Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

“Ku Tsare Kanku Cikin Kaunar Allah”

 BABI NA 4

Me Ya Sa Za a Girmama Hukuma?

Me Ya Sa Za a Girmama Hukuma?

“Ku girmama dukan mutane.”—1 BITRUS 2:17.

1, 2. (a) Wace kokawa ce muke fuskanta sa’ad da ya zo ga hukuma? (b) Waɗanne tambayoyi ne za a amsa?

KA TAƁA ganin yadda yaro ƙarami ya yi idan aka ce ya yi wani abin da ba ya son ya yi? Daga yadda zai haɗa fuska za ka gane cewa da wani abu da ke zuciyar yaron. Ya ji abin da iyayensa suka ce, kuma ya san cewa ya kamata ya girmama ikonsu. Amma a wannan yanayin, shi dai ba ya so ya yi biyayya. Wannan jayayyar ta bayyana wani abin da ke faruwa ga kowannenmu a lokaci lokaci.

2 Girmama hukuma ba koyaushe ba ne yake da sauƙi a gare mu. Yana yi maka wuya wani lokaci ka girmama wasu da suke da ɗan iko a kanka? Idan haka ne, ba kai kaɗai ba ne a wannan kokawar. Muna zaune ne a lokacin da girmama hukuma bai da farin jini sosai. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ce muna bukatar mu girmama waɗanda suke da iko a kanmu. (Misalai 24:21) Hakika, yin haka ya zama dole idan muna so mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah. Saboda haka, wasu tambayoyi sun taso. Me ya sa girmama hukuma yake yi mana wuya sosai? Me ya sa Jehobah ya nemi mu yi musu biyayya, kuma menene zai taimake mu mu yi haka? A ƙarshe, ta waɗanne hanyoyi ne za mu girmama hukuma?

DALILI DA YA SA YA KASANCE ƘALUBALE

3, 4. Ta yaya zunubi da ajizanci suka fara, kuma me ya sa yanayinmu na zunubi ya sa girmama hukuma ya kasance ƙalubale?

3 Bari mu ba da taƙaitattun dalilai biyu da ya sa girmama  hukuma ya kasance ƙalubale. Na farko, mu ajizai ne; na biyu kuma mutanen da suke da iko ma ajizai ne. Zunuban mutane da ajizancinsu sun samu asali ne tun da daɗewa, a can lambun Adnin sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka yi wa Allah tawaye. Saboda haka, mafarin zunubi tawaye ne. Har wa yau, muna da muradin yin tawaye.—Farawa 2:15-17; 3:1-7; Zabura 51:5; Romawa 5:12.

4 Domin yanayinmu na zunubi, fahariya da faɗin rai suna iya bayyana a yawancinmu nan da nan, amma kuma tawali’u hali ne mai wuya wanda mu duka muke bukatar mu ƙoƙarta sosai idan muna son mu koye shi kuma mu ci gaba da nuna shi. Har bayan shekaru masu yawa na hidima cikin aminci ga Allah, muna iya soma nuna taurin kai da fahariya. Alal misali, ka yi la’akari da Kora, wanda cikin aminci ya kasance da mutanen Jehobah cikin wahaloli masu yawa da suka sha. Duk da haka, ya kasance da kwaɗayin iko kuma ya ja-goranci tawaye ga Musa, mutum mai tawali’u gaba da kowa a wannan zamanin. (Litafin Lissafi 12:3; 16:1-3) Ka yi kuma tunanin Sarki Uzziya wanda fahariyarsa ta sa ya shiga cikin haikalin Jehobah ya yi ayyukan da aka ka’ida wa firistoci. (2 Labarbaru 26:16-21) Waɗannan mutanen sun sha wahala sosai a sakamakon tawayen da suka yi. Duk da haka, misalansu marasa kyau sun kasance da amfani wajen tunasar da mu. Muna bukatar mu yi kokawa da fahariyar da ke sa girmama hukuma yake yi mana wuya.

5. Ta yaya mutane ajizai suka ci zali da ikonsu?

5 A wani ɓangare kuma, mutane ajizai da suke da iko sun raunana muradin da ake da shi na girmama hukuma. Yawancinsu sun kasance mazalunta, ko miyagu. Hakika, mafi yawan tarihin ’yan adam tarihin cin zali ne na masu iko. (Karanta Mai-Wa’azi 8:9) Alal misali, Saul mutumin kirki ne, kuma mai tawali’u sa’ad da Jehobah ya zaɓe shi ya zama sarki. Amma, ya fara nuna fahariya da kishi; bayan haka,  ya tsananta wa Dauda mutum mai aminci. (1 Samuila 9:20, 21; 10:20-22; 18:7-11) Daga baya, Dauda ya zama ɗaya daga cikin sarakunan nagari da aka taɓa yi a Isra’ila, duk da haka, ya ci zali da ikonsa sa’ad da ya kwace matar Uriah kuma ya tura wannan mutumin zuwa bakin daga domin a kashe shi a yaƙi. (2 Samuila 11:1-17) Hakika, ajizanci yana sa ya yi wuya mutane su riƙe iko da kyau. Kuma idan waɗanda suke da iko suka ƙi daraja Jehobah, suna wuce gona da iri. Bayan da ya kwatanta yadda wasu Fafaroma na Katolika suka tsananta wa mutane, wani baturen Ingila ya rubuta: “Iko yana lalata mutane, cikakken iko kuma yana lalatarwa gabaki ɗaya.” Da tunanin irin wannan abin da suka yi, bari mu amsa tambayar nan: Me ya sa za mu girmama hukuma?

ME YA SA ZA A GIRMAMA HUKUMA?

6, 7. (a) Menene ƙaunarmu ga Jehobah take motsa mu mu yi, kuma me ya sa? (b) Wane hali ne miƙa kai ya ƙunsa, kuma ta yaya za mu nuna shi?

6 Dalili mafi kyau na girmama hukuma ya fito ne daga ƙauna, wato, ƙaunarmu ga Jehobah, ga ’yan’uwanmu mutane, da kuma kanmu. Muna son mu faranta wa Jehobah rai domin mun fi ƙaunarsa fiye da kome. (Karanta Misalai 27:11; Markus 12:29, 30.) Mun san cewa an ƙalubalanci ikon mallakarsa, wato, damansa ya mallaki dukan sararin samaniya a duniya tun daga lokacin tawaye a Adnin, kuma yawancin ’yan adam suna gefen Shaiɗan sun kuma ƙi sarautar Jehobah. Muna farin cikin kasancewa a ɓangaren Allah. Sa’ad da muka karanta kalmomi masu muhimmanci na Ru’ya ta Yohanna 4:11, suna taɓa zuciyarmu. Mun fahimta ƙwarai da gaske cewa Jehobah ne Mamallakin dukan sararin samaniya! Mun rungumi ikon mallaka na Jehobah, ta wajen yin na’am da sarautarsa a rayuwarmu ta yau da kullum.

7 Irin wannan girmamawa tana nufin biyayya da kuma  wasu abubuwa. Muna yi wa Jehobah biyayya domin muna ƙaunarsa. Amma kuma, da akwai lokatai da yin biyayya zai kasance da wuya ƙwarai. A irin wannan lokaci, kamar wannan ɗan yaron da aka ambata da farko, muna bukatar mu koyi miƙa kai. Mu tuna cewa Yesu ya miƙa kai ga nufin Ubansa duk da cewa yin haka yana da wuya ƙwarai. “Ba nawa nufi ba, naka za a yi,” ya ce wa Ubansa.—Luka 22:42.

8. (a) Miƙa kai ga ikon Jehobah a yau sau da yawa ya ƙunshi menene, kuma menene ya nuna yadda Jehobah yake ji game da irin wannan? (b) Menene zai taimake mu mu saurari gargaɗi kuma mu karɓi horo? (Dubi akwati a  shafi na 46-47.)

8 Hakika, Jehobah ba ya magana da mu baki da baki a yau, yana amfani ne da Kalmarsa da kuma wakilansa a duniya. Sau da yawa, muna nuna miƙa kai ga Jehobah ta wajen girmama mutanen da ya ba iko, ko kuma waɗanda ya ƙyale su ci gaba da kasancewa a matsayi na iko a kanmu. Idan muka yi tawaye ga waɗannan mutane, alal misali, ta wajen ƙin bin gargaɗin da suka yi mana daga Nassosi da kuma gyaran da suka yi mana, za mu yi wa Allahnmu laifi. Sa’ad da Isra’ilawa suka yi gunaguni da tawaye ga Musa, Jehobah ya ɗauki abin da suka yi kamar shi suka yi wa.—Litafin Lissafi 14:26, 27.

9. Me ya sa ƙaunarmu ga Allah da kuma mutum za ta motsa mu mu girmama hukuma? Ka kwatanta.

9 Muna kuma girmama hukuma domin ƙaunarmu ga ’yan’uwanmu ’yan adam. Ta yaya? A ce kai soja ne. Nasarar dukan wani dakaru, wataƙila ya dangana ne bisa ba da haɗin kan kowane soja da kuma yin biyayya ga umurni. Idan ka yi wa wannan ƙungiyar maƙarƙashiya ta wajen yin tawaye, dukan sojoji za su shiga cikin haɗari. Hakika, sojoji suna kashe mutane masu yawa a duniya ta yau. Amma, Jehobah yana da sojojin da abin kirki kawai suke yi. Littafi Mai Tsarki ya kira Allah sau da yawa Jehobah “mai-runduna.” (1 Samuila 1:3) Shi Shugaban runduna ne mai girma na ruhohi. A wasu lokatai kuma, Jehobah yana kwatanta  bayinsa a duniya da runduna. (Zabura 68:11; Ezekiel 37:1-10) Idan muka yi tawaye ga mutanen da Jehobah ya ba iko, ba muna saka ’yan’uwanmu sojoji na ruhaniya cikin haɗari ba ne? Sa’ad da Kirista ya yi tawaye ga dattawan da aka naɗa, sauran mutanen da ke cikin ikilisiya ma za su iya shan wahala. (1 Korintiyawa 12:14, 25, 26) Sa’ad da yaro ya yi tawaye, hakan na iya shafan dukan iyalin. Saboda haka, za mu nuna ƙauna ga ’yan’uwanmu ’yan adam ta wajen koyon halin girmamawa da kuma ba da haɗin kai.

10, 11. Ta yaya muradi mai kyau na amfanin kanmu zai motsa mu mu yi biyayya ga hukuma?

10 Muna daraja hukuma domin amfanin mu. Sa’ad da Jehobah ya ce mu girmama hukuma, sau da yawa yana faɗin amfanin da za mu samu idan muka yi haka. Alal misali, ya gaya wa yara su yi biyayya ga iyayensu domin kwanakinsu ya yi tsawo. (Kubawar Shari’a 5:16; Afisawa 6:2, 3) Ya gaya mana mu girmama dattawan ikilisiya domin ƙin yin haka  zai ɓata dangantakarmu da shi. (Ibraniyawa 13:7, 17) Kuma ya gaya mana mu yi biyayya ga hukuma domin kāriyarmu.—Romawa 13:4.

11 Ba za ka yarda ba ne cewa sanin abin da ya sa Jehobah yake so mu yi biyayya zai taimake mu mu girmama hukuma? Bari mu tattauna yadda za mu girmama hukuma a hanyoyi uku ta rayuwa.

GIRMAMAWA CIKIN IYALI

12. Wane hakki ne Jehobah ya ba maigida kuma uba a cikin iyali, kuma yaya zai cika hakkinsa?

12 Jehobah ne da kansa ya tsara iyali. Da yake Allah ne mai tsari, ya tsara iyali a hanyar da za ta kasance da kyau. (1 Korintiyawa 14:33) Ya ba maigida kuma uba ikon zama shugaban iyali. Maigidan yana girmama Shugabansa, Yesu Kristi, ta wajen yin koyi da yadda yake nuna ikonsa bisa ikilisiya. (Afisawa 5:23) Saboda haka, kada maigida ya guji hakkinsa amma ya cika hakkinsa kamar namiji; kada kuma ya zama mai cin zali, maimakon haka, ya kasance mai ƙauna, mai sanin ya kamata, kuma mai kirki. Ya tuna cewa ikonsa yana da iyaka, bai fi na Jehobah ba.

Uba Kirista yana yin koyi da yadda Kristi ya bi da shugabanci

13. Ta yaya mata kuma uwa za ta cika hakkinta cikin iyali a hanyar da zai faranta wa Jehobah rai?

13 Mace kuma uwa za ta kasance mataimakiyar maigidanta ne. Ita ma an  ba ta iko cikin iyali, domin Littafi Mai Tsarki ya yi maganar “dokar uwa.” (Misalai 1:8) Hakika, ikonta yana ƙasa da na mijinta. Mace Kirista tana girmama ikon mijinta ta wajen taimaka masa ya cika hakkinsa na shugabancin iyali. Ba za ta raina shi ba, ko ta yaudare shi, ko kuma ta ƙwace matsayinsa. Maimakon haka, za ta kasance mai taimako kuma mai ba da haɗin kai. Sa’ad da ba ta son shawarar da ya yanke, za ta furta ra’ayinta cikin bangirma, amma kuma za ta miƙa kai. Idan maigidan ba mai bi ba ne, za ta iya fuskantar yanayi mai wuya, duk da haka miƙa kanta zai iya motsa maigidanta ya nemi Jehobah.​—Karanta 1 Bitrus 3:1.

14. Ta yaya ne yara za su faranta ran iyayensu da kuma Jehobah?

14 Yara suna faranta wa Jehobah rai sa’ad da suka yi wa babansu da mamarsu biyayya. Suna daraja iyayensu kuma suna sa su farin ciki. (Misalai 10:1) A iyalan gwauraye, yara suna bukatar su bi wannan mizani na biyayya, da sanin cewa mahaifinsu ko mahaifiyarsu yana ko tana bukatar haɗin  kansu da taimako. A iyalin da kowa yake cika hakkin da Allah ya ba shi, tana kasancewa da salama da kuma farin ciki mai yawa. Hakan kuma yana daraja Wanda ya tsara dukan iyali, Jehobah Allah.—Afisawa 3:14, 15.

GIRMAMAWA CIKIN IKILISIYA

15. (a) Ta yaya za mu nuna cewa muna girmama ikon Jehobah a cikin ikilisiya? (b) Waɗanne mizanai ne za su taimake mu mu yi biyayya ga waɗanda suke ja-gora? (Dubi akwati a  shafi na 48-49.)

15 Jehobah ya naɗa Ɗansa a matsayin Masarauci bisa ikilisiyar Kirista. (Kolossiyawa 1:13) Yesu kuma ya ba “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” hakkin kula da bukatu na ruhaniya na mutanen Allah a duniya. (Matta 24:45-47) Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ne suke wakiltan wannan bawa. Kamar yadda yake a ikilisiyoyin Kirista na ƙarni na farko, dattawa a yau suna samun umurni da kuma gargaɗi daga Hukumar Mulki kai tsaye ko kuma ta bakin wakilanta masu kula masu ziyara. Sa’ad da kowanenmu ya girmama ikon dattawa, Jehobah ne muke yi wa biyayya.​—Karanta 1 Tassalonikawa 5:12; Ibraniyawa 13:17.

16. Kamar yaya ake naɗa dattawa ta hanyar ruhu mai tsarki?

16 Dattawa da kuma bayi masu hidima ba kamiltattun mutane ba ne. Suna da kurakuransu kamar yadda muke da su. Duk da haka, dattawa “kyautai ga mutane” ne da aka yi tanadi domin su taimaki ikilisiya ta kasance da ƙarfi a ruhaniya. (Afisawa 4:8) Ruhu mai tsarki ne yake naɗa dattawa. (Ayukan Manzanni 20:28) Ta yaya? Domin dole ne waɗannan mutanen su cika mizanai na cancanta da ke rubuce cikin Kalmar Allah da ruhu mai tsarki ya hure. (1 Timothawus 3:1-7, 12; Titus 1:5-9) Bugu da ƙari, dattawan da suke bincike su ga ko ɗan’uwa ya cancanta suna yin addu’a domin ruhu mai tsarki na Jehobah ya yi musu ja-gora.

17. A ayyukansu na ikilisiya, me ya sa a wasu lokatai mata suke rufe kansu?

17 A cikin ikilisiya, zai kasance a wani lokaci babu  dattawa ko kuma bayi masu hidima da za su yi ayyukan da ainihi su suke yi, kamar su gudanar da taron fita hidima. A irin wannan yanayi, wani ɗan’uwa da ya yi baftisma yana iya gudanar da taron. Idan babu ɗan’uwan da ya yi baftisma, ’yar’uwa da ta ƙware tana iya gudanar da taron. Amma kuma, idan ’yar’uwa za ta cika hakkin namiji da ya yi baftisma, sai ta rufe kanta. * (1 Korintiyawa 11:3-10) Wannan mizani bai ƙasƙantar da mata ba. Maimakon haka, ya ba da zarafi ne na girmama tsarin Jehobah na shugabanci, a cikin iyali da kuma a ikilisiya.

GIRMAMA GWAMNATI

18, 19. (a) Yaya za ka kwatanta mizanan da ke rubuce a Romawa 13:1-7? (b) Ta yaya za mu girmama gwamnati?

18 Kiristoci na gaskiya suna bin mizanin da ke rubuce a Romawa 13:1-7. (Karanta.) Sa’ad da ka karanta waɗannan ayoyin, za ka ga cewa “ikon masu-mulki” da aka ambata a nan gwamnati ce. Duk iya tsawon lokacin da Jehobah ya ƙyale gwamnatin mutane ta ci gaba da wanzuwa, suna cika hakkoki masu muhimmanci, suna kawo ɗan zaman lafiya kuma suna biyan wasu bukatu. Muna girmama irin waɗannan hukumomin ta wajen bin doka. Mu tabbata cewa mun biya dukan wani haraji da ake bin mu, mu cika dukan wani fom da gwamnati take bukata da kyau, kuma mu bi dukan wani doka da ta shafi mu, iyalinmu, sana’armu ko kuma dukiyoyinmu. Amma kuma, ba za mu miƙa kai ga hukuma ba idan suka ce mu yi wa Allah rashin biyayya. Maimakon haka, za mu amsa kamar yadda manzanni na zamanin dā suka amsa: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.”—Ayukan Manzanni 5:28, 29; dubi akwatin nan “ Ikon Wanene Zan Yi wa Biyayya?” da ke shafi na 42.

19 Muna kuma daraja gwamnati ta wajen yadda muke cuɗanya  da wasu. A wani lokaci za mu iya yin cuɗanya kai tsaye da ma’aikatan gwamnati. Manzo Bulus ya yi cuɗanya da mutane masu mulki kamar su Sarki Hirudus Agaribas da Gwamna Fastos. Waɗannan mutane masu kurakurai ne ƙwarai, amma Bulus ya tattauna da su cikin daraja. (Ayukan Manzanni 26:2, 25) Muna bin misalin manzo Bulus, ko da mutumin da muke tattaunawa da shi mai iko ne sosai ko kuma ɗan sanda. A makaranta, ya kamata matasa Kiristoci su ƙoƙarta su nuna irin wannan girmamawa ga malamansu da kuma ma’aikatan makaranta. Hakika, ba waɗanda suka yarda da bangaskiyarmu ba ne ka kawai muke girmamawa; muna girmama waɗanda suke hamayya da Shaidun Jehobah. Hakika, ya kamata dukan marasa bi su fahimci cewa muna girmama su.—Karanta Romawa 12:17, 18; 1 Bitrus 3:15.

20, 21. Waɗanne albarka ne ake samu daga girmama hukuma?

20 Manzo Bulus ya rubuta: “Ku girmama dukan mutane.” (1 Bitrus 2:17) Bari mu ci gaba da girmama mutane sosai. Sa’ad da mutane suka ga cewa muna girmama su da gaske, za su yi farin ciki. Ka tuna cewa wannan hali yana kasancewa da wuyar samu yanzu. Nuna shi wata hanya ce ta bin umurnin Yesu: “Ku bari haskenku shi haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu-kyau, su girmama Ubanku wanda ke cikin sama.”—Matta 5:16.

21 A wannan duniya mai duhu, mutane masu zuciyar kirki suna zuwa wurin haske na ruhaniya. Saboda haka, nuna girmamawa a cikin iyali, da ikilisiya, da kuma ga gwamnati, za ta iya jawo wasu kuma ta motsa su su yi tafiya cikin haske tare da mu. Wannan bege ne mai kyau! Ko da hakan bai faru ba, da wani abin da tabbatacce ne. Girmama mutane da muke yi tana faranta wa Jehobah Allah rai kuma tana taimakonmu mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah. Akwai albarkar da ta fi wannan?

^ sakin layi na 17 A shafuffuka na 209-212, Rataye ya tattauna wasu hanyoyin da za a yi amfani da wannan mizani.