Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Mulkin Allah Yana Sarauta!

 BABI NA 13

Masu Wa’azin Mulkin Sun Kai Ƙara Kotu

Masu Wa’azin Mulkin Sun Kai Ƙara Kotu

MANUFAR WANNAN BABIN

Kamar yadda Yesu ya annabta, mabiyansa suna fuskantar hamayya don wa’azin da suke yi

1, 2. (a) Mene ne limaman addini suka yi game da yin wa’azi, kuma wane mataki ne manzannin suka ɗauka? (b) Me ya sa manzannin suka ƙi biyayya sa’ad da aka hana su yin wa’azi?

JIM KAƊAN bayan Fentakos na shekara ta 33 a zamaninmu, wato ’yan makonni bayan an kafa ikilisiyar da ke Urushalima, Shaiɗan ya ga cewa ya dace ya kai wa Kiristoci hari. Yana so ya halaka Kiristoci kafin su bunƙasa. Nan da nan sai ya sa limaman addinai suka hana yin wa’azin Mulkin Allah. Amma, manzannin sun ci gaba da yin wa’azi da gaba gaɗi, kuma maza da mata da yawa suka ‘ba da gaskiya’ ga Ubangiji.—A. M. 4:18, 33; 5:14.

Manzannin sun yi murna domin “sun . . . sha wulakanci saboda sunan Yesu”

2 Sa’ad da magabta suka ga hakan, sai suka fusata kuma suka jefa dukan manzannin cikin kurkuku. Amma da dare, mala’ikan Jehobah ya buɗe ƙofofin kurkuku kuma manzannin suka fito. Sa’ad da gari ya waye, sai suka ci gaba da yin wa’azi. Bayan haka, sai aka sake kama su, aka kai su gaban shugabanni kuma suka tuhume manzannin da karya dokar da ta hana yin wa’azi. Amma cike da gaba gaɗi suka ce: “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.” Hakan ya ɓata wa shugabannin rai sosai har ma suka so su “kashe” manzannin. Amma nan da nan, wani babban malami mai suna Gamaliel ya gargaɗi shugabannin cewa: “Ku kula fa . . . ku fita sha’anin mutanen nan, ku ƙyale su.” Abin mamaki, shugabannin suka saurare shi kuma suka sake manzannin. Mene ne manzannin suka yi? Da gaba gaɗi, suka ci gaba da “koyarwa da yin bishara, cewa Yesu shi ne Almasihu.”—A. M. 5:17-21, 27-42, Littafi Mai Tsarki; Mis. 21:1, 30.

3, 4. (a) Wace hanya ce Shaiɗan ya daɗe yana amfani da ita wajen hana aikin bayin Allah? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan babin da kuma biyu da ke gaba?

3 Shari’ar da aka yi a shekara ta 33 a zamaninmu ita ce hamayya ta farko da Kiristoci na gaskiya suka fuskanta daga hukuma, amma ba ita ce ta ƙarshe ba. (A. M. 4:5-8; 16:20; 17:6, 7) A yau ma, Shaiɗan yana sa magabtan ibada ta gaskiya su zuga hukuma su hana mu yin wa’azi. Magabta sun yi wa bayin Allah sharrin karya doka a hanyoyi dabam-dabam. Ɗaya daga cikin sharrin shi ne cewa mu masu ta da zaune tsaye ne, wato masu ta da rikici. Na biyu kuma cewa muna sa mutane su yi tawaye da gwamnati. Ƙari ga haka, sun ce mu masu talla ne. ’Yan’uwanmu sun je kotu don su ƙaryata waɗannan sharrin da aka  yi musu kuma suna hakan a lokacin da suka ga ya dace. Waɗanne sakamako ne aka samu? Ta yaya hukuncin da aka yanke a dā ya shafe ka a yau? Bari mu yi la’akari da wasu ƙara da aka kai kotu kuma mu ga yadda suka taimaka a “yin kariyar bishara da tabbatar da ita.”—Filib. 1:7, LMT.

4 A wannan babin, za mu tattauna yadda muka je kotu don mu kāre ’yancinmu na yin wa’azi. A babobi biyu da ke gaba, za mu tattauna yadda muka fafata a kotu don kada mu saka hannu a harkokin duniya kuma mu bi ƙa’idodin Mulkin Allah.

Masu Ta da Rikici ko Kuwa Amintattu Magoya Bayan Mulkin Allah?

5. Me ya sa ’Yan sanda suka kama masu wa’azin Mulki a shekarun 1936-1939, kuma wace shawara ce waɗanda suke ja-gora suka yi?

5 A shekara ta 1937 zuwa 1939, wasu birane da jihohi a ƙasar Amirka sun ƙoƙarta su tilasta wa Shaidun Jehobah su karɓi lasisi kafin su yi wa’azi. Amma ’yan’uwanmu ba su karɓa ba. Me ya sa? Domin za a iya soke lasisi, kuma sun yi imani cewa babu wata gwamnati da take da ikon hana mu bin umurnin da Yesu ya ba Kiristoci cewa su yi wa’azin Mulkin Allah. (Mar. 13:10) Sakamakon haka, aka kama masu bisharar Mulki da yawa. Amma, ’yan’uwan da suke ja-gora a ƙungiyar Jehobah sun yanke shawarar kai ƙara kotu. Maƙasudinsu shi ne su nuna cewa gwamnati ta saka takunkumi da ya saɓa wa doka don ta hana Shaidun Jehobah yin wa’azi. A shekara ta 1938, wani abu ya faru da ya sa aka yi wata shari’a mai muhimmanci a kotu. Shin mene ne ya faru?

6, 7. Mene ne ya faru da iyalin Cantwell?

6 Wani ɗan’uwa mai suna Newton Cantwell ɗan shekara 60 tare da matarsa Esther da kuma ’ya’yansu Henry da Russell da kuma Jesse sun fita wa’azi a ranar Talata, 26 ga Afrilu, 1938, a birnin New Haven da ke jihar Connecticut. Dukan su majagaba na musamman ne kuma sun fita da niyyar yin wa’azi har yamma. Sun san cewa wataƙila ba za su dawo gida ranar ba. Me ya sa? Domin ’Yan sanda sun sha kama su, saboda haka sun san cewa za a iya kama su a ranar. Amma, sanin hakan bai hana su fita wa’azi ba. Sun je birnin New Haven da motoci biyu. Newton ne ya tuƙa babbar motarsu da ke ɗauke da ƙaramin garmaho da kuma littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki. Henry, ɗan shekara 22, ya tuƙa ƙaramar motarsu mai lasifika. Hakika, ba da daɗewa ba sai ’Yan sanda suka tare su kamar yadda suka zata.

7 Da farko, ’Yan sandan sun kama Russell, wanda yake da shekara 18, sa’an nan suka kama iyayen, wato Newton da Esther. Jesse kuma, mai shekara 16, yana kallo daga nesa yayin da ’yan sandan suke tafiya da iyayensa da kuma yayansa. Aka bar Jesse shi kaɗai a wurin, da yake ɗayan yayan nasa, wato Henry, na wa’azi a wani yanki dabam. Duk da hakan, Jesse ya ɗauki garmaho ɗinsa ya ci gaba da yin wa’azi. Sa’ad da yake  wa’azi, sai wasu maza biyu ’yan Katolika suka ce ya saka musu jawabin Ɗan’uwa Rutherford mai jigo “Enemies” (Magabta). Amma, yayin da suke sauraron jawabin, sai suka fusata ƙwarai har suka so su yi wa Jesse dūka. Da ganin haka, sai Jesse ya bar wajen, amma jim kaɗan bayan ya bar wurin, sai ’Yan sanda suka kama shi kuma suka sa shi a bayan kanta. ’Yan sandan sun tuhumi Ɗan’uwa Cantwell da ’ya’yansa da laifi amma ba su tuhumi matarsa ba, kuma an yi belinsu a ranar.

8. Me ya sa kotun ta kama ɗan’uwa Jesse Cantwell da laifin ta da rikici?

8 Bayan ’yan watanni, a watan Satumba 1938, sai aka kai Ɗan’uwa Cantwell da iyalinsa wani kotun da ke New Haven. An kama Newton da Russell da kuma Jesse da laifin karɓan gudummawa ba tare da lasisi ba. Duk da ɗaukaka ƙara da suka yi a Kotun Ƙoli na jihar Connecticut, an kama Jesse da laifin ta da hayaniya. Me ya sa suka yi hakan? Domin maza biyu ’yan Katolika da suka saurari jawabin da Jesse ya saka musu sun shaida a kotu cewa a jawabin an yi sūkar addininsu kuma hakan ya ɓata musu rai sosai. Tun da yake ba a yi adalci a shari’ar ba, wasu ’yan’uwa a cikin ƙungiyarmu suka kai ƙara Kotun Ƙoli na Amirka, wato kotu mafi girma a ƙasar.

9, 10. (a) Wane hukunci ne Kotun Ƙoli na Amirka ya yanke game da ƙarar Iyalin Cantwell? (b) Ta yaya muke amfana a yau daga hukuncin da aka yanke?

9 Daga ranar 29 ga Maris, 1940, wani Babban Alƙali mai suna Charles E. Hughes da wasu alƙalai takwas, suka saurari lauyan Shaidun Jehobah, wato Ɗan’uwa Hayden Covington  sa’ad da yake gaya musu abubuwan da suka faru. * Sa’ad da lauyan jihar Connecticut ya faɗi nasa zancen don ya nuna cewa Shaidun Jehobah masu ta da rikici ne, wani alƙali ya tambaye shi: “Shin ba gaskiya ba ne cewa mutane da yawa ba su amince da wa’azin da Yesu Kristi ya yi a zamaninsa ba?” Sai lauyan jihar Connecticut ya amsa da cewa: “Gaskiya ne, Littafi Mai Tsarki ma ya faɗi abin da ya faru da Yesu sa’ad da ya yi wannan wa’azin.” Babu shakka, wannan kalamin ya tona asirinsu! Ba da saninsa ba, lauyan ya misalta Shaidun Jehobah da Yesu kuma ya misalta jihar da waɗanda suka hukunta Yesu. A ranar 20 ga Mayu, 1940, alƙalan baki ɗaya suka yanke hukunci cewa Shaidun Jehobah ba su da laifi.

Hayden Covington (gaba, tsakiya), Glen How (hagu), da wasu ’yan’uwa suna barin kotu bayan an sami nasara a wata shari’ar da aka yi

10 Me ya sa hukuncin yake da muhimmanci? Hakan ya shafi ’yancin gudanar da hidimomin addini kuma babu dokar gwamnati ko jiha ko ta ƙaramar hukuma da za ta iya hana wannan ’yancin. Ƙari ga haka, kotun ya ce wa’azin da Jesse ya yi “bai yi barazana ga zaman lafiyar jama’a ba.” Saboda haka, hukuncin da aka yanke ya nuna cewa Shaidun Jehobah ba masu ta da rikici ba ne. Hakika, wannan ba ƙaramar nasara ba ce da bayin Allah suka yi! Ta yaya hakan yake amfanarmu har wa yau? Wani lauya Mashaidi ya ce: “’Yancin gudanar da hidimomin addini ya ba Shaidun Jehobah damar yi wa maƙwabtansu wa’azin Mulkin a duk inda suke da zama a yau.”

Masu Tawaye da Gwamnati ko Kuwa Masu Shelar Gaskiya?

Warƙar nan Quebec’s Burning Hate for God and Christ and Freedom Is the Shame of All Canada

11. Wane kamfen ne ’yan’uwanmu da ke Kanada suka yi, kuma me ya sa?

11 Tsakanin shekarun 1940 da 1949 Shaidun Jehobah sun fuskanci hamayya mai tsanani a ƙasar Kanada. Saboda haka, a shekara ta 1946, ’yan’uwanmu sun yi kamfen na kwana 16 suna rarraba wata warƙa mai jigo Quebec’s Burning Hate for God and Christ and Freedom Is the Shame of All Canada don sanar da jama’a game da hana ’yancin gudanar da hidimomin addini da gwamnatin ƙasar ta yi. Wannan warƙa mai shafuffuka huɗu ta bayyana dalla-dalla yadda malaman addini suke rinjayar jama’a su ta da hankali wa ’yan’uwanmu da ke lardin Quebec, kuma su sa ’Yan sanda su wulaƙanta su. An bayyana a cikin warƙar cewa: “’Yan sanda sun ci gaba da kama Shaidun Jehobah ba gaira ba dalili. . . . Yanzu haka, an shigar da ƙararraki 800 a kan Shaidun Jehobah a yankin Greater Montreal.”

12. (a) Wane mataki ne magabta suka ɗauka game da kamfen ɗin warƙar? (b) Wane laifi ne aka tuhumi ’yan’uwanmu da shi? (Ka duba ƙarin bayani.)

12 Shugaban Quebec, Maurice Duplessis tare da Villeneuve, wani Shugaban Cocin Katolika sun sanar cewa za su yaƙi Shaidun Jehobah. A sakamakon hakan, ƙararrakin sun ƙaru daga 800 zuwa 1,600. Wata majagaba ta ce: “’Yan sanda sun kama mu sau da yawa har ma mun mance ko sau nawa suka yi hakan.” An tuhumci duk wani Mashaidin Jehobah da aka kama yana rarraba warƙar da laifin rarraba warƙa da ke sa mutane tawaye da gwamnati. *

13. Su wane ne aka soma tuhumarsu da laifin yi wa gwamnati tawaye, kuma wane hukunci ne kotu ya yanke?

 13 Ɗan’uwa Aimé Boucher da ’ya’yansa mata biyu, wato Gisèle, ’yar shekara 18, da kuma Lucille, ’yar shekara 11 ne aka soma tuhuma a kotu da laifin yin tawaye da gwamnati. Sun rarraba warƙoƙin kusa da gonarsu da ke kan tudu a kudancin Birnin Quebec. Amma halinsu bai nuna cewa su masu ta da rikici ne ba. Ɗan’uwa Boucher mutumi ne mai hankali da yake da ƙaramar gona kuma yakan shiga gari loto-loto da karusarsa. Duk da haka, iyalinsa sun fuskanci wasu daga cikin ire-iren wulaƙancin da aka ambata a cikin warƙar. Alƙalin da ke gudanar da shari’ar ya ƙi jinin Shaidun Jehobah kuma saboda haka, ya ƙi amincewa da shaidar da ta nuna cewa iyalin Boucher ba su da laifi. A maimakon haka, ya amince da zargin da gwamnati ta yi cewa warƙar Shaidun Jehobah ta haifar da tawaye kuma aka sami iyalin Boucher da laifi. Wannan shari’ar da alƙalin ya yanke tana nufin cewa laifi ne a faɗi gaskiya ke nan! An sami Ɗan’uwa Boucher da kuma ’yarsa Gisèle da laifin yin tawaye da gwamnati kuma aka saka su cikin kurkuku, har ma ƙaramar yarinyarsu Lucille, ta yi kwana biyu a cikin kurkuku. ’Yan’uwanmu sun ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli na ƙasar Kanada, wato kotu mafi iko a ƙasar, kuma kotun ya amince ya bincika shari’ar.

14. Wane mataki ne ’yan’uwanmu da ke Quebec suka ɗauka a shekarun da ake tsananta musu?

14 Duk da hamayya da wulaƙancin da ’yan’uwanmu maza da mata da ke lardin Quebec suka fuskanta, sun ci gaba da yin wa’azi game da Mulkin Allah da gaba gaɗi kuma hakan ya haifar da sakamako masu kyau. Shekaru huɗu bayan da aka soma rarraba warƙar a shekara ta 1946, adadin Shaidun Jehobah ya ƙaru daga 300 zuwa 1,000! *

15, 16. (a) Wane hukunci ne Kotun Ƙoli na Kanada ya yanke a ƙarar iyalin Boucher? (b) Mene ne wannan nasarar ta motsa ’yan’uwanmu su yi?

15 A watan Yuni na shekara ta 1950, Kotun Ƙoli na ƙasar Kanada mai alƙalai tara, ya saurari ƙarar Aimé Boucher. Watanni shida bayan haka, wato a ranar 18 ga Disamba, 1950, Kotun ya yanke hukunci kuma mun yi nasara. Me ya sa? Ɗan’uwa Glen How, wanda shi ne lauyan Shaidun Jehobah, ya bayyana cewa Kotun ya amince da bayanin da aka yi cewa yin “tawaye da gwamnati” ya ƙunshi zuga jama’a su yi wa gwamnati rigima. Amma warƙar “ba ta ƙunshe da wani abin da ke sa mutane tawaye da gwamnati, saboda haka hanya ce ta bayyana ra’ayi bisa doka.” Ɗan’uwa How ya ƙara da cewa: “Na shaida da idona yadda Jehobah ya ba mu nasara.” *

16 Hukuncin da Kotun Ƙolin ya yanke gagarumar nasara ce ga Mulkin Allah. Ya ƙaryata sauran ƙararraki guda 122 da aka shigar game da Shaidun Jehobah a lardin Quebec a kan laifin yin tawaye da gwamnati. Ƙari ga haka, hukuncin da aka yanke ya ba wa mazauna ƙasar Kanada da kuma Ƙungiyar Ƙasashen Rainon Ingila ’yancin bayyana ra’ayinsu game da yadda gwamnati take gudanar da al’amura. Ban da hakan, wannan nasarar ta kawo ƙarshen farmakin da coci da kuma gwamnatin Quebec suke kai wa Shaidun Jehobah. *

 ’Yan Talla ko Kuwa Masu Wa’azin Mulkin Allah da Himma?

17. Mene ne wasu hukumomi suka bukace mu mu yi game da wa’azinmu?

17 Kamar Kiristoci na farko, bayin Jehobah a yau ba masu “yi wa maganar Allah algus” ba ne. (Karanta 2 Korintiyawa 2:17.) Duk da haka, wasu hukumomi suna so mu bi dokokin ’yan kasuwa a yadda muke gudanar da wa’azinmu. Bari mu tattauna wasu shari’o’i guda biyu da aka yi da suka amsa wannan tambayar: Shaidun Jehobah ’yan talla ne ko kuwa masu wa’azin Mulkin Allah?

18, 19. Ta yaya hukuma a ƙasar Denmark ta yi ƙoƙarin hana yin wa’azi?

18 Denmark. A ranar 1 ga Oktoba, 1932, an kafa wata doka da ta hana sayar da littattafai ba tare da yin amfani da lasisi ba. Amma, ’yan’uwanmu ba su nemi lasisi daga gwamnati ba. Washegari, masu shela guda biyar suka fita yin wa’azi a Roskilde, wani garin da ke da nisan mil 20 daga yammacin Copenhagen, babban birnin Denmark. A ranar, ’Yan sanda suka kama August Lehmann, wato ɗaya daga cikin masu shelan. Sun tuhume shi da laifin sayar da kayayyaki ba tare da lasisi ba.

19 An kai August Lehmann kotu a ranar 19 ga Disamba, 1932. Ya bayyana cewa ya ziyarci mutane don ya ba su littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki, amma bai amince da cewa yana tallar su ba. Kotun ya yarda da abin da ɗan’uwanmu ya faɗa. A hukuncin da aka yi, an ce: “Wanda aka yi wa zargi . . . yana iya ciyar da kansa kuma bai karɓi kuɗi daga mutane don yin riba ba, ƙari ga haka, bai da niyar yin hakan. A maimakon haka, yana amfani kuɗinsa don gudanar da ayyukansa.” Kotun ya yanke hukunci cewa aikin da Lehmann yake yi ba ya cikin “fannonin kasuwanci” kuma ta hakan, kotun ya goyi bayan Shaidun Jehobah. Amma magabtan bayin Allah sun ƙuduri niyyar hana Shaidun Jehobah gudanar da ayyukansu a ƙasar baki ɗaya. (Isha. 10:1) Lauyan gwamnati ya ɗaukaka ƙarar zuwa Kotun Ƙolin ƙasar. Wane mataki ne ’yan’uwan suka ɗauka?

20. Wane hukunci ne Kotun Ƙoli na ƙasar Denmark ya yanke, kuma mene ne ’yan’uwanmu suka yi?

20 A makon da za a gudanar da shari’ar a Kotun Ƙoli, Shaidun Jehobah sun daɗa ƙwazo a yin wa’azi a ƙasar Denmark baki ɗaya. A ranar 3 ga Oktoba, 1933, kotun ya sanar da hukuncin da ya yanke. Hukuncin ya jitu da wanda kotu na farko ya yanke wa August Lehmann, wato cewa bai ƙarya doka ba. Wannan hukuncin ya ba Shaidun Jehobah ’yancin yin wa’azi. ’Yan’uwa da yawa sun faɗaɗa hidimarsu sosai don su nuna godiyarsu ga Jehobah, wanda ya sa sun yi nasara. Tun da aka yanke wannan hukuncin, ’yan’uwanmu da ke ƙasar Denmark suna wa’azi ba tare da wata barazana daga gwamnati ba.

Shaidun da suka nuna gaba gadi a kasar Denmark tsakanin 1930 da 1939

21, 22. Wane hukunci ne Kotun Ƙoli na Amirka ya yanke a ƙarar Ɗan’uwa Murdock?

21 Amirka. A ranar Lahadi, 25 ga Fabrairu, 1940, an kama wani majagaba mai suna Robert Murdock Junior, da kuma wasu ’yan’uwa guda 7 yayin da suke wa’azi a Jeannette, wani birni da ke kusa da Pittsburgh a jihar Pennsylvania. An kama  su ne don ba su sayi lasisin da zai ba su ’yancin rarraba littattafai ba. Sa’ad da suka ɗaukaka ƙararsu zuwa Kotun Ƙoli na Amirka, sai kotun ya yarda ya saurari ƙararsu.

22 A ranar 3 ga Mayu, 1943, Kotun Ƙoli ya sanar da hukuncin da ya yanke, kuma Shaidun Jehobah ne suka yi nasara. Kotun bai amince da dokar kasancewa da lasisi ba domin hakan yana hana mazauna ƙasar “moran ’yancin da gwamnati ta ba da.” Kotun ya ƙaryata dokar da birnin ya kafa domin dokar ta “tauye ’yancin addini da kuma na faɗan ra’ayi.” Alƙali William O. Douglas, wanda ya faɗi ra’ayin Kotun, ya ce ayyukan Shaidun Jehobah “ya ƙunshi yin wa’azi da kuma rarraba littattafan addini.” Ya daɗa da cewa: “Irin wannan hanyar gudanar da ayyukan addini ɗaya ce da . . . irin hidimar da ake yi a cikin coci da kuma wa’azin da ake yi daga kan dakalin magana.”

23. Me ya sa nasarorin da aka yi a kotuna a shekara ta 1943 suke da muhimmanci a gare mu yau?

23 Wannan hukuncin da Kotun Ƙoli ya yanke wani babban nasara ne ga bayin Allah. Ya nuna cewa mu Kiristoci masu hidima ne, ba masu yawon talla ba. A wannan rana mai muhimmanci a shekara ta 1943, Shaidun Jehobah sun yi nasarar ƙararraki 12 cikin 13 da suka kai Kotun Ƙoli, hakan ya haɗa da hukuncin da aka yanke game da ƙarar Murdock. Waɗannan hukunce-hukunce da aka yanke sun taimaka a shari’o’i da aka  yanke daga baya inda masu hamayya suka ƙalubalanci ’yancinmu na yin wa’azin Mulkin ga jama’a da kuma gida-gida.

“Wajibi Ne Mu Yi wa Allah Biyayya Fiye da Mutum”

24. Wane mataki ne muke ɗaukawa sa’ad da hukuma ta yi ƙoƙarin hana mu yin wa’azi?

24 A matsayin bayin Jehobah, muna godiya sosai sa’ad da hukumomi suka ba mu ’yancin yin wa’azin Mulkin ba tare da tangarɗa ba. Amma, sa’ad da hukuma ta hana mu yin wa’azi, mukan canja tsarin wa’azinmu kuma mu ci gaba da yin wa’azi a duk wata hanyar da hakan zai yiwu. “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum” kamar yadda manzannin suka yi. (A. M. 5:29; Mat. 28:19, 20) Ƙari ga haka, mukan ɗaukaka ƙara zuwa kotu don a ba mu ’yancin yin wa’azi. Ga wasu misalai biyu.

25, 26. Wane abu ne ya faru a ƙasar Nicaragua da ya sa aka kai ƙara Kotun Ƙoli a ƙasar, kuma mene ne sakamakon hakan?

25 Nicaragua. Wani ɗan’uwa mai suna Donovan Munsterman, mai wa’azi a ƙasashen waje wanda shi ne ke kula da reshen ƙasar Nicaragua, ya je ofishin Hukumar Shiga da Fitan Ƙasa a Managua, babban birnin ƙasar a ranar 19 ga Nuwamba, 1952. Shugaban wannan hukumar, Kyaftin Arnoldo García ne ya bukaci ganinsa. Kyaftin ɗin ya gaya wa ɗan’uwa Donovan cewa an ‘hana Shaidun Jehobah da ke Nicaragua wa’azi da kuma gudanar da ayyukan addini.’ Sa’ad da ɗan’uwa Donovan ya tambaye shi dalilin, sai Kyaftin García ya bayyana cewa ministan gwamnati bai ba Shaidun Jehobah izinin gudanar da ayyukansu ba kuma an zarge su da yaɗa ra’ayin kwaminisanci. Su wane ne suka zarge su? Shugabannin addinin Katolika ne.

’Yan’uwa a Nicaragua sa’ad da aka hana wa’azi

26 Nan da nan, sai Ɗan’uwa Munsterman ya ɗaukaka ƙara zuwa Ma’aikatar Harkokin Gwamnati da Addini da kuma Shugaban ƙasar, wato Anastasio Somoza García, amma ba a yi nasara ba. Saboda haka, Shaidun Jehobah suka canja tsarin  wa’azinsu. Sun rufe Majami’ar Mulki sai suka riƙa yin taro a ƙananan rukuni. Ƙari ga haka, sun daina wa’azi a kan titi amma sun ci gaba da yin wa’azin Mulkin Allah. A wannan lokacin, sun aika takardar ƙara zuwa Kotun Ƙoli na ƙasar Nicaragua cewa a soke wannan takunkumi. Jaridu ko-ta-ina a ƙasar sun ɗauki labarin takunkumin da kuma bayanin da ke cikin takardar ƙarar, kuma Kotun Ƙolin ya amince ya saurari ƙarar. Wane sakamako aka samu? A ranar 19 ga Yuni, 1953, Kotun Ƙolin ya yanke hukunci kuma Shaidun Jehobah sun yi nasara. Kotun ya gano cewa takunkumin da aka yi ya saɓa wa dokokin ’yancin faɗin ra’ayi da lamiri da kuma bayyana imani. Ƙari ga haka, Kotun ya ba da oda wa gwamnatin ta yi sulhu da Shaidun Jehobah.

27. Me ya sa mutanen Nicaragua suka yi mamaki a kan hukuncin da Kotun ya yanke, kuma mene ne ’yan’uwanmu suka tabbata game da wannan nasarar?

27 Mazauna ƙasar Nicaragua sun yi mamaki cewa Kotun Ƙoli ya kāre Shaidun Jehobah. Kafin wannan lokacin, Kotun ba ya son wani saɓani ya shiga tsakaninsu da limaman coci don irin tasirin da suke da shi. Ƙari ga haka, a yawancin lokatai Kotun ba ya ƙalubalantar matakan da ma’aikatan gwamnati suke ɗauka domin suna da iko sosai. ’Yan’uwanmu sun tabbata cewa Sarki Yesu ne ya sa suka yi wannan nasarar kuma suka ci gaba da yin wa’azi.—A. M. 1:8.

28, 29. Tsakanin shekara ta 1984 da 1986, yaya abubuwa suka canja wa bayin Jehobah a ƙasar Zaire ba zato ba tsammani?

28 Zaire. Tsakanin shekara ta 1984 da 1986, Shaidun Jehobah wajen 35,000 ne suke ƙasar Zaire, wato Jamhuriyar Kwango. An sami ci gaba sosai a ayyukan Mulki a ƙasar, saboda haka ofishin reshen ya soma yin gine-gine don a kula da ƙarin aikin da wannan ci gaban ya kawo. A watan Disamba 1985, an yi wani taron ƙasashe a babban birnin ƙasar, wato Kinshasa, kuma baƙi guda 32,000 daga wurare dabam-dabam a faɗin duniya ne suka halarci taron a filin wasan birnin. Amma, abubuwa suka soma canja wa bayin Jehobah. Me ya faru?

29 Ɗan’uwa Marcel Filteau wani mai wa’azi a ƙasashen waje da ya fito daga lardin Quebec na ƙasar Kanada, wanda ya shaida tsanantawa da aka yi a zamanin Shugaba Duplessis yana hidima a ƙasar Zaire a lokacin. Ya bayyana abin da ya faru, cewa: “A ranar 12 ga Maris, 1986, an ba wa ’yan’uwa wata wasiƙa da ke cewa gwamnati ba ta san da zaman Shaidun Jehobah a ƙasar ba.” Shugaban ƙasar, wato Mobutu Sese Seko ne ya sa hannu a wasiƙar.

30. Wane babban mataki ne Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Reshe yake bukata ya ɗauka, amma wace shawara ce mambobin kwamitin suka yanke?

30 Washegari sai aka yi sanarwa a rediyo cewa: “Ba za mu ƙara ganin Shaidun Jehobah a [Zaire] ba.” Nan da nan aka soma tsananta wa Shaidun Jehobah. An ƙona Majami’un Mulki, aka saci kayayyakin ’yan’uwa kuma ’Yan sanda suka kama su suka jefa su cikin kurkuku kuma suka yi musu dūka. Har ma aka jefa ’ya’yan Shaidun Jehobah a cikin kurkuku. A ranar 12 ga Oktoba 1988, sai gwamnati ta ƙwace mallakar ƙungiyar Jehobah kuma ta saka ’Yan tsaro da ake kira Civil Guard a ofishin reshenmu. ’Yan’uwa da ke ja-gora sun kai ƙara wa  Shugaban Ƙasa, Mobutu, amma ba su sami amsa daga wajensa ba. A wannan lokacin, Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Reshe ya ga ya dace ya ɗauki babban mataki. Suna tunani ko su ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli ne ko kuwa su jira. Ɗan’uwa Timothy Holmes mai wa’azi a ƙasashen waje, wanda shi ne mai tsara ayyukan Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Reshe a lokacin ya tuna abin da ya faru, kuma ya ce: “Mun dogara ga Jehobah ya ba mu hikima kuma ya yi mana ja-gora.” Bayan yawan tattaunawa da addu’a, kwamitin ya kammala cewa lokacin yin shari’a bai yi ba. A maimakon haka, sun nemi wasu hanyoyin yin wa’azi kuma suka ci gaba da yin haka.

“A lokacin da ake shari’ar, mun shaida yadda Jehobah yake canja abubuwa”

31, 32. Wane hukunci mai muhimmanci ne Kotun Ƙoli na Zaire suka yanke, kuma yaya hukuncin ya shafe ’yan’uwanmu?

31 Bayan shekaru da dama, an sauƙaƙa tsanantawar da ake yi wa Shaidun Jehobah, kuma aka soma daraja hakkin ɗan Adam a ƙasar. A wannan lokacin ne Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Reshe ya ga cewa ya dace ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli na ƙasar Zaire. Kotun ya yarda ya saurari ƙarar. A ranar 8 ga Janairu 1993, kusan shekaru bakwai da shugaban ƙasar ya hana aikinmu, kotun ya yanke hukunci cewa hana aikin Shaidun Jehobah da gwamnati ta yi ya saɓa wa doka, kuma aka soke wannan takunkumin. Ka yi tunanin abin da hakan ke nufi! Ba ƙaramin kasada ba ne waɗannan alƙalan suka yi sa’ad da suka yanke hukuncin soke dokar da shugaban ƙasa ya kafa! Ɗan’uwa Holmes ya ce, “A lokacin da ake shari’ar, mun shaida yadda Jehobah yake canja abubuwa.” (Dan. 2:21) Wannan nasarar da aka yi ta ƙarfafa bangaskiyar ’yan’uwanmu. Sun ga cewa Sarki Yesu ne ya yi wa mutanensa ja-gora game da lokaci da kuma yadda ya kamata su ɗauki mataki.

Shaidun Jehobah a Jamhuriyar Kwango sun yi murna sa’ad da suka sami ’yancin bauta wa Jehobah

 32 Sa’ad da aka cire takunkumin, an yarda ofishin reshe ya gayyato masu wa’azi a ƙasashen waje, ya yi sababbin gine-gine a ofishin reshe, kuma ya shigo da littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki daga ƙasar waje. * Abin farin ciki ne wa bayin Allah a faɗin duniya sa’ad da suka ga yadda Jehobah yake kāre ibadar mutanensa.—Isha. 52:10.

“Ubangiji Mai-Taimakona Ne”

33. Mene ne muka koya daga waɗannan hukunce-hukunce da aka yanke?

33 Babu shakka, yadda muka tattauna wasu hukunce-hukunce da aka yanke ya nuna cewa Yesu ya cika alkawarin da ya yi cewa: “Zan ba ku baki da hikima wadda dukan maƙiyanku ba za su sami iko su yi tsayayya ba ko kuwa su yi musunta.” (Karanta Luka 21:12-15.) A wasu lokatai, Jehobah ya yi amfani da mutane kamar Gamaliel don ya kāre bayinsa, kuma ya motsa alƙalai da kuma lauyoyi masu gaba gaɗi su yi adalci. Jehobah ya sa makaman ’yan hamayya su ƙi ci. (Karanta Ishaya 54:17.) Hamayya ba za ta iya dakatar da aikin Allah ba.

34. Me ya sa nasarorin da muka yi a kotu suke da muhimmanci, kuma wane tabbaci ne suka ba da? (Ka kuma duba akwatin nan “ Muhimman Nasarori da Muka Yi a Manyan Kotuna da Suka Bunƙasa Wa’azin Mulki.”)

34 Me ya sa nasarorin da muka yi a shari’a suke da muhimmanci? Ka yi la’akari da wannan: Shaidun Jehobah ba sanannu ba ne kuma ba masu-faɗa-a-ji ba ne. Ba ma jefa ƙuri’a, ba ma goyon bayan kamfen ɗin siyasa ko kuma ’yan siyasa da kansu. Ƙari ga haka, ana ɗaukan mu da muka sami kanmu a gaban alƙalai a matsayin “mutane marasa karatu” da kuma “talakawa.” (A. M. 4:13) Saboda haka, ’yan Adam ba su da ikon da za su iya yanke hukuncin da zai kayar da magabtanmu, wato shugabannin addini masu iko sosai kuma su ba mu nasara. Duk da haka, kotuna sun ba mu nasara ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba! Waɗannan nasarorin sun tabbatar da cewa muna tafiya “a gaban Allah” tare da “Kristi.” (2 Kor. 2:17) Saboda haka, za mu iya furta abin da manzo Bulus ya faɗa cewa: “Ubangiji mai-taimakona ne; ba zan ji tsoro ba.”—Ibran. 13:6.

^ sakin layi na 9 Shari’ar da aka yi tsakanin Cantwell da Jihar Connecticut ita ce ta farko cikin ƙara 43 da ke Kotun Ƙoli na Amirka da Ɗan’uwa Hayden Covington ya tsaya kai a madadin ’yan’uwanmu. Ya rasu a shekara ta 1978. Matarsa mai suna Dorothy mai shekara 90 tana hidima a matsayin majagaba har ila.

^ sakin layi na 12 Wannan zargin yana bisa wata doka da aka kafa a shekara ta 1606. Dokar ta ba wa alƙalai dama su kama mutum da laifi idan suna ganin abin da mutumin ya faɗa zai iya jawo tashin hankali, ko da abin da aka faɗa gaskiya ne.

^ sakin layi na 14 A shekara ta 1950, masu hidima ta cikakken lokaci guda 164 ne a lardin Quebec, haɗe da waɗanda suka sauke karatu a makarantar Gilead guda 63 da suka amince su yi wa’azi a wurin duk da hamayya da za su fuskanta.

^ sakin layi na 15 Ɗan’uwa W. Glen How lauya ne mai gaba gaɗi kuma ya kāre Shaidun Jehobah a ɗarurruwan shari’o’i da suka yi daga 1943 zuwa 2003, a Kanada da kuma da wasu ƙasashe.

^ sakin layi na 16 Don ƙarin bayani game da wannan shari’ar, ka duba talifin nan “The Battle Is Not Yours, but God’s” a Awake! ɗin 22 ga Afrilu, 2000, shafuffuka na 18-24.

^ sakin layi na 32 ’Yan tsaron sun bar ofishin reshen; amma an gina sabon ofishin reshe a wani wuri.