Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?

 BABI NA SHA BIYU

Ta Yaya Za Ka Iya Zama Aminin Allah?

Ta Yaya Za Ka Iya Zama Aminin Allah?

1, 2. Su waye ne wasu cikin aminan Jehobah?

WANE irin mutumi ne za ka so ya zama amininka? Babu shakka, mutumin da kake ƙauna da wanda kuke shiri da shi da kuma wanda zai fahimce ka. Ƙari ga haka, za ka so mutumin da yake da halayen kirki irin waɗanda kake so.

2 Jehobah ya zaɓi wasu mutane su zama aminansa. Alal misali, Jehobah ya zaɓi Ibrahim ya zama amininsa. (Ishaya 41:8; Yaƙub 2:23) Jehobah ya ƙaunaci Dauda. Ya ce Dauda mutumi ne ‘da yake ƙauna ƙwarai.’ (Ayyukan Manzanni 13:22, Littafi Mai Tsarki) Ya kuma ce Daniyel “ƙaunatacce ne ƙwarai” a gare shi.—Daniyel 9:23.

3. Me ya taimaka wa Ibrahim da Dauda da kuma Daniyel su zama aminan Jehobah?

3 Me ya taimaka wa Ibrahim da Dauda da kuma Daniyel su zama aminan Jehobah. Jehobah ya gaya wa Ibrahim cewa: “Ka yi biyayya da maganata.” (Farawa 22:18) Jehobah yana zaɓan masu tawali’u da kuma masu biyayya ne su zama aminansa. Al’umma gabaki ɗaya ma za ta iya zama amininsa. Jehobah ya gaya wa al’ummar Isra’ila cewa: “Ku kasa kunne ga muryata; ni kuma in zama Allahnku, ku kuma ku zama mutanena.” (Irmiya 7:23) Don haka, kai ma za ka iya zama aminin Jehobah idan kana masa biyayya.

JEHOBAH YANA KĀRE AMINANSA

4, 5. Ta yaya Jehobah yake kāre aminansa?

4 Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah yana neman hanyoyin da zai “bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu  ta kamalta gareshi.” (2 Labarbaru 16:9) Jehobah ya yi wa aminansa alkawari a littafin Zabura 32:8 cewa: ‘Zan sanar da kai, zan koya maka cikin tafarkin da za ka bi: da idona a kanka zan ba ka shawara.’

5 Akwai wani mugun da yake so ya hana mu mu zama aminan Allah. Amma Jehobah yana so ya kāre mu. (Karanta Zabura 55:22.) Da yake mu aminan Jehobah ne, muna masa ibada da zuciya ɗaya. Mun tsai da shawarar kasancewa da aminci ko da a wane irin yanayi ne muka sami kanmu. Kuma muna da tabbacin da marubucin zabura ya kasance da shi. Ya ce game da Jehobah: “Da shi ke yana ga hannun damana ba zan jijjigu ba.” (Zabura 16:8; 63:8) Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙari ya hana mu mu zama aminan Allah?

ƘARYAR DA SHAIƊAN YA YI

6. Wace ƙarya ce Shaiɗan ya yi a kan ’yan Adam?

6 A Babi na 11, mun koya cewa Shaiɗan ya yi wa Jehobah sharri cewa shi maƙaryaci ne marar adalci domin bai ƙyale Adamu da Hawwa’u su tsai da shawara a kan abin da ya dace da wanda bai dace ba. Littafin Ayuba ya nuna cewa Shaiɗan ya zargi dukan mutanen da suke so su zama aminan Allah. Shaiɗan ya ce ai suna bauta wa Allah don abubuwan da yake ba su ne, ba domin suna ƙaunar sa ba. Shaiɗan ya ma yi da’awar cewa zai iya juya kowane mutum daga bautar Allah. Bari mu bincika darasin da za mu iya koya daga labarin Ayuba kuma mu ga yadda Jehobah ya kāre shi.

7, 8. (a) Wane irin mutumi ne Ayuba? (b) Wace ƙarya ce Shaiɗan ya yi a kan Ayuba?

7 Wane irin mutumi ne Ayuba? Shi mutumin kirki ne da ya taɓa rayuwa wajen shekara dubu uku da ɗari shida da suka shige. Jehobah ya ce babu wani mutum irinsa a duniya a lokacin. Ayuba ya yi biyayya ga Allah kuma  ya tsani mugunta. (Ayuba 1:8) Hakika, Ayuba aminin Jehobah ne sosai.

8 Shaiɗan ya yi da’awar cewa Ayuba yana bauta wa Allah ne don abubuwa masu kyau da Allah yake ba shi. Ya gaya wa Jehobah: “Ba ka kewaye shi da shinge ba, da shi da gidansa, da dukan abin da yake da shi, a kowane sassa? Ka albarkaci aikin hannuwansa, dabbobinsa sun ƙaru a ƙasa. Miƙa hannunka kaɗai yanzu, ka taɓa dukan abin da yake da shi, za ya la’anta ka a fuskarka!”—Ayuba 1:10, 11.

9. Mene ne Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya yi?

9 Shaiɗan ya yi ƙarya cewa Ayuba yana bauta wa Jehobah don abubuwa masu kyau da yake samu. Shaiɗan ya ce zai iya hana Ayuba bauta wa Jehobah. Jehobah bai amince da ƙaryar da Shaiɗan ya yi ba, shi ya sa ya ƙyale Shaiɗan ya gwada shi don ya nuna cewa Ayuba ya gaskata da Allah kuma yana ƙaunarsa.

SHAIƊAN YA TA DA HANKALIN AYUBA

10. Ta yaya Shaiɗan ya ta da hankalin Ayuba, kuma yaya Ayuba ya bi da yanayin?

10 Da farko, Shaiɗan ya sace ko kuma halaka dabbobin Ayuba. Bayan haka, sai ya kashe yawancin bayinsa. Ayuba ya rasa dukan abin da yake da shi. A ƙarshe, Shaiɗan ya kashe ’ya’yan Ayuba goma da guguwa. Duk da haka, Ayuba ya kasance da aminci ga Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ko da yake waɗannan al’amura duka sun faru, duk da haka Ayuba bai sa wa Allah laifi ba.”—Ayuba 1:12-19, 22, LMT.

Jehobah ya sāka wa Ayuba don amincinsa

11. (a) Mene ne kuma Shaiɗan ya yi wa Ayuba? (b) Mene ne Ayuba ya yi?

11 Shaiɗan bai gaji ba. Ya zargi Allah cewa: “Ka taɓa ƙashinsa da namansa, sai shi la’anta ka a fuskarka.” Sai Shaiɗan ya sa Ayuba ya yi wani mugun ciwo. (Ayuba 2:5, 7)  Har ila, Ayuba ya kasance da aminci ga Jehobah. Ya ce: “Har in mutu ba ni rabuwa da gaskiyata.”—Ayuba 27:5.

12. Ta yaya Ayuba ya tabbatar da cewa Shaiɗan maƙaryaci ne?

12 Ayuba bai san zargin da Shaiɗan ya yi a kansa ba kuma bai fahimci dalilin da ya sa yake shan wahala ba. Ya ɗauka cewa Jehobah ne ya sa yake shan wahala. (Ayuba 6:4; 16:11-14) Duk da haka, Ayuba ya kasance da aminci ga Jehobah. Babu shakka, Ayuba bai bauta wa Jehobah don abubuwa masu kyau da yake ba shi ba. Hakika, shi aminin Allah ne domin yana ƙaunarsa. Ƙarya Shaiɗan ya yi!

13. Mene ne sakamakon amincin Ayuba?

13 Ko da yake Ayuba bai san abin da ya faru a sama ba, duk da haka, ya kasance da aminci ga Allah kuma hakan ya nuna cewa Shaiɗan mugu ne. Jehobah ya albarkaci Ayuba don amincinsa.—Ayuba 42:12-17.

YADDA SHAIƊAN YAKE ZARGINKA

14, 15. Ta yaya Shaiɗan ya zargi dukan mutane maza da mata?

14 Za ka iya koyan darussa daga abin da ya faru da Ayuba. A yau, Shaiɗan yana zarginmu cewa muna bauta wa Jehobah don abubuwa masu kyau da muke samu daga wurinsa ne. A littafin Ayuba 2:4, Shaiɗan ya ce: ‘Dukan abin da mutum yake da shi, zai bayar a bakin ransa.’ Wannan ya nuna cewa Shaiɗan ya zargi dukan mutane maza da mata, ba Ayuba kaɗai ba. Shaiɗan ya ci gaba da zargin Jehobah da kuma bayinsa shekaru da yawa bayan mutuwar Ayuba. Alal misali, littafin Misalai 27:11 ya ce: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayar da magana ga wanda ya zarge ni.”

15 Kai ma za ka iya tsai da shawarar yin biyayya ga Jehobah kuma ka zama amininsa don a san cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Ko da kana bukata ka canja salon rayuwarka  don ka zama aminin Jehobah, yin hakan shawara ce mai kyau da ya kamata ka yanke! Wannan ba abin da ya kamata mu ɗauka da wasa ba ne. Me ya sa? Don Shaiɗan ya yi da’awa cewa ba za ka iya kasancewa da aminci ba idan kana fuskantar matsaloli. Yana ƙoƙarin ya sa mu daina kasancewa da aminci. Ta yaya?

16. (a) Waɗanne dabaru ne Shaiɗan yake amfani da su don ya hana mutane bauta wa Jehobah? (b) Ta yaya Shaiɗan zai yi ƙoƙarin hana ka bauta wa Jehobah?

16 Shaiɗan yana amfani da hanyoyi da yawa don ya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Yana yin hakan “kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.” (1 Bitrus 5:8) Kada ka yi mamaki idan abokanka da danginka da kuma wasu suka yi ƙoƙarin hana ka yin nazarin Littafi Mai Tsarki ko kuma yin abin da ya dace. Za ka ji kamar ana tsananta maka ne. * (Yohanna 15:19, 20) Shaiɗan yakan mai da kansa kamar shi “mala’ika na haske” ne. Saboda haka, zai yi ƙoƙari ya yaudare mu don mu ƙi yin biyayya ga Jehobah. (2 Korintiyawa 11:14) Wata dabara kuma da Shaiɗan yake amfani da ita don ya sa mu daina bauta wa Jehobah ita ce yana sa mu ga kamar ba mu cancanci mu bauta wa Jehobah ba.—Misalai 24:10.

KU BI DOKOKIN JEHOBAH

17. Me ya sa muke biyayya ga Jehobah?

17 Idan muka yi biyayya da Allah, muna tabbatar da cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Mene ne zai taimaka mana mu yi biyayya? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka ƙaunaci  Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka.” (Kubawar Shari’a 6:5) Muna biyayya ga Jehobah don muna ƙaunarsa ne. Idan muka ci gaba da ƙaunar Jehobah, za mu yi iya ƙoƙarinmu don mu yi abin da ya umurce mu mu yi. Manzo Yohanna ya ce: “Gama ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo.”—1 Yohanna 5:3.

18, 19. (a) Waɗanne abubuwa ne Jehobah ba ya so? (b) Me ya tabbatar mana cewa Jehobah ba ya gaya mana mu yi abin da ya fi ƙarfinmu?

18 Waɗanne abubuwa ne Jehobah ya gaya mana cewa ba su da kyau? Akwai wasu misalai a akwatin nan “ Ka Guji Abubuwan da Jehobah Ba Ya So.” Da farko, za ka ɗauka cewa waɗannan abubuwan ba su da muni sosai. Amma idan ka karanta wasu ayoyi kuma ka yi tunani a kansu sosai, za ka fahimci cewa bin dokokin Jehobah, zai sa ka kasance da hikima. Ƙari ga haka, za ka ga cewa kana bukata  ka canja salon rayuwarka. Ko da yake hakan zai yi wuya a wasu lokatai, waɗannan canje-canje da za ka yi za su sa ka kasance da kwanciyar hankali da farin ciki a matsayin aminin Allah. (Ishaya 48:17, 18) Ta yaya muka san cewa zai yiwu mu bar munanan halayenmu na dā?

19 Jehobah ba zai taɓa gaya mana mu yi abin da ya fi ƙarfinmu ba. (Kubawar Shari’a 30:11-14) Da yake shi Amininmu ne, ya san mu sosai fiye da yadda muka san kanmu. Ya san abin da za mu iya yi da wanda ba za mu iya yi ba. (Zabura 103:14) Shi ya sa Manzo Bulus ya ƙarfafa mu cewa: “Allah mai-aminci ne, da ba za ya bari a yi muku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi muku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.” (1 Korintiyawa 10:13) Muna da tabbaci cewa a kullum, Jehobah zai ba mu ƙarfin yin abin da ya dace. Zai ba ka “mafificin girman iko” don ka iya jimre matsaloli masu tsanani. (2 Korintiyawa 4:7) Manzo Bulus ya yi wannan furucin bayan da Jehobah ya taimaka  masa. Ya ce: “Zan iya yin abu duka ta wurin Kristi da yake ƙarfafani.”—Filibiyawa 4:13.

KA KOYI YIN ABIN DA ALLAH YAKE SO

20. Waɗanne halaye ne ya kamata ka yi koyi da su kuma me ya sa?

20 Idan muna so mu zama aminan Allah, ya kamata mu daina yin abubuwan da ba ya so, amma ba shi ke nan ba. (Romawa 12:9) Aminan Allah suna son abin da yake so. Littafin Zabura 15:1-5 ya nuna halayen da aminan Allah za su kasance da su. (Karanta.) Aminan Allah suna koyi da halayensa kuma suna da ‘ƙauna, farin ciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa.’—Galatiyawa 5:22, 23.

21. Me zai taimaka maka ka kasance da halayen da Allah yake so?

21 Me zai taimaka maka ka kasance da waɗannan halaye masu kyau? Zai dace ka koya yin abin da Jehobah yake so ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki da kuma nazarta shi a koyaushe. (Ishaya 30:20, 21) Idan ka yi hakan, ƙaunarka ga Jehobah za ta ƙaru kuma hakan zai taimaka maka ka bi dokokinsa.

22. Wace lada ce za ka samu idan ka yi biyayya ga Jehobah?

22 Canja halayenka na dā yana nan kamar yadda mutum yake tuɓe tsohon kaya sa’an nan ya saka sabo. Littafi Mai Tsarki ya ce kana bukata ka tuɓe ‘halinka na dā’ kuma ka saka ‘sabon hali.’ (Kolosiyawa 3:9, 10, LMT) Ko da yake zai iya zama da wuya mu bar halaye na dā, idan muka yi iya ƙoƙarinmu kuma muka yi biyayya ga Jehobah, ya yi alkawari zai ba mu “lada mai-girma.” (Zabura 19:11) Babu shakka, zai dace ka tsai da shawarar yin biyayya ga Jehobah kuma ka nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Ka bauta wa Jehobah ba domin ladar da za ka samu a nan gaba ba, amma domin kana ƙaunarsa da zuciya ɗaya. Bayan ka yi haka ne za ka zama aminin Allah.

^ sakin layi na 16 Hakan ba ya nufin cewa Shaiɗan ne yake ja-gorar mutanen da suke ƙoƙarin hana ka yin nazarin Littafi Mai Tsarki ba. Amma Shaiɗan shi ne “allah na wannan zamani” kuma ‘duniya duka tana kwance cikin Shaiɗan.’ Saboda haka, idan mutane suka yi ƙoƙarin hana ka bauta wa Jehobah, kada ka yi mamaki.—2 Korintiyawa 4:4; 1 Yohanna 5:19.