Hali ne marar kyau a ruhaniya, tsaranci yana sa mutum ya koyi son kai kuma mai tunanin lalata. * Mai tsaranci zai kai ga ɗaukan wasu a matsayin abubuwa ne kawai na jima’i, domin biyan bukatarsa ta jima’i. Ga mai tsaranci jima’i zai kasance abu ne kawai da ke ba da gamsuwa na ɗan lokaci kuma ya biya bukata amma ba hanyar nuna ƙauna tsakanin mutane biyu ba. Amma wannan gamsuwar na ɗan lokaci ne kawai. Kuma, maimakon ya matarda gaɓoɓinsa ga “fasikanci, ƙazanta, kwaɗayi, . . .da sha’awa [da ba ta dace ba,]” mai tsaranci zai ta da ita.—Kolossiyawa 3:5.

Manzo Bulus ya rubuta: “Ƙaunatattu, . . . bari mu tsarkake kanmu daga dukan ƙazamtar jiki da ta ruhu, muna kāmala tsarki cikin tsoron Allah.” (2 Korintiyawa 7:1) Idan kana kokawa ka bi waɗannan kalmomin, kada ka tsorata. Jehobah “mai-hanzarin gafartawa” ne kuma zai taimake ka. (Zabura 86:5; Luka 11:9-13) Hakika, zuciyarka da take tsauta maka da kuma ƙoƙarinka ka bar wannan hali, ko da kana komawa, ya nuna cewa kana da hali mai kyau. Ka tuna cewa  “Allah ya fi zuciyarmu girma, ya kuwa san abu duka.” (1 Yohanna 3:20) Allah yana ganin fiye da zunubanmu; yana ganin yadda muke. Wannan yana sa ya saurari roƙonmu na neman gafara da tausayi. Saboda haka kada ka gaji wajen zuwa ga Allah cikin addu’ar tawali’u, kamar yaron da ke zuwa wurin ubansa sa’ad da yake cikin matsala. Jehobah ya albarkace ka da lamiri mai kyau. (Zabura 51:1-12, 17; Ishaya 1:18) Hakika, kana bukatar ka ɗauki wasu matakai da suka jitu da addu’arka. Alal misali, dole ka yi ƙoƙari ga guji dukan ire-iren batsa da kuma abokai da ba na kirki ba. *

Idan matsalarka da tsaranci ya ci gaba, don Allah ka yi magana game da batun da iyayenka Kiristoci ko kuma wani aboki Kirista da ya manyanta. *Misalai 1:8, 9; 1 Tassalunikawa 5:14; Titus 2:3-5.

^ sakin layi na 1 Tsarance shafa al’aura ne da sau da yawa yana sa mutum ya kawo.

^ sakin layi na 2 Domin kula da yadda ake amfani da kwamfuta a gida, wasu iyalai suna ajiye shi a inda jama’a suke. Ƙari ga haka, wasu iyalai sun sayi wani tsari da zai riƙa tace abin da ba a bukata. Amma babu wani tsari da yake tabbatacce.

^ sakin layi na 1 Domin shawara game da yadda za a yi nasara bisa tsaranci, dubi talifin nan “Young People Ask . . . How Can I Conquer This Habit?” (Matasa Sun Yi Tambaya . . . Ta Yaya Zan Daina Wannan Hali?) a Awake!, na Nuwamba 2006, da kuma shafuffuka na 205-211 na Littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work, Na 1.