ABIN DA YA SA HAKAN YAKE DA MUHIMMANCI

Shawarwarin da ka yanke game da yin zina ko a’a za su shafi rayuwarka sosai a nan gaba.

MENE NE ZA KA YI?

Ka yi tunanin wannan yanayin: Heather ta yi wata biyu kawai tana fita zance da Mike, amma ji take kamar ta daɗe da saninsa. Suna aika wa juna saƙonni kowane lokaci, sukan yi sa’o’i da yawa suna magana a waya, har ma ya kai ga cewa sun san abin da kowannensu zai faɗa! Amma Mike yana so su san juna fiye da haka.

A wata biyun da suka yi suna fita zance, abin da suke yi bai wuce su riƙe hannayen juna kuma su ɗan sumbaci juna ba. Heather ba ta son dangantakar ta wuce hakan. Amma ba ta so su rabu da Mike domin babu wanda yake ganin kyaunta da mutuncinta kamar Mike. Ban da haka, ta tabbata cewa ita da Mike suna son juna sosai . . .

Idan shekarunki sun kai ki soma fita zance kuma kin sami kanki a irin yanayin Heather, mene ne za ki yi?

KI DAKATA KI YI TUNANI!

Jima’i kyauta ce da Allah ya ba ma’aurata kawai. Kwana da mace kafin aure yana kama da yin amfani da wannan kyautar a hanyar da ba ta dace ba. Zai zama kamar mai da tufa mai kyau da aka ba ka tsumma

Idan kika yi tsalle daga bishiya kuma kika yi ƙoƙarin tashi sama kamar tsuntsu, za ki faɗi kuma ki ji rauni. Hakazalika, idan kika ƙi bin dokar da ta shafi ɗabi’a, kamar wadda ta ce: “Ku guje wa fasikanci,” za ki fuskanci mugun sakamako.—1 Tasalonikawa 4:3, Littafi Mai Tsarki.

Mene ne sakamakon ƙin bin wannan dokar? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai-aikin fasikanci yana yi wa jiki nasa zunubi.” (1 Korintiyawa 6:18) Hakan gaskiya ne. Ta yaya?

 Masu bincike sun gano cewa matasa da yawa da suka yi zina sun fuskanci ɗaya daga cikin waɗannan mugayen sakamakon da aka ambata a gaba.

  • BAƘIN CIKI. Yawancin matasan da suka yi jima’i kafin su yi aure sun ce sun yi da-na-sani daga baya.

  • RASHIN YARDA. Bayan mace da namiji sun kwana da juna, za su soma tunani, ‘Wataƙila ya taɓa yin zina da wata ko kuma ta taɓa yin zina da wani.’

  • ƁACIN RAI. A cikin zukatansu, ’yan mata da yawa sun fi son wanda zai kāre su, ba wanda zai yi lalata da su ba. Kuma samari da yawa ba sa son yarinyar da suka riga suka kwana da ita.

  • Gaskiyar al’amari: Idan ka kwana da mace kafin ka yi aure, za ka zub da mutuncinka kuma za ka rasa wani abu mai muhimmanci. (Romawa 1:24) Kada ka rage darajarka ta wajen yin zina!

Ka nuna cewa kana da ƙarfin halin “guje wa fasikanci.” (1 Tasalonikawa 4:3, LMT) Idan ka yi aure, za ka iya yin jima’i. Kuma a lokacin, za ka ji daɗin yin hakan ba tare da wani damuwa ko ɓacin rai, ko kuma rashin yarda da ke tattare da kwana da mace kafin ku yi aure ba.—Misalai 7:22, 23; 1 Korintiyawa 7:3.

 MENE NE RA’AYINKI?

  • Kina ganin wanda yake ƙaunarki da gaske zai so ya yi abin da zai sa ki cikin damuwa ko kuma abin da zai ɓata rayuwarki?

  • Kina ganin wanda yake son ki zai so ya sa ki yi abin da zai ɓata dangantakarki da Allah?—Ibraniyawa 13:4.