MANUFAR WANNAN BABIN

Jehobah yana ci gaba da sa mutanensa su kasance da tsari

1, 2. Wane canji aka yi wa Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona a watan Janairu 1895, kuma yaya ’yan’uwa suka ji?

SA’AD DA wani ɗalibin Littafi Mai Tsarki mai kuzari mai suna John A. Bohnet ya karɓi mujallar Zion’s Watch Tower (Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona) ta watan Janairu 1895, abin da ya gani ya burge shi sosai. Mujallar tana da sabon bango da ke ɗauke da zanen hasumiya mai wuta a bakin teku mai hauka kuma wutarta tana haskaka ko’ina. Jigon sanarwar da aka yi a cikin mujallar game da sabon fasalin shi ne, “Sabon Bangonmu.”

2 Da yake abin ya burge shi, Ɗan’uwa Bohnet ya aika wa Ɗan’uwa Russell wasiƙa. Ya ce: “Na yi murnar ganin yadda aka yi wa mujallar HASUMIYAR TSARO sabon bango mai kyau.” Wani Ɗalibin Littafi Mai Tsarki mai aminci, mai suna John H. Brown, ya rubuta game da bangon: “Sabon fasalin nan yana da ban sha’awa. Hasumiyar tana tsaye a kan harsashi mai ƙwari sosai, duk da cewa ruwa da iska suna bubbuga ta.” Wannan sabon bangon shi ne canji na farko da ’yan’uwanmu suka gani a shekarar, amma hakan soma-taɓi ne. A watan Nuwamba na shekarar, sun sake samun labarin wani gagarumin canji. Wani abin ban sha’awa shi ne, canjin ya shafi wata matsala da ke kama da teku mai hauka.

3, 4. Wace matsala ce aka tattauna a Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ta 15 ga Nuwamba, 1895, kuma wane babban canji ne aka sanar?

3 Wani talifi mai tsawo da aka wallafa a Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ta 15 ga Nuwamba, 1895, ta bayyana matsalar: Matsaloli da ke kama da teku mai hauka suna yi wa zaman lafiya da ke tsakanin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki barazana. Gardama tana ƙara yin zafi a tsakanin ’yan’uwa game da wanda zai kasance shugaba a ikilisiya. Don a taimaka wa ’yan’uwan su ga abin da ya kamata su yi don su magance wannan matsalar, talifin ya kwatanta ƙungiyar da jirgin ruwa. Talifin ya kuma bayyana cewa waɗanda suke ja-gora sun kasa kafa ƙungiya mai kama da jirgin ruwan da zai iya jimre guguwa da ruwa. Me ya kamata a yi?

4 Talifin ya bayyana cewa ƙwararren matuƙin jirgin ruwa yana tabbatar da cewa akwai abubuwan ceton rai a cikin jirgin kuma abokan aikinsa suna shirye su sa jirgin ya ci gaba  da tafiya idan aka fara ruwa da iska. Hakazalika, waɗanda suke ja-gora a ƙungiyar Jehobah suna bukatar su tabbatar da cewa dukan ikilisiyoyi suna shirye su magance duk wata matsala da za ta taso mai kama da ruwa da kuma iska. Don a cim ma hakan, talifin ya sanar da wani babban canji. Ya ba da umurni cewa nan take, “a zaɓi dattawa a kowace ikilisiya” don “‘su riƙa kula’ da garken.”—A. M. 20:28.

5. (a) Me ya sa tsari na farko da aka kafa na naɗa dattawa ya dace? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

5 Wannan shiri na naɗa dattawa mataki ne mai kyau na kafa ikilisiyoyin da za su ɗore. Shirin ya taimaka wa ’yan’uwanmu su jimre matsalolin da Yaƙin Duniya na Ɗaya ya jawo. A shekaru da yawa bayan haka, ci gaban da aka samu a ƙungiyar ya taimaka wa mutanen Allah su bauta wa Jehobah sosai. A wane nassi ne aka annabta wannan ci gaban? Waɗanne canji ne ka shaida a ƙungiyar Jehobah? Ta yaya ka amfana daga waɗannan canjin kuwa?

“Zan Sa Salama ta Zama Mulkinki”

6, 7. (a) Mene ne annabcin da ke Ishaya 60:17 yake nufi? (b) Masu ‘mulki’ da ‘mahukunta’ da aka ambata suna nuni ga mene ne?

6 Kamar yadda muka tattauna a Babi na 9, Ishaya ya annabta cewa Jehobah zai sa mutanensa su sami ƙaruwa. (Isha. 60:22) Amma, Jehobah ya yi alkawarin yin fiye da hakan. A annabcin, ya ce: “Maimakon jangaci zan kawo zinariya, maimakon baƙin ƙarfe kuma zan kawo azurfa, maimakon itace kuma jangaci, maimakon duwatsu kuma baƙin ƙarfe: zan sa salama ta zama mulkinki, adalci kuma ya zama mahukuncinki.” (Isha. 60:17) Mece ce ma’anar annabcin nan? Ta yaya ya shafe mu a yau?

Sauyin bai canja abubuwa marasa kyau da masu kyau ba, amma ya canja masu kyau ne da mafi kyau

7 Annabcin Ishaya ya ce za a yi wasu sauya za a sauya wasu abubuwa. Amma idan ka duba, za ka ga cewa sauyin bai canja abubuwa marasa kyau da masu kyau ba, amma ya canja masu kyau ne da mafi kyau. Sauya jangaci da zinariya ci gaba ne sosai, haka ma da sauran abubuwan da aka ambata a ayar. Da wannan bayanin, Jehobah ya annabta cewa zai inganta yanayin mutanensa da sannu-sannu. Amma wane irin ci gaba ne wannan annabcin yake nufi? Ta wajen ambata masu ‘mulki’ da ‘mahukunta,’ Jehobah ya nuna cewa za a samu ci gaba a hankali a yadda ake kula da kuma tsara mutanensa.

8. (a) Wane ne ya sa aka sami ci gaban da aka ambata a annabcin Ishaya? (b) Ta yaya muka amfana daga canjin da aka yi? (Ka kuma duba akwatin nan “ Ya Amince da Gyara Cikin Tawali’u.”)

8 Wane ne ya kawo ci gaba ga ƙungiyar? Jehobah ya ce: ‘Zan kawo zinariya, . . . Zan kawo azurfa, . . . zan sa salama.’ Hakika, Jehobah ne da kansa ya sa aka sami ci gaba a yadda aka tsara ikilisiya, ba ƙoƙarin mutum ba. Kuma tun da aka naɗa Yesu Sarki, Jehobah ya yi amfani da Ɗansa don a sami waɗannan ci gaban. Ta yaya muka amfana daga waɗannan canjin? Wannan nassin ya ce ci gaban zai kawo “salama” da “adalci.” Yayin da muka bi ja-gorar Allah kuma muka yi gyara, salama za ta kasance a tsakaninmu. Ƙari ga haka, za mu daɗa son yin adalci, kuma hakan zai motsa mu mu bauta wa  Jehobah, wanda manzo Bulus ya kira ‘Allah na salama.’—Filib. 4:9.

9. Mene ne tushen tsari da haɗin kai da ake da shi a cikin ikilisiya, kuma me ya sa?

9 Bulus ya rubuta game da Jehobah cewa: ‘Allah ba Allah na yamutsai ba ne, amma na kwanciyar rai ne.’ (1 Kor. 14:33) Ka lura cewa Bulus bai ce akasin yamutsi shi ne tsari ba, amma ya ce akasin yamutsi shi ne salama. Me ya sa? Yi la’akari da wannan: Kasancewa da tsari kawai ba ya nufin cewa za a sami salama. Alal misali, rukunin sojoji suna iya yin maci da tsari idan za su bakin dāga, amma maci da tsari da suke yi don zuwa yaƙi ne, ba don kawo salama ba. Shi ya sa a matsayinmu na Kiristoci, ya kamata mu riƙe wannan a zuciya: Duk wani tsarin da tushensa ba salama ba ne zai rushe ko bajima ko ba daɗe. Akasin haka, salama daga Allah tana kawo tsarin da zai kasance har abada. Saboda haka, muna matuƙar godiya cewa “Allah na salama” ne yake wa ƙungiyar nan ja-gora kuma shi yake kawo ci gaba! (Rom. 15:33) Salama daga wurin Allah ita ce tushen tsari mai kyau da kuma haɗin kai da muke da muke da shi a ikilisiyoyinmu a faɗin duniya.—Zab. 29:11.

10. (a) Waɗanne ci gaba ne aka samu a ƙungiyarmu a shekarun baya? (Ka duba akwatin nan “ Yadda Aka Kyautata Tsarin Ja-Goranci.”) (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

10 Akwatin nan “ Yadda Aka Kyautata Tsarin Ja-goranci” ya nuna tsari da kuma canji masu kyau da aka samu a ƙungiyar nan a shekarun baya. Amma waɗanne canji makamantan ‘jangaci zuwa zinariya’ ne Jehobah ya yi ta wurin Sarkinmu a kwanan nan? Ta yaya gyarar da aka yi a yadda ake ja-gora ta ƙarfafa salama da haɗin kan ikilisiyoyi a faɗin duniya? Ta yaya suke taimaka maka ka bauta wa “Allah na salama”?

Yadda Yesu Yake Ja-gorantar Ikilisiya

11. (a) Wace gyara ce aka yi bayan nazarin Nassosi? (b) Sauran shafaffun sun ƙuduri yin me?

11 Daga shekara ta 1964 zuwa 1971, hukumar da ke kula da ayyukan Shaidun Jehobah ta kafa tsarin binciken Littafi Mai Tsarki da ya shafi batutuwa da yawa, har da tsarin ikilisiyar Kirista ta ƙarni na farko. * Nazarin ya nuna cewa a ƙarni na farko, rukunin dattawa ne ke kula da ikilisiyoyi maimakon dattijo guda. (Karanta Filibiyawa 1:1; 1 Timotawus 4:14.) Sa’ad da suka fahimci hakan, hukumar da ke kula da ayyukan Shaidun Jehobah ta fahimci cewa Sarki Yesu ne yake yin gyara a tsarin ƙungiyar mutanen Allah don ta sami ci gaba. Sauran shafaffu kuma sun ƙuduri niyyar bin ja-gorancin Sarkin kuma sun yi gyara nan da nan domin su bi ja-gorar da ke cikin Nassosi game da naɗin dattawa. Waɗanne canji ne aka yi a daga shekara ta 1970 zuwa 1973?

12. (a) Wane canji ne aka yi wa hukumar da ke kula da ayyukan Shaidun Jehobah? (b) Ka kwatanta yadda aka tsara Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah a yau. (Ka duba akwatin nan “ Yadda Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah Take Kula da Al’amuran Mulki,” a shafi na 130.)

12 Canji na farko da aka yi ya shafi hukumar da ke kula da ayyukan Shaidun Jehobah ne da kanta. Kafin wannan lokacin, wannan rukuni na ’yan’uwa shafaffu ya ƙunshi mutane bakwai ne da suka haɗu suka zama darektocin Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. Amma a shekara ta  1971, adadin hukumar ta ƙaru daga 7 zuwa 11 kuma ta ba da aikin darektocin ga wasu. Mambobin hukumar ba su ɗauki wani da muhimmanci fiye da wani a tsakaninsu ba, kuma suka fara yin karɓa-karɓa da matsayin mai kujera bisa ga harufan sunayensu a kowace shekara.

13. (a) Wane tsari ne aka yi shekaru 40 ana bi? (b) Mene ne Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta yi a 1972?

13 Canji na biyu ya shafi kowace ikilisiya. Ta yaya? Daga shekara ta 1932 zuwa 1972, mutum ɗaya ne kawai yake kula da ikilisiya. Har shekara ta 1936, ana kiran wannan ɗan’uwan da aka naɗa darektan hidima. Daga baya, an canja sunan zuwa bawan ikilisiya, kuma a ƙarshe aka soma kiransa mai kula da ikilisiya. Waɗannan ’yan’uwan da aka naɗa sun taimaka wa garken su ƙarfafa dangantakarsu da Allah. Mai kula da ikilisiya yakan yanke shawara a madadin ikilisiya ba tare da tuntuɓar sauran masu hidima a cikin ikilisiya ba. Amma, a shekara ta 1972, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta kawo wani babban canji. Wane canji ke nan?

14. (a) Wane sabon tsari ne aka fara bi a ranar 1 ga Oktoba, 1972? (b) Ta yaya ne mai tsara ayyukan rukunin dattawa yake amfani da shawarar da ke Filibiyawa 2:3?

14 Maimakon ɗan’uwa guda ya riƙa kula da ikilisiya, za a naɗa ’yan’uwa da suka cancanta bisa ga umurnin Littafi Mai Tsarki a matsayin dattawa. Za su zama rukunin dattawa da zai riƙa kula da ikilisiyarsu. An soma bin wannan sabon tsarin naɗa dattawa a ranar 1 ga Oktoba, 1972. A yau, mai tsara  ayyukan rukunin dattawa ba ya ɗaukan kansa da muhimmanci fiye da sauran dattawan, amma yana ɗaukan kansa kamar ‘ƙanƙanin cikinsu duka.’ (Luk 9:48) Waɗannan ’yan’uwa masu sauƙin kai albarka ne ga dukan ’yan’uwa a faɗin duniya!—Filib. 2:3.

  Babu shakka, da yake Sarkinmu yana da hikima, ya yi wa mabiyansa tanadin makiyaya masu taimako a kan kari

15. (a) Wane amfani ne aka samu daga tsarin rukunin dattawa da aka kafa? (b) Mene ne ya nuna cewa Sarkinmu yana da hikima?

15 Tsarin da aka kafa na raba ayyukan ikilisiya a tsakanin mambobin rukunin dattawa ci gaba ne sosai. Ka yi la’akari da hanyoyi uku da aka amfana daga wannan tsarin: Hanya ta farko ita ce, tsarin ya taimaka wa dukan dattawa su tuna cewa Yesu ne Shugaban ikilisiya kome yawan ayyukan da suke da shi a ikilisiya. (Afis. 5:23) Ta biyu, kamar yadda Misalai 11:14 ta ce: “Cikin taron masu-shawara akwai lafiya.” Yayin da dattawa suka zauna tare suka tattauna batutuwan da suka shafi ikilisiya kuma suka saurari shawarwarin juna, hakan yana taimaka musu su yanke shawarwarin da suka jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (Mis. 27:17) Jehobah yana sa waɗannan shawarwarin su kasance da albarka. Ta uku, da yake ana samun ƙarin ’yan’uwa da suka cancanta, ƙungiyar tana ci gaba da tanadar da dattawa don kula da ’yan’uwa a cikin ikilisiya da yake ana samun ƙaruwa a kai a kai. (Isha. 60:3-5) Ka yi la’akari da wannan, an sami ƙarin ikilisiyoyi a faɗin duniya daga sama da 27,000 a shekara ta 1971 zuwa sama da  113,000 a shekara ta 2013! Babu shakka, da yake Sarkinmu yana da hikima, ya yi wa mabiyansa tanadin makiyaya masu taimako a kan kari.—Mi. 5:5.

“Ku Zama Abin Koyi ga Garken”

16. (a) Wane hakki ne dattawa suke da shi? (b) Yaya Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka ɗauki umurnin da Yesu ya bayar na ‘zama makiyayin tumakinsa’?

16 Tun zamanin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki, dattawa sun riga sun fahimci cewa suna da hakkin taimaka wa ’yan’uwa su ci gaba da bauta wa Allah. (Karanta Galatiyawa 6:10.) A shekara ta 1908, wani talifin Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ya tattauna umurnin Yesu da ya ce: “Ka zama makiyayin tumakina.” (Yoh. 21:15-17) An gaya wa dattawa a cikin talifin cewa: “Ya kamata mu ɗauki umurnin da Ubangiji ya bayar game da garkensa da muhimmanci sosai, kuma mu ɗauki aikin ciyar da kuma kula da mabiyan Ubangiji a matsayin gata mai girma.” A shekara ta 1925, Hasumiyar Tsaro ta sake nanata muhimmancin hidimar makiyaya sa’ad da ta tunasar da dattawa cewa: “Allah ne yake da cocinsa, . . . kuma kowa zai ba da lissafin yadda yake amfani da gatan da aka ba shi na yi wa ’yan’uwa hidima.”

17. Ta yaya ne aka taimaka wa masu kula su zama ƙwararrun makiyaya?

17 Ta yaya ne ƙungiyar Jehobah ta taimaka wa dattawa su yi canji da ke kama da ‘baƙin ƙarfe zuwa azurfa’ a yadda suke gudanar da ziyarar ƙarfafawa? Ta hanyar horarwa. A shekara ta 1959, an gudanar da Makarantar Hidima ta Mulki ta farko domin dattawa. Wani sashe na makarantar ya tattauna batun nan, “Mai da Hankali ga Bukatun ’Yan’uwa.” An ƙarfafa dattawan su “kasance da tsari na ziyartar masu shela a gidajensu.” Wannan sashen ya nuna hanyoyi dabam-dabam da makiyayan za su iya sa ziyarar ta ƙarfafa ’yan’uwa. A shekara ta 1966, an soma wata sabuwar Makarantar Hidima ta Mulki.  An tattauna batun nan, “Muhimmancin Ziyarar Ƙarfafawa,” a makarantar. Mene ne ainihin abin da aka tattauna a wannan sashen? An tattauna cewa waɗanda suke yin ja-gora “su kula da garken Allah sosai ba tare da yin watsi da tasu iyalin da kuma wa’azi ba.” A ’yan shekarun da suka wuce, an gudanar da makarantun dattawa da dama. Mene ne sakamakon wannan horarwa da ƙungiyar Jehobah take ci gaba da tanadarwa? A yau, ikilisiyar Kirista tana da dubban ƙwararrun ’yan’uwa maza da suke hidima a matsayin dattawa.

Makarantar Hidima ta Mulki a kasar Filifin a 1966

18. (a) Wane hakki mai nauyi ne aka danƙa wa dattawa? (b) Me ya sa Jehobah da Yesu suke ƙaunar dattawa?

18 Jehobah ne ya yi amfani da Sarkinmu Yesu wajen naɗa dattawa Kiristoci don su ɗauki hakki mai nauyi. Mene ne wannan hakkin? Hakkin shi ne yi wa tumakin Allah ja-gora a wannan lokaci mafi wuya a tarihin ’yan Adam. (Afis. 4:11, 12; 2 Tim. 3:1) Jehobah da Yesu suna ƙaunar dattawa sosai don yadda suke aiki tuƙuru da kuma yin biyayya ga wannan umurnin Littafi Mai Tsarki: “Ku yi kiwon garken Allah wanda ke wurinku, . . . da yardan rai . . . , da karsashin zuciya . . .  kuna nuna kanku gurbi ne ga garken.” (1 Bit. 5:2, 3) Za mu tattauna hanyoyi biyu daga cikin hanyoyi da dama da Kiristoci makiyaya suka zama abin koyi ga garke da kuma yadda suka ƙara sa salama da farin ciki ta kasance a cikin ikilisiya.

Yadda Dattawa Suke Kula da Garken Allah a Yau

19. Yaya muke ɗaukan dattawan da muke zuwa wa’azi tare?

19 Na ɗaya, dattawa suna fita wa’azi tare da waɗanda suke cikin ikilisiya. Ga abin da Luka marubucin Linjila ya ce game da Yesu: ‘Ya zagaye birni da ƙauye yana wa’azi, yana yin bisharar Mulkin Allah. Sha biyun nan kuwa suna tare da shi.’ (Luk 8:1, Littafi Mai Tsarki) Kamar yadda Yesu ya fita wa’azi tare da manzanninsa, hakazalika a yau dattawa masu kafa misali mai  kyau suna aiki tare da ’yan’uwansu masu bi in sun fita wa’azi. Sun fahimci cewa ta wajen yin hakan, suna inganta hali mai kyau da ikilisiyar take da shi. Yaya waɗanda suke cikin ikilisiya suke ɗaukan irin waɗannan dattawan? Jeannine, wata ’yar’uwa ’yar wajen shekara 90 ta ce: “Fita wa’azi tare da dattijo yana ba ni damar tattaunawa da shi da kuma ƙara saninsa.” Wani ɗan’uwa ɗan wajen shekara 35 mai suna Steven, ya ce: “Idan na fita wa’azi tare da dattijo, na san cewa zai taimaka mini sosai, kuma irin wannan taimakon yana faranta mini rai.”

Kamar yadda makiyayi yake neman tunkiyar da ta ɓace, su ma dattawa suna yin iya ƙoƙarinsu su nemi waɗanda suka bar ikilisiya

20, 21. Ta yaya dattawa za su iya yin koyi da makiyayin da ke cikin almarar da Yesu ya bayar? Ka ba da misali. (Ka duba kuma akwatin nan “ Ziyarar Mako-mako Mai Amfani Sosai.”)

20 Na biyu, ƙungiyar Jehobah ta koyar da dattawa su riƙa nuna cewa sun damu da waɗanda suka bar ikilisiya. (Ibran. 12:12) Me ya sa ya kamata dattawa su taimaka wa waɗanda dangantakarsu da Jehobah ta yi sanyi, kuma ta yaya za su yi hakan? Amsar tana cikin almarar da Yesu ya bayar na makiyayi da tunkiyar da ta ɓace. (Karanta Luka 15:4-7.) Sa’ad da makiyayin da aka ambata a cikin almarar ya lura cewa tunkiyarsa ta ɓace, ya nemi tunkiyar kamar ita ce kaɗai tunkiyarsa. Ta yaya dattawa a yau suke yin koyi da wannan makiyayin? Kamar yadda tunkiyar da ta ɓace take da tamani a idanun makiyayin, haka su ma waɗanda suka bar ikilisiya suke da tamani a gaban dattawa. Suna ɗaukan mutumin da dangantakarsa da Jehobah ta yi sanyi kamar tunkiyar da ta ɓace, ba kamar mutumin da ya yi nisan da ba zai ji kira ba. Bugu da ƙari, kamar yadda makiyayin ya “je neman abin da ya ɓace har ya samu,” dattawa ma suna neman waɗanda dangantakarsu da Jehobah ta yi sanyi kuma suna taimaka musu.

21 Mene ne makiyayin da ke cikin almarar ya yi sa’ad da ya ga tunkiyar da ta ɓace? Ya ɗauke ta a hankali, ya saɓe ta a “kafaɗunsa,” kuma ya mayar da ita cikin garken. Hakazalika, idan dattijo ya nuna cewa ya damu da mutumin da dangantakarsa da Jehobah ta yi sanyi, hakan zai iya ƙarfafa shi kuma ya mai da shi cikin ikilisiya. Abin da ya faru da Victor ke nan, wani ɗan’uwa a Afirka wanda ya daina tarayya da ikilisiya. Ya ce: “A shekaru takwas da na yi ba na zuwa taro da kuma wa’azi, dattawa sun ci gaba da nema na don su taimaka mini.” Mene ne ya fi ratsa zuciyarsa? Ya ce: “Wata rana, wani dattijo mai suna John, wanda muka halarci Makarantar Hidima ta Majagaba tare ya ziyarce ni kuma ya nuna mini wasu hotunan da muka ɗauka a makarantar. Hotunan sun tuna mini abubuwa da dama masu ban sha’awa har na soma ɗokin sake farin ciki kamar yadda nake yi a dā, sa’ad da nake bauta wa Jehobah.” Ba da daɗewa ba bayan ziyarar John, Victor ya koma yin tarayya da ikilisiya. A yau, yana hidimar majagaba kamar dā. Hakika, dattawa Kiristoci da ke nuna sun damu da ’yan’uwansu suna sa mu farin ciki sosai.—2 Kor. 1:24. *

 Ja-goranci Mai Kyau Ya Inganta Haɗin Kan Mutanen Allah

22. Ta yaya adalci da salama suke kawo haɗin kai a cikin ƙungiyar Jehobah? (Ka kuma duba akwatin nan “ Mun Yi Mamaki.”)

22 Kamar yadda aka faɗa a baya, Jehobah ya annabta cewa adalci da salama za su ci gaba da ƙaruwa a tsakanin mutanen Allah. (Isha. 60:17) Waɗannan halayen sun sa ’yan’uwa a ikilisiyoyi sun kasance da haɗin kai sosai. Ta yaya? A batun adalci, ‘Ubangiji Allahnmu Ubangiji ɗaya ne.’ (K. Sha 6:4) Babu bambanci a mizaninsa na adalci a ikilisiyoyin wannan ƙasar da kuma ikilisiyoyin da ke wata ƙasa. Mizanansa na abin da ya dace da wanda bai dace ba ɗaya ne, kuma haka suke a “cikin dukan ikilisiyai na tsarkaka.” (1 Kor. 14:33) Saboda haka, ikilisiya za ta samu ci gaba ne kawai idan aka bi mizanan Allah. A batun salama, Sarkinmu yana so mu more salama a cikin ikilisiya kuma mu zama “masu-sada zumunta.” (Mat. 5:9) Shi ya sa muke himma wajen “yin abubuwan da ke kawo salama.” Muna ɗaukan mataki don mu magance matsalolin da za su iya tasowa a tsakaninmu. (Rom. 14:19, LMT) Ta haka, muna sa ikilisiyarmu ta kasance da salama da kuma haɗin kai.—Isha. 60:18.

23. A matsayinmu na Shaidun Jehobah, mene ne muke morewa a yau?

23 A watan Nuwamba ta 1895, sa’ad da Hasumiyar Tsaro ta sanar da tsari na farko da aka kafa na naɗa dattawa, ’yan’uwan da ke ja-gora sun furta muradinsu. Mene ne muraɗin? Sun yi fata da addu’a cewa wannan sabon shirin da ƙungiyar ta yi zai taimaka wa mutanen Allah su ‘haɗa kai nan da nan a bangaskiya.’ Muna godiya sosai saboda yadda Jehobah ya yi amfani da Sarkinmu wajen kyautata yadda ake ja-goranci a shekarun nan da dama, kuma hakan ya sa mun kasance da haɗin kai sosai a ibadarmu. (Zab. 99:4) A sakamakon haka, dukan mutanen Jehobah a yau suna murna domin suna bin “ruhu ɗaya,” da “sawu ɗaya,” kuma suna bauta wa ‘Allah na salama’ “da zuciya ɗaya.”—2 Kor. 12:18; karanta Zafaniya 3:9.

^ sakin layi na 11 An wallafa sakamakon wannan bincike mai zurfi a cikin wani littafin bincike mai suna Aid to Bible Understanding.

^ sakin layi na 21 Ka duba talifin nan “Dattawa Kirista Suna Aiki Don Mu Yi ‘Farin Ciki,’” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Janairu, 2013, shafuffuka na 27-31.