MANUFAR WANNAN BABIN

Sarkin ya shirya masu wa’azi da yawa

1, 2. Wane annabci ne Yesu ya yi, kuma hakan ya jawo wace muhimmiyar tambaya ce?

’YAN SIYASA suna yawan yin alkawura amma ba sa cika su. Har masu kyakkyawan nufi a cikinsu ma ba sa iya cika alkawuransu a yawancin lokatai. Amma abin farin ciki shi ne Sarki Almasihu, wato Yesu Kristi, ya sha bambam da su domin yana cika alkawuransa a kowane lokaci.

2 Bayan Yesu ya zama Sarki a shekara ta 1914, ya kasance a shirye ya cika annabcin da ya yi tun shekaru 1,900 da suka shige. Jim kaɗan kafin Yesu ya mutu, ya ce: ‘Wannan bishara kuwa ta Mulkin za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya.’ (Mat. 24:14) Cikar wannan annabcin zai zama ɗaya daga cikin alamun bayyanuwar Yesu a matsayin sarkin Mulkin Allah. Amma, wata muhimmiyar tambaya ita ce: Ta yaya Sarkin zai shirya jama’a da za su yi wa’azi da yardan rai a waɗannan kwanaki na ƙarshe, inda son zuciya da kuma rashin ƙauna da ƙin ibada suka zama ruwan dare? (Mat. 24:12; 2 Tim. 3:1-5) Muna bukata mu san amsar wannan tambayar domin yin wa’azi ya zama wajibi ga Kiristoci na gaskiya.

3. Wane tabbaci ne Yesu yake da shi, kuma me ya sa ya kasance da irin wannan tabbacin?

3 Bari mu sake yin la’akari da wannan annabcin da Yesu ya yi. Shin kalmomin nan “za a yi wa’azinta” suna sa mu kasance da tabbaci kuwa? Hakika! Yesu yana da tabbaci cewa zai samu mutanen da za su ba da kansu da yardan rai a kwanaki na ƙarshe. A ina ne ya koyi kasancewa da irin wannan tabbacin? Ya koyi hakan ne a wurin Ubansa. (Yoh. 12:45; 14:9) Kafin ya zo duniya, Yesu ya lura cewa Jehobah ya yarda da bayinsa kuma ya san cewa za su sadaukar da kansu da son rai. Bari mu tattauna yadda Jehobah ya yi hakan.

‘Mutanenka Za Su Ba da Kansu da Yardan Rai’

4. Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa su goyi bayan wane aiki, kuma mene ne suka yi?

4 Ka yi la’akari da abin da ya faru sa’ad da Jehobah ya umurci Musa ya gina mazauni ko tanti wanda ya zama cibiyar bauta na Isra’ilawa. Jehobah ya ce wa Musa ya gayyaci dukan mutanen su goyi bayan aikin. Sai Musa ya ce musu: “Duk wanda ya yi niyya, bari ya kawo wa Ubangiji sadaka  [gudummawa].” Wane sakamako ne aka samu? ‘Jama’a suka yi ta kawo masa sadaka [gudummawa] ta yardan rai kowace safiya.’ Sun kawo gudummawa mai yawa sosai har aka ce su daina “kawowa.” (Fit. 35:5; 36:3, 6, Littafi Mai Tsarki) Jehobah ya amince da Isra’ilawa kuma ba su kunyata shi ba.

5, 6. Wane hali ne Jehobah da Yesu suke so bayin Allah su kasance da shi a waɗannan kwanaki na ƙarshe kamar yadda aka ambata a Zabura 110:1-3?

5 Shin Jehobah ya sa rai cewa bayinsa za su kasance da yardan rai a kwanaki na ƙarshe? Hakika! Shekaru fiye da 1,000 kafin a haifi Yesu a duniya, Jehobah ya hure sarki Dauda ya yi rubutu game da lokacin da Almasihu zai soma sarauta. (Karanta Zabura 110:1-3.) Yesu, sabon Sarkin da aka naɗa, zai yi magabta da za su yi adawa da shi. Duk da haka, zai sami mutane masu yawan gaske da za su goyi bayansa. Ba za a tilasta musu su yi wa Sarkin hidima ba. Har yara ƙanana da ke tsakaninsu ma za su ba da kansu da yardan rai, kuma yawansu zai yi kama da raɓa da ke jiƙa ƙasa da safe. *

Wadanda suke goyon bayan Mulkin da yardan rai sun yadu kamar raba (Ka duba sakin layi na 5)

6 Yesu ya san cewa an yi annabcin da ke Zabura ta 110 a kansa ne. (Mat. 22:42-45) Saboda haka, ya kasance da tabbaci cewa zai sami magoya baya da za su ba da kansu da yardan rai don yin wa’azi a dukan duniya. Mene ne tarihi ya nuna game da hakan? Sarkin ya sami masu wa’azi da yardan rai a waɗannan kwanaki na ƙarshe kuwa?

“Gatana da Kuma Aikina Shi Ne In Sanar da Saƙon Nan”

7. Bayan da aka naɗa Yesu Sarki, waɗanne matakai ne ya ɗauka don ya shirya magoya bayansa su yi gagarumin aikin da ya ba su?

7 Jim kaɗan bayan Yesu ya soma sarauta a sama, ya ɗauki mataki don ya shirya mabiyansa su yi wannan gagarumin aikin. Kamar yadda muka tattauna a Babi na 2, Yesu ya yi bincike da kuma tsarkakewa daga shekara ta 1914 zuwa somawar 1919. (Mal. 3:1-4) Sa’an nan a shekara ta 1919, Yesu ya naɗa bawa mai aminci don ya ja-goranci mabiyansa. (Mat. 24:45) Tun daga lokacin, bawan ya soma  koyar da bayin Allah ta hanyar jawabai a taron gunduma da kuma littattafai da suke nanata cewa dukan Kiristoci suna bukata su yi wa’azi.

8-10. Ta yaya manyan taro suka ƙarfafa mutane su yi wa’azi? Ka ba da misali. (Ka kuma duba akwatin nan “ Manyan Taron da Suka Ƙarfafa Yin Wa’azi.”)

8 Jawabai a taron gunduma. Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun taru a filin shaƙatawa na Cedar Point, a jihar Ohio, a Amirka daga ranar 1 zuwa 8 ga Satumba, 1919. Wannan ne babban taron na farko da suka yi bayan Yaƙin Duniya na Ɗaya. Me ya sa suka yi wannan taron? Domin suna neman ja-gora. A rana ta biyu, Ɗan’uwa Rutherford ya yi wannan bayanin a wani jawabin da ya bayar: “Aikin da kowane Kirista yake da shi a duniya . . . shi ne ya yaɗa bisharar mulkin Ubangiji.”

9 A rana ta ƙarshe, Ɗan’uwa Rutherford ya ba da wani jawabi mai jigo “Address to Co-laborers,” (Jawabi ga Abokan Aiki). Bayan haka, an wallafa jawabin cikin Hasumiyar Tsaro da wannan jigon “Announcing the Kingdom” (Yin Shelar Mulkin). A cikin jawabin, ya ce: “A wasu lokatai Kirista yakan yi tunani sosai kuma ya tambayi kansa, Me ya sa aka halicce ni? Ya kamata amsarsa ta zama, Ubangiji ya halicce ni ne don in sanar da saƙon da zai sulhunta mutane da Allah, saboda haka, gatana da kuma aikina shi ne in sanar da saƙon nan.”

10 A wannan muhimmin jawabi, Ɗan’uwa Rutherford ya sanar da cewa za a soma wallafa wata sabuwar mujalla mai jigo The Golden Age (wadda ake kira Awake! yanzu), kuma manufar mujallar ita ce a sanar da mutane cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai magance matsalolin ’yan Adam. Sai ya yi tambaya cewa mutane nawa ne a cikin masu sauraro za su so su rarraba wannan mujallar. Wani rahoto da aka bayar game da taron ya ce: “Amsar da aka bayar a lokacin abin ƙarfafa ne. Dukan mutane dubu shida da suka hallara suka tashi tsaye don su nuna cewa za su rarraba mujallar.” * Hakika, Sarkin yana da magoya baya da suke shirye su yaɗa bishara game da Mulkinsa da yardan rai!

11, 12. Mece ce Hasumiyar Tsaro ta shekara ta 1920 ta faɗa a kan lokacin da za a yi aikin da Yesu ya annabta?

11 Littattafai. Mujallun Hasumiyar Tsaro sun ba da ƙarin haske a kan muhimmancin aikin da Yesu ya annabta, wato yin wa’azi game da Mulkin Allah. Ka yi la’akari da wasu misalai daga shekara ta 1920 zuwa 1923.

12 Wane saƙo ne za a sanar kamar yadda aka annabta a littafin Matta 24:14? A yaushe ne za a yi wannan aikin? Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuli, 1920, a talifi mai jigo “Gospel of the Kingdom” (Bishara ta Mulkin) ta ce: “Wannan bisharar game da ƙarshen wannan muguwar duniya ce da kuma kafawar mulkin Almasihu.” Talifin ya bayyana lokacin da za a yi wannan aikin, ya ce: “Wajibi ne a yaɗa wannan saƙon tsakanin lokacin babban yaƙin duniya [Yaƙin Duniya na  Ɗaya] da kuma lokacin ‘ƙunci mai girma.’” Saboda haka, talifin ya daɗa cewa: “Yanzu ne lokacin . . . da za mu yi shelar wannan bishara ga Kiristendom a faɗin duniya.”

13. Yaya Hasumiyar Tsaro ta shekara ta 1921 ta ƙarfafa Kiristoci shafaffu su kasance da halin sadaukar da kai?

13 Shin za a matsa wa bayin Allah su yi aikin da Yesu ya annabta ne? A’a. Talifin nan “Be of Good Courage,” (Ka Kasance da Gaba Gaɗi) da aka wallafa a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Maris, 1921, ya ƙarfafa Kiristoci shafaffu su kasance da halin sadaukar da kai. An ƙarfafa kowannensu ya yi wa kansa wannan tambayar: “Shin yin wannan aikin ba babban gata da kuma hakki ne a gare ni ba?” Talifin ya daɗa da cewa: “Muna da tabbaci cewa idan ka ɗauki [wannan aikin a matsayin babban gata] za ka zama kamar Irmiya, wanda maganar Ubangiji ta zama ‘kamar wuta mai-ƙonewa a kulle cikin ƙasusuwansa,’ wadda take sa ya ci gaba da yin magana.” (Irm. 20:9) Wannan ƙarfafawar da aka bayar ta nuna cewa Jehobah da kuma Yesu sun san cewa suna da magoya baya masu aminci.

14, 15. Hasumiyar Tsaro ta shekara ta 1922 ta ƙarfafa Kiristoci shafaffu su yi amfani da wace hanya don yaɗa saƙon Mulki?

14 A wace hanya ce ya kamata Kiristoci na gaskiya su yaɗa saƙon Mulkin? Wani gajeren talifi da ke cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta, 1922, mai jigo, “Service Essential,” Muhimmiyar Hidima) ya ƙarfafa Kiristoci shafaffu su “riƙa rarraba wa mutane littattafai kuma su yi musu wa’azi a gidajensu da ƙwazo, suna cewa mulkin sama ya kusa.”

15 Hakika, daga shekara ta 1919, Kristi ya yi amfani da bawa mai aminci mai hikima don ya nanata cewa dukan Kiristoci suna da gata da kuma hakkin yaɗa saƙon Mulki a duniya. Wane mataki ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka ɗauka sa’ad da aka ƙarfafa su su yaɗa bisharar Mulkin?

“Masu Aminci Za Su Ba da Kai”

16. Wane mataki ne wasu dattawa suka ɗauka sa’ad da aka ce su yi wa’azi?

16 A tsakanin shekara ta 1920 zuwa 1939, wasu ba su yarda da ra’ayin nan cewa ya kamata dukan Kiristoci shafaffu su yi wa’azi ba. Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 1927, ta bayyana abin da ya faru cewa: “Akwai wasu a cikin coci [ikilisiya] a yau waɗanda dattawa ne . . . da suka ƙi ƙarfafa ’yan’uwa su yi wannan wa’azin kuma su ma sun ƙi yin hakan. . . . Suna watsi da shawarar da aka bayar cewa ya kamata a bi ƙofa-ƙofa ana wa’azi game da Allah da Mulkinsa da kuma Sarkin Mulkinsa.” Talifin ya bayyana dalla-dalla cewa: “Lokaci ya yi da ya kamata amintattu su kiyayi irin waɗannan mutanen kuma su daina tarayya da su, kuma su gaya musu cewa ba za a sake naɗa su dattawa ba.” *

17, 18. Ta yaya yawancin ’yan’uwa a cikin ikilisiyoyi suka bi umurni da bawa mai aminci ya bayar, kuma mene ne miliyoyi suka yi a cikin shekaru 100 nan da suka shige?

17 Abin farin ciki shi ne, yawancin ’yan’uwan a cikin ikilisiyoyi dabam-dabam sun bi shawarar da bawa mai aminci ya bayar. Sun ɗauki yin wa’azi game da Mulkin Allah a  matsayin gata. Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Maris, 1926, ta ce: “Masu aminci za su ba da kansu da yardan rai . . . don su yaɗa wannan saƙon ga mutane.” Irin waɗannan ’yan’uwa masu aminci sun cika annabcin da ke Zabura 110:3 kuma sun nuna cewa suna goyon bayan Mulkin Almasihu da yardan rai.

18 A cikin shekaru 100 da suka shige, miliyoyin mutane sun ba da kansu da yardan rai don su yaɗa bishara ta Mulkin Allah. A cikin babobi na gaba, za mu tattauna hanyoyi da kayayyakin aikin da suka yi amfani da su a yin wa’azi da kuma sakamakon da aka samu. Amma, bari mu soma da tattauna dalilin da ya sa miliyoyin mutane suke yin wa’azin Mulkin Allah da yardan rai, duk da cewa muna zaune ne a duniyar da take cike da mutane masu son kai. Yayin da muke tattauna wannan dalilin, ya kamata mu tambayi kanmu, ‘Me ya sa nake yin wa’azi?’

“Ku Fara Biɗan Mulkinsa”

19. Me ya sa muke bin umurnin da Yesu ya bayar cewa mu “fara biɗan mulkin” Allah?

19 Yesu ya shawarci mabiyansa su “fara biɗan mulkinsa.” (Mat. 6:33) Me ya sa muke bin wannan umurnin? Dalili mafi muhimmanci shi ne domin mun san cewa Mulkin ne zai sa nufin Allah ya cika. Kamar yadda muka tattauna a babi na 5, ruhu mai tsarki yana bayyana wannan muhimmiyar gaskiya game da Mulkin Allah da sannu-sannu. Sa’ad da wannan gaskiyar ta shiga zuciyarmu, hakan yana sa mu biɗi Mulkin Allah farko a rayuwarmu.

Kamar mutumin da ya ga ɓoyayyiyar dukiya, Kiristoci suna farin ciki saboda gaskiyar da suka koya game da Mulki (Ka duba sakin layi na 20)

20. Ta yaya kwatancin Yesu na ɓoyayyiyar dukiya ya nuna muhimmancin biɗan Mulkin da farko a rayuwarmu?

20 Yesu ya san cewa mabiyansa za su bi shawarar da aka ba su na biɗar Mulkin farko a rayuwarsu. Ka yi la’akari da kwatancin da ya bayar na ɓoyayyiyar dukiya. (Karanta Matta 13:44.) Yayin da mutumin da aka ambata a kwatancin yake aiki, sai ya iske ɓoyayyiyar dukiya kuma ya san tamaninsa nan da nan. Me ya yi? “Don farin cikin abin kuma ya tafi ya sayar da dukan abin da yake da shi, ya sayi gonan.” Wane darasi za mu iya koya daga wannan kwatancin? Sa’ad da muka koyi gaskiya game da Mulkin Allah kuma muka san tamaninsa, za mu yi duk wata sadaukarwar da muke bukatar mu yi domin mu biɗi Mulkin Allah farko a rayuwarmu. *

21, 22. Ta yaya amintattun magoya bayan Mulkin suke nuna cewa suna biɗan Mulkin da farko a rayuwarsu? Ka ba da misali.

21 Ta ayyukansu, amintattun magoya bayan Mulkin suna nuna cewa suna biɗan Mulkin farko a rayuwarsu. Suna yin amfani da rayuwarsu da iyawarsu da kuma dukiyarsu wajen yin wa’azin Mulkin Allah. ’Yan’uwa da yawa sun yi sadaukarwa don su yi hidima ta cikakken lokaci. Waɗanda suka yi hakan sun lura cewa Jehobah yana yi wa mutanen da suke biɗan Mulkinsa farko a rayuwarsu albarka. Ka yi la’akari da wani misali.

 22 Ɗan’uwa Avery Bristow da matarsa Lovenia sun soma hidimar majagaba tare a kudancin Amirka tsakanin shekara ta 1927-1929. Bayan wasu shekaru, Lovenia ta faɗi abin da ya faru: “Ni da Avery mun ji daɗin yin hidimar majagaba tare tun wannan lokacin. Akwai lokuta da yawa da ba mu san yadda za mu sami kuɗin sayan fetur ko kuma abinci ba. Amma a kowane lokaci, Jehobah yana yi mana tanadi. Ba mu daina hidimarmu ba. Mun sami ainihin bukatunmu.” Lovenia ta kuma tuna wata rana da suke hidima a birnin Pensacola, a Jihar Florida kuma ba su da kuɗin sayan abinci. Sa’ad da suka dawo gidansu, sai suka ga jakunkuna guda biyu cike da abinci tare da wata wasiƙa da aka ce, “Daga Ikilisiyar Pensacola.” * Lovenia ta tuna shekarun da ta yi a hidimar majagaba kuma ta ce: “Jehobah bai taɓa yasar da mu ba. Bai taɓa yin abin da zai sa mu daina dogara da shi ba.”

23. Mene ne ra’ayinka a kan gaskiyar da ka koya game da Mulkin Allah, kuma me ka ƙuduri niyyar yi?

23 Sa’o’in da kowannenmu zai yi yana wa’azi ba zai kasance iri ɗaya ba, domin yanayinmu ya bambanta. Amma dai, dukanmu muna more gatan yaɗa bishara da dukan zuciyarmu. (Kol. 3:23) Muna daraja gaskiyar da muka koya game da Mulkin Allah, shi ya sa muke shirye mu yi kowace irin sadaukarwar domin mu yi wa’azi da dukan ƙarfinmu. Ƙudurinka ke nan?

24. Wane abu mafi muhimmanci ne Mulkin ya cim ma a waɗannan kwanaki na ƙarshe?

24 A cikin ƙarnin da ya shige, Sarkin ya cika annabcinsa da ke littafin Matta 24:14 kuma bai tilasta wa mutane kafin ya cika wannan annabcin ba. Bayinsa da suka fito daga wannan duniyar da take cike da son kai suna yin hakan da yardan rai. Wa’azin da suke yi a dukan duniya alama ce da ta nuna cewa Yesu ya soma Mulki, kuma hakan wani gagarumin abu ne da Mulkin ya cim ma a waɗannan kwanaki na ƙarshe.

^ sakin layi na 5 A cikin Littafi Mai Tsarki, ana yin amfani da kalmar nan raɓa don a kwatanta yalwa.—Far. 27:28; Mi. 5:7.

^ sakin layi na 10 Ƙasidar nan To Whom the Work Is Entrusted (Ga Wanda Aka Danƙa Wa Aikin) ta ce: “An wallafa mujallar The Golden Age don a yaɗa bisharar mulki gida-gida. . . . Ƙari ga hakan, za a riƙa barin kofi guda na wannan mujallar a gidajen mutane ko da sun ce a riƙa kawo musu kowane wata ko a’a.” Shekaru da yawa bayan hakan, an ƙarfafa ’yan’uwa su rarraba wa mutane mujallar The Golden Age da kuma Hasumiyar Tsaro. Daga ranar 1 ga Fabrairu, 1940, an ƙarfafa bayin Jehobah su rarraba mujallu kuma su ba da rahoton adadin mujallun da suka rarraba.

^ sakin layi na 16 A lokacin, ’yan’uwa a cikin ikilisiya ne suke jefa ƙuri’a don su zaɓi dattawa. Saboda haka, ikilisiyar za ta iya ƙin zaɓan ɗan’uwan da ba ya son yin wa’azi. Za mu tattauna yadda aka daina wannan zaɓen a Babi na 12.

^ sakin layi na 20 Yesu ya sake yin amfani da irin waɗannan kalmomin sa’ad da yake ba da kwatancin wani mutum da ya je neman lu’u lu’u mai tamanin gaske. Sa’ad da ya sami lu’u lu’un, sai ya sayar da dukan dukiyarsa don ya saye shi. (Mat. 13:45, 46) Waɗannan kwatanci guda biyu sun koya mana cewa za mu iya koyon gaskiya game da Mulkin Allah a hanyoyi dabam-dabam. Wasu suna samun ta cikin sauƙi, wasu kuma sai sun neme ta da gaske. Amma, ko da ta wace hanya ce muka sami wannan gaskiyar, muna shirye mu yi sadaukarwa don mu saka Mulkin farko a rayuwarmu.

^ sakin layi na 22 Ana kiran Ikilisiyoyi kamfanoni a lokacin.