“Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki.” (Yaƙub 1:17) Babu shakka, wannan ayar tana magana ne game da alherin Ubanmu na sama, wato Jehobah Allah. Amma a cikin dukan kyaututtukan da Allah ya ba mu, da akwai wata kyauta da ta fi su daraja. Wace kyauta ke nan? Yesu ya ambata wannan kyautar a littafin Yohanna 3:16. Ya ce: “Gama Allah ya yi ƙaunar duniya har ya ba da (makaɗaicin, NW ) Ɗansa, . . . domin dukan wanda yana ba da gaskiya gare shi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.”

Allah ya ba da Ɗansa wanda yake ƙauna sosai domin ya cece mu daga zunubi da tsufa da kuma mutuwa. Hakika wannan ita ce kyauta mafi tamani da aka taɓa ba mu. (Zabura 51:5; Yohanna 8:34) Ko da me muka yi, ba za mu taɓa iya fanshi kanmu ba. Amma domin Allah yana ƙaunar mu sosai, ya yi tanadin abin da zai fanshe mu. Jehobah Allah ya ba da Ɗansa Yesu Kristi wanda yake ƙauna sosai a matsayin fansa, kuma hakan ya ba ’yan Adam masu aminci damar yin rayuwa har abada. Mene ne fansa take nufi? Me ya sa muke bukatar ta? Ta yaya za mu amfana daga fansar?

Fansa wani abu ne da ake bayarwa don a maido da wani abu da ya ɓace ko kuma don a ’yantar da wani. Littafi Mai Tsarki ya ce ba a halicci iyayenmu na farko, wato Adamu da Hauwa’u da zunubi ba. Kuma suna da damar yin rayuwa a aljanna har abada tare da yaran da za su haifa. (Farawa 1:​26-28) Abin baƙin ciki, Adamu da Hauwa’u ba su yi wa Allah biyayya ba kuma hakan ya sa sun zama masu zunubi. Mene ne sakamakon zunubin? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.” (Romawa 5:12) Maimakon yaran Adamu da Hauwa’u su zama kamiltattu, rashin biyayyar da suka yi ya janyo wa yaransu zunubi da kuma mutuwa.

Don a iya fanshe mu, wajibi ne a ba da fansar da ta yi daidai da abin da aka rasa. Adamu ya yi zunubi sa’ad da ya yi wa Allah rashin biyayya da gangan kuma hakan ya sa ya rasa kamiltarsa, wato ya zama ajizi. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce, abin da ya yi ya sa yaran Adamu sun gāji zunubi da kuma mutuwa. Don haka, ana bukatar wani kamili, wato Yesu don a fanshe mu daga zunubi. (Romawa 5:19; Afisawa 1:⁠7) Don ƙaunar da Allah yake mana ne ya sa ya ba da wannan fansar. Shi ya sa muke da damar morar abin da Adamu da Hauwa’u suka rasa, wato damar yin rayuwa har abada a duniya.​—⁠Ru’ya ta Yohanna 21:​3-5.

Hakika wannan kyautar da Allah ya bayar da ta sa za mu iya rayuwa har abada ce kyauta mafi daraja a cikin dukan kyaututtuka. Don mu san cewa wannan “cikakkiyar kyauta” ce, bari mu ga yadda kyautar ta cika abubuwa guda huɗu da muka tattauna a talifin baya.

Ta biya muradinmu. ’Yan Adam suna da muradin yin rayuwa har abada. (Mai-Wa’azi 3:11) Tun da ba za mu iya biyan wannan muradin da kanmu ba, fansar da Allah ya bayar ta sa za mu iya yin rayuwa har abada. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce:  “Gama hakkin zunubi mutuwa ne; amma kyautar Allah rai na har abada ce cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.”​—Romawa 6:23.

Ta biya bukatarmu. ’Yan Adam ba za su iya fanshi kansu ba. Domin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama kuɗin biyan ran mutum ba shi da iyaka. Abin da zai iya biya, sam ba zai isa ba.” (Zabura 49:​8, LMT) Saboda haka, muna bukatar taimakon Allah don mu iya samun ’yanci daga zunubi da kuma mutuwa. Allah ya biya bukatarmu “ta wurin fansa da ke cikin Yesu Kristi.”​—Romawa 3:​23, 24.

An bayar a lokacin da ya dace. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tun muna masu-zunubi tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu.” (Romawa 5:⁠8) Allah ya ba da wannan fansar “tun muna masu-zunubi,” kuma hakan ya nuna irin ƙaunar da Allah yake mana duk da cewa mu ajizai ne. Ko da yake za mu sha wahala domin zunubanmu, wannan fansar ta sa muna da bege mai kyau a nan gaba.

An bayar da dalili mai kyau. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana dalilin da ya sa Allah ya ba da Ɗansa a matsayin fansa. Ya ce: “Ta haka aka bayyana ƙaunar Allah gare mu, da Allah ya aiko da Ɗansa makaɗaici a duniya, domin mu sami rai madawwami ta wurinsa. Ta haka ƙauna take, wato ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu.”​—⁠1 Yohanna 4:​9, 10, LMT.

Ta yaya za ka nuna godiya don wannan kyauta mafi daraja? Ka tuna cewa Yesu ya ambata a littafin Yohanna 3:16 cewa waɗanda suka “ba da gaskiya gare shi” ne za su sami ceto. Littafi Mai Tsarki ya ce bangaskiya “ainihin abin da muke begensa ne.” (Ibraniyawa 11:⁠1) Idan muna so mu kasance da wannan begen, wajibi ne mu koyi game da Allah da kuma nufinsa. Don haka, muna ƙarfafa ka ka koyi game da Jehobah Allah, wanda ya ba da wannan “cikakkiyar kyauta.” Ƙari ga haka, ka koyi abin da za ka yi don ka mori albarkar da fansar Yesu ta tanadar maka, wato rai na har abada.

Za ka iya koya game da waɗannan abubuwan a dandalinmu na www.jw.org/ha. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin taimaka maka. Muna da tabbaci cewa idan ka koya game da wannan kyauta mafi daraja da kuma albarkarta, hakan zai motsa ka ka ce: “Na gode wa Allah ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu.”​—Romawa 7:25.