Shin ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan kuwa? Ka bincika ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:

Me ya sa iyaye baƙi hijira suke bukatar su tattauna game da yaren da zai fi taimaka wa yaransu su kusaci Jehobah?

Yaranka za su iya koyan yaren da ake yi a makarantarsu da unguwa kuma yana da kyau su iya wasu yaruka ma. Don haka, ya kamata iyaye su yi tunani a kan ikilisiyar da za su riƙa zuwa taro da ake yaren da zai taimaka wa yaransu matasa su kusaci Jehobah, ko da yarensu ne ake yi a ikilisiyar ko kuma yaren da ake yi a yankin. Don Kiristoci suna ɗaukan dangantakar yaransu da Jehobah da muhimmanci sosai.​—w17.05, shafi na 9-11.

Da Yesu ya ce wa Bitrus: “Kana ƙaunata fiye da waɗannan?” me furucin nan “waɗannan” yake nufi? (Yoh. 21:15)

Kamar dai Yesu yana magana ne game da kifin da ke wurin ko kuma sana’ar kama kifi. Bayan mutuwar Yesu, Bitrus ya koma yin sana’arsa na kama kifin. Bai kamata Kirista ya ɗauki sana’a da muhimmanci fiye da ibada ba.​—w17.05, shafi na 22-23.

Me ya sa Ibrahim ya ce matarsa ta ce ita ’yar’uwarsa ce? (Far. 12:​10-13)

Saratu ’yar’uwarsa ce da gaske. Da a ce ta ce ita matar Ibrahim ne, ƙila da an kashe shi kuma da hakan ya sa bai haifi ɗan da zai zama zuriyar da aka yi alkawarinsa ba.​—wp17.3, shafi na 14-15.

Mene ne Elias Hutter ya yi don ya taimaka ma waɗanda suke so su koyi Ibrananci?

Yana so ya taimaka ma ɗaliban su san bambanci da ke tsakanin kalmomin Ibrananci da ke cikin Baibul da ɗoriyar farko da na ƙarshe da aka saka wa kalmomin. Ya rubuta kowace kalma da fasali na yau da kullum. Amma ya saka wa baƙaƙen ɗoriyar farko da na ƙarshe rami a tsakiya. An yi amfani da wannan dabarar ma a ƙarin bayani da ke juyin New World Translation of the Holy Scriptures​With References.​—wp17.4, shafi na 11-12.

Mene ne zai taimaka wa Kirista ya san ko yana bukatar makamai kamar bindiga don ya tsare kansa daga wasu mutane?

Wasu cikinsu su ne: Allah yana daraja rai. Kuma Yesu bai ce mabiyansa su kāre kansu da makamai ba. (Luk. 22:​36, 38) Don haka, muna bukatar mu bugi takobanmu su zama garmuna domin muna daraja rai fiye da kayan duniya. Muna daraja ra’ayin wasu kuma muna son mu riƙa kafa misali mai kyau. (2 Kor. 4:2)​—w17.07, shafi na 31-32.

Me ya sa abin da Matta da Luka suka rubuta game da rayuwar Yesu ya bambanta?

Matta ya mai da hankali ne ga abubuwan da suka shafi Yusufu. Kamar abin da ya yi da Maryamu take da juna biyu da umurnin da aka ba shi cewa ya gudu zuwa Masar da kuma dawowarsu daga ƙasar. Amma Linjilar Luka ta mai da hankali ga labarin Maryamu ne. Alal misali, ta ambata yadda Maryamu ta kai wa ’yar’uwarta Alisabatu ziyara da abin da Maryamu ta faɗa a lokacin da Yesu ya je haikali yana magana da malamai da yake yaro.​—w17.08, shafi na 32.

Ta yaya Kalmar Allah ta tsaya har abada?

Da shigewar lokaci, yaruka suna canjawa har da kalmomi da yadda ake furta su. Siyasa takan kawo canje-canje da ke shafan yaruka. Wasu kuma ba sa so a fassara Baibul zuwa yaren da mutane suka fi yi.​—w17.09, shafi na 19-21.

Akwai mala’ikan da ke kāre mu?

A’a. Amma me Yesu yake nufi da ya ce mala’ikun almajiransa suna duban fuskar Allah? (Mat. 18:10) Yesu yana nufin cewa mala’iku suna ƙaunar kowane cikin almajiransa, ba wai mala’iku suna kāre kowannensu a hanyar mu’ujiza ba.​—wp17.5, shafi na 5.

Wace irin ƙauna ce ta fi muhimmanci?

Ƙauna ta a·gaʹpe da ke bisa ƙa’idodin da suka dace ita ce ƙaunar da ta fi muhimmanci. Kuma irin wannan ƙaunar ta ƙunshi yin la’akari da mutane da kuma nuna mun damu da su. Ban da haka ma, ta ƙunshi nuna ƙauna ba tare da son kai ba don mutane su amfana.​—w17.10, shafi na 7.