɓarna kamar kurciyoyi.” (Karanta Matta 10:16, 17.) Idan muka zama masu azanci za mu yi tunanin abubuwan da za su iya faruwa a nan gaba. Kuma za mu kasance marasa laifi idan muka guji saka hannu a harkokin siyasa a waɗannan mawuyacin yanayi ba. Bari mu tattauna wasu cikin waɗannan yanayi da kuma abubuwan da za mu iya yi don mu kasance ‘yan ba ruwanmu.

9. Me ya sa ya kamata mu yi hattara sa’ad da muke tattaunawa da mutane?

9 Tattaunawa da mutane. Muna bukatar mu guji saka baki sa’ad da mutane suke tattauna batutuwan siyasa. Alal misali, sa’ad da muke wa wani wa’azi game da Mulkin Allah, ba zai dace mu ce mun amince ko ba mu amince da ra’ayin wani rukunin siyasa ko kuma shugaban siyasa ba. Maimakon mu riƙa tattauna abin da ‘yan Adam za su yi don su magance matsalolin da muke fuskanta, ya kamata mu riƙa nuna wa mutane yadda Mulkin Allah zai magance matsalolin ‘yan Adam gaba ɗaya. Idan mutane suna son su yi gardama a kan batutuwan auren jinsi ɗaya ko kuma zubar da ciki, ya kamata mu gaya musu abin da Kalmar Allah ta ce da yadda kake ƙoƙari ka bi umurninta a rayuwarka. Idan wani ya ce yana so a kawar da wasu dokoki ko kuma a canja su, bai kamata mu goyi bayansa ba, kuma kada mu nace cewa mutumin ya canja ra’ayinsa.

10. Ta yaya za mu tabbata cewa ba ma saka hannu a siyasa da yaƙi sa’ad da muke sauraron ko kuma karanta labarai?

10 Kafofin yaɗa labarai. Wani lokaci ana yaɗa labarai a hanyar da ke nuna cewa ana goyon baya wani batu. Ana yin hakan musamman a ƙasashen da kafofin yaɗa labarai suna ƙarƙashin gwamnati. Idan kafofin yaɗa labarai ko kuma ‘yan jarida suka goyi bayan wani rukuni, muna bukatar mu mai  da hankali kada mu kasance da irin ra’ayinsu. Alal misali, ka tambayi kanka, ‘Ina jin daɗin sauraron wani ɗan jarida domin yadda yake ba da rahoto game da siyasa?’ Ka guji kallo ko karanta rahotanni da ke goyon bayan batutuwan siyasa, don hakan zai taimaka maka ka guji saka baki a batun. Maimakon haka, ka yi ƙoƙari ka nemi labarai da ba sa goyon bayan wani rukunin siyasa. Ƙari ga haka, ka riƙa gwada abin da ka ji da “kwatancin sahihiyan kalmomi” da ke rubuce a cikin Littafi Mai Tsarki.2 Timotawus 1:13.

11. Ta yaya zai yi mana wuya mu nisanta kanmu daga harkokin siyasa idan muna son abin duniya?

11 Son abin duniya. Idan muka saka kuɗi da dukiyarmu kan gaba a rayuwa, zai yi mana wuya mu guji saka hannu a batun siyasa. Bayan shekara ta 1970, Shaidun Jehobah da yawa a Malawi sun rasa dukan abubuwan da suka mallaka don sun ƙi goyon bayan wani rukunin siyasa. Amma, abin baƙin ciki shi ne, waɗansu ‘yan’uwa sun kasa barin irin rayuwar jin daɗi da suka yi a dā. Wata ‘yar’uwa mai suna Ruth ta ce, “Wasu sun yi gudun hijira tare da mu amma daga baya sun soma goyon bayan wani rukunin siyasa kuma suka koma gida domin ba su iya sun jimre irin rayuwa da ake yi a sansanin ‘yan gudun hijira ba.” Amma yawancin mutanen Allah ba su yi hakan ba. Sun yi zaman ‘yan ba ruwansu a batun siyasa, ko da yake sun rasa abubuwan da suka mallaka kuma ba su da isashen kuɗi.Ibraniyawa 10:34.

12, 13. (a) Yaya Jehobah yake ɗaukan’yan Adam? (b) Ta yaya za mu iya sani cewa muna yin fahariya game da ƙasarmu?

12 Fahariya. Mutane sukan yi fahariya game da launin fatarsu ko ƙabilarsu ko al’adarsu ko kuma ƙasarsu. Amma a gaban Jehobah, babu mutum ko kuma rukunin mutane da suka fi wasu daraja. Dukanmu ɗaya ne a gare shi. Hakika, Jehobah ya halicce mu dabam da wasu, kuma muna iya yin farin ciki game da hakan. Ba ya son mu ƙi al’adarmu. Amma kuma ba ya son mu riƙa ganin cewa mun fi wasu daraja.Romawa 10:12.

13 Bai kamata mu riƙa fahariya da ƙasar mu ba har mu soma ganin cewa ta fi sauran ƙasashe kyau. Idan muna yin hakan, zai yi mana wuya mu guji saka hannu a batun siyasa. Hakan ya faru a ƙarni na farko. Wasu ‘yan’uwa Ibraniyawa sun yi wa gwaurayen Helenawa rashin adalci. (Ayyukan Manzanni 6:1) Ta yaya za mu san ko mun soma fahariya kamar waɗannan mutanen? Sa’ad da wani ɗan’uwa ko wata ‘yar’uwa da launin fatarmu ko ƙabilarmu ba ɗaya ba ne ta ba mu wata shawara, shin za ka soma tunani cewa, shawarar ba ta da ta kyau kuma ka ƙi shawarar? Idan haka ne, ka tuna da wannan shawara mai muhimmanci: “A cikin tawali’u kowa ya maida wani ya fi kansa.”Filibbiyawa 2:3.

JEHOBAH ZAI TAIMAKE KA

14. Ta yaya yin addu’a zai taimaka mana, kuma wane misali a Littafi Mai Tsarki ne ya nuna hakan?

14 Hanya ta uku da za mu guji saka hannu a batun siyasa ita ce ta wurin dogara ga Jehobah. Ƙari ga haka, ka yi addu’a Jehobah  ya ba ka ruhu mai tsarki, don zai sa ka zama mai haƙuri da kama kai. Waɗannan halayen za su taimaka maka idan gwamnati ta yi rashin adalci. Ka roƙi Jehobah ya ba ka hikima don ka san lokacin da zai yi wuya ka guje wa harkokin siyasa. Ka roƙe shi ya taimaka maka ka yi abin da ya dace a irin wannan yanayin. (Yaƙub 1:5) Kasancewa da aminci ga Jehobah zai iya sa a jefa ka a kurkuku ko kuma a yi maka horo. Idan hakan ya faru da kai, ka yi addu’a ga Jehobah ya ba ƙarfin zuciya don ka bayyana wa wasu dalla-dalla abin da ya sa ka ƙi saka hannu a batun siyasa. Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka maka ka jimre da yanayin.—Karanta Ayyukan Manzanni 4:27-31.

Ka yi nazarin ayoyin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka maka ka guji saka hannu a siyasa da kuma ayoyin da za su taimaka maka ka ga kanka a sabuwar duniya

15. Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu guji saka hannu a siyasa? (Za ka sami ƙarin bayani a cikin akwatin nan “ Kalmar Allah Ta sa Sun Kasance da Gaba Gaɗi.”)

15 Jehobah ya ba mu Littafi Mai Tsarki don ya ƙarfafa mu. Ka yi bimbini a kan ayoyin da za su taimaka maka ka guji saka hannu a batun siyasa. Ka yi ƙoƙari ka san waɗannan ayoyin kuma ka tuna da su, domin za su taimaka maka idan ka sami kanka a cikin yanayin da babu Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki zai iya ƙarfafa ka ka kasance da bege ga abin da Allah ya ce game da nan gaba. Muna bukatar wannan begen don mu jimre da tsanantawa. (Romawa 8:25) Ka zaɓi ayoyin da suka kwatanta abubuwan da kake son ka more a sabuwar duniya, kuma ka riƙa ganin kamar kana wajen.

ZA KA AMFANA DAGA LABARAN AMINTATTUN BAYIN JEHOBAH

16, 17. Mene ne za mu iya koya daga amintattun bayin Allah da suka nisanta kansu daga harkokin siyasa da yaƙi? (Ka duba hoton da ke shafi na 21.)

16 Abu na huɗu da zai taimaka mana mu guji saka hannu a siyasa shi ne yin bimbini a kan misalan da amintattun bayin Jehobah suka kafa. Mutane da yawa a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki suna da gaba gaɗi, kuma sun tsai da shawarwari masu kyau da ya taimaka musu su guji saka hannu a siyasa. Ka yi tunanin Shadrach da Meshach, da kuma Abednego, waɗanda suka ƙi bauta wa sifofi da ke wakiltar gwamnatin Babila. (Karanta Daniyel 3:16-18.) Wannan labarin Littafi Mai Tsarki yana taimaka  wa Shaidu da yawa a yau su kasance da gaba gaɗi kuma su ƙi sara wa tutar ƙasarsu. Yesu bai saka hannu a siyasa ko kuma wasu batutuwa da ke raba mutane ba. Ya san cewa misali mai kyau da ya kafa zai taimaka wa almajiransa. Ya ce: “Ku yi farin ciki, na yi nasara da duniya.”Yohanna 16:33.

17 Shaidu da yawa a zamaninmu sun guji saka hannu a siyasa. An azabtar da wasu cikinsu, an saka wasu a kurkuku, har ma an kashe wasu domin sun kasance da aminci ga Jehobah. Misalin da suka kafa zai iya taimaka mana mu kasance da gaba gaɗi. Wani ɗan’uwa daga ƙasar Turkiya ya ce: “An kashe wani ɗan’uwa matashi mai suna Franz Reiter domin ya ƙi zama sojan Hitler. Wasiƙar da ya rubuta zuwa ga mahaifiyarsa a daren da aka so a kashe shi ya nuna cewa yana da bangaskiya sosai kuma ya dogara ga Jehobah. Kuma zan so in yi koyi da shi sa’ad da na fuskanci irin wannan gwajin.” [2]—Ka duba ƙarin bayani.

18, 19. (a) Ta yaya waɗanda suke cikin ikilisiyarku za su iya taimaka maka ka guji saka hannu a siyasa? (b) Mene ne ka ƙudura niyyar yi a yanzu?

18 ‘Yan’uwa da ke cikin ikilisiyarku za su iya taimaka maka ka guji saka hannu a harkokin siyasa da yaƙi da makamantansu. Idan ka sami kanka a cikin yanayi mai wuya, ka gaya wa dattawa. Za su iya ba ka shawara daga cikin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ‘yan’uwa da ke cikin ikilisiyarku za su ƙarfafa ka idan sun san yanayin da kake ciki. Ka gaya musu su yi addu’a a madadinka. Ya kamata mu ma mu tallafa wa ‘yan’uwanmu kuma mu yi addu’a a madadinsu. (Matta 7:12) Don ka sami sunayen ‘yan’uwa da ke cikin kurkuku, ka duba wani talifi da ke dandalin jw.org/ha mai jigo: “Shaidun Jehobah da Aka Tsare a Kurkuku Saboda Imaninsu—Bisa ga Kasa” da ke sashen LABARAI > LABARAN SHARI’A. Ka zaɓi wasu sunaye, kuma ka roƙi Jehobah ya taimaka wa waɗannan ‘yan’uwa maza da mata su yi ƙarfin zuciya don su kasance da aminci a gare shi.—Afisawa 6:19, 20.

19 Yayin da ƙarshen wannan duniyar yake gabatowa, gwamnatoci za su iya daɗa matsa mana mu goyi bayansu. Saboda haka, yana da muhimmanci mu kasance a shirye yanzu don mu nisanta kanmu daga harkokin wannan duniyar da babu haɗin kai!

^ [1] (sakin layi na 1) Sa’ad da Yesu ya ambaci Kaisar, yana magana ne game da gwamnati. A lokacin, Kaisar ne yake sarauta kuma shi ne mai matsayi mafi girma a gwamnatin ‘yan Adam.

^ [2] (sakin layi na 17) Ka duba akwatin da ke shafi na 150 mai jigo “Ya Mutu don Yana So Ya Ɗaukaka Allah” a cikin littafin nan, Mulkin Allah Yana Sarauta!

Ka riƙa gwada abin da ka ji da “sahihiyan kalmomi” da ke rubuce a cikin Littafi Mai Tsarki