Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro  |  Na 6 2017

Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Mene ne Armageddon?

Wasu sun yi imani cewa . . .

Lokaci ne da za a halaka duniya da makaman nukiliya ko kuma a gurɓata mahalli. Mene ne ra’ayinka?

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

Armageddon yana nufin “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka,” wato yaƙin da zai yi da masu yin mugunta.​—Ru’ya ta Yohanna 16:​14, 16.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

  • Allah zai yi yaƙin Armageddon ne ba don ya halaka duniya ba, amma don ya cece ta daga waɗanda suke son su halaka ta.​—Ru’ya ta Yohanna 11:18.

  • Yaƙin Armageddon zai kawo ƙarshen dukan yaƙoƙi.​—Zabura 46:​8, 9.

Za mu iya tsira daga yaƙin Armageddon?

Me za ka ce?

  • E

  • A’a

  • Wataƙila

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

“Taro mai girma” daga dukan ƙasashe za su tsira daga “babban tsanani,” wanda zai ƙare a yaƙin Armagedon.​—Ru’ya ta Yohanna 7:​9, 14.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

  • Allah yana son dukan mutane su tsira daga yaƙin Armageddon. Kafin ya halaka mutane, sai ya daɗe yana musu gargaɗi.​—Ezekiyel 18:32.

  • Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da za mu yi don mu tsira a Armageddon.​—Zafaniya 2:3.