“Ga mai-tsabta za ka nuna kanka mai-tsabta.”—ZABURA 18:26.

1-3. (a) Me ya sa uwa take tabbata cewa ɗanta yana da tsabta? (b) Me ya sa Jehobah yake so masu bauta masa su kasance da tsabta, kuma me yake motsa mu mu kasance da tsabta?

UWA ta shirya ɗanta su fita unguwa. Ta tabbata cewa ta yi masa wanka kuma kayan da ta sa masa masu tsabta ne. Ta san cewa tsabta yana da muhimmanci don lafiyar jikinsa. Kuma ta fahimci cewa yadda ɗanta ya bayyana zai shafi iyayensa.

2 Jehobah, Ubanmu na samaniya, yana son bayinsa su kasance da tsabta. Kalmarsa ta ce: “Ga mai-tsabta za ka nuna kanka mai-tsabta.” * (Zabura 18:26) Jehobah yana ƙaunarmu; ya san cewa kasancewa da tsabta yana da muhimmanci  sosai a gare mu. Kuma yana so mu Shaidunsa mu jawo yabo ga sunansa. Hakika, kasancewarmu da tsabta da kuma halinmu na kirki zai jawo ɗaukaka ga sunan Jehobah mai tsarki ba zagi ba.—Ezekiel 36:22; karanta 1 Bitrus 2:12.

3 Sanin cewa Allah yana ƙaunar mutane masu tsabta yana motsa mu mu kasance masu tsabta. Muna son hanyar rayuwarmu ta kawo daraja ga Allah domin muna ƙaunarsa. Muna so kuma mu tsare kanmu cikin ƙaunarsa. Saboda haka, bari mu bincika abin da ya sa muke bukatar mu kasance da tsabta, abin da kasancewa da tsabta ya ƙunsa, da kuma yadda za mu kasance da tsabta. Irin wannan bincike zai taimake mu mu ga ko da akwai wurare da muke bukata mu yi gyara.

ME YA SA MUKE BUKATAR MU KASANCE DA TSABTA?

4, 5. (a) Menene ainihin dalilin da ya sa ya kamata mu kasance da tsabta? (b) Ta yaya tsabta ta Jehobah ya bayyana cikin abin da ya halitta a zahiri?

4 Hanya ɗaya da Jehobah yake mana ja-gora ita ce ta wajen misali. Saboda haka, Kalmarsa ta aririce mu mu “zama fa masu-koyi da Allah.” (Afisawa 5:1) Ga ainihin dalilin da ya sa za mu kasance da tsabta: Jehobah, Allah da muke bauta wa, mai tsabta ne, mai tsarki a kowace hanya.—Karanta Leviticus 11:44, 45.

5 Tsabta ta Jehobah, kamar halayensa masu yawa, ta bayana a cikin abubuwa da ya halitta. (Romawa 1:20) An tsara duniya domin ta kasance gida mai tsabta don ’yan adam. Jehobah ya kafa tsarin da ke sa ruwa da iska su kasance da tsabta. Wasu irin halitta suna aiki kamar ma’aikatan tsabtace mahalli, suna mai da datti su zama ba su da illa. ’Yan kimiyya suna yi amfani da irin waɗannan halittun wajen tsabtace mahalli sa’ad da man fetur ya zube ko kuma wasu irin gurɓata mahalli da ke faruwa don son kai da haɗamar ’yan adam. A bayyane yake cewa tsabta yana  da muhimmanci ga Mahaliccin “duniya.” (Irmiya 10:12) Ya kamata hakan ya kasance da muhimmanci a gare mu.

6, 7. Ta yaya Dokar Musa ta nanata cewa ana bukatar tsabta wajen masu bauta wa Jehobah?

6 Wani dalili kuma da ya sa ya kamata mu kasance da tsabta shi ne cewa Jehobah, Mai Iko Duka, yana bukatar masu bauta masa su kasance da tsabta. A Dokar da Jehobah ya bai wa Isra’ilawa, ba a raba tsabta da bauta. Dokar ta ka’ide cewa a ranar Kafara, dole babban firist ya yi wanka sau biyu. (Leviticus 16:4, 23, 24) An bukaci firistoci masu hidima su wanke hannayensu da ƙafafunsu kafin su miƙa hadaya ga Jehobah. (Fitowa 30:17-21; 2 Labarbaru 4:6) Dokar ta lissafa abubuwa 70 da suke sa mutum ya kasance ba shi da tsabta a zahiri. Sa’ad da mutum ya kasance ba shi da tsabta, Ba’isra’ile ba zai iya yin bauta ba, a wasu yanayi ma, zai fuskanci hukuncin kisa. (Leviticus 15:31) Dukan wanda ya ƙi bin tsarin tsarkaka, wanda ya haɗa da wanke jiki da kuma wanke tufafi, “za a datse shi daga cikin taron jama’a.”—Litafin Lissafi 19:17-20.

7 Ko da yake ba ma ƙarƙashin Dokar Musa, ta sa mun fahimci yadda Allah yake tunani a kan abubuwa. A bayyane yake cewa Dokar ta nanata cewa ana bukatar tsabta daga waɗanda suke bauta wa Allah. Jehobah bai canja ba. (Malachi 3:6) Zai karɓi bautarmu idan “marar-ɓaci” ce. (Yaƙub 1:27) Saboda haka muna bukatar mu san abin da yake bukata a gare mu game da wannan.

ABIN DA KASANCEWA DA TSABTA A GABAN ALLAH YA ƘUNSA

8. Waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake so mu kasance da tsabta?

8 A cikin Littafi Mai Tsarki, tsabta ta wuce tsabta ta jiki. Kasancewa da tsabta a gaban Allah ya shafi dukan ɓangarorin rayuwarmu. Jehobah yana so mu kasance da tsabta musamman a ɓangarori huɗu, a ruhaniya, ɗabi’a, hankali da kuma ta jiki. Bari mu tattauna su ɗaɗɗaya.

9, 10. Menene kasancewa da tsabta ta ruhaniya take nufi, kuma menene Kiristoci na gaskiya suke guje wa?

 9 Tsabta ta ruhaniya. A taƙaice, kasancewa da tsabta a ruhaniya yana nufin kada a haɗa bauta ta gaskiya da ta ƙarya. Sa’ad da Isra’ilawa suka fita daga Babila za su koma Urushalima, an bukace su su bi wannan hurarren gargaɗi: “Ku fita daga can, kada ku taɓa wani abu mai-ƙazamta; . . . ku tsarkaka.” (Ishaya 52:11) Isra’ilawa sun koma ƙasarsu ne domin su kafa bauta ta Jehobah. Dole ne wannan bauta ta kasance da tsabta, marar aibi daga kowane irin koyarwa marar kyau, ayyuka ko kuma al’adun Babila.

10 A yau, dole ne mu Kiristoci na gaskiya mu mai da hankali domin kada mu gurɓata da bauta ta ƙarya. (Karanta 1 Korintiyawa 10:21) Mai da hankali yana da muhimmanci game da wannan, domin rinjayar addinin ƙarya ya kewaye mu. A ƙasashe da yawa, al’adu masu yawa, da kuma wasu ayyuka suna da alaƙa da bauta ta ƙarya, kamar koyarwa da ta ce, da wani abu a jikin ’yan adam da ba ya mutuwa sa’ad da mutum ya mutu. (Mai-Wa’azi 9:5, 6, 10) Kiristoci na gaskiya suna guje wa al’adu da suka shafi addinin ƙarya. * Ba za mu ƙyale matsi daga wasu ya sa mu bar mizanan Littafi Mai Tsarki game da bauta ta gaskiya ba.—Ayukan Manzanni 5:29.

11. Menene tsabta ta ɗabi’a ta ƙunsa, kuma me ya sa yake da muhimmanci mu kasance da tsabta a nan?

11 Tsabta ta ɗabi’a. Kasancewa da tsabta ta ɗabi’a ta haɗa da guje wa kowane irin lalata. (Karanta Afisawa 5:5) Yana da muhimmanci mu kasance da tsabta ta ɗabi’a. Kamar yadda za mu gani a babi na gaba na wannan littafin, domin mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah, dole ne mu “guje ma fasikanci.” Masu fasikanci da suka ƙi tuba “ba za su gāji mulkin Allah ba.” (1 Korintiyawa 6:9, 10, 18) A gaban Allah, irin waɗannan suna cikin “masu-ƙazanta.” Idan suka ƙi su kasance da  tsabta ta ɗabi’a, “rabonsu yana cikin . . . mutuwa ta biyu.”—Ru’ya ta Yohanna 21:8.

12, 13. Wace alaƙa ce ke tsakanin tunani da aikatawa, kuma ta yaya za mu kasance da tsabta ta hankali?

12 Tsabta ta hankali. Tunani ne ke kai ga aikatawa. Idan muka ƙyale mugun tunani ya sami gindin zama a zukatanmu, ba da daɗewa ba za mu aikata aiki marar tsabta. (Matta 5:28; 15:18-20) Amma idan muka cika zukatanmu da tunani mai kyau, zai motsa mu mu ci gaba da kasancewa da halin kirki. (Karanta Filibbiyawa 4:8) Ta yaya za mu kasance da tsabta ta hankali? Muna bukatar mu guji dukan wani irin nishaɗi da zai ɓata tunaninmu. * Ƙari ga haka, za mu iya cika zukatanmu da tunani masu kyau ta wajen yin nazarin Kalmar Allah a kai a kai.—Zabura 19:8, 9.

13 Domin mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah, yana da muhimmanci mu kasance da tsabta a ruhaniya, ɗabi’a, da kuma a hankalinmu. An tattauna waɗannan ɓangarorin tsabta a wasu babi na wannan littafin. Bari yanzu mu tattauna na huɗun—tsabta ta jiki.

TA YAYA ZA MU KASANCE DA TSABTA TA JIKI?

14. Me ya sa tsabta ta jiki ba ra’ayin mutum ba ne kawai?

14 Tsabta ta jiki ta ƙunshi tsabtace jikinmu da kuma mahallinmu. Irin wannan tsabta ra’ayi ne na mutum da bai shafi kowa ba? Ba zai kasance haka ba ga masu bauta wa Jehobah. Kamar yadda muka gani, tsabtarmu a jiki tana da muhimmanci ga Jehobah ba domin tana da kyau a gare mu ba amma domin tana shafansa. Ka yi tunanin misali da aka bayar da farko. Idan kana ganin yaron da kullum yana da datti ba shi da tsabta yana sa ka yi tunanin iyayensa ko ba haka ba ne? Ba za mu so wani abu game da adonmu ko kuma salon rayuwarmu ya sa a zagi Ubanmu na samaniya  ba ko kuma saƙon da muke wa’azinsa. Kalmar Allah ta ce: “Kada mu bada dalilin tuntuɓe cikin komi, domin kada a yi zargin hidimarmu; amma cikin kowace matsala mu koɗa kanmu masu-hidimar Allah.” (2 Korintiyawa 6:3, 4) To, ta yaya za mu kasance da tsabta a zahiri?

15, 16. Menene tsabta ta ƙunsa, kuma yaya tufafinmu ya kamata su kasance?

15 Tsabtace jikinmu da kuma adonmu. Ko da yake al’adu da yanayin rayuwa sun bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, za mu iya samun isasshen sabulu da ruwa domin mu yi wanka kullum kuma mu tabbata cewa mu da kuma ’ya’yanmu muna da tsabta. Tsabta kuma ta ƙunshi wanke hannunmu da sabulu kafin mu ci abinci ko kuma mu taɓa abinci, bayan mun je bayan gida da kuma bayan mun yi wa jaririn da ya yi ba haya wanka. Wanke hannu da sabulu kāriya ce daga cututtuka kuma zai kāre rayuka. Zai kāre yaɗuwar ƙwayoyin cuta, saboda haka ya sa mutane su guji cututtuka masu sa  gudawa. A ƙasashe da gidaje ba su da irin bayan gida na zamani, ana iya binne ba haya kamar yadda ake yi a Isra’ila ta dā.—Kubawar Shari’a 23:12, 13.

16 Tufafinmu ma suna bukatar wanki a kai a kai domin su kasance da tsabta. Ba dole ba ne tufafin Kiristoci ya kasance mai tsada ko kuma wanda ake yayinsa, amma ya kamata ya kasance da tsabta. (Karanta 1 Timothawus 2:9, 10) Ko a ina muke da zama, muna son adonmu ya “ƙawatar da koyarwar Allah Mai Cetonmu.”—Titus 2:10.

17. Me ya sa gidajenmu da kewayensu ya kamata su kasance da tsabta?

17 Gidajenmu da kuma kewayensu. Wataƙila gidajenmu ba kyawawa ba ne na shagali, amma ya kamata su kasance da tsabta abin sha’awa kamar yadda yanayi ya ƙyale. Hakazalika, idan muna da mota da muke amfani da ita zuwa taro da kuma hidimar fage, mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu tsabtace ta, ciki da waje. Kada mu manta cewa gida da kewaye mai tsabta suna ba da shaida. Ban da haka ma, muna koya wa mutane cewa Jehobah Allah ne mai tsaba, cewa zai “hallaka waɗanda ke hallaka duniya,” da kuma cewa ba da daɗewa ba zai mai da duniya ta zama aljanna. (Ru’ya ta Yohanna 11:18; Luka 23:43) Hakika muna son yadda gidanmu ya bayyana ya nuna wa wasu cewa a yanzu muna nuna tsabta da zai jitu da sabuwar duniya da take zuwa.

Tsabta ta jiki ta ƙunshi tsabtace jikinmu da kuma gidajenmu

18. Ta yaya za mu daraja Majami’ar Mulkinmu?

18 Wurin bautarmu. Ƙaunarmu ga Jehobah tana motsa mu mu daraja Majami’ar Mulkinmu, wato, cibiyar bauta ta gaskiya a inda take. Saboda idan baƙi suka shiga majami’ar, muna son wajen bautarmu ta burge su. Ana bukatar tsabtacewa a kai a kai da kuma kula da gyare-gyare domin majami’ar Mulkinmu ta kasance da ban sha’awa. Ya kamata mu daraja Majami’ar Mulkinmu ta wajen yin dukan abin da za mu iya yi domin ta kasance da tsabta. Gata ne mu ba da lokacinmu domin mu tsabtace wajen bautarmu da kuma yin  wasu ‘gyare-gyare.’ (2 Labarbaru 34:10) Wannan mizanin kuma ya shafi Majami’ar Babban Taron ko kuma wurin da muke yin babban taro ko taron gunduma.

TSABTACE KANMU DAGA HALAYE DA AYYUKAN ƘAZAMTA

19. Domin mu kasance da tsabta ta jiki, menene muke bukatar mu guje wa, kuma ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimake mu game da wannan?

19 Domin mu kasance da tsabta ta jiki, muna bukatar mu guji halaye da ayyukan ƙazamta, kamar su shan taban sigari, maye da giya, da kuma shan miyagun ƙwayoyi ko kuma wasu abubuwa masu ta da hankali. Littafi Mai Tsarki bai ambaci dukan halaye da ayyuka da ake yi a yau ba, amma yana ɗauke da mizanai da za su taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah yake ji game da irin waɗannan abubuwa. Domin mu san ra’ayin Jehobah game da abubuwa, ƙaunar da muke masa za ta motsa mu mu bi tafarkin da zai yarda da shi. Bari mu bincika mizanan Nassosi biyar daga cikin waɗannan.

20, 21. Waɗanne irin halaye ne Jehobah yake so mu bari, kuma wani babban dalili ne muke da shi na yin haka?

20 “Da shi ke fa, ƙaunatattu, muna da waɗannan alkawarai, bari mu tsarkake kanmu daga dukan ƙazamtar jiki da ta ruhu, muna kāmala tsarki cikin tsoron Allah.” (2 Korintiyawa 7:1) Jehobah ba ya so mu yi ayyuka da za su yi wa jikinmu lahani kuma su ɓata ruhunmu, da kuma hankalinmu. Saboda haka, dole ne mu daina shan abubuwa da aka sani suna la’anta jiki ko kuma ƙwaƙwalwa.

21 Littafi Mai Tsarki ya ba da babban dalilin da ya sa ya kamata “mu tsarkake kanmu daga dukan ƙazamta.” Ka lura cewa 2 Korinthiyawa 7:1, ta ce: “Muna da waɗannan alkawarai.” Waɗanne alkawura ke nan? Kamar yadda aka ambata a ayoyi na baya, Jehobah ya yi alkawari: “Ni ma in karɓe ku, In zama Uba gareku.” (2 Korintiyawa 6:17, 18) Ka yi tunani: Jehobah ya yi alkawari zai kāre ku kuma ya ƙaunace  ku kamar yadda uba yake yi ga ’ya’yansa maza da mata. Amma Jehobah zai cika wannan alkawari ne kawai idan ka guji ƙazamta ta “jiki da ta ruhu.” Zai kasance wauta ce ka ƙyale ƙazaman halaye da ayyuka su hana ka wannan dangantaka ta kud da kud da Jehobah!

22-25. Waɗanne mizanai ne na Littafi Mai Tsarki za su taimake mu mu guji halaye da ayyuka marasa tsabta?

22 “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka.” (Matta 22:37) Yesu ya ce wannan ita ce doka mafi girma tsakanin duka. (Matta 22:38) Jehobah ya cancanci irin wannan ƙaunar daga gare mu. Don mu ƙaunace shi da dukan zuciyarmu, ranmu, da azancinmu, dole ne mu guji ayyuka da za su iya rage tsawon ranmu da kuma hankalin da Allah ya ba mu.

23 [Jehobah] yana ba kowa rai, da numfashi, da abu duka.” (Ayukan Manzanni 17:24, 25) Rai kyauta ce daga Allah. Muna ƙaunar mai ba da rai, saboda haka, muna so mu daraja wannan kyautar. Muna ƙin dukan wani hali da kuma ayyuka da suke iya cutarwa, domin mun fahimci cewa irin wannan ayyuka ba sa daraja kyautar rai.—Zabura 36:9.

24 “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Matta 22:39) Halaye marasa tsabta da kuma ayyuka sau da yawa ba mai yin su kawai suke shafa ba amma suna shafan waɗanda suke kusa da shi. Alal misali, hayaki na mai shan taba yana iya yi wa waɗanda suke sheƙansa lahani ƙwarai. Mutumin da ke cutar da waɗanda suke kusa da shi yana ƙeta dokar Allah da ta ce mu ƙaunaci maƙwabtanmu. Saboda haka ya ƙaryata dukan wani da’awar da yake yi cewa yana ƙaunar Allah.—1 Yohanna 4:20, 21.

25 Ka “yi biyayya ga mahukunta, ga masu-iko.” (Titus 3:1) A ƙasashe da yawa, kasancewa ko kuma yin amfani da wasu irin ƙwayoyi ƙeta doka ne. Mu Kiristoci na gaskiya ba ma saya ko kuma mu yi amfani da irin waɗannan haramtattun ƙwayoyi.—Romawa 13:1.

26. (a) Domin mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah, menene muke bukatar mu yi? (b) Me ya sa kasancewa da tsabta a gaban Allah shi ne salon rayuwa mafi kyau?

 26 Domin mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah, muna bukatar mu kasance da tsabta a dukan ɓangarorin rayuwa. Barin halaye da ayyuka na ƙyama da kuma kasancewa da tsabta ba zai kasance da sauƙi ba, amma yana yiwuwa. * Hakika, babu wata hanyar rayuwa mai kyau fiye da wannan, domin Jehobah a kullum yana koyar da mu mu amfana kanmu. (Karanta Ishaya 48:17) Mafi muhimmanci ma, ta wajen kasancewa da tsabta za mu sami gamsuwa da ke zuwa daga sanin cewa muna daraja Allahn da muke ƙauna, ta haka kuma mu tsare kanmu cikin ƙaunarsa.

^ sakin layi na 2 Kalmar Ibrananci da aka fassara “tsabta” tana kwatanta tsabta ta jiki da kuma ta ɗabi’a ko kuma ta ruhaniya.

^ sakin layi na 10 Dubi Babi na 13 na wannan littafin domin bayani game da takamammun bukukuwa da al’adu da Kiristoci na gaskiya suke guje wa.

^ sakin layi na 26 Dubi akwatunan nan “ Ina Kokawa Kuwa Domin In Yi Abin da ke Daidai?” a shafi na 94, da kuma “ Ga Allah Dukan Abu Ya Yiwu,” da ke sama.

^ sakin layi na 67 An canja suna.