KIMIYYA

KO DA YAKE LITTAFI MAI TSARKI BA LITTAFIN KIMIYYA BA NE, AMMA YANA FAƊAN ABIN DA ZAI FARU A NAN GABA. BARI MU BINCIKA WASU MISALAI.

Shin sama da ƙasa suna da mafari ne?

A dā ’yan kimiyya sun ce a’a. Yanzu sun yarda cewa sama da ƙasa suna da mafari. Amma Littafi Mai Tsarki ya riga ya faɗa tun dā cewa suna da mafari.​—Farawa 1:1.

Yaya fasalin duniya yake?

A dā, mutane da yawa sun gaskata cewa duniya a shimfiɗe take. A ƙarni na biyar kafin haihuwar Yesu, masana kimiyya na Helenawa sun ce tana kama da ƙwallo. Amma tun da daɗewa, a ƙarni na takwas kafin haihuwar Yesu, wani marubucin Littafi Mai Tsarki mai suna Ishaya ya ambata cewa duniya tana kama da ‘ƙwallo.’​—Ishaya 40:​22, New World Translation.

Abubuwan da ke sararin samaniya suna ruɓewa kuwa?

Ɗan kimiyya na ƙasar Girka mai suna Aristotle da ya yi rayuwa a ƙarni na huɗu kafin haihuwar Yesu ya ɗauka cewa abubuwa suna ruɓewa a doron ƙasa ne kawai, amma waɗanda ke sararin samaniya ba sa canjawa ko ruɓa. Mutane sun yi shekaru da yawa da wannan ra’ayin. Amma a ƙarni na sha tara, ’yan kimiyya sun gano cewa abubuwan da ke sararin samaniya ko ƙasa suna iya ruɓewa ko lalacewa. Lord Kelvin, da ya ɗaukaka ra’ayin nan ya ce Littafi Mai Tsarki ma ya ambata cewa sararin samaniya da ƙasa za su ‘tsufa kamar tufa.’ (Zabura 102:​25, 26) Amma ra’ayin Kelvin ya jitu da Littafi Mai Tsarki don ya gaskata cewa Allah yana da ikon hana halittunsa ruɓewa.​—Mai-Wa’azi 1:4.

Me ya riƙe duniya?

Aristotle ya koyar da cewa duniyoyi suna rataye ne da juna cikin wani abu mai kama da ƙwallo kuma tamu duniyar ce take tsakiya. Amma a ƙarni na sha takwas bayan haihuwar Yesu, masana sun amince da cewa ba a rataye taurari da duniyoyi bisa kome ba. Kuma littafin Ayuba da aka rubuta a ƙarni na sha biyar kafin haihuwar Yesu ya nuna cewa Mahalicci ‘ya rataye duniya ba komi ƙarƙashinta.’​—Ayuba 26:7.

KIWON LAFIYA

KO DA YAKE LITTAFI MAI TSARKI BA LITTAFIN KIWON LAFIYA BA NE, AMMA YA BA DA SHAWARA A KAN KIWON LAFIYA KAFIN MASANA SU SAN DA HAKAN.

 Ware marasa lafiya.

Dokar da aka bayar ta hannun Musa ta ce a keɓe kutare a wani wuri dabam. Amma sai da cuta ta halakar mutane bayan zamanin manzannin Yesu ne likitoci suka gano muhimmancin dokar nan. Kuma har yau ana amfani da wannan dokar.​—Levitikus sura 13 da 14.

Yin wanka bayan an taɓa gawa.

Kafin ƙarshen ƙarni na sha tara, ma’aikatan kiwon lafiya suna taɓa gawa, bayan haka, sai su yi jinyar marasa lafiya ba tare da wanke hannayensu ba. Hakan ya sa mutane da yawa sun mutu. Amma Dokar da aka bayar ta hannun Musa ta nuna cewa duk wanda ya taɓa gawa zai zama marar tsarki. Kuma dokar ta ce mutum zai wanke jikinsa da tufafinsa da ruwa kafin ya zama da tsarki. Wannan tsarin ya kāre mutane daga kamuwa da cuta.​—Littafin Lissafi 19:​11, 19.

Zubar da datti.

A kowace shekara, yara fiye da rabin miliyan suna mutuwa sanadiyyar cutar kwalera. Me ya sa? Domin ana yin bayan gida a wurin da bai dace ba. Amma Dokar da aka bayar ta hannun Musa ta ce idan mutum zai yi bayan gida, ya tona rami ya yi a ciki kuma idan ya gama sai ya rufe ramin.​—Kubawar Shari’a 23:13.

Lokacin da ya dace a yi kaciya.

Dokar Allah ta ce a yi wa yaro kaciya a rana ta takwas da haihuwa. (Levitikus 12:3) An gano cewa bayan mako ɗaya da haihuwar yaro, ciwo yana saurin warkewa. Kafin ma’aikatan kiwon lafiya su sami ci gaba a binciken da suke yi, bayin Allah tun dā can sun san muhimmancin yi wa yaro kaciya a rana ta takwas da haihuwa.

Alaƙa tsakanin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali.

Masu bincike a fannin kiwon lafiya da ’yan kimiyya sun ce farin ciki da bege da godiya da gafartawa suna taimaka wa mutane su zama da lafiya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciya mai-jin daɗi magani ce mai-kyau: Amma karyayyen ruhu yana ƙeƙasa ƙasussuwa.”​—Misalai 17:22.