‘Ka kasance da lamiri mai kyau.’—1 BITRUS 3:16.

1, 2. Idan za ka inda ba ka sani ba, me ya sa ya kamata ka saurari wanda yake yi maka ja-gora, kuma ta yaya za a kwatanta wannan mai ja-gora da lamiri?

MATUƘIN jirgin ruwa ya ja jirginsa cikin raƙuman ruwan babbar teku; matafiyi yana tafiya cikin hamada, kuma matuƙin jirgin sama yana tuƙa jirginsa bisa gajimaren da ya rufe sama. Ka san abin da waɗannan mutanen suke fuskanta? Kowannen su zai iya kasancewa cikin babbar matsala idan ba shi da wani abu ko wani mutum da zai yi masa ja-gora.

2 Ka yi tunanin kana tafiya wurin da ba ka sani ba. Kana tafiya da wani wanda ka amince da shi kuma wanda ya san wurin. Idan ya san wurin sosai zai yi maka ja-gora. Idan ka bi umurninsa, ba za ka ɓace ba. A wata hanya, ana iya kwatanta  wannan mai ja-gora da kyauta mai tamani da Jehobah ya ba mu, wato, lamiri. (Yaƙub 1:17) Idan ba mu da lamiri, za mu ɓace. Idan muka yi amfani da shi da kyau, zai taimake mu mu sami hanya kuma mu ci gaba kan hanyar zuwa rai. Bari mu tattauna ko menene lamiri da kuma yadda yake aiki. Za mu tattauna waɗannan batutuwa: (1) Yadda za a koyar da lamiri, (2) abin da ya sa za mu yi la’akari da lamirin wasu, da kuma na (3) yadda lamiri mai kyau yake kawo albarka.

ABIN DA LAMIRI YAKE NUFI DA KUMA YADDA YAKE AIKI

3. Menene ma’anar wannan kalmar Helenanci “lamiri” a zahiri, kuma wane abu ne mai muhimmanci ya kwatanta da ’yan adam za su iya yi?

3 A Littafi Mai Tsarki, kalmar Helenanci ta “lamiri” a zahiri tana nufin “sani na kai, ko kuma sanin kanka.” Ba kamar dukan wasu halittu na duniya ba, muna da iyawa da Allah ya ba mu na sanin kanmu. Muna iya duban kanmu mu yi wa kanmu shari’a. Lamiri yana aiki ne kamar shaida a cikinmu, ko kuma alƙali, yana bincika halinmu da kuma irin abubuwa da muka zaɓa. Zai iya yi mana ja-gora wajen yanke shawara mai kyau ko kuma ya yi mana gargaɗi game da wadda ba ta da kyau. Daga baya, zai iya yaba mana domin mun yi zaɓi mai kyau ko kuma ya riƙa sūkanmu domin mun yi wauta.

4, 5. (a) Ta yaya muka sani cewa Adamu da Hauwa’u suna da lamiri, kuma menene ya faru domin sun ƙeta dokar Allah? (b) Waɗanne misalai ne suka nuna cewa mutane masu aminci a dā kafin lokacin Kiristoci suna da lamiri?

4 An saka wannan iyawar cikin namiji da tamace tun daga farko. Adamu da Hauwa’u sun nuna cewa suna da lamiri. Mun ga tabbacin wannan daga kunyar da suka ji bayan sun yi zunubi. (Farawa 3:7, 8) Abin baƙin ciki, lamirinsu da ya damu ba zai iya amfane su ba a wannan lokacin.  Da gangan suka ƙeta dokar Allah. Saboda da haka, da saninsu suka zaɓi su zama ’yan tawaye, abokan gaban Jehobah Allah. Da yake su mutane ne kamilai sun san abin da suke yi, kuma babu ja da baya.

5 Ba kamar Adamu da Hauwa’u ba, ’yan adam ajizai masu yawa, sun saurari lamirinsu. Alal misali, mutumin nan mai aminci Ayuba ya ce: “Ina riƙe da adilcina, ba ni sakewa: Muddar raina zuciyata ba ta zarge ni ba.” * (Ayuba 27:6) Hakika Ayuba mutum ne mai lamiri. Ya mai da hankali wajen saurarar lamirinsa, kuma ya ƙyale shi ya yi masa ja-gora a dukan shawararsa da ayyukansa. Saboda haka, ya ce da gamsuwa cewa lamirinsa bai dame shi ba, ko kuma ya azabtar da shi, da kunya da laifi. Ka kula da bambancin da ke tsakanin Ayuba da Dauda. Sa’ad da Dauda ya nuna rashin daraja ga Saul, sarki da Jehobah ya naɗa, “ya zama kuwa daga baya, zuciyar Dauda ta buga shi.” (1 Samuila 24:5) Wannan bugu na lamiri babu shakka sun amfani Dauda, tun daga lokacin sun koya masa ya guji nuna rashin daraja.

6. Menene ya nuna cewa lamiri kyauta ce ga dukan ’yan adam?

6 Shin bayin Jehobah ne kawai suke da wannan kyauta ta lamiri? Ka lura da hurarrun kalmomin manzo Bulus: “Al’ummai, waɗanda ba su da shari’a, kadan bisa ga tabi’a su ke aika abin da ke na shari’a, waɗannan, domin ba su da shari’a sun zama shari’a ga kansu; da shi ke suna bayana aikin shari’a a rubuce cikin zukatansu, lamirinsu kuwa yana shaida tare, tunaninsu kuma yasu yasu suna kai ƙara ko kuwa suna kawo hujja.” (Romawa 2:14, 15) Har waɗanda  ba su san dokokin Jehobah ba ko kaɗan a wani lokaci lamirinsu yana motsa su yi abubuwan da suka jitu da mizanan Allah.

7. Me ya sa lamiri yana iya yin kuskure a wasu lokatai?

7 Amma kuma a wani lokaci lamiri yana iya yin kuskure. Me ya sa? Ka yi la’akari da misalin da aka bayar a baya, idan mai ja-gorar ya rikice, zai iya ɓatar da kai. Kuma idan ka yi musu da shi, ka ƙi ja-gorarsa, kuma ka bi hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ka iya ɓata. Hakazalika, idan muka bar sha’awoyi marasa kyau da ke zuciyarmu suka yi tasiri a kan lamirinmu, za su iya kai mu inda bai dace ba. Kuma idan aka yi amfani da shi ba tare da ja-gorancin Kalmar Allah ba, ba za mu iya bambance abin da ke kyau da marar kyau ba a wasu batutuwa masu muhimmanci. To, domin lamirinmu ya yi aiki yadda ya dace, muna bukatar ja-gorancin ruhu mai tsarki na Jehobah. Bulus ya rubuta: “Lamirina yana shaida tare da ni cikin Ruhu Mai-tsarki.” (Romawa 9:1) To, ta yaya za mu tabbata cewa lamirinmu ya jitu da ruhu mai tsarki na Jehobah? Batu ne na koyarwa.

YADDA ZA A KOYAR DA LAMIRI

8. (a) Ta yaya zuciya za ta iya shafan lamiri, amma menene ya kamata ya fi damunmu a shawarar da za mu yanke? (b) Me ya sa lamirin da bai dame mu ba ba koyaushe ba ne ya dace ga Kiristoci? (Dubi hasiya.)

8 Ta yaya za ka yanke shawarar da take bisa lamiri? Wasu, kamar dai, suna bincika kansu ne, kuma su dubi yadda suke ji, bayan haka sai su yanke shawarar abin da za su yi. Suna iya cewa, “Bai dami lamiri na ba.” Muradin zuciya yana iya kasancewa da ƙarfi, har ya rinjayi lamiri. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciya ta fi komi rikici, ciwuta gareta ƙwarai irin ta fidda zuciya: wa za ya san ta?” (Irmiya 17:9) Saboda haka, ba abin da zuciyarmu take bukata ba ne ya kamata mu fi mai da wa hankali. Maimakon haka, muna  so da farko mu yi la’akari da abin da zai faranta wa Jehobah Allah rai. *

9. Menene tsoron Allah, kuma ta yaya kasancewa da tsoron Allah zai shafi lamirinmu?

9 Idan shawararmu ta kasance ne bisa lamirinmu da aka koyar, za ta nuna muna tsoron Allah, ba muradinmu ba. Ga wani misali. Gwamna Nehemiah yana da ’yancin ya karɓi wasu kuɗi da haraji daga mutanen Urushalima. Amma ya ƙi yin hakan. Me ya sa? Baya son ya baƙanta wa Jehobah rai ta wajen musgunawa mutanen Allah. Ya ce: “Ba haka ni na yi ba, domin tsoron Allah.” (Nehemiah 5:15) Tsoron Allah na gaskiya, tsoron ɓata wa Ubanmu na samaniya rai yana da muhimmanci. Irin wannan tsoron zai motsa mu mu nemi ja-gora daga Kalmar Allah sa’ad da muke da shawarar da za mu yanke.

10, 11. Waɗanne mizanai na Littafi Mai Tsarki ne suka shafi shan giya, kuma ta yaya za mu sami ja-goranci na Allah wajen yin amfani da su?

10 Alal misali, ka yi la’akari da batun giya. Wannan wata shawara ce da yawancinmu muke fuskanta a wajen liyafa, In sha ne ko kada in sha? Da farko, muna bukatar mu koyar da kanmu. Wane mizanin Littafi Mai Tsarki ne ya shafi wannan? Hakika, Littafi Mai Tsarki bai haramta shan giya daidai kima ba. Ya yaba wa Jehobah domin kyautar giya da ya bayar. (Zabura 104:14, 15) Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya haramta shan giya da yawa da buguwa. (Luka 21:34; Romawa 13:13) Bugu da ƙari, ya saka maye cikin zunubai  masu tsanani, irinsu fasikanci da zina. *1 Korintiyawa 6:9, 10.

11 Irin waɗannan mizanan suna koyar da lamirin Kirista kuma suna motsa shi. Saboda haka, sa’ad da muka fuskanci yanke shawarar ko za mu sha giya a inda jama’a suka taru, muna bukatar mu yi wa kanmu waɗannan tambayoyin: ‘Wane irin taro ne aka shirya? Zai kasance ne da hayaniya? Yaya halina? Ina da muradin shan giya ne, ina dogara a kanta ne, ina amfani da ita wajen kame halina ne? Ina da kame kai da ake bukata don na tabbatar da cewa ban sha da yawa ba?’ Sa’ad da muka yi bimbini a kan mizanan Littafi Mai Tsarki da tambayoyin da suka ta da, ya kamata mu yi addu’a domin ja-gorar Jehobah. (Karanta Zabura 139:23, 24) A wannan hanyar, muna roƙon Jehobah ya ja-gorance mu da ruhu mai tsarki. Muna kuma koyar da lamirinmu ya jitu da mizanai na Allah. Da kuma wani abin da ya kamata ya shafi shawararmu.

ME YA SA ZA MU YI LA’AKARI DA LAMIRIN WASU?

Lamiri da aka koyar da Littafi Mai Tsarki zai taimake mu wajen yanke shawarar mu sha ko kada mu sha giya

12, 13. Ka ba da dalilai da suka sa lamiri na Kirista ya bambanta, kuma ta yaya za mu bi da irin wannan bambanci?

12 Wataƙila ka yi mamakin ganin bambancin da ke tsakanin lamirin Kiristoci. Wani sai ya ga wani abu ko kuma al’ada ba shi da kyau; wani kuma sai ya so su domin bai ga dalilin ƙinsu ba. Alal misali game da shan giya da abokai, wani zai so ya ɗan sha kaɗan tare da abokai sa’ad da suke hutawa da yamma, wani kuma ba ya son hakan. Me ya sa da irin wannan bambancin, kuma ta yaya hakan zai shafi shawararmu?

13 Mutane sun bambanta domin dalilai da yawa. Yadda aka yi renonsu ya bambanta. Wasu kuma suna sane da irin  abubuwa da suka yi kokawa da su a dā, wataƙila kuma ba ko yaushe ba ne suke nasara. (1 Sarakuna 8:38, 39) Sa’ad da ya kai ga giya, irin waɗannan mutane wataƙila suna da lamirin da ba ya son giya. Idan irin wannan mutumin ya zo gidanku ziyara, lamirinsa yana iya hana shi shan giya. Za ka yi fushi ne? Za ka nace ne? A’a. Ko da ka san dalilin da ya sa ya ɗauki wannan matakin ko a’a, ba zai faɗi dalilai da suka sa ya zaɓi yin hakan a wannan yanayi ba, ƙauna ga ’yan’uwa za ta hana ka tilasta masa.

14, 15. Game da wane batu ne lamirin Kiristoci na ƙarni na farko ya bambanta, kuma wace shawara ce Bulus ya bayar?

14 Manzo Bulus ya ga cewa lamiri ya bambanta ƙwarai tsakanin Kiristoci na ƙarni na farko. A dā can, wasu Kiristoci sun damu domin wani abinci da aka yi hadaya da shi ga gumaka. (1 Korintiyawa 10:25) Lamirin Bulus bai hana shi cin irin waɗannan abincin da ake sayarwa a kasuwanni ba. A gare shi, gunki ba wani abu ba ne; gumaka ba su suke da abinci ba, Jehobah ne ya halicci abinci. Duk da haka, Bulus ya fahimci cewa wasu ba su yarda da ra’ayinsa ba a kan wannan batu. Wasu ƙila masu bautar gumaka ne ƙwarai kafin su zama Kiristoci. A gare su, dukan wani abu da yake da alaƙa da bautar gumaka a dā ba shi da kyau. To, yaya zai magance wannan matsalar?

15 Bulus ya ce: “Mu fa da ke ƙarfafa ya wajaba mu ɗauki kumamancin raunana, kada mu yi son kai. Gama Kristi kuma ba ya yi son kai ba.” (Romawa 15:1, 3) Bulus ya ga ya kamata mu saka bukatun ’yan’uwanmu gaba da namu, kamar yadda Kristi ya yi. A wani bayani kuma da ya shafi wannan, Bulus ya ce gwamma kada ya ci nama da a ce ya saka tumaki da Kristi ya ba da ransa a gare su tuntuɓe.—Karanta 1 Korintiyawa 8:13; 10:23, 24, 31-33.

16. Me ya sa waɗanda suke da lamirin da ya hana su wani abu za su guji hukunta waɗanda lamirinsu ya bambanta da nasu?

16 A wani ɓangare kuma waɗanda lamirinsu ya hana su  yin wani abu kada su riƙa sūkan wasu, suna nacewa sai kowa ya kasance da irin ra’ayinsu game da batun da ya shafi lamiri. (Karanta Romawa 14:10) Ya kamata lamirinmu ya zama alƙalinmu na ciki, ba na hukunta wasu ba. Ka tuna da kalmomin Yesu: “Kada ku zartar, domin kada a zartar muku.” (Matta 7:1) Ya kamata dukan waɗanda suke cikin ikilisiya su guje wa yin gardama a kan lamirin wasu. Maimakon haka, mu nemi hanyoyin ɗaukaka ƙauna da haɗin kai, mu riƙa ƙarfafa juna, ba rushe juna ba.—Romawa 14:19.

YADDA LAMIRI MAI KYAU YAKE KAWO ALBARKA

Lamiri mai kyau zai ja-gorance mu a rayuwa, ya kawo mana farin ciki da kwanciyar hankali

17. Menene ya faru da lamirin wasu mutane a yau?

17 Manzo Bitrus ya rubuta: Ku riƙe “lamiri mai-kyau.” (1 Bitrus 3:16) Lamiri mai kyau a gaban Jehobah Allah  albarka ce mai yawa. Ba kamar lamirin mutane da yawa ba ne a yau. Bulus ya kwatanta mutane da “an yi ma lamirinsu lalas sai ka ce da ƙarfe mai-wuta.” (1 Timothawus 4:2) Ƙarfe mai wuta yana ƙona jiki, ya sa masa tabo ya kasance ba ya ji. Mutane da yawa suna da lamiri da hakika a mace yake, yana da tabo kuma ba ya ji kuma ba ya yin gargaɗi, ba ya ƙin yarda, ko kuma ya sa mutum ya ji kunya ko kuma ya ji ya yi laifi. Yawancin mutane a yau cike da farin ciki suna yin watsi da lamirinsu da ke gaya musu cewa sun yi laifi.

18, 19. (a) Jin yin laifi ko kunya suna da wane amfani? (b) Menene za mu iya yi idan lamirinmu ya ci gaba da tsawata mana game da zunubi da muka yi a dā da muka riga muka tuba?

18 A gaske, jin mu yi laifi zai kasance hanya ce ɗaya da  lamiri yake gaya mana cewa mun yi abin da bai dace ba. Sa’ad da irin wannan lamiri ya motsa mai zunubi ya tuba, ana iya gafarta masa zunubi mai tsanani ma. Alal misali, Sarki Dauda, ya yi zunubi mai tsanani amma an gafarta masa domin ya tuba da gaske. Ƙin tafarkin laifi da ya yi da kuma ƙudurin da ya yi na bin dokokin Jehobah tun daga wannan lokacin ya sa ya ga cewa Jehobah “nagari ne, . . . mai-hanzarin gafartawa.” (Zabura 51:1-19; 86:5) To, idan muka ci gaba da jin kunya da jin mun yi laifi bayan mun riga mun tuba kuma an gafarta mana fa?

19 Wani lokaci lamiri yana da yawan tsautawa, ya yi ta bugun mai zunubi na dogon lokaci bayan hakan ba shi da wani amfani kuma. A irin wannan yanayi, muna bukatar mu tabbatar wa zuciyarmu cewa Jehobah ya fi dukan yadda muke ji. Muna bukatar mu gaskata da ƙaunarsa da kuma gafararsa, kamar yadda muke ƙarfafa wasu su yi. (Karanta 1 Yohanna 3:19, 20) A wani gefe kuma, lamiri mai kyau yana kawo kwanciyar hankali, da kuma farin ciki mai yawa da ba a yawan samu a wannan duniyar. Mutane da yawa da sun taɓa yin zunubi mai tsanani sun sami irin wannan sauƙi kuma a yau suna bauta wa Jehobah da lamiri mai kyau.—1 Korintiyawa 6:11.

20, 21. (a) Menene aka tsara wannan littafin ya taimake ka ka yi? (b) Mu Kiristoci muna da wane ’yanci, duk da haka, yaya za mu yi amfani da ’yancinmu?

20 An tsara wannan littafi ne domin ya taimake ka ka sami irin wannan farin ciki, ka sami lamiri mai kyau a cikin sauran wannan kwanaki na ƙarshe na zamanin Shaiɗan da suke cike da masifu. Hakika, ba zai iya magana game da dukan dokoki na mizanai na Littafi Mai Tsarki ba da za ka bukaci ka yi tunani a kai kuma a yi amfani da su a yanayi da za su taso a rayuwar yau da kullum. Ƙari ga haka, kada ka yi tsammanin amsa mai sauƙi, game da batun lamiri. Manufar wannan littafin shi ne ya taimake ka ka  koyar da lamirinka ta wajen yin nazarin yadda za ka yi amfani da Kalmar Allah a rayuwarka ta yau da kullum. Ba kamar Dokar Musa ba, “Shari’ar Kristi” ta gayyaci masu bin ta su yi rayuwarsu galibi bisa lamiri da kuma mizanai fiye da rubutattun dokoki. (Galatiyawa 6:2) Ta haka, Jehobah ya bai wa Kiristoci ’yanci ba kaɗan ba. Duk da haka, Kalmarsa ta tuna mana cewa kada mu yi amfani da wannan ’yancin a matsayin “mayafin ƙeta.” (1 Bitrus 2:16) Maimakon haka, irin wannan ’yanci yana ba mu dama mu nuna ƙaunarmu ga Jehobah.

21 Ta wajen addu’a kana la’akari da yadda za ka yi amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki wajen yanke shawara, za ka ci gaba da wannan abu mai muhimmanci sa’ad da da farko ka zo ga sanin Jehobah. ‘Hankalinka wasasshe’ zai zama “bisa ga aikaceya.” (Ibraniyawa 5:14) Lamirinka da aka koyar da Littafi Mai Tsarki zai zama maka albarka a dukan rayuwarka. Kamar mai ja-gora da ya ja-goranci matafiyi, lamirinka zai taimake ka ka yanke shawarar da za ta faranta wa Ubanmu na samaniya rai. Wannan tabbatacciyar hanya ce ta tsare kanka cikin ƙaunar Allah.

^ sakin layi na 5 Babu wata takamaiman kalma a Nassosin Ibrananci ta “lamiri.” Amma lamiri ya bayyana a misalai kamar wannan. Furcin nan “zuciya” galibi tana nufin mutumin da ke ciki. A irin wannan yanayi, yana nuni ne ga wani ɓangare takamaimai na mutumin da ke ciki, wato, lamiri. A Nassosin Helenanci na Kiristoci, kalmar Helenanci da aka fassara “lamiri” ta bayyana sau 30.

^ sakin layi na 8 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa kasancewa da lamiri mai kyau bai isa ba kawai. Alal misali, Bulus ya ce: “Wannan ba ya sa na barata ba: amma mai-yi mini ƙwanƙwanto Ubangiji ne.” (1 Korintiyawa 4:4) Har waɗanda suke tsananta wa Kiristoci kamar yadda Bulus ya taɓa yi, za su yi haka da lamiri mai kyau domin suna tsammanin cewa Allah ya yarda da abin da suke yi. Yana da muhimmanci lamirinmu ya kasance yana da kyau a idanunmu da kuma a gaban Allah.—Ayukan Manzanni 23:1; 2 Timothawus 1:3.

^ sakin layi na 10 Ya kamata a lura cewa likitoci sun ce shan giya kaɗan ba zai yiwu ba ga masu jarabar shan giya; domin a gare su, “daidai kima” yana nufin rashin sha.