Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Allah Yana Albarkar Wadanda Suka Kasance da Aminci

Allah Yana Albarkar Wadanda Suka Kasance da Aminci

“Ku zama masu koyi da waɗanda ke gāda alkawarai ta wurin bangaskiya da haƙuri.”IBRANIYAWA 6:12.

WAƘOƘI: 86, 54

1, 2. Wane ƙalubale ne Jephthah da ‘yarsa suka fuskanta?

WATA budurwa ta ruga a guje don ta marabci mahaifinta. Tana farin ciki ƙwarai cewa ya je yaƙi kuma ya dawo lafiya. Wannan gagarumin nasara da ya yi ya sa ta soma rawa da waƙa sa’ad da ta gan shi. Amma, abin da mahaifinta ya yi ya ba ta mamaki sosai. Ya yage tufafinsa kuma ya ce: “Kaito, ɗiyata! Kin kashe mani gwiwa ƙwarai.” Bayan haka, sai ya gaya mata cewa ya yi wa Jehobah wani alkawari da zai shafi rayuwarta har abada. Hakan yana nufin cewa ba za ta yi aure ba kuma ba za ta haifi ‘ya’ya ba. Amma, sai ta ba shi amsa mai ƙayatarwa kuma ta ƙarfafa mahaifinta ya cika alkawarin da ya yi wa Jehobah. Amsar da ta bayar ya nuna cewa ta ba da gaskiya cewa duk wani abin da Jehobah ya bukata a gare ta zai amfane ta. (Alƙalawa 11:34-37) Bangaskiyar da ta nuna ya sa mahaifinta farin ciki sosai don ya san cewa hakan zai faranta wa Jehobah rai.

 2 Jephthah da ‘yarsa sun dogara ga Jehobah da kuma yadda yake gudanar da al’amuransa. Sun kasance da aminci duk da cewa a lokacin hakan bai yi musu sauƙi ba. Suna so Allah ya amince da su kuma suna shirye su yi duk wani abin da Jehobah yake bukata don su faranta masa rai.

3. Me ya sa misalin Jephthah da ‘yarsa zai taimaka mana a yau?

3 Kasancewa da aminci ga Jehobah bai da sauƙi. Muna bukata mu ‘dage ƙwarai a kan bangaskiya.’ (Yahuda 3, Littafi Mai Tsarki) Labarin Jephthah da ‘yarsa zai taimaka mana mu yi hakan. Bari mu tattauna yadda suka jure da matsaloli a rayuwarsu. Ta yaya suka kasance da aminci?

KASANCEWA DA AMINCI A DUNIYAR NAN MAI MUGUN TASIRI

4, 5. (a) Wace doka ce Jehobah ya ba wa Isra’ilawa sa’ad da suka shiga Ƙasar Alkawari? (b) Kamar yadda aka ambata a Zabura 106, mene ne ya faru da Isra’ilawa saboda rashin biyayyarsu?

4 Jephthah da ‘yarsa sun zauna tare da Isra’ilawa da suka yi rashin biyayya ga Jehobah kuma suna ganin mugun sakamakon wannan rashin biyayya kullum. Wajen shekaru 300 kafin lokacin, Jehobah ya umurci Isra’ilawa su kashe dukan masu bautar ƙarya da ke Ƙasar Alkawari, amma ba su yi hakan ba. (Kubawar Shari’a 7:1-4) Saboda haka, Isra’ilawa da yawa suka soma bauta wa allolin ƙarya kuma suka riƙa yin lalata kamar mutanen Kan’ana.Karanta Zabura 106:34-39.

5 Rashin biyayya da Isra’ilawa suka yi ya sa Jehobah ya ƙi ya kāre su daga maƙiyansu. (Alƙalawa 2:1-3, 11-15; Zabura 106:40-43) Hakika, kasancewa da aminci bai da sauƙi a waɗannan mawuyacin lokaci musamman ma ga iyalai da ke ƙaunar Jehobah. Amma Littafi Mai Tsarki ya ambata cewa akwai mutane da suka kasance da aminci, kamar Jephthah da ‘yarsa da Elkanah da Hannatu da Sama’ila. Sun ƙudura anniya cewa za su faranta wa Jehobah rai.1 Sama’ila 1:20-28; 2:26.

6. Wane mummunan tasiri ne muke fuskanta a yau, kuma mene ne ya wajaba mu yi?

6 A zamaninmu, mutane suna tunani da kuma yin abubuwa kamar mutanen ‘yan Kan’ana. Sun mai da hankali ga yin lalata da aikata mugunta da kuma son kuɗi. Amma Jehobah yana ba mu shawarwari masu kyau don yana so ya kāre mu kamar yadda ya kāre Isra’ilawa daga irin wannan mummunan tasiri. Shin za mu koyi darasi daga abin da ya faru da su? (1 Korintiyawa 10:6-11) Wajibi ne mu yi iya ƙoƙarinmu mu guji ra’ayin mutanen duniya. (Romawa 12:2) Shin mun ƙudiri yin hakan kuwa?

JEPHTHAH YA KASANCE DA AMINCI A MAWUYACIN YANAYI

7. (a) Mene ne ‘yan’uwan Jephthah suka yi masa? (b) Mene ne Jephthah ya yi?

7 A zamanin Jephthah, Isra’ilawa sun yi rashin biyayya. Saboda haka, Allah ya ƙyale Filistiyawa da Ammonawa su taƙura musu. (Alƙalawa 10:7, 8) Ban da haka, ‘yan’uwan Jephthah da kuma shugabanni a Isra’ila sun matsa wa Jephthah. Da yake ‘yan’uwansa suna kishinsa kuma sun tsane shi, sun tilasta masa ya bar gādonsa. (Alƙalawa 11:1-3) Jephthah bai yarda mugun  halinsu ya shafe shi ba. Ta yaya muka san haka? Sa’ad da dattawan ƙasar suka roƙe shi ya taimaka musu, ya yi hakan ba tare da ɓata lokaci ba. (Alƙalawa 11:4-11) Mene ne ya sa Jephthah ya taimaka musu?

8, 9. (a) Waɗanne ƙa’idodin dokar da aka ba da ta hannun Musa ne suka taimaka wa Jephthah? (b) Mene ne ya fi muhimmanci ga Jephthah?

8 Jephthah babban jarumi ne, kuma ya san tarihin al’ummar Isra’ila da kuma dokar da Allah ya ba su. Ya yi la’akari da yadda Jehobah ya bi da mutanensa kuma hakan ya sa ya san ƙa’idodin Allah game da nagarta da mugunta. (Alƙalawa 11:12-27) Jephthah ya yanke shawarwari bisa ga waɗannan ƙa’idodin. Ya san ra’ayin Jehobah game da yin ramako da kuma yadda Jehobah ya bukace mutanensa su ƙaunaci juna. Ƙari ga haka, ya bi da mutane yadda ya kamata, har da waɗanda suka tsane shi, kamar yadda doka ta umurta.Karanta Fitowa 23:5; Levitikus 19:17, 18.

9 Wataƙila, misalin Yusufu ya taimaka wa Jephthah. Ya koyi darasi daga yadda Yusufu ya nuna wa ‘yan’uwansa jin kai duk da cewa sun tsane shi. (Farawa 37:4; 45:4, 5) Wataƙila, Jephthah ya yi bimbini a kan wannan misalin kuma hakan ya taimaka masa ya faranta wa Jehobah rai. Abin da ‘yan’uwan Jephthah suka yi ya ɓata masa rai sosai. Amma, a gaban Jephthah, ɗaukaka sunan Jehobah da kuma kāre mutanensa ya fi muhimmanci. (Alƙalawa 11:9) Ya ƙudura ya kasance da aminci ga Jehobah. Wannan halin ya sa Jehobah ya albarkace Jephthah da sauran Isra’ilawa.—Ibraniyawa 11:32, 33.

Kada mu yarda ɓacin rai ya sa mu daina bauta wa Jehobah

10. Ta yaya bin ƙa’idodin Allah zai taimaka mana mu riƙa yin abubuwa kamar Kiristoci a yau?

10 Wane darasi ne za mu iya koya daga misalin Jephthah? Shin mene ne za mu yi idan ‘yan’uwanmu Kiristoci suka ɓata mana rai ko kuma muna gani kamar ba su bi da mu yadda ya dace ba? Kada mu yarda ɓacin rai ya sa mu daina bauta wa Jehobah. Kada mu fasa halartan taro da kuma kasancewa da ‘yan’uwa a ikilisiya. Bari mu bi misalin Jephthah kuma mu yi biyayya ga Jehobah. Hakan zai taimaka mana mu sha kan mawuyacin yanayi kuma mu kafa misali mai kyau wa ‘yan’uwanmu.Romawa 12:20, 21; Kolosiyawa 3:13.

MUNA NUNA BANGASKIYA IDAN MUKA YI SADAUKARWA DA SON RAI

11, 12. Wane alkawari ne Jephthah ya yi, kuma mene ne hakan yake nufi?

11 Jephthah ya san cewa Jehobah ne zai iya taimaka masa ya ‘yantar da Isra’ilawa daga hannun Ammonawa. Sai ya yi wa Jehobah alkawari cewa idan ya sa ya yi nasara, zai ba wa Jehobah mutumin da ya fara fitowa daga gidansa sa’ad da ya dawo daga yaƙin a matsayin “hadaya ta ƙonawa.” (Alƙalawa 11:30, 31) Mene ne hakan yake nufi?

12 A gaban Jehobah, yin hadaya da  ɗan Adam haram ne. Saboda haka, mun san cewa ba hadaya ta zahiri ne Jephthah yake nufi ba. (Kubawar Shari’a 18:9, 10) A cikin dokar da aka ba da ta hannun Musa, hadaya ta ƙonawa yana nufin kyauta ta musamman da mutum ya ba wa Jehobah. Saboda haka, Jephthah yana nufin cewa zai ba da mutumin don ya yi hidima ga Jehobah a mazauni har mutuwarsa. Jehobah ya ji addu’ar Jephthah kuma ya sa ya yi gagarumin nasara. (Alƙalawa 11:32, 33) Shin wane ne Jephthah ya ba wa Jehobah?

13, 14. Ta yaya abin da Jephthah ya faɗa a Alƙalawa 11:35 ya nuna cewa yana da bangaskiya?

13 Ka yi la’akari da abin da aka ambata a farkon talifin nan. Sa’ad da Jephthah ya dawo daga yaƙin, ‘yarsa guda ɗaya tak da ya haifa, ita ce ta fara fitowa daga gidan don ta tarbe shi! Shin Jephthah ya kasance da aminci kuma ya cika alkawarin da ya yi? Shin ya yarda ya sadaukar da ‘yarsa don ta yi hidima wa Jehobah a mazauni har mutuwarta?

14 Babu shakka, Jephthah ya sake yin la’akari da ƙa’idodin da ke cikin dokar da aka ba da ta hannun Musa kuma hakan ya taimaka masa ya yi abin da ya dace. Wataƙila ya yi la’akari da abin da aka rubuta a Fitowa 23:19, inda Allah ya umurci mutanensa su ba wa Jehobah hadaya mafi kyau daga amfaninsu. Dokar ta ƙara cewa idan mutum ya ɗauki alkawarin yin wani abu a gaban Jehobah, “ba za ya warware maganarsa ba; sai shi aika dukan abin da bakinsa ya furta.” (Littafin Lissafi 30:2) Kamar Hannatu da wataƙila ta yi rayuwa a zamaninsa, Jephthah ya bukaci ya cika alkawarinsa, ko da ya san cewa yin hakan ba zai kasance da sauƙi a gare shi da kuma ‘yarsa ba. Don ‘yarsa za ta yi hidima a mazauni kuma ba za ta haifi ‘ya’ya ba. Saboda haka, babu wanda zai  gāji Jephthah da kuma filinsa. (Alƙalawa 11:34) Duk da haka, Jephthah ya ce: “Na riga na yi wa’adi ga Ubangiji, ba kuwa zan iya warware shi ba.” (Alƙalawa 11:35, LMT) Jehobah ya amince da hadaya mai tamani da Jephthah ya yi kuma ya albarkace shi. Da a ce kai ne, da ka kasance da aminci kamar Jephthah kuwa?

15. Wane alkawari ne muka yi, kuma ta yaya za mu iya kasancewa da aminci?

15 Sa’ad da muka keɓe kanmu ga Jehobah, mun gaya masa cewa za mu yi nufinsa a kowane yanayi. Mun san cewa cika wannan alkawarin ba zai kasance da sauƙi a kowane lokaci ba. Amma, yaya muke ji sa’ad da aka ce mu yi wani aikin da ba ma so? Idan muka kasance da gaba gaɗi kuma muka yi biyayya ga Allahnmu, hakan zai nuna cewa muna cika alkawari. Yin sadaukarwa ba zai kasance da sauƙi ba, amma Jehobah zai albarkace mu sosai. (Malakai 3:10) Shin mene ne ‘yar Jephthah ta yi sa’ad da ta ji alkawarin da mahaifinta ya yi?

Ta yaya za mu nuna cewa muna da bangaskiya kamar Jephthah da ‘yarsa? (Ka duba sakin layi na 16, 17)

16. Wane mataki ne ‘yar Jephthah ta ɗauka game da alkawarin da mahaifinta ya yi? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.)

16 Alkawarin da Jephthah ya yi dabam ne da na Hannatu. Ta yi alkawari cewa za ta ba da ɗanta Sama’ila don ya yi hidima a mazauni a matsayin Banazare. (1 Sama’ila 1:11) Banazare zai iya yin aure kuma ya haifi ‘ya’ya. Amma an ba da ‘yar Jephthah a matsayin “hadaya ta ƙonawa” gaba ɗaya. Saboda haka, ba za ta yi aure ba kuma ba za ta haifi ‘ya’ya ba. (Alƙalawa 11:37-40) Ka yi la’akari da abin da hakan yake nufi! Da wataƙila ta auri mutum mafi daraja don mahaifinta ne shugaban al’ummar Isra’ila a lokacin. Amma yanzu, za ta zama baiwa mai hidima a mazauni. Shin mene ne ta yi? Ta nuna cewa hidimar Jehobah ce ta fi muhimmanci a rayuwarta kuma ta gaya wa mahaifinta cewa: “Ka yi mani bisa ga abin da ya fito daga cikin bakinka.” (Alƙalawa 11:36) Ta sadaukar da muradinta na yin aure da kuma haifan yara don ta yi wa Jehobah hidima. Shin ta yaya za mu bi misalinta?

’Yar Jephthah ta sadaukar da muradinta na yin aure da kuma haifan yara don ta yi wa Jehobah hidima

17. (a) Ta yaya za mu iya bin misalin Jephthah da ‘yarsa? (b) Ta yaya kalaman da ke Ibraniyawa 6:10-12 za su ƙarfafa mu mu yi sadaukarwa?

 17 Dubban matasa Kiristoci maza da mata suna sadaukarwa ta wajen kasancewa marasa aure ko kuma ta wajen ƙin haifan ‘ya’ya na ɗan lokaci. Me ya sa? Don suna son su mai da hankali a yin hidima sosai a bautar Jehobah. Ƙari ga haka, ‘yan’uwa da suka manyanta da yawa sun sadaukar da lokacin da ya kamata su kasance da yaransu ko jikokinsu don su yi amfani da lokacinsu da kuzarinsu a bautar Jehobah. Wasu daga cikinsu suna aikin gine-gine a ƙungiyar Jehobah, wasu kuma suna halartan Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki kuma su je hidima a wata ikilisiya da ake bukatar masu shela sosai. Wasu kuma suna tsara ayyukansu don su daɗa yin wa’azin bishara a lokacin taron Tuna da Mutuwar Yesu. Jehobah ba zai manta da waɗannan sadaukarwa da dukan waɗannan masu aminci suke yi ba. (Karanta Ibraniyawa 6:10-12.) Kai kuma fa? Shin za ka iya yin sadaukarwa don ka daɗa yin hidima a bautar Jehobah?

WAƊANNE DARUSSA NE MUKA KOYA?

18, 19. Mene ne muka koya daga labarin Littafi Mai Tsarki game da Jephthah da ‘yarsa, kuma ta yaya za mu yi koyi da su?

18 Mene ne ya taimaka wa Jephthah ya sha kan matsaloli da yawa da ya fuskanta? Ya sa Jehobah ya yi masa ja-gora a rayuwa. Bai bar halayen mutane su sa shi sanyin gwiwa ba. Jephthah ya kasance da aminci duk da cewa wasu sun ɓata masa rai. Jehobah ya albarkaci Jephthah da ‘yarsa don sun yi sadaukarwa da son rai, kuma ya yi amfani da su wajen taimaka wa wasu su bauta wa Jehobah. Jephthah da ‘yarsa sun kasance da aminci ga Jehobah har ma a lokacin da wasu suka daina yin abin da ya dace.

19 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku zama masu koyi da waɗanda ke gāda alkawarai ta wurin bangaskiya da haƙuri.” (Ibraniyawa 6:12) Bari mu yi koyi da Jephthah da ‘yarsa don mun san cewa idan muka kasance da aminci, Jehobah zai albarkace mu.