“Ku matarda gaɓaɓuwanku fa waɗanda ke a duniya; fasikanci, ƙazanta, kwaɗayi, mugun guri, da sha’awa, watau bautar gumaka ke nan.”—KOLOSSIYAWA 3:5.

1, 2. Ta yaya Bala’am ya ƙulla ya cutar da mutanen Jehobah?

MASUNCI ya je wurin da yake son kamun kifi. Yana da niyyar kama wani irin kifi. Ya zaɓi tana ya sa a ƙugiya ya jefa cikin ruwa. Ba da daɗewa ba, sai ya ji kifi yana jan ƙugiyar, sai ya jawo kifin da ya kama. Yana murmushi don ya yi amfani da tana da ta dace.

2 A shekara ta 1473 K.Z., wani mutum mai suna Bala’am ya yi tunanin irin wannan rinjayar. Amma abin da yake so ya kama mutanen Allah ne, waɗanda suka yi zango a Filayen Mowab, a iyakar Ƙasar Alkawari. Bala’am ya yi da’awar shi annabin Jehobah ne, amma mutum ne kawai mai haɗama da aka yi hayarsa ya la’anci Isra’ilawa. Amma, da taimakon Jehobah, Bala’am ya albarkaci Isra’ila. Da niyyar ya karɓi ladansa, Bala’am ya yi tunani zai iya sa Allah ya la’anci mutanensa da kansa, idan aka jarabta su su yi zunubi mai tsanani. Da wannan buri a zuciyarsa, Bala’am ya shirya musu abin da zai jarabta su, wato, ’yan matan Mowab.—Litafin Lissafi 22:1-7; 31:15, 16; Ru’ya ta Yohanna 2:14.

3. Yaya ƙullin Bala’am ya yi nasara?

3 Wannan ƙullin nasa ya yi nasara kuwa? E, ya yi ɗan nasara. Mazan Isra’ila wajen dubbai suka jarrabu ta wajen yin “fasikanci da yan matan Moab.” Har suka fara bauta wa allolin Mowabawa, har da bin Ba’al na Peor, allahn  haihuwa da na jima’i. Domin wannan, Isra’ilawa 24,000 suka halaka a kan iyakar Ƙasar Alkawari. Wannan babu shakka babban bala’i ne.—Litafin Lissafi 25:1-9.

4. Me ya sa dubban Isra’ilawa suka jarrabu da lalata?

4 Menene ya jawo wannan bala’in? Da yawa cikin mutanen sun zama masu muguwar zuciya ta wajen janyewa daga Jehobah, Allahn da ya cece su daga ƙasar Masar, ya ciyar da su a cikin daji, kuma ya ja-gorance su zuwa iyakar ƙasar alkawari. (Ibraniyawa 3:12) Da ya yi bimbini a kan wannan batu, manzo Bulus ya rubuta: “Kada mu yi fasikanci kuma, kamar yadda waɗansu daga cikinsu suka yi, rana ɗaya kuwa suka faɗi, mutum zambar ashirin da uku.” *1 Korintiyawa 10:8.

5, 6. Me ya sa labarin Isra’ilawa a Filayen Mowab yake da muhimmanci a gare mu a yau?

5 Labarin da yake Littafin Lissafi yana da darussa masu muhimmanci ga mutanen Allah a yau, waɗanda suke kan iyakar ƙasar alkawari mafi girma. (1 Korintiyawa 10:11) Alal misali, jarabar jima’i ta duniya irin ta Mowabawa ne amma ya fi yaɗuwa. Ƙari ga haka, kowace shekara Kiristoci  dubbai suna faɗawa lalata, irin jaraba da ta rinjayi Isra’ilawa. (2 Korintiyawa 2:11) Kuma wajen koyi da Zimri, wanda da gaba gaɗi ya shigo da ’yar Midiyanawa har cikin zangon Isra’ilawa zuwa cikin tantinsa, wasu da suke tarayya da mutanen Allah a yau sun zama masu ɓata mutane a cikin ikilisiyar Kiristoci.—Litafin Lissafi 25:6, 14; Yahuda 4.

6 Kana ganin kanka a Filayen Mowab na zamanin nan kuwa? Kana ganin ladarka, sabuwar duniya da ka daɗe kana jira a gabanka kuwa? Idan haka yake, to ka yi iyaka ƙoƙarinka ka tsare kanka cikin ƙaunar Allah ta wajen yi wa dokarsa biyayya: “Ku guje ma fasikanci.”—1 Korintiyawa 6:18.

Yadda Filayen Mowab Suke

MENENE FASIKANCI?

7, 8. Menene “fasikanci” kuma ta yaya waɗanda suke yinsa suke girbe abin da suka shuka?

7 Kamar yadda aka yi amfani da shi cikin Littafi Mai Tsarki, “fasikanci” (Helenanci, por·neiʹa) yana nufin haramtaccen jima’i, wato, yin jima’i da wadda ba a aura bisa Nassosi ba. Wannan ya haɗa da zina, karuwanci, da kuma jima’i tsakanin waɗanda ba su auri juna ba, da tsotsan al’aura ko farji, jima’i ta wajen dubura da kuma tattaɓa al’aura tsakanin waɗanda ba su yi aure ba. Ya kuma haɗa da irin waɗannan ayyuka tsakanin mutanen masu jinsi ɗaya ko kuma da dabba. *

8 Nassosi ya faɗi sarai cewa: Waɗanda suke yin fasikanci ba za a bar su cikin ikilisiya ta Kirista ba kuma ba za su sami rai madawwami ba. (1 Korintiyawa 6:9; Ru’ya ta Yohanna 22:15) Ƙari ga haka, har a yanzu ma suna cutar da  kansu, ta wajen rashin yarda da daraja, rashin jituwa a aurensu, lamiri mai laifi, cikin shege, cututtuka, har ma da mutuwa. (Karanta Galatiyawa 6:7, 8) Me ya sa mutum zai aza kafa a hanyar da take cike da bala’i? Abin baƙin ciki, mutane da yawa ba sa hangen nesa sa’ad da suka yi takunsu na farko, wanda sau da yawa ya ƙunshi hotunan batsa.

HOTUNAN BATSA TAKU NE NA FARKO

9. Hotunan batsa ba su da lahani ne kamar yadda wasu suke da’awa? Ka ba da bayani.

9 A ƙasashe da yawa, ana tallar hoton batsa, a waƙa, a talabijin, da kuma ko’ina a Intane. * Ba shi da lahani ne, kamar yadda wasu suke da’awa? Yana da lahani sosai! Waɗanda suke kallon hotunan batsa za su iya su zama masu tsarance da kuma masu “sha’awace-sha’awace masu banƙyama,” wanda zai iya kai wa ga jarabar jima’i, muguwar sha’awa, matsaloli masu tsanani a aure, har ma da kisan aure. * (Romawa 1:24-27; Afisawa 4:19) Wani mai bincike ya kwatanta jarabar jima’i da wata muguwar cuta mai bazuwa a jiki. Ya ce: “Sai ta ci gaba da girma kuma ta bazu. Kuma ba ta iya ƙarewa da kanta, kuma tana da wuya a yi maganinta har ta warke.”

10. A wace hanya ce za mu yi amfani da mizanin da ke Yaƙub 1:14, 15? (Dubi akwatin nan da ke  shafi na 101.)

10 Ka yi la’akari da kalmomin da ke rubuce a Yaƙub 1:14, 15, sun ce: “Kowane mutum yakan jarabtu in mugun burinsa ya ruɗe shi, ya kuma yaudare shi. Mugun buri kuma in ya yi ciki, yakan haifi zunubi. Zunubi kuma in ya balaga, yakan jawo mutuwa.” Saboda haka, idan muguwar  sha’awa ta shiga zuciyarka, ka ɗauki mataki nan take ka kawar da ita! Alal misali, idan ka ga hoton batsa ba da sonka ba, ka kawar da idanunka babu ɓata lokaci, ko kuma ka kashe kwamfutar ko kuma ka canja gidan talabijin ɗin. Ka yi dukan abin da ya zama dole domin ka guji ba da kai ga sha’awar lalata kafin ta fi ƙarfinka!—Karanta Matta 5:29, 30.

Yin amfani da Intane a inda jama’a suke a cikin gida hikima ne

11. Sa’ad da muke kokawa da muguwar sha’awa, ta yaya za mu nuna muna dogara ga Jehobah?

11 Da dalili mai kyau, wanda ya san mu fiye da yadda muka san kanmu ya ba da gargaɗi: “Ku matarda gaɓaɓuwanku fa waɗanda ke a duniya; fasikanci, ƙazanta, kwaɗayi, mugun guri, da sha’awa, watau bautar gumaka ke  nan.” (Kolossiyawa 3:5) Hakika, yin haka zai kasance ƙalubale ne sosai. Amma ka tuna, muna da Uba mai ƙauna mai haƙuri da za mu nemi taimako daga wurinsa. (Zabura 68:19) Ka juya da wuri a gare shi sa’ad da mugun tunani ya shiga zuciyarka. Ka yi addu’a don “mafificin ikon nan na Allah” kuma ka yi tunanin wasu batutuwa.—2 Korintiyawa 4:7; 1 Korinthiyawa 9:27; ka duba akwati nan “ Ta Yaya Zan Bar Mugun Hali?” a shafi na 104.

12. Mecece “zuciyarmu” kuma me ya sa za mu kiyaye ta?

12 Sulemanu mutum mai hikima ya rubuta: “Ka kiyaye zuciyarka gaba da dukan abin da ka ke kiyayewa: gama daga cikinta mafitan rai su ke.” (Misalai 4:23) “Zuciyarmu” ita ce yadda muke a ciki, da kuma yadda muke a gaban Allah. Bugu da ƙari, yadda Allah yake ganin ‘zuciyarmu’ ne ba yadda wasu suke ɗaukanmu ba, zai sa mu sami rai madawwami ko kada mu samu. Haka yana da sauƙi, amma batu ne da ya kamata mu mai da wa hankali sosai. Saboda kada ya yi wa mace kallon sha’awa, Ayuba mai aminci ya yi wa’adi da idanunsa. (Ayuba 31:1) Wannan misali ne mai kyau a gare mu! Mai zabura ya nuna irin wannan ra’ayin sa’ad da ya yi addu’a: “Ka kawasda idanuna ga barin duban abin banza.”—Zabura 119:37.

RASHIN HIKIMAR DINAH

13. Wacece Dinah, kuma me ya sa abokanan da ta zaɓa ba masu kyau ba ne?

13 Kamar yadda muka gani a Babi na 3, abokananmu za su iya rinjayarmu ta hanya mai kyau ko marar kyau. (Misalai 13:20; karanta 1 Korintiyawa 15:33) Ka yi la’akari da Dinah, ’yar Yakubu. (Farawa 34:1) Duk da reno mai kyau da aka yi mata, don rashin hikima Dinah ta yi abota da ’yan matan Kan’ana. Kamar Mowabawa Kan’ananwa ma malalata ne ƙwarai. (Leviticus 18:6-25) Ga mazan Kan’ananwa, har da Shechem, wanda aka fi “ba shi girma” gaba da dukan  gidan ubansa, Dinah mace ce da za ta so lalata.—Farawa 34:18, 19.

14. Ta yaya abokane da Dinah ta zaɓa ya kai ga bala’i?

14 Wataƙila sa’ad da Dinah ta ga Shechem ba ta yi tunanin jima’i ba. Amma ya yi abin da yawancin Kan’ananwa maza suke ganin ya yi daidai sa’ad da sha’awar jima’i ta taso. Dukan wani ƙoƙarin da Dinah ta yi a banza ne, domin ya “kwana da ita” kuma “ya ɓata ta.” Kamar dai daga baya Shechem ya yi “ƙaunar” Dinah, amma hakan bai canja abin da ya yi mata ba. (Karanta Farawa 34:1-4) Kuma ba Dinah ba ce kawai ta wahala domin wannan ba. Abokan da ta zaɓa ne sanadin abubuwa da suka jawo zagi da kunya ga dukan iyalinta.—Farawa 34:7, 25-31; Galatiyawa 6:7, 8.

15, 16. Ta yaya za mu sami hikima ta gaskiya? (Dubi akwati da ke  shafi na 109.)

15 Idan Dinah ta koyi darassi mai muhimmanci, ta koye shi ta hanya mai wuya. Waɗanda suke ƙauna kuma suke  yi wa Jehobah biyayya ba za su koyi darussan rayuwa ta hanya mai wuya ba. Domin suna ƙaunar Allah, sun zaɓi su “yi tafiya tare da masu-hikima.” (Misalai 13:20a) Saboda haka sun fahimci “kowace hanya mai-kyau” kuma suka guji matsaloli da kuma baƙin ciki.—Misalai 2:6-9; Zabura 1:1-3.

16 Dukan waɗanda suke bukatar hikimar Allah da kuma  waɗanda suka yi aiki domin wannan bukata ta wajen nacewa cikin addu’a da yin nazarin Kalmar Allah a kai a kai da kuma abubuwa da bawan nan mai aminci ya yi tanadi suna samunta. (Matta 24:45; Yaƙub 1:5) Wani kuma abin da yake da muhimmanci shi ne tawali’u, wanda ake nuna ta wajen bin gargaɗin Nassosi da son rai. (2 Sarakuna 22:18, 19) Alal misali, Kirista zai amince cewa zuciyarsa tana iya ruɗarsa. (Irmiya 17:9) Amma sa’ad da yanayi ya taso, yana da tawali’u da zai sa ya karɓi takamaiman gargaɗin da aka yi masa cikin ƙauna da taimako?

17. Ka kwatanta yanayi da zai iya tasowa a iyali, kuma ka nuna yadda uba zai iya tattaunawa da ’yarsa.

17 Ka yi tunanin wannan yanayin. Uba ba ya ƙyale ’yarsa ta fito hira da wani Kirista ba tare da ’yar rakiya ba. ’Yar ta ce: “Baba ba ka yarda da ni ba ne? Ba za mu yi abin da bai dace ba!” Zai kasance tana ƙaunar Jehobah kuma tana da kyakkyawar niyya, amma tana tafiya cikin ‘hikimar Allah kuwa?’ Tana ‘guje wa fasikanci’ ne? Ko kuwa dai tana ‘dogara ga zuciyarta’? (Misalai 28:26) Wataƙila za ka iya tunanin wasu mizanai da za su taimaka wa wannan uba da ’yarsa su yi tunani a kan wannan batun.—Dubi Misalai 22:3; Matta 6:13; 26:41.

YUSUFU YA GUJE WA FASIKANCI

18, 19. Wace jaraba ce Yusufu ya fuskanta a rayuwarsa, kuma yaya ya bi da ita?

18 Yusufu ɗan uban Dinah saurayi ne na kirki wanda ya ƙaunaci Allah kuma ya guje wa fasikanci. (Farawa 30:20-24) Sa’ad da yake yaro ya shaida wautar ’yar’uwarsa da idanunsa. Babu shakka tuna wannan da kuma muradinsa na tsare kansa cikin ƙaunar Allah, sun kāre shi bayan shekaru masu yawa a ƙasar Masar sa’ad da matar ubangidansa ta yi ƙoƙari ta rinjaye shi “yau da gobe.” Hakika, tun da Yusufu bawa ne ba zai iya yin murabus ba! Amma dole ya  bi da yanayin cikin hikima da kuma gaba gaɗi. Ya yi haka ta wajen gaya wa matar Fotifar a’a, kuma a ƙarshe ya guje mata.—Karanta Farawa 39:7-12.

19 Ka yi la’akari: Da a ce Yusufu yana tunanin jima’i da matar ko kuma yana wasiƙar jaki game da jima’i, da zai iya kasancewa da amincinsa kuwa? Da ƙyar. Maimakon yin tunani na zunubi, Yusufu ya ɗauki dangantakarsa da Jehobah da muhimmanci, wanda ya bayyana a kalmominsa ga matar Fotifar. Ya ce mata, “Ubangijina . . . ba ya kuwa hana ni komi sai ke, domin ke matatasa ce: ƙaƙa fa zan yi wannan mugunta mai-girma, in yi zunubi ga Allah kuma?”—Farawa 39:8, 9.

20. Ta yaya Jehobah ya saka hannu a batun Yusufu?

20 Ka yi tunanin irin farin cikin da Jehobah ya yi sa’ad da ya lura da saurayi Yusufu, da ke nesa da iyalinsa, yana riƙe da amincinsa yau da gobe. (Misalai 27:11) Daga baya, Jehobah ya sa aka saki Yusufu daga kurkuku kuma ya zama firayim minista kuma mai kula da abinci! (Farawa 41:39-49) Kalmomin Zabura 97:10 gaskiya ne: “Ya ku masu-ƙaunar Ubangiji, sai ku ƙi mugunta: Shi mai-kiyayadda rayukan tsarkakansa ne; Yana fishe su daga hannun masu-mugunta.”

21. Ta yaya wani matashi a ƙasar Afirka ya nuna gaba gaɗi ta ɗabi’a?

21 Haka yake a yau, bayin Allah da yawa sun nuna cewa  sun ‘ƙi mugunta, sun ƙaunaci nagarta.’ (Amos 5:15) Wani matashi a wata ƙasa a Afirka ya tuna cewa wata ’yar ajinsa ta ce za ta yi jima’i da shi idan ya taimake ta a jarabawarsu na lissafi. Ya ce: “Ba tare da ɓata lokaci ba na ƙi. Ta wajen kasancewa da aminci na, na kasance da darajata, wadda ta fi zinari da azurfa.” Hakika, zunubi yana kawo farin ciki na ɗan lokaci, amma irin wannan sau da yawa yana kawo baƙin ciki mai yawa. (Ibraniyawa 11:25) Bugu da ƙari, farin cikin ba wani abu ba ne idan aka gwada shi da madawwamin farin ciki da yi wa Jehobah biyayya zai kawo.—Misalai 10:22.

KARƁI TAIMAKO DAGA ALLAH MAI JIN ƘAI

22, 23. (a) Idan Kirista ya yi zunubi mai tsanani, me ya sa har yanzu yake da bege? (b) Wane taimako ne mai zunubi zai iya samu?

22 Da yake mu ajizai ne, dukanmu muna kokawa domin mu danne sha’awa ta jiki kuma mu yi abin da ke mai kyau a gaban Allah. (Romawa 7:21-25) Jehobah ya san da wannan, “ya kan tuna mu turɓaya ne.” (Zabura 103:14) Amma kuma wani lokaci sai Kirista ya yi zunubi mai tsanani. Ba shi da bege ne? Hakika yana da shi! Babu shakka, mai zunubin ƙila ya fuskanci sakamakon zunubi, kamar yadda Sarki Dauda ya yi. Duka da haka, Allah “mai-hanzarin gafartawa” ne ga waɗanda suka yi baƙin ciki kuma suka ‘faɗi zunubansu.’—Zabura 86:5; Yaƙub 5:16; karanta Misalai 28:13.

23 Ƙari ga haka, Allah ya yi wa ikilisiyar Kirista tanadin “kyautai ga mutane,” wato, masu kiwo na ruhaniya da suka ƙware kuma waɗanda suke ɗokin ba da taimako. (Afisawa 4:8, 12; Yaƙub 5:14, 15) Makasudinsu shi ne su taimake mai laifi ya gyara dangantakarsa da Allah, kuma kamar yadda mai hikima ya ce, su sami “fahimi” saboda kada su maimaita zunubin.—Misalai 15:32.

 KA ‘SAMI FAHIMI’

24, 25. (a) Ta yaya saurayi da aka kwatanta a Misalai 7:6-23 ya nuna cewa ba shi da “fahimi”? (b) Ta yaya za mu sami “fahimi”?

24 Littafi Mai Tsarki ya yi maganar mutane ‘marasa-fahimi’ da kuma waɗanda suke da “fahimi.” (Misalai 7:7) Domin rashin manyanta a ruhaniya da kuma rashin jimawa a bautar Allah, wani “marar-fahimi’ zai kasance ba shi da hangen nesa. Kamar saurayi da aka kwatanta a Misalai 7:6-23, zai iya faɗawa cikin zunubi mai tsanani babu wuya. Duk da haka, shi mai “fahimi” yana mai da hankali ƙwarai ga mutumin da yake a ciki ta wajen nazarin Kalmar Allah da addu’a a kai a kai. Kuma kamar yadda zai yiwu a yanayinsa na ajizanci, yana sa tunaninsa, muradinsa, motsin zuciyarsa da makasudinsa na rayuwa su jitu da abin da Allah ya amince da shi. Ta haka, yana “ƙaunar ransa” ko kuma yana yi wa kansa albarka, kuma zai “ruske alheri.”—Misalai 19:8.

25 Ka tambayi kanka: ‘Na tabbata kuwa cewa mizanan Allah daidai ne? Na gaskata kuwa cewa manne musu zai kawo farin ciki mai yawa?’ (Zabura 19:7-10; Ishaya 48:17, 18) Idan kana ɗan shakka, to ka mai da hankali ga wannan yanayi. Ka yi bimbini bisa sakamakon ƙeta dokokin Allah. Ƙari ga haka, ka ‘ɗanɗana, ka duba, Ubangiji nagari ne’ ta wajen rayuwa bisa gaskiya kuma cika zuciyarka da tunanin kirki, abubuwa masu gaskiya, masu adalci, masu tsabta, abin ƙauna, abin yabo. (Zabura 34:8; Filibbiyawa 4:8, 9) Ka tabbata cewa, da zarar ka ci gaba da yin haka, za ka ƙara ƙaunarka ga Allah, ka ƙaunaci abin da yake ƙauna, kuma ka ƙi abin da ya ƙi. Yusufu ba kamili ba ne. Duk da haka, “ya guje wa fasikanci” domin ya ƙyale Jehobah ya mulmula shi cikin shekaru masu yawa kuma ya ba shi fahimi. Bari haka ya kasance a gare ka.—Ishaya 64:8.

26. Wane batu mai muhimmanci ne za a tattauna a gaba?

 26 Mahaliccinmu ne ya halicci al’auranmu, ba don a yi wasa da su domin farin ciki ba ne kawai, amma domin su sa mu haifi ’ya’ya kuma mu more aurenmu. (Misalai 5:18) Za a tattauna ra’ayin Allah game da aure a babi biyu na gaba.

^ sakin layi na 4 Adadi da aka bayar a Littafin Lissafi ya haɗa da “hakiman jama’a,” da Alƙalai suka kashe kusan mutane 1,000, da kuma waɗanda Jehobah ya halaka da kansa.—Litafin Lissafi 25:4, 5.

^ sakin layi na 7 Domin bayani game da ma’anar ƙazanta da lalata, ka duba “Questions From Readers” a cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Yuli, 2006, a Turanci, Shaidun Jehobah ne suka buga.

^ sakin layi na 9 “Hotunan batsa,” kamar yadda aka yi amfani da shi a nan, yana nuna zane a hoto, ko a rubuce, ko kuma a murya da aka yi da niyyar ya ta da sha’awar jima’i. Hotunan batsa sun kama daga hoton mutum da ya shirya kansa domin jima’i zuwa hotunan mutane biyu ko fiye da haka suna kan jima’i.

^ sakin layi na 9 An tattauna batun biyan bukata a Rataye, shafi na 218-219.