Littafi Mai Tsarki ya ce shawarar da ke cikinsa hurarriya ce kuma “mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa.” (2 Timotawus 3:16) Hakan gaskiya ne? Bari mu ga yadda shawarar da ke Littafi Mai Tsarki ta taimaka wa mutane su guji faɗawa cikin matsaloli.

YIN MAYE DA GIYA

Delphine da aka ambata a talifin baya ta lura cewa yawan damuwa sun sa ta soma yin maye da giya. Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai hana shan giya ba, amma ya ce: “Kada ka kasance kana cikin masu shaye-shaye.” (Misalai 23:20) Yin maye da giya na janyo munanan cututtuka, yana ɓata dangantakar mutane kuma miliyoyin mutane suna mutuwa saboda yin maye da giya. Idan mutane suna bin shawarar da Littafi Mai Tsarki ya bayar game da shan giya, hakan ba zai riƙa faruwa ba.

Abin da Delphine ta yi ke nan. Ta ce: “Na fahimci cewa shan giya ba ya magance matsalolina. Don haka, sai na bi shawarar da ke littafin Filibiyawa 4:​6, 7 da ta ce: ‘Kada ku yi alhini cikin kowane abu . . . ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah.’ A kowane dare, ina yin addu’a ga Jehobah idan na soma wannan tunani. Ina gaya masa yadda nake ji, har da abubuwan da ke ci min tuwo a ƙwarya. Kuma ina roƙon sa ya taimaka min in daina yawan damuwa. In gari ya waye, ina iya ƙoƙarina kada na riƙa damuwa game da abubuwan. Hakan ya taimaka mini in mai da hankali a kan abin da nake da shi maimakon abin da ban da shi. Ƙari ga haka, na yanke shawara cewa ba zan ƙara shan giya ba. Domin ba na so na rasa kwanciyar hankali da nake da shi yanzu.”

 LALATA

Lalata ce ya fi janyo munanan sakamako da kuma baƙin ciki. Amma Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu guji faɗawa cikin wannan jarrabar. Ya ba mu shawara a kan wasu abubuwan da suke sa mutum ya yi lalata kamar su kwarkwasa da kuma kallon hotunan batsa. Wani matashi mai suna Samuel ya ce: “Yin kwarkwasa yana da sauƙi. A wasu lokuta nakan ga yarinyar da ba na sonta amma ita tana so na. A irin wannan yanayin, kwarkwasa tana da daɗin yi.” Sai Samuel ya ji cewa mutane suna kiransa mai kwarkwasa. Ko da yake ba shi da niyyar yin kwarkwasa amma abubuwan da mutane suke faɗa ya sa ya soma yin kwarkwasa. Wannan halin ya dame shi sosai. Ya ce: “Kwarkwasa tana da haɗari sosai domin tana sa mutum ya zama mai son kai.”

Samuel ya karanta wani talifin da aka wallafa don matasa a dandalin jw.org. Ya yi tunani a kan littafin Misalai 20:11 da ya ce: “Ayyukan da saurayi ke yi suke bayyana yadda yake, kana iya sani ko shi amintacce ne, mai nagarta.” (Littafi Mai Tsarki) Ta yaya wannan ayar ta taimaka masa? Samuel ya gano cewa kwarkwasar da yake yi bai dace ba. Ya ce: “Na kuma fahimci cewa duk wanda yake yin kwarkwasa ba zai zama abokin aure nagari ba. Na soma tunanin yadda matar da zan aura a nan gaba za ta ji idan ta gan ni ina kwarkwasa da wata mace. Hakan ya sa na gane cewa kwarkwasa ba ta da kyau. Ko da yake yin kwarkwasa tana da sauƙi, hakan ba ya nufi cewa yana da kyau.” Samuel ya canja halinsa kuma hakan ya taimaka masa ya guji yin lalata.

Yanayin wani mai suna Antonio ya fi na sauran muni sosai. Ya shaƙu da kallon hotunan batsa. Ko da yake yana son matarsa sosai amma ya ci gaba da kallon hotunan batsa. Ya ce yin tunani a kan abin da ke littafin 1 Bitrus 5:8 ya taimaka masa sosai. Ayar ta ce: “Ku yi hankali shimfiɗe, ku yi zaman tsaro: magabcinku Shaiɗan, kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.” Antonio ya ce: “A wannan zamanin, akwai hotunan batsa a ko’ina. Kuma idan mun kalli hotunan, ba za su fita daga zuciyar mu ba. Amma wannan ayar ta taimaka mini in yi tunani a kan wanda yake sa mutane su kalli hotunan batsa. Don haka, ina bukatar in riƙa tuna cewa waɗannan hotunan daga wurin Shaiɗan suke. Yanzu na san cewa Jehobah ne kaɗai zai iya taimaka mini in ‘yi hankali kuma in zama da tsaro’ don in guji abubuwan da za su ɓata tunanina da kuma aurena.” Antonio ya nemi taimako kuma yanzu ya daina wannan halin da bai dace ba. Abin da ya yi ya taimaka masa don kada ya faɗa cikin matsala.

Misalan nan sun nuna cewa Littafi Mai Tsarki zai iya ba mu shawarwari da za su taimaka mana mu guji faɗawa cikin matsala. To idan mun riga mun faɗa cikin matsalar da ta fi ƙarfinmu kuma ba za mu iya magance ta ba fa? Bari mu ga yadda Kalmar Allah za ta iya taimaka mana mu magance matsalolin da muke ciki.

Shawarar da ke Littafi Mai Tsarki za ta iya taimaka mana mu guji matsaloli