Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 BABI NA 5

Sarkin Yana Bayyana Mana Mulkin Dalla-dalla

Sarkin Yana Bayyana Mana Mulkin Dalla-dalla

MANUFAR WANNAN BABIN

Bayin Allah sun koyi gaskiya game da Mulkin, wato gaskiya game da waɗanda za su yi mulki, da talakawan, da kuma yadda za su kasance da aminci ga Mulkin

1, 2. Ta yaya Yesu ya zama mai ja-gora mai hikima?

A CE kun isa wani birnin da ba ku taɓa zuwa ba, sai wani mutumin da ya san garin sosai ya ce zai kai ku yawon buɗe ido don ku ga wannan birni mai kyan gaske. Kai da waɗanda kuke tare kun amince da duk abin da mutumin ya ce domin ba ku taɓa zuwa birnin ba. A wasu lokatai, kai da abokan tafiyarka kukan yi mamaki ko yaya wasu fasalolin birnin da ba ku gani ba tukun suke. A duk lokacin da kuka tambayi mai zagayawa da ku game da abubuwan nan, ba ya ba ku amsa nan take, sai lokacin da ya dace, wato sa’ad da kuka yi kusa da inda fasalolin suke. Da shigewar lokaci, sai kuka soma jin daɗin yadda yake yi muku bayani cikin hikima, don yana gaya muku abin da kuke bukatar sani daidai a lokacin da ya dace.

2 Za a iya kwatanta yanayin Kiristoci na gaskiya da waɗannan masu yawon buɗe ido. Muna marmarin koyan abubuwa game da birni mafi kyau, wanda ke da “tussa” na gaskiya, wato Mulkin Allah. (Ibran. 11:10) Sa’ad da Yesu yake duniya, ya yi wa mabiyansa ja-gora ta wajen koya musu abubuwa masu zurfi game da Mulkin. Amma, Yesu ya amsa dukan tambayoyinsu kuma ya gaya musu kome game da Mulkin nan take ne? A’a. Ya ce: “Ina da sauran zance da yawa da zan yi maku tukuna, amma ba ku iya ku ɗauke su yanzu ba.” (Yoh. 16:12) Da yake Yesu mai ja-gora ne da ya ƙware sosai, bai cika almajiransa da bayanan da ba za su iya fahimta a lokacin ba.

3, 4. (a) Ta yaya Yesu ya ci gaba da koyar da mutane masu aminci game da Mulkin Allah? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan babin?

3 Yesu ya yi wannan furucin da aka rubuta a Yohanna 16:12 a dare na ƙarshe kafin ya mutu. Bayan mutuwarsa, ta yaya zai ci gaba da koyar da mutanensa masu aminci game da Mulkin Allah? Ya gaya wa manzanninsa cewa: “Ruhu na gaskiya . . . zai bishe ku cikin dukan gaskiya.” * (Yoh. 16:13) Ruhu mai tsarki yana kama ne da mai ja-gora mai haƙuri. Yesu yana amfani da ruhu mai tsarki ne wajen koya wa mabiyansa dukan abubuwan da ya kamata su sani game da Mulkin Allah, kuma yana yin hakan a lokacin da ya dace.

4 Bari mu tattauna yadda ruhu mai tsarki yake yi wa Kiristoci na gaskiya ja-gora don su sami ilimi mai zurfi game da  Mulkin Allah a hankali. Na farko, za mu tattauna abubuwan da muka fahimta game da lokacin da Mulkin Allah ya soma sarauta. Bayan haka, za mu tattauna ko su waye ne za su yi sarauta a Mulkin, su waye ne talakawansu, da kuma begen da suke da shi. A ƙarshe kuma, za mu tattauna abin da mabiyan Kristi suka fahimta game da yadda za su kasance da aminci ga Mulkin.

Yadda Aka Fahimci Wata Muhimmiyar Shekara

5, 6. (a) Wane irin fahimta da ba daidai ba ne bayin Yesu suka kasance da shi game da kafa Mulkin da kuma aikin girbin? (b) Me ya sa bai kamata irin wannan fahimtar da ba daidai ba ya sa mu yi shakka ko Yesu ne da gaske yake yi wa mutanensa ja-gora a yau?

5 Kamar yadda muka gani a Babi na 2 na wannan littafin, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi shekaru da yawa suna nuni ga shekara ta 1914 a matsayin shekara mai muhimmanci a cikar annabcin Littafi Mai Tsarki. Amma a lokacin sun gaskata cewa bayyanuwar Kristi ta soma ne a shekara ta 1874, kuma Yesu ya soma sarauta daga sama a shekara ta 1878, har ila sun gaskata cewa ba za a gama kafa Mulkin ba sai a watan Oktoba na 1914. Sun kuma fahimci cewa za a soma girbi daga shekara ta 1874 zuwa 1914, kuma a ƙarshen za a tattara shafaffu zuwa sama. Shin irin wannan fahimtar da ba daidai ba yana nufin cewa Yesu bai yi wa amintattun nan ja-gora da ruhu mai tsarki ba ne?

6 A’a! Ka sake yin tunani a kan kwatancin da muka yi a baya. Shin abubuwan da masu yawon buɗe idon suka faɗa da tambayoyin da suka yi a lokacin da bai dace ba yana nufin cewa mai zagayawa da su ba ƙwararre ba ne? A’a! Hakazalika, ko da yake mutanen Allah sukan yi hanzarin ba da bayanai game da nufin Jehobah kafin ruhu mai tsarki ya bayyana musu wannan gaskiyar, a bayyane yake cewa Yesu yana yi musu ja-gora. Saboda haka, masu aminci suna yarda a yi musu gyara kuma suna daidaita ra’ayinsu cikin tawali’u.—Yaƙ. 4:6.

7. Wane ƙarin haske ne Allah ya albarkaci mutanensa da shi?

7 A shekarun da suka bi bayan 1919, Allah ya albarkaci mutanensa da ƙarin haske game da nufinsa. (Karanta Zabura 97:11.) A shekara ta 1925, an buga wani muhimmin talifi mai jigo “Birth of the Nation” (Kafuwar Al’umma) a cikin Hasumiyar Tsaro. Wannan talifin ya yi bayani daga Littafi Mai Tsarki cewa an kafa Mulkin Almasihu a shekara ta 1914, kuma wannan ya cika annabcin da aka yi game da wata mace na alama, wato Mulkin Allah da ke sama da ya haifi ɗa, kamar yadda aka rubuta a Ru’ya ta Yohanna sura 12. * Talifin ya daɗa nuna cewa tsanantawa da kuma matsalolin da bayin Jehobah suka fuskanta a lokacin da aka yi yaƙin duniya sun nuna dalla-dalla cewa an jefo Shaiɗan daga sama, yana “hasala mai-girma . . . , domin ya san sauran zarafinsa kaɗan ya rage.”—R. Yoh. 12:12.

8, 9. (a) Ta yaya aka fahimci muhimmancin Mulkin Allah? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

8 Wannan Mulkin yana da muhimmanci sosai kuwa? A shekara ta 1928 Hasumiyar Tsaro ta soma nanata cewa Mulkin yana da muhimmanci fiye da ceton da za mu samu ta hanyar  fansa. Hakika, ta hanyar Mulkin Almasihu ne Jehobah zai tsarkake sunansa, ya nuna cewa sarautarsa ce mafi kyau, kuma ta Mulkin ne zai cika dukan nufinsa ga ’yan Adam.

9 Su wane ne za su yi sarauta da Kristi a Mulkin? Su wane ne za su zama talakawan Mulkin? Wane aiki ne mabiyan Kristi za su duƙufa yi?

An Mai da Hankali ga Tattara Shafaffu

10. Mene ne mutanen Allah suka fahimta tun da daɗewa game da adadin nan 144,000?

10 Shekaru da yawa kafin 1914, Kiristoci na gaskiya sun fahimci cewa amintattun mabiyan Kristi guda 144,000 za su yi sarauta da shi a sama. * Waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun fahimci cewa wannan adadin na zahiri ne, kuma an soma zaɓan su tun ƙarni na farko a zamaninmu.

11. Ta yaya waɗanda za su zama abokan sarautar Kristi suka sami ƙarin haske game da aikinsu a duniya?

11 Amma, wane aiki ne aka ba waɗannan abokan sarautar Yesu sa’ad da suke duniya? Sun fahimci cewa a lokacin da Yesu yake duniya, ya mai da hankali ga yin wa’azi kuma ya kwatanta hakan da lokacin girbi. (Mat. 9:37; Yoh. 4:35) Kamar yadda muka koya a Babi na 2, sun ɗauka cewa girbin zai ɗauki shekaru 40 ne, kuma a ƙarshen girbin za a tattara shafaffu zuwa sama. Amma, domin aikin ya ci gaba har bayan shekaru 40, an bukaci ƙarin haske. Yanzu mun fahimci cewa an soma girbin ne a shekara ta 1914. Wannan shi ne lokacin da aka fara wāre alkama daga zawan, wato, wāre shafaffu masu aminci daga Kiristoci na ƙarya. Hakan ya nuna cewa lokaci ya yi da za a mai da hankali ga tattara sauran waɗanda za su je sama!

An soma girbin ne a shekara ta 1914 (Ka duba sakin layi na 11)

12, 13. Ta yaya kwatancin da Yesu ya yi game da budurwai goma da kuma na talanti suka cika a kwanaki na ƙarshe?

12 Daga shekara ta 1919 har zuwa yau, Kristi ya ci gaba da yi wa bawan nan mai aminci mai hikima ja-gora don ya mai da hankali ga yin wa’azi. Yesu ya ba da wannan aikin tun ƙarni na farko. (Mat. 28:19, 20) Ya kuma nuna halayen da mabiyansa shafaffu suke bukata don su iya yin wannan wa’azin. Ta yaya? A kwatancin da Yesu ya yi game da budurwai goma, Yesu ya nuna cewa shafaffun suna bukata su kasance a faɗake a ibadarsu idan suna so su cim ma burinsu na kasancewa a babban bikin da za a yi a sama, a lokacin auren Kristi da  ‘amaryarsa,’ wato shafaffu 144,000. (R. Yoh. 21:2) Ƙari ga haka, Yesu ya nuna a kwatancin talinti cewa bayinsa shafaffu za su nuna ƙwazo wajen yin wa’azi.—Mat. 25:1-30.

13 Shafaffun sun nuna ƙwazo kuma sun kasance a faɗake tun shekaru ɗari da suka shige. Babu shakka, Jehobah zai albarkaci hakan! Amma, aikin girbin ya ƙunshi tattara sauran abokan sarautar Yesu guda 144,000 ne kawai?

Mulkin Ya Soma Tattara Talakawansa da Za Su Zauna a Duniya

14, 15. Waɗanne rukunoni huɗu ne aka ambata a littafin nan The Finished Mystery?

14 Maza da mata masu aminci sun daɗe suna marmarin samun bayani game da “taro mai-girma” da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 7:9-14. Kafin lokacin da Kristi zai bayyana waɗanda suke cikin wannan taro mai girma, an yi bayanai dabam-dabam da suka bambanta da bayani mai sauƙi daga Littafi Mai Tsarki da muka sani kuma muke bi a yau.

15 A shekara ta 1917, littafin nan The Finished Mystery ya bayyana cewa “rukunoni dabam-dabam guda biyu ne za su je sama, kuma rukunoni biyu ne za su gāji duniya.” Su wane ne suke cikin rukunoni huɗun nan da za su sami ceto? Na farko su ne shafaffu 144,000 da za su yi sarauta tare da Kristi. Na biyu kuma su ne taro mai girma. A lokacin, an yi zato cewa Kiristoci da suke zuwa coci ne taro mai girma kuma za a ba su matsayi a sama da bai kai na shafaffu a rukuni na farko ba domin ba su da isashen bangaskiyar da za ta sa su kasance a rukunin. Game da rukuni ne uku kuma, an ɗauka cewa amintattun mutane kamar su Ibrahim da Musa ne ke ciki. Su ne za su kasance a duniya kuma za su shugabanci waɗanda suke cikin rukuni na huɗu, wato sauran ’yan Adam.

16. Wane ƙarin haske ne aka samu a shekara ta 1923 da kuma 1932?

16 Ta yaya ruhu mai tsarki ya ja-goranci mabiyan Kristi har suka fahimci gaskiyar da muka sani a yau? Hakan ya faru ne da sannu-sannu, ta wajen ƙarin haske a kan nufin Allah da muke samu a kai a kai. A shekara ta 1923, mujallar Hasumiyar Tsaro ta yi magana a kan wani rukuni da ba su da begen zuwa sama, amma za su yi rayuwa a duniya a ƙarƙashin sarautar Kristi. A shekara ta 1932, mujallar Hasumiyar Tsaro ta tattauna batun Jonadab (Jehonadab), wanda ya ba da haɗin kai ga Sarki Jehu wanda Allah ya naɗa don su yaƙi masu bauta ta ƙarya. (2 Sar. 10:15-17) Talifin ya ce akwai rukunin mutane a zamaninmu da suke kama da Jonadab, ya daɗa da cewa Jehobah zai kāre wannan rukunin “a lokacin yaƙin Armageddon” don su zauna a duniya.

17. (a) Wane ƙarin haske aka samu a shekara ta 1935? (b) Ta yaya wannan ƙarin haske game da taro mai girma ya shafi Kiristoci masu aminci? (Ka duba akwatin   nan “Sun Sami Kwanciyar Hankali.”)

17 A shekara ta 1935, an samun ƙarin haske a kan nufin Allah. A taron gunduma da aka yi a Washington, D.C., an gano cewa taro mai girma su ne rukunin da za su gāji duniya, kuma su ne tumakin da Yesu ya ambata a kwatancinsa na tumaki  da awaki. (Mat. 25:33-40) Wannan taro mai girma za su kasance cikin “waɗansu tumaki” da Yesu ya ce: “Su kuma dole zan kawo.” (Yoh. 10:16) Sa’ad da mai ba da jawabin, J. F. Rutherford ya ce: “Dukan waɗanda suke da begen zama a duniya su tashi tsaye,” fiye da rabin masu sauraro suka tashi! Sai ya ce: “Ku duba, taro mai girma!” Mutane da yawa sun yi murna sosai domin sun fahimci begen da suke da shi na shiga aljanna a duniya.

18. Ta yaya mabiyan Kristi suka mai da hankali ga yin wa’azi, kuma wace albarka ce suka samu?

18 Tun daga lokacin, Kristi ya ci gaba da yi wa mutanensa ja-gora don su mai da hankali ga tattara waɗanda suke cikin rukunin taro mai girma da za su tsira daga ƙunci mai girma. Da farko dai kamar waɗanda suke cikin wannan rukunin ba za su yi yawa ba. Har ma Ɗan’uwa Rutherford ya taɓa cewa: “Kamar dai ‘taro mai girma’ ɗin ba zai yi yawa ba.” Amma yanzu mun gan yadda Jehobah ya albarkaci aikin girbin tun daga lokacin! A ƙarƙashin ja-gorancin Yesu da ruhu mai tsarki, shafaffu da ’yan’uwansu “waɗansu tumaki” sun zama “garke guda” a ƙarƙashin ‘makiyayi guda’ kamar yadda Yesu ya annabta.

Dan’uwa Rutherford bai san wai taro mai girma zai yi yawa ba (Daga hagu zuwa dama: Nathan H. Knorr da Joseph F. Rutherford da Hayden C. Covington)

19. Ta yaya za mu taimaka wajen faɗaɗa taro mai girma?

19 Yawancin mutane masu aminci za su zauna a duniya har abada a ƙarƙashin sarautar Yesu da abokan sarautarsa 144,000. Idan muka yi tunani a kan yadda Yesu ya yi wa mutanen Allah ja-gora har suka fahimci koyarwa ta Littafi Mai Tsarki game da begen da muke da shi a nan gaba, hakan yana sa mu farin ciki, ko ba haka ba? Gaya wa mutane wannan begen sa’ad da muke wa’azi gata ne babba! Bari mu ci gaba da yin hakan da ƙwazo iyakacin gwargwadonmu don taro mai girma ɗin ya ƙaru sosai kuma dukan yabo ya tabbata ga sunan Jehobah!—Karanta Luka 10:2.

Taro mai girma yana ci gaba da karuwa

Yadda Za Mu Nuna Aminci ga Mulkin

20. Waɗanne fannoni ne ƙungiyar Shaiɗan ta ƙunsa, kuma ta yaya Kiristoci za su kasance da aminci?

20 Yayin da bayin Allah suka ci gaba da koyo game da Mulkin, suna bukata su fahimci ma’anar kasancewa da aminci ga Mulkin. A shekara ta 1922, Hasumiyar Tsaro ta nuna cewa ƙungiyoyi biyu ne ake da su, wato ƙungiyar Jehobah da ta Shaiɗan. Ƙungiyar Shaiɗan ta ƙunshi tsarin kasuwanci da addini da kuma siyasa. Wajibi ne waɗanda suka amince da Mulkin Allah da Kristi yake sarauta su guji yin cuɗanya da ba ta dace ba da waɗannan fannonin ƙungiyar Shaiɗan. (2 Kor. 6:17) Mene ne hakan yake nufi?

21. (a) Ta yaya bawan nan mai aminci ya gargaɗi mutanen Allah game da manyan kasuwanci? (b) Wane bayani ne Hasumiyar Tsaro ta yi game da “Babila Babba” a shekara ta 1963?

21 Bawan nan mai aminci ya ci gaba da fallasa cin hanci da rashawa da ake yi a manyan kasuwanci kuma ya gargaɗi bayin Allah su guji son abin duniya. (Mat. 6:24) Hakazalika, littattafanmu sun ci gaba da fallasa ƙungiyoyin addinai da ke ƙarƙashin ikon Shaiɗan. A shekara ta 1963, Hasumiyar Tsaro ta nuna cewa Kiristendom da kuma dukan addinan ƙarya suna cikin “Babila Babba.” Saboda haka, a Babi na 10 na wannan littafin, za mu ga yadda aka taimaka wa mutanen Allah  a ko’ina a faɗin duniya su “fito daga cikinta” kuma su tsabtace kansu daga ayyukan addinan ƙarya.—R. Yoh. 18:2, 4.

22. Ta yaya mutanen Allah da yawa suka fahimci umurnin da ke littafin Romawa 13:1 a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya?

22 Sashen siyasa na ƙungiyar Shaiɗan fa? Shin ya dace Kiristoci su saka hannu a yaƙe-yaƙe da kuma tashin hankali da ake yi a ƙasashe? Sa’ad da ake Yaƙin Duniya na Ɗaya, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun fahimci cewa bai kamata mabiyan Kristi su yi kisa ba. (Mat. 26:52) Amma da yawa daga cikinsu sun ɗauka cewa umurnin da ke Romawa 13:1 da ta ce a yi biyayya ga “masu-mulki” yana nufin Kiristoci su shiga soja, su saka kayan soja kuma su ɗauki makamai, amma sa’ad da aka umurce su su kashe magabtansu sai su harbi sama.

23, 24. Ta yaya muka fahimci Romawa 13:1 a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu, kuma yaya mabiyan Kristi suka sami ƙarin haske a kan batun?

23 Sa’ad da aka soma Yaƙin Duniya na Biyu a shekara ta 1939, Hasumiyar Tsaro ta wallafa batu mai zurfi game da kasancewa ’yan-ba-ruwanmu. Talifin ya bayyana dalla-dalla cewa Kiristoci ba za su saka hannu a yaƙe-yaƙe da tashin hankalin da ake yi a duniyar Shaiɗan ba. Babu shakka, wannan gargaɗi ne a kan kari! Da yake mabiyan Kristi sun bi wannan gargaɗin, ba su ɗauki alhakin jinin mutane da aka kashe sa’ad da ake wannan yaƙin ba. Daga shekara ta 1929, littattafanmu sun bayyana cewa “masu mulki” da aka ambata a Romawa 13:1 ba masu mulkin gwamnati ba ne, amma Jehobah da Yesu ne. Har ila, ana bukatar cikakken bayani a kan wannan koyarwar.

24 Ruhu mai tsarki ya taimaka wa mabiyan Kristi su fahimci wannan koyarwar a shekara ta 1962, kuma sun wallafa  wasu muhimman talifofin da suka bayyana littafin Romawa 13:1-7 a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba da ta 1 ga Disamba na shekara ta 1962. A lokacin ne bayin Allah suka fahimci irin biyayyar da ake nufi kamar yadda Yesu ya bayyana a wannan sanannen furucin: “Dukan abin da ke na Kaisar fa, ku bayar ga Kaisar; na Allah kuwa ku bayar ga Allah.” (Luk 20:25) A yanzu, Kiristoci na gaskiya sun fahimci cewa masu mulki suna nufin gwamnatocin duniya kuma wajibi ne Kiristoci su yi masu biyayya. Amma biyayyar tana da iyaka. Sa’ad da gwamnatocin ’yan Adam suka ce mu yi abin da Jehobah ya haramta, za mu bi gurbin manzanni na dā sa’ad da suka ce: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.” (A. M. 5:29) A Babi na 13 da 14 na wannan littafin, za mu ƙara koyon yadda bayin Allah suke bin ƙa’idar zama ’yan-ba-ruwanmu.

Muna da babban gatan yi wa mutane wa’azin aljanna!

25. Me ya sa kake godiya ga yadda ruhu mai tsarki yake mana ja-gora mu fahimci abubuwa game da Mulkin Allah?

25 Ka yi tunani a kan dukan abubuwan da mabiyan Kristi suka koya game da Mulkin a cikin shekaru ɗari da suka wuce. Mun san lokacin da aka kafa Mulkin Allah a sama da kuma yadda Mulkin yake da muhimmanci. Mun koyi cewa an raba masu aminci kashi biyu, waɗanda za su je sama da kuma waɗanda za su zauna a duniya har abada. Kuma mun koyi yadda za mu kasance da aminci ga Mulkin Allah da kuma yadda za mu yi biyayya ga gwamnatin ’yan Adam idan dokarta ba ta saɓa wa ta Allah ba. Ka tambayi kanka, ‘Ta yaya zan san waɗannan gaskiya masu tamani idan Yesu Kristi bai yi wa bawansa mai aminci ja-gora don ya fahimci waɗannan gaskiyar kuma ya koyar da su ba?’ Babu shakka, ja-gorancin da muke samu daga Kristi da kuma ruhu mai tsarki albarka ce babba!

^ sakin layi na 3 Wani binciken da aka yi ya nuna cewa kalmar nan “bishe” a Helenanci yana nufin “nuna hanya.”

^ sakin layi na 7 Kafin wannan lokaci, an ɗauka cewa wahayin yana nufin yaƙi tsakanin waɗanda ke ƙarƙashin Paparuma da Romawa arna ne.

^ sakin layi na 10 A watan Yuni na shekara ta 1880, Zion’s Watch Tower (Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona) ta ce shafaffun guda 144,000 Yahudawa ne da za su zama Kiristoci kafin shekara ta 1914. Amma, ’yan watanni bayan hakan, an sake wallafa wani bayani da ya zo ɗaya da abin da muka gaskata a yau.