Ko da wasu sun yashe ka, akwai wani da ba zai yashe ka ba. Wane ne wannan?

Sarki Dauda wanda ya yi mulki a dā, ya ce: “Ko da babana da mamata sun yashe ni, Yahweh zai lura da ni.”​—Zabura 27:10.

Jehobah ne “Uba mai yawan tausayi, Allah wanda yake yi mana kowace irin ta’aziyya, Allah yana yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalarmu.”​—2 Korintiyawa 1:​3, 4.

“Ku danƙa masa dukan damuwarku, gama shi ne mai lura da ku.”​—1 Bitrus 5:7.

Don sanin yadda Allah yake so ya taimake ka, ka duba babi na 12 na littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? Shaidun Jehobah ne suka wallafa. Kuma za ka iya samun sa a www.jw.org/ha