Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro  |  Na 1 2018

Littafi Mai Tsarki Zai Kyautata Rayuwarka a Nan Gaba

Littafi Mai Tsarki Zai Kyautata Rayuwarka a Nan Gaba

ALAL MISALI, a ce kana tafiya daddare kuma ko’ina ya yi duhu. Amma duk da cewa wurin ya yi duhu sosai, ba ka ji tsoro cewa za ka ɓata hanya domin kana da tocila mai haske sosai. Idan ka haska ƙasa, kana iya ganin kome da ke gabanka, idan kuma ka haska gaba kana iya ganin wurare masu nisa sosai.

Littafi Mai Tsarki yana kama da wannan tocilar a wasu hanyoyi. Kamar yadda muka koya a talifin baya, Kalmar Allah za ta iya taimaka mana mu magance matsalolin da muke fuskanta a wannan muguwar duniyar. Amma fiye da haka ma, Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu iya sanin yadda rayuwarmu za ta kasance a nan gaba kuma zai taimaka mana mu bi tafarkin da zai sa mu yi farin ciki sosai. (Zabura 119:105) Ta yaya zai yi hakan?

Bari mu bincika yadda Littafi Mai Tsarki ya ba mu bege game da rayuwarmu a nan gaba ta hanyoyi biyu: 1 Yana sa rayuwarmu ta zama da ma’ana, kuma 2 Yana koya mana yadda za mu kasance da dangantaka mai kyau da Mahaliccinmu.

1 RAYUWA MAI MA’ANA

Littafi Mai Tsarki ya ba da shawarwari masu amfani game da yadda za mu magance matsalolinmu, amma hakan ba ya nufin cewa za mu riƙa amfani da shi kawai don taimakon kanmu ba. Littafi Mai Tsarki bai gaya mana mu mai da hankali ga namu matsaloli ba kawai, a maimakon haka, ya ƙarfafa mu mu riƙa la’akari da wasu. Yin hakan zai sa rayuwarmu ta zama da ma’ana.

Bari mu yi misali da ƙa’idar da ke wannan nassi: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.” (Ayyukan Manzanni 20:35) Shin za ka iya tuna lokacin da ka taimaki wani da yake da bukata? Ko kuma sa’ad da ka saurari wani abokinka da kyau yayin da yake gaya maka abin da yake damun sa? Ba ka ji daɗi cewa ka taimaka masa ba?

Za mu yi farin ciki sosai idan muka bayar ba tare da sa rai cewa wanda muka ba shi zai ba mu wani abu ba. Wani marubuci ya ce: “Ba zai yiwu mutum  ya yi taimako kuma ya gagara samun fiye da yadda ya bayar ba, musamman ma in ya bayar ba tare da niyyar samun lada ba.” Duk da haka, idan muka taimaka wa mutane, musamman ma waɗanda ba za su iya biyan mu ba, za mu sami lada. Yin hakan na nufin cewa muna aiki tare da Mahaliccinmu, wanda yake ɗaukan wannan alherin a matsayin rance. (Misalai 19:17) Yana jin daɗin ƙoƙarin da muke yi don mu taimaka wa mabukata, kuma ya yi alkawarin ba mu ladan rayuwa ta har abada a aljanna. Babu shakka, wannan bege ne da babu kamar sa!​—Zabura 37:29; Luka 14:​12-14. *

Mafi muhimmanci ma, Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa za mu yi rayuwa mai ma’ana idan muka bauta wa Jehobah, Allah na gaskiya. Kalmarsa ta ƙarfafa mu mu yi masa yabo mu ɗaukaka shi kuma mu yi masa biyayya. (Mai-Wa’azi 12:13; Ru’ya ta Yohanna 4:11) Idan muka yi hakan, za mu cim ma abu mai muhimmanci. Za mu sa Mahaliccinmu farin ciki sosai domin ya ce: “Ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata.” (Misalai 27:11) Ka yi tunanin yadda hakan yake da muhimmanci, idan muka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma muka yi abin da ya dace, za mu sa Mahaliccinmu farin ciki. Me ya sa? Domin yana ƙaunar mu kuma yana so mu amfana ta wurin bin shawararsa. (Ishaya 48:​17, 18) Hakika, rayuwarmu za ta kasance da ma’ana sosai idan muna bauta wa Mahaliccin sama da ƙasa kuma muna yin rayuwar da ke faranta masa rai.

2 YADDA ZA MU ZAMA AMINAN MAHALICCINMU

Littafi Mai Tsarki ya kuma ƙarfafa mu mu zama aminan Mahaliccinmu. Ya ce: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.” (Yaƙub 4:8) A wasu lokuta, muna iya yin shakka ko zai yiwu mu yi abokantaka da Mahaliccinmu. Amma Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana da cewa idan muka “nemi Allah,” za mu “same shi,” domin “ba shi da nisa da kowane ɗayanmu.” (Ayyukan Manzanni 17:27) Shawarar da Littafi Mai Tsarki ya ba mu cewa mu kusaci Allah, zai amfane mu a nan gaba. Ta yaya?

Ka yi la’akari da wannan: Duk ƙoƙarin da muka yi, ba za mu iya kauce wa magabcinmu, wato mutuwa ba. (1 Korintiyawa 15:26) Amma Jehobah Sarkin zamanai ne. Bai zai taɓa mutuwa ba kuma yana son dukan aminansa su yi rayuwa har abada. Da waɗannan kalmomin Littafi Mai Tsarki ya bayyana irin rayuwar da Jehobah yake so waɗanda suke biɗan sa su yi. Wurin ya ce: “Bari zuciyarku ta rayu har abada.”​—Zabura 22:26.

Ta yaya za ka iya zama aminin Allah har abada? Ka ci gaba da karanta Kalmarsa Littafi Mai Tsarki. (Yohanna 17:3; 2 Timotawus 3:16) Ka roƙe shi ya taimaka maka ka fahimci Littafi Mai Tsarki. Kalmar Allah ta tabbatar mana da cewa idan muka “roƙi Allah” ya ba mu hikima, zai ba mu hannu sake. * (Yaƙub 1:5) A ƙarshe, ka yi ƙoƙari ka aikata abin da ka koya, kana barin Kalmar Allah ta zama ‘fitila ga sawayenka, da kuma haske ga tafarkinka.’​—Zabura 119:105.

^ sakin layi na 8 Don ƙarin bayani game da alkawarin da Allah ya yi na rayuwa har abada a Aljanna, ka duba babi na 3 na littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi.

^ sakin layi na 13 Shaidun Jehobah suna tattauna Littafi Mai Tsarki da mutane kyauta, kuma hakan zai taimaka maka ka fahimci Littafi Mai Tsarki sosai. Don ƙarin bayani a kan tattaunawar, ka kalli bidiyon nan Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki? Za ka iya samun sa a jw.org/ha, ka danna inda za ka bincika bidiyon, sai ka rubuta jigon bidiyon.

Jehobah Sarkin zamanai ne kuma yana son dukan aminansa su yi rayuwa har abada