Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Mulkin Allah Yana Sarauta!

Miliyoyin mutane suna jin dadi a karkashin sarautar Allah. Za ka so ka yi rayuwa a wurin kuwa?

Wasiƙa Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah

Ta yaya sanarwar da C. T. Russell ya yi a ranar 2 ga Oktoba, 1914 ta zama gaskiya?

BABI NA 1

‘Bari Mulkinka Ya Zo’

Yesu ya fi tattaunawa game da Mulkin Allah fiye da kome. A wane lokaci kuma ta yaya ne Mulkin zai zo?

BABI NA 2

An Kafa Mulkin a Sama

Wa ya taimaka wajen shirya mabiyan Kristi a duniya don Mulkin da za a kafa? Waɗanne abubuwa ne suka sa muka gaskata cewa Mulkin gwamnati ce ta gaske?

BABI NA 3

Jehobah Ya Bayyana Nufinsa

Mulkin yana cikin shirin da Allah ya yi da farko kuwa? Ta yaya Yesu ya ba da ƙarin haske a kan Mulkin?

BABI NA 4

Jehobah Ya Ɗaukaka Sunansa

Mene ne Mulkin Allah ya cim ma game da sunan Allah? Ta yaya za ka saka hannu wajen tsarkake sunan Jehobah?

BABI NA 5

Sarkin Yana Bayyana Mana Mulkin Dalla-dalla

Ka sami ƙarin bayani game da Mulkin, masu sarautan da talakawan da kuma ma’anar kasancewa da aminci ga Mulkin.

BABI NA 6

Masu Wa’azi—Masu Wa’azi Sun Ba da Kansu da Yardan Rai

Me ya sa Yesu ya kasance da tabbaci cewa zai sami mutanen da za su yi wa’azi da yardan rai a kwanaki na ƙarshe? Ta yaya za ka nuna cewa kana biɗan Mulkin farko a rayuwarka?

BABI NA 7

Hanyoyin Yin Wa’azi—Yin Amfani da Hanyoyi Dabam-dabam don Yin Wa’azi

Ka koya hanyoyi dabam-dabam da bayin Allah suka yi amfani da su don yaɗa bishara ga jama’a kafin ƙarshe ya zo.

BABI NA 8

Kayan Aiki don Yin Wa’azi—Wallafa Littattafai Domin Mutane a Faɗin Duniya

Ta yaya aikin fassara da muke yi ya nuna cewa muna da goyon bayan Yesu? Waɗanne abubuwa game da littattafanmu ne suka tabbatar maka cewa Mulkin na gaskiya ne?

BABI NA 9

Sakamakon Yin Wa’azi—‘Gonaki Sun Nuna Sun Isa Girbi’

Yesu ya koya wa almajiransa muhimman darussa guda biyu game da wannan aikin girbi mai girma. Ta yaya waɗannan darussan suke shafarmu a yau?

SASHE NA 3

Ƙa’idodin Mulkin—Biɗan Adalcin Allah

A wannan sashen, za mu ga yadda Mulkin Almasihu yake wa bayin Allah gyara.

BABI NA 10

Sarkin Ya Tsabtace Ibadar Mutanensa

Daga ina bikin Kirsimati da kuma gicciye suka samo tushensu?

BABI NA 11

Yin Gyara a Dabi’a Ya Nuna Cewa Allah Mai Tsarki Ne

Dakunan tsaro da kofofin haikali da Ezekiyel ya gani a wahayi suna da ma’ana ta musamman ga bayin Allah tun daga 1914.

BABI NA 12

An Tsara Su Don Su Yi wa ‘Allah na Salama’

Littafi Mai Tsarki ya bambanta yamutsi ba da tsari ba, amma da salama. Me ya sa? Ta yaya amsar ta shafi Kiristoci a yau?

BABI NA 13

Masu Wa’azin Mulkin Sun Kai Ƙara Kotu

Ra’ayin alƙalai a wasu manyan kotuna na zamani ya zo ɗaya da na babban malami na dā mai suna Gamaliel.

BABI NA 15

Gwagwarmaya don Samun ’Yancin Yin Ibada

Bayin Allah sun yi gwagwarmaya don samun ’yancin yin biyayya ga dokokin Mulkin Allah.

BABI NA 14

Sun Goyi Bayan Mulkin Allah Ne Kaɗai

An kawo ƙarshen tsanantawa da Shaidun Jehobah suke fuskanta don sun ƙi yin siyasa, kuma ta hannun waɗanda ba a zata ba

BABI NA 16

Yin Taro don Ibada

Ta yaya za mu amfana sosai sa’ad da muka halarci taro don mu bauta wa Jehobah?

BABI NA 17

Koyar da Masu Hidimar Mulkin

Ta yaya makarantu na ƙungiyar Jehobah ta shirya masu hidimar Mulkin Allah su cika aikinsu?

BABI NA 19

Aikin Gini da Ke Ɗaukaka Jehobah

Wuraren ibada suna ɗaukaka Allah, amma akwai abin da ya fi ɗaukawa da tamani sosai.

BABI NA 20

Hidimar Agaji

Ta yaya muka san cewa aikin agaji sashe ne na bautarmu ga Jehobah?

BABI NA 18

Yadda Ake Tallafa wa Ayyukan Mulkin

A ina ake samun kuɗin? Yaya ake amfani da shi?

BABI NA 21

Mulkin Allah Ya Halaka Maƙiyansa

Za ka iya yin shiri yanzu don yaƙin Armageddon.

BABI NA 22

Mulkin Ya Sa Ana Yin Nufin Allah a Duniya

Me ya sa ka tabbata cewa alkawuran Jehobah za su cika?