Shin ya dace ne Kiristoci su yi amfani da maganin hana ɗaukar ciki da ake kira IUD, wato intrauterine device?

A wannan batun ya kamata ma’aurata su yi bincike kuma su bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don su tsai da shawarar da za ta hana su yin zunubi ga Allah.

Jehobah ya umurci Adamu da Hauwa’u kuma daga baya Nuhu da iyalinsa cewa: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu.” (Far. 1:28; 9:1) Amma, Littafi Mai Tsarki bai ce wajibi ne Kiristoci su bi wannan umurnin ba. Saboda haka, ma’aurata ne ya kamata su tsai da shawara ko za su yi amfani da maganin hana ɗaukar ciki don su ƙayyade yawan yaran da za su haifa ko kuma lokacin da za su so su haihu. Waɗanne abubuwa ne ya kamata su yi tunani a kansu?

Ya kamata Kiristoci su bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a batun yin amfani da maganin hana ɗaukar ciki. Shi ya sa ba sa zub da ciki. Littafi Mai Tsarki ya ce mu riƙa daraja rai kuma zub da ciki ya saɓa ma wannan umurnin. Kiristoci ba za su halaka ɗan tāyin da zai girma ya zama jariri ba. (Fit. 20:13; 21:​22, 23; Zab. 139:16; Irm. 1:5) Amma, zai dace ne su yi amfani da maganin hana ɗaukar ciki da ake kira IUD?

An yi magana a kan wannan batun a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Mayu, 1979 shafuffuka na 30-31 a Turanci. A lokacin, ana amfani da IUD na roba ne kuma ana saka shi ne a mahaifa don kada mace ta ɗauki ciki. An bayyana a talifin cewa ba a san yadda IUD yake aiki sosai ba. Ƙari ga haka, masana da yawa sun bayyana cewa wannan maganin hana ɗaukar ciki yana hana maniyyin namiji ya haɗu da ƙwan mace, kuma idan hakan bai faru ba mace ba za ta iya ɗaukan ciki ba.

 Amma, wasu binciken sun nuna cewa a wasu lokuta ƙwan yakan zama ɗan tāyi. Kuma ɗan tāyin yakan yi girma daga wajen mahaifa, wato ectopic pregnancy ko kuma a cikin mahaifa. Idan ɗan tāyin ya shiga cikin mahaifa, sai wannan maganin hana ɗaukan ciki na IUD ya kashe ɗan tāyin da zai girma ya zama jariri. Hakan yana kama ne da zubar da ciki. Talifin ya kammala da cewa: “Ya kamata Kirista da take son ta yi amfani da maganin hana ɗaukan ciki na IUD ta yi tunani sosai ta wurin bincika ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da suka nuna cewa ɗaukan rai da daraja yana da muhimmanci sosai.”​—Zab. 36:9.

Amma an samu ci gaba sosai a fannin magani da kimiyya tun daga shekara ta 1979 da aka wallafa wannan talifin.

Yanzu akwai IUD iri biyu. Ɗaya na jan ƙarfe ne kuma an soma amfani da shi sosai a Amirka a shekara ta 1988. Ƙari ga haka, a shekara ta 2001 an soma amfani da IUD da ke ɗauke da wani sinadari da ake kira Hormone. Amma, ta yaya ake amfani da waɗannan magungunan hana ɗaukar ciki?

Na jan ƙarfe: Kamar yadda aka ambata ɗazu, kamar dai IUD yana hana maniyyi kai wurin da ƙwan mace yake. Ƙari ga haka, IUD na jan ƙarfe yana zama guba ne ga maniyyin kuma ya kashe ƙarfinsa. * Ban da haka ma, irin wannan IUD yana canja yadda mahaifar take aiki.

Sinadarin hormone: Da akwai magungunan hana ɗaukar ciki na IUD dabam-dabam da ke ɗauke da sinadarin hormone irin wanda yake cikin magungunan da mata suke sha da ke hana su ɗaukar ciki. Waɗannan IUD suna saka sinadarin hormone a cikin mahaifa. A wasu matan, hakan yana hana su yin ƙwai. Mace ba za ta iya samun juna biyu ba idan ba ta da ƙwai. Ban da haka ma, waɗannan IUD suna canja yadda mahaifa take aiki. * Ƙari ga haka, suna sa majinar da ke bakin mahaifa ta yi ƙauri, kuma hakan zai hana maniyyi daga farjin ya shiga cikin mahaifar. Waɗannan suna cikin abubuwan da IUD yake yi.

Kamar yadda aka ambata ɗazu, dukan ire-iren IUD suna canja yadda mahaifa take aiki. Amma idan mace ta yi ƙwai kuma ƙwan ya haɗu da maniyyi, hakan zai iya zama ɗan tāyi. Idan ɗan tāyin ya shiga cikin mahaifa, IUD zai iya halaka ɗan tāyin. Kuma hakan zai iya sa cikin ya zube. Amma, masana kimiyya sun ce da ƙyar ne hakan ya faru, kamar yadda yakan faru a wasu lokuta da matan da suke shan ƙwayoyin da ke hana ɗaukan ciki.

Saboda haka, ba wanda zai iya cewa IUD na jan ƙarfe ko kuma na sinadarin hormone yana hana maniyyi haɗuwa da ƙwan mace kuma ya zama ɗan tāyi. Amma, bincike da masana kimiyya suka yi ya nuna cewa domin abubuwan da aka ambata ɗazu da ƙyar mace ta ɗauki ciki idan tana amfani da magungunan IUD.

Ma’aurata da suke tunanin yin amfani da IUD suna iya tattaunawa da likitocin da suka ƙware a wannan ɓangaren, don su gaya musu irin waɗanda suke da shi a yankinsu. Ƙari ga haka, su nemi sanin amfaninsu da kuma haɗarin yin amfani da su. Bai kamata ma’auratan su sa rai cewa wani ne ko kuma likita ne zai gaya musu wanda za su yi amfani da shi ba, sune za su tsai da wannan shawarar. (Rom. 14:12; Gal. 6:​4, 5) Ya kamata su tsai da shawararsu don suna so su faranta wa Allah rai kuma ba sa so su yi wani abin da zai ɓata dangantakarsu da Jehobah.​—Gwada 1 Timotawus 1:​18, 19; 2 Timotawus 1:3.

^ sakin layi na 4 A wani bincike da England’s National Health Service suka yi, an ce: “IUD mai jan ƙarfe sosai ya fi aiki. Hakan yana nufin cewa da ƙyar mace da take amfani da wannan IUD ta yi juna biyu. Amma, IUD da ba shi da jan ƙarfe da yawa ba ya aiki sosai.”

^ sakin layi na 5 Wannan sinadarin hormone da ke cikin IUD yana canja yadda mahaifa take aiki. A wasu lokuta, likitoci suna gaya wa ma’aurata da marasa aure da suke zub da jini da yawa a lokacin da suke haila su yi amfani da maganin nan.