Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro (Ta Nazari)  |  Disamba 2017

Matasa​—“Ku Yi Aikin Cetonku”

Matasa​—“Ku Yi Aikin Cetonku”

‘Kamar yadda kuke biyayya kullum, . . . ku yi aikin cetonku da tsoro da rawan jiki.’​—FILIB. 2:12.

WAƘOƘI: 133, 135

1. Me ya sa yin baftisma yake da muhimmanci? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

A KOWACE shekara, mutane da yawa suna yin baftisma kuma da yawa daga cikinsu yara ne da matasa. Wataƙila iyayensu Shaidu ne. Shin kai ma ɗaya ne daga cikinsu? Idan kana cikinsu, muna yaba maka sosai. Wajibi ne Kirista ya yi baftisma don yin hakan yana da muhimmanci don samun ceto.​—Mat. 28:​19, 20; 1 Bit. 3:21.

2. Me ya sa bai kamata mu ji tsoron yin alkawarin bauta wa Jehobah ba?

2 Idan mutum ya yi baftisma, zai sami albarka sosai. Amma yin hakan zai sa ya kasance da hakki a gaban Jehobah. Me ya sa? A ranar da kuka yi baftisma mai jawabin ya yi muku wannan tambayar: “Bisa ga hadayar Yesu Kristi, kun tuba daga zunubanku kuma kun keɓe kanku ga Jehobah domin ku yi nufinsa?” Kuma kun amsa E. Yin baftisma ya nuna cewa kun yi alkawarin bauta wa Jehobah. Kuma kun yi alkawari cewa za ku yi ƙaunarsa kuma ku sa yin nufinsa a kan gaba a rayuwarku. Wannan babban alkawari ne, ko ba haka ba? To zai dace ne mutum ya riƙa yin da-na-sani? A’a. Yadda ka ba da kanka don Jehobah ya riƙa maka  ja-goranci yana da kyau sosai. Ka yi la’akari da wannan! Duk wanda ya ƙi Jehobah ya masa ja-goranci yana bin ra’ayin Shaiɗan ne. Shaiɗan ba ya son mutane su sami ceto. Kuma idan ka daina bauta wa Jehobah, Shaiɗan zai yi farin ciki sosai kuma hakan zai hana ka samun rai na har abada.

3. Wace albarka za ku samu idan kuka yi alkawarin bauta wa Jehobah?

3 Amma ka yi tunani sosai a kan albarkar da kake samu don alkawarin da ka yi na bauta wa Jehobah da kuma baftisma. Yanzu da yake ka riga ka ɗauki wannan matakin bauta wa Jehobah, kai ma za ka kasance da wannan tabbacin cewa: “Ubangiji yana wajena; ba zan ji tsoro ba: Ina abin da mutum za ya yi mani?” (Zab. 118:6) Babu wata albarkar da ta fi wadda za mu samu don muna goyon bayan Jehobah kuma mun san cewa yana farin ciki sosai don hakan.

HAKKIN DA MATASA SUKE DA SHI

4, 5. (a) A wace hanya ce yin alkawarin bauta wa Jehobah ya zama hakkin da kowannenmu ya kamata ya ɗauka? (b) Waɗanne matsaloli ne dukanmu za mu iya fuskanta?

4 Da yake ka yi baftisma, kai kake da hakkin yin ayyukan da za su sa ka sami ceto, domin samun ceto ba kamar fili ko kuma dukiya ba ne da za ka iya gāda. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa tunawa da hakan? Domin ba za ka iya sanin matsalolin da za ka fuskanta a nan gaba ba. Alal misali, idan ka yi baftisma tun ba ka kai shekara sha uku ba kuma yanzu kai matashi ne, za ka fuskanci wasu matsaloli da ba ka taɓa fuskanta ba. Wata matashiya ta ce: “Babu yaron da zai yi fushi ya ce shi ba zai ƙara zama Mashaidin Jehobah ba domin ba a yarda ya ci abincin bikin tuna da ranar haihuwa a makaranta ba. Amma bayan wasu shekaru idan ya soma sha’awar jima’i, wajibi ne a tabbatar masa da cewa bin dokokin Jehobah shi ne ya fi kyau.”

5 Ba matasa ba ne kawai suke fuskantar matsalolin da ba su taɓa fuskanta ba. Ko manya da suka yi baftisma ma suna fuskantar matsaloli da yawa a rayuwa. Irin waɗannan abubuwan sun ƙunshi matsaloli a iyali ko rashin lafiya ko matsaloli a wurin aikinsu. Dukanmu za mu iya fuskantar matsalolin da za su iya gwada bangaskiyarmu ga Jehobah ko da mu matasa ne ko kuma manya.​—Yaƙ. 1:​12-14.

6. (a) Mene ne kake bukata ka riƙa tunawa game da alkawarin da ka yi wa Jehobah? (b) Wane darasi za mu koya daga Filibiyawa 4:​11-13?

6 Don ka ci gaba da kasancewa da aminci, zai dace ka riƙa tunawa cewa ka yi wa Jehobah alkawarin za ka bauta masa da zuciya ɗaya. Kuma hakan yana nufin cewa za ka riƙa bauta masa ko da abokanka ko iyayenka sun daina yin hakan. (Zab. 27:10) Ko da wane yanayi ka sami kanka a ciki, za ka iya yin iya ƙoƙarinka da taimakon Jehobah don ka cika alkawarinka.​—Karanta Filibiyawa 4:​11, 12; Ishaya 12:2.

7. Mene ne yin “aikin cetonku da tsoro da rawan jiki” yake nufi?

7 Jehobah yana son ka zama abokinsa. Amma kana bukatar ka yi ƙoƙari sosai kafin ka iya ci gaba da zama abokin Jehobah kuma ka yi ayyukan da za su sa ka sami ceto. Littafin Filibiyawa 2:12 ya ce: “Ku yi aikin cetonku da tsoro da rawan jiki.” Wannan furucin yana nufin cewa zai dace ka yi tunani a kan abin da za ka yi don ka ci gaba da zama abokin Jehobah kuma ka kasance da aminci duk da matsalolin da kake fuskanta. Bai kamata mu buga kirji mu ce ba za mu taɓa daina bauta wa Jehobah ba. Domin akwai wasu bayin Allah da suka daɗe suna bauta wa Jehobah da suka bijire. Saboda haka, waɗanne  matakai ne ya kamata ka ɗauka don ka yi ayyukan da za su sa ka sami ceto?

NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI YANA DA MUHIMMANCI

8. Me yin nazarin Littafi Mai Tsarki ya ƙunsa kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci?

8 Yin abokantaka da Jehobah ya ƙunshi sauraronsa da yi masa magana. Kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki ita ce babbar hanya da muke saurarar abin da Jehobah yake gaya mana. Hakan ya ƙunshi karatu da yin bimbini a kan Kalmar Allah da kuma littattafanmu. Amma a lokacin da kake nazarin, zai dace ka tuna cewa ba wai kana son ka koyi abubuwa ba ne kawai kamar karatun da ’yan makaranta suke yi don su ci jarabawa. Za a iya kwatanta irin wannan nazarin da bincike sosai da mutum yake yi don ya koyi abubuwa game da Jehobah. Yin hakan zai taimaka maka ka kusaci Jehobah, shi kuma ya kusace ka.​—Yaƙ. 4:8.

Shin kana sauraron Jehobah da kuma yi masa magana? (Ka duba sakin layi na 8-11)

9. Waɗanne abubuwa ne suka taimaka maka sa’ad da kake nazari?

9 Ƙungiyar Jehobah ta yi mana tanadin abubuwa da yawa da za su taimaka mana mu tsara yadda za mu riƙa nazari. Alal misali, “Ayyuka don Nazarin Littafi Mai Tsarki” da ke sashen “Matasa” a dandalin jw.org/ha zai taimaka maka ka koyi wasu darussa daga labaran Littafi Mai Tsarki. Ban da haka ma, “Ja-goranci Don Nazari” da ke dandalinmu a sashen “Mene ne Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?” zai taimaka mana mu tabbata da abubuwan da muka yi imani da su. Waɗannan abubuwan za su taimaka maka ka san yadda za ka iya tabbatar ma wasu abin da ka yi imani da su. Za ka sami ƙarin bayani game da yin nazari a talifin nan “Young People Ask . . . How Can I Make Bible Reading Enjoyable?” a Awake! na Afrilu na shekara ta 2009. Yin nazari da bimbini suna cikin ayyukan da za mu yi don mu sami ceto.​—Karanta Zabura 119:105.

ADDU’A TANA DA MUHIMMANCI

10. Me ya sa addu’a take da muhimmanci ga kowane bawan Jehobah da ya yi baftisma?

10 Ko da yake yin nazarin Littafi Mai Tsarki hanya ɗaya ce da muke sauraron Jehobah, addu’a kuma ita ce hanyar da muke yi masa magana. Bai kamata Kirista ya ga cewa addu’a abu ne kawai da mutane suke yi da ba shi da wani amfani ba. Har ila, bai dace su ɗauka cewa yin addu’a ga Jehobah zai sa su riƙa samun albarka ba. A maimakon haka, zai dace mu fahimta  cewa addu’a ita ce hanya mai muhimmanci da muke magana da Mahaliccinmu. Jehobah yana son ka riƙa masa magana. (Karanta Filibiyawa 4:6.) Littafi Mai Tsarki ya shawarce mu cewa a duk lokacin da muke cikin matsala mu riƙa ‘zuba nawayarmu bisa Ubangiji.’ (Zab. 55:22) Shin ka gaskata da hakan kuwa? Akwai ’yan’uwa da yawa da suka tabbata da hakan. Saboda haka, kai ma za ka iya samun taimako daga hakan!

11. Me ya sa ya dace mu riƙa gode wa Jehobah?

11 Amma bai kamata mu yi addu’a kawai a lokacin da muke son Jehobah ya taimaka mana ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku zama masu-godiya.” (Kol. 3:15) A wasu lokuta, matsalolin da muke fuskanta za su sa mu manta da albarkar da Jehobah yake mana. Ya kamata kowace rana ka yi tunani a kan a ƙalla abubuwa uku da Jehobah ya albarkace ka da su kuma ka gode masa. Wata matashiya mai suna Abigail da ta yi baftisma sa’ad da take shekara 12, ta ce: “Ina ganin Jehobah ne kaɗai ya kamata mu fi gode masa. Kuma mu riƙa yin hakan kullum don kyautar da yake mana.”

MUHIMMANCIN ABIN DA KUKA FUSKANTA A RAYUWA

12, 13. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi tunani a kan yadda Jehobah yake nuna mana alheri?

12 Sarki Dauda da Jehobah ya taimaka wa ya shawo kan matsaloli da yawa ya ce: “Ku ɗanɗana, ku duba, Ubangiji nagari ne: mai-albarka ne mutum wanda yake dogara gare shi.” (Zab. 34:8) Wannan ayar ta nuna yadda yake da muhimmanci mutum ya shaida alherin Jehobah a lokacin da yake shan wahala. Sa’ad da ka karanta Littafi Mai Tsarki da littattafanmu kuma ka halarci taro, za ka ji labaran yadda Allah ya taimaka ma wasu su kasance da aminci. Amma sa’ad da kake zama wanda ya manyanta kana bukatar ka ga yadda Jehobah yake taimaka maka. Ta yaya Jehobah ya taɓa taimaka maka?

13 Jehobah yana nuna wa dukan bayinsa alheri. Ya yi hakan ta wurin samu zama abokansa da kuma na ɗansa. Yesu ya ce: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.” (Yoh. 6:44) Shin kana ganin wannan furucin ya shafe ka kuwa? Wasu matasa za su iya cewa, ‘Jehobah ne ya sa iyayena suka soma bauta masa kuma na bi su.’ Amma, a lokacin da ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma kana nuna cewa kana son ka zama abokinsa. Kuma a wannan lokacin zai san ka domin kai abokinsa ne. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan kowane mutum yana ƙaunar Allah, wannan mutum sananne ne gare shi.” (1 Kor. 8:3) Saboda haka, zai dace ka daraja da kuma mutunta hidimar da kake yi a ƙungiyar Jehobah.

14, 15. Ta yaya wa’azi zai taimaka maka ka ƙarfafa bangaskiyarka?

14 Wata hanya da Jehobah yake taimaka mana shi ne ta wurin sa mu kasance da ƙarfin hali sa’ad da kake bayyana ma wasu abin da ka yi imani da shi. Kuma za ka iya yin hakan sa’ad da ka fita wa’azi ko kuma a makaranta. Wasu ba sa iya yi wa tsaransu wa’azi a makaranta don wataƙila ba su san yadda tsararsu za su ji ba. Hakan ma zai fi wuya sa’ad da kake wa matasa da yawa da suka taru a wuri ɗaya wa’azi. Me zai taimaka maka ka yi hakan?

15 Da farko, ka yi tunanin dalilin ya sa ka tabbata da abubuwan da ka yi imani da su. Shin kuna da umurni ja-goranci don nazari da ke dandalin jw.org a yarenku kuwa? Idan ba ka sani ba, zai dace ka bincika don ka sani. An wallafa waɗannan talifofin ne don su taimaka maka ka yi tunani a kan abin da ka gaskata da dalilin da ya sa ka  gaskata da hakan da kuma yadda za ka bayyana ma wasu abin da ka yi imani da su. Idan ka tabbata da hakan kuma ka yi shiri sosai, za ka so ka riƙa wa mutane wa’azi game da Jehobah.​—Irm. 20:​8, 9.

16. Me zai iya taimaka maka kada ka ji tsoron bayyana ma wasu abubuwan da ka yi imani da su?

16 A wasu lokuta, za ka iya jin tsoron bayyana abubuwan da ka yi imani da su ko da ka yi shiri sosai. Wata ’yar’uwa mai shekara 18 da ta yi baftisma sa’ad da take shekara 13, ta ce: “Na san abin da na yi imani da shi, amma a wasu lokuta ina jin tsoron gaya ma wasu waɗannan abubuwan.” Ta yaya ta shawo kan wannan matsalar? Ta ce: “Na yi ƙoƙari in yi magana yadda na saba yi. Domin ’yan ajinmu ba sa jin kunyar faɗan abubuwan da suke yi. Ni ma zai dace in yi kamar yadda suke yi. Don haka, idan ina hira, sai in ce, ‘Wata rana ina koya ma wani Littafi Mai Tsarki sai kazā da kazā ya faru.’ Ko da yake hirar da muke yi ba game da Littafi Mai Tsarki ba ne, a yawancin lokaci suna so su san yadda nake koyar da Littafi Mai Tsarki, don haka sai su riƙa min tambayoyi. Yin hakan yana taimaka mini in iya yin wa’azi. Kuma ina farin ciki bayan na yi hakan!”

17. Ta yaya ra’ayinka game da abin da ka yi imani da shi zai taimaka maka ka iya gaya ma wasu abin da ka gaskata da shi?

17 Idan ka daraja mutane kuma ka nuna cewa ka damu da su, za su saurare ka. Alal misali, wata ’yar’uwa mai suna Olivia mai shekara 17 da ta yi baftisma a lokacin da ba ta kai shekara sha uku ba ta ce: “A dā ina jin tsoron yin wa’azi don ina ganin cewa idan na soma magana game da Littafi Mai Tsarki sa’ad da nake hira da wasu, mutane za su ɗauke ni mai tsattsauran ra’ayi.” Amma daga baya ta canja ra’ayinta kuma maimakon ta riƙa jin tsoro, sai ta ce: “Matasa da yawa ba su san abubuwan da Shaidun Jehobah suka yi imani da su ba. Mu ne kaɗai Shaidun Jehobah da suka sani. Don haka, yadda muke yin abubuwa zai sa su daraja mu ko kuma su ƙi yin hakan. Idan mu masu jin kunya ne ko tsoro ko kuma ba ma iya bayyana wa mutane abin da muka yi imani da shi ko kuwa muna rawan jiki sa’ad da muke yin hakan fa? Za su ɗauka cewa ba ma alfahari da abin da muka yi imani da shi ko kuma su ƙi saurararmu da yake ba mu da gaba gaɗi. Amma idan muna bayyana musu abin da muka yi imani da shi kamar yadda muka saba hira da su kuma ba ma jin tsoro, za su saurari abin da muke gaya musu.”

KU CI GABA DA YIN AIKIN CETONKU

18. Mene ne yin ayyukan da za su sa ka sami ceto ya ƙunsa?

18 Kamar yadda muka riga muka bincika, yin ayyukan da za su sa ka sami ceto babban hakki ne da kowa yake da shi. Wasu abubuwa da hakan ya ƙunsa shi ne karanta Littafi Mai Tsarki da yin bimbini sosai. Ban da haka ma, yin addu’a da yin tunani sosai a kan hanyoyin da Jehobah ya albarkace ka za su taimaka maka sosai. Idan ka yi hakan, za ka ci gaba da zama abokin Jehobah. Kuma hakan zai sa ya yi maka sauƙi ka bayyana abin da ka yi imani da shi.​—Karanta Zabura 73:28.

19. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi iya ƙoƙarinmu wajen yin ayyukan da za su sa mu sami ceto?

19 Yesu ya ce: “Idan kowane mutum yana da nufi shi bi baya na, sai shi yi musun kansa, shi ɗauki [“gungumen azaba,” NW ], shi biyo ni.” (Mat. 16:24) Babu shakka, wajibi ne duk wanda yake son ya bi Yesu ya yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ya yi baftisma. Hakan zai sa mutum ya sami albarka yanzu kuma ya sami rai na har abada a sabuwar duniya a nan gaba. Don haka, zai dace ka yi iya ƙoƙarinka don ka yi ayyukan da za su sa ka sami ceto!