Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

“Ku Tsare Kanku Cikin Kaunar Allah”

 RATAYE

Ra’ayin Littafi Mai Tsarki Game da Kisan Aure da Kuma Rabuwa

Ra’ayin Littafi Mai Tsarki Game da Kisan Aure da Kuma Rabuwa

Jehobah yana son waɗanda suka yi aure su kasance da aminci ga alkawarin aurensu. Sa’ad da ya haɗa mace da namiji na farko a aure, Jehobah ya ce: “Mutum za ya . . . manne ma matatasa: za su zama nama ɗaya kuma.” Daga baya, Yesu ya maimaita wannan furci kuma ya daɗa cewa: “Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.” (Farawa 2:24; Matta 19:3-6) Saboda haka, ga Jehobah da kuma Yesu, aure alkawari na dindindin ne da ke ƙarewa a  lokacin da ɗaya tsakanin ma’auratan ya mutu. (1 Korintiyawa 7:39) Tun da aure tsari ne mai tsarki, kashe aure ba abu ba ne da za a ɗauka da wasa. Hakika, Jehobah yana ƙin kashe aure da ba shi da tushe cikin Nassosi.—Malachi 2:15, 16.

Menene dalili na Nassi na kashe aure? To, Jehobah ya ƙi zina da fasikanci. (Farawa 39:9; 2 Samuila 11:26, 27; Zabura 51:4) Hakika, yana ƙyamar fasikanci ƙwarai har ya ƙyale kashe aure domin wannan. (Domin bayani game da abin da fasikanci ya ƙunsa, ka dubi Babi na 9, sakin layi na 7, inda aka ba da bayani a kan fasikanci.) Jehobah ya bai wa marar laifi izinin ya yanke shawarar ko zai so ya zauna da mai laifin ko kuma a kashe aure. (Matta 19:9) Saboda haka, idan marar laifi ya ɗauki matakin kashe aure, ba tafarkin da Jehobah ya ƙi yake bi ba. Hakanan kuma, ikilisiyar Kirista ba ta ba kowa shawarar kashe aure. Wasu yanayi za su motsa marar laifi ya ci gaba da zama da mai laifin, musamman ma idan wannan mai laifi ya ko ta tuba da gaske. Waɗanda suke da dalili na Nassi na kashe aure dole ne su yanke shawararsu kuma su karɓi dukan wani sakamako da hakan zai kawo.—Galatiyawa 6:5.

A wani yanayi mai tsanani, wasu Kiristoci sun yanke shawarar rabuwa ko ma kashe aure ko da yake mijin bai yi fasikanci ba. A irin wannan yanayi, Littafi Mai Tsarki ya ce wadda ta tafi “ta zauna haka ba aure, ko kuwa ta sāke shiryawa da mijinta.” (1 Korintiyawa 7:11) Irin wannan Kirista ba ta da ’yancin neman aure kuma. (Matta 5:32) Ga wasu yanayi da wasu suka ga dalili ne na rabuwa.

Rashin kula da iyali da gangan. Iyali za ta iya talaucewa ƙwarai, ba ta da wajibi na rayuwa, domin maigidan ya ƙi kula da su, ko da yake zai iya yin haka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duk wanda bai kula da . . . iyalinsa ba, ya mūsa wa bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya mugunta.” (1 Timothawus 5:8) Idan irin wannan mutumin  ya ƙi canja halayensa, matar za ta iya yanke shawarar ko tana so ta kāre kanta da na ’ya’yanta ta wajen rabuwa. Hakika, ya kamata dattawa Kiristoci su mai da hankali sosai ga tuhuma cewa wani Kirista ya ƙi kula da iyalinsa. Idan mutum ya ƙi kula da iyalinsa, hakan zai iya kai ga yankan zumunci.

Cin zali. Mutum mai dukan matarsa zai iya sa ranta da lafiyarta cikin haɗari. Idan mai yin hakan Kirista ne, dattawa su binciki wannan tuhuma. Faɗa da kuma nuna ƙarfi dalilai ne na yanke zumunci.—Galatiyawa 5:19-21.

Saka rayuwa ta ruhaniya cikin haɗari. Miji na iya sa ya kasance marar yiwu wa matarsa ta yi bauta ta gaskiya ko kuma ya yi ƙoƙarin tilasta wa matar ta ƙeta dokar Allah a wasu hanyoyi. A irin wannan yanayi, matar tana iya yanke shawarar cewa hanya ɗaya kawai na “biyayya ga Allah [fiye] da mutane” ita ce rabuwa.—Ayukan Manzanni 5:29.

A wasu irin waɗannan yanayi masu tsanani da kuma waɗanda muka tattauna, kada kowa ya matsa wa matar ta rabu da mijinta ko kada ta yi hakan. Ko da yake abokai da suka manyanta a ruhaniya da kuma dattawa za su tallafa da gargaɗi na Littafi Mai Tsarki, ba za su iya sanin cikakke abin da yake faruwa tsakanin mata da miji ba. Jehobah kawai ne yake ganin wannan. Hakika, mace Kirista ba za ta daraja Allah ko kuma tsarin aure ba idan ta ƙara gishiri a kan matsala da take fuskanta a gida domin kawai ta rabu da mijinta ba, haka kuma mijin. Jehobah yana ganin dukan wani ƙulle-ƙulle da ya kai ga rabuwa, ko da yaya mutum ya yi ƙoƙarin ɓoye wa. Hakika, “abubuwa duka a tsiraice su ke, buɗaɗu kuma gaban idanun wannan wanda mu ke gareshi.” (Ibraniyawa 4:13) Amma idan yanayi mai haɗari ƙwarai ya ci gaba, kada kowa ya sūki Kiristan da ta nemi rabuwa. A ƙarshe “kowane ɗayanmu fa za ya kawo lissafin kansa ga Allah.”—Romawa 14:10-12.