1, 2. Yaya yawar nagartar Allah, kuma wane nanaci Littafi Mai Tsarki ya yi game da wannan halin?

MANOMI ya dubi gonarsa ya yi murmushi domin hadari ya haɗu kuma ruwan fari yana saukowa a kan irinsa da suke da bukatar ruwa. A wata ƙasa kuma, tsofaffin abokanai, suna ci suna taɗi suna dariya da magariba yayin da suke sha’awar yadda rana take faɗuwa. A wani wurin kuma, mata da miji suna matuƙar farin ciki yayin da suke ganin ɗansu yana yin tetensa na farko.

2 Ko sun sani ko ba su sani ba, dukan waɗannan mutane suna amfana ne daga abu ɗaya—nagartar Jehovah Allah. Wasu masu addini sau da yawa suna cewa “Allah mai nagarta.” Littafi Mai Tsarki ya fi ma nanata hakan. Ya ce: ‘Ina misalin girman nagartarsa!’ (Zechariah 9:17) Amma kamar dai mutane kalilan ne ainihi suka fahimci abin da waɗannan kalmomi suke nufi. Mecece nagartar Jehovah Allah ainihi ta ƙunsa, kuma yaya wannan halin Allah ya shafi kowannenmu?

Fitaccen Ɓangare na Ƙaunar Allah

3, 4. Mecece nagarta, kuma me ya sa ya fi a kwatanta nagartar Jehovah da cewa nuna ƙauna ce ta Allah?

3 A cikin harsuna da yawa na zamani, “nagarta” kalma ce da ta zama ta kullum. Amma, kamar yadda aka bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki, nagarta ta wuce abu na kullum. Ainihi, tana nufin kirki da kuma tarbiyya mai kyau. Watau, za mu iya cewa Jehovah yana da alheri ƙwarai. Dukan halayensa—haɗe da iko, shari’a, da kuma hikima—suna da kyau ƙwarai da gaske. Har wa yau, nagarta za a kwatanta ta da kyau idan aka ce nuna ƙauna ce na Jehovah. Me ya sa?

 4 Nagarta hali ne da ake yi, ana yi wa wasu. Manzo Bulus ya nuna cewa a wajen mutane ta fi adalci ma ban sha’awa. (Romawa 5:7) Za a iya tabbata cewa mutum mai adalci zai bi abin da doka take bukata daidai, amma nagarin mutum zai yi fiye ma da haka. Zai ɗauki zarafi, yana neman hanyoyin da zai amfani wasu. Kamar yadda za mu gani, Jehovah babu shakka nagari ne a wannan hanyar. Alhali ma, irin wannan nagartar ta taso ne daga ƙaunar Jehovah marar iyaka.

5-7. Me ya sa Yesu ya ƙi a kira shi “Malam managarci,” kuma wace gaskiya ce mai zurfi wannan ya tabbatar?

5 Jehovah farda ne wajen nagartarsa. Ba da daɗewa ba kafin Yesu ya mutu, wani mutum ya dumfare shi, ya yi tambaya, ya kira shi da “Malam managarci.” Yesu ya ce: “Don me ka ke ce da ni managarci? Babu wani managarci sai ɗaya, Allah.” (Markus 10:17, 18) Wannan amsar za ta ba ka mamaki. Me ya sa Yesu ya yi wa mutumin gyara? Shin Yesu, hakikanin gaskiya, ba “Malam managarci” ba ne?

6 A bayyane yake cewa mutumin ya yi amfani da kalmomin “Malam managarci” laƙabi ne na ɗaukaka. Yesu cikin filako ya ba da wannan ɗaukaka ga Ubansa na samaniya, wanda shi ne ƙarshen nagarta. (Misalai 11:2) Yesu yana kuma tabbatar da gaskiya ce mai zurfi. Jehovah ne kaɗai mizani na abin da yake da kyau. Shi ne kawai yake da cikakken iko ya kafa abin da yake da kyau da abin da ba shi da kyau. Adamu da Hauwa’u, ta wajen cin itacen sanin nagarta da mugunta cikin tawaye, sun nemi su ɗauki wannan matsayin ga kansu. Ba kamar su ba, Yesu cikin tawali’u ya bar kafa mizanin a hannun Ubansa.

7 Bugu da ƙari, Yesu ya sani cewa Jehovah shi ne tushen dukan abin da yake da kyau da gaske. Shi ne mai ba da “kowacce kyakkyawar baiwa da kowacce cikakkiyar kyauta.” (Yaƙub 1:17) Bari mu bincika yadda nagartar Jehovah ta bayyana cikin karimancinsa.

 Tabbaci na Yawar Nagartar Jehovah

8. Ta yaya Jehovah ya yi nagarta ga dukan mutane?

8 Duk wanda ya taɓa rayuwa ya amfana daga nagartar Jehovah. Zabura 145:9 ta ce: “Ubangiji mai-alheri ne ga dukan mutane.” (Tafiyar tsutsa tamu ce.) Menene misalin wasu nagartarsa da take ga dukan mutane? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba ya bar kansa babu shaida ba, da shi ke yana yin alheri, yana ba ku ruwaye daga sama da kwanukan ƙoshi, yana cika zukatanku da abinci da farinciki.” (Ayukan Manzanni 14:17) Ka taba farin ciki sa’ad da kake cin abinci mai ɗanɗano? Idan ba don Jehovah cikin nagartarsa ya zana tsarin kewaya na ruwa na wannan duniya ba, da kuma ‘damina mai albarka’ ta ba da yalwar abinci ba, da babu jibi. Jehovah yana yin nagartarsa ba kawai ga waɗanda suke ƙaunarsa ba amma ga kowa. Yesu ya ce: “Ya kan sa ranatasa  ta fito ma miyagu da nagargaru, ya kan aiko da ruwa bisa masu-adalci da marasa-adalci.”—Matta 5:45.

Jehovah yana “ba ku ruwaye daga sama da kwanukan ƙoshi”

9. Ta yaya gawasa ta kwatanta nagartar Jehovah?

9 Mutane da yawa suna wasa da karimanci da aka tara bisa mutane domin aiki mai ci gaba na rana, ruwan sama, da kuma damina mai albarka. Alal misali, ka yi la’akari da ’ya’yan gawasa. A dukan wajaje masu sanyi na duniya itace ne gama gari. Duk da haka, yana da kyan gani, yana da zaƙi, kuma yana cike da ruwa mai wartsakarwa da kuma abubuwa na gina jiki. Ka sani cewa da akwai gawasa iri-iri har 7,500, da suke da launi daga ja zuwa mai ruwan zinariya zuwa mai ruwan ɗorawa zuwa kore kuma girmansu daga  wadda ta fi ’ya’yan magarya kaɗan zuwa girman manyan lemo? Idan ka riƙe ƙwayar iri na gawasa a hannunka, kamar ba shi da wani muhimmanci. Amma daga shi ɗaya ake samun itatuwa masu kyan gani. (Waƙar Waƙoƙi 2:3) Kowacce bazara itacen gawasa yakan cika da dami dami na furanni; kowacce kaka sai ta yi ’ya’ya. Kowacce shekara—har zuwa shekara 75—matsakaicin itacen gawasa zai yi ’ya’ya isashe da zai cika kwali 20 da kowanne zai kai nauyin kilogiram 19!

Daga wannan ƙwayar ’yar mitsitsi irin itace yake girma ya ciyar kuma ya faranta wa mutane rai na shekaru da yawa

10, 11. Ta yaya ƙofofin hankali suke nuna nagartar Allah?

10 Cikin nagartarsa marar iyaka, Jehovah ya ba mu jiki da ‘ƙirarsa abin al’ajabi’ ne, da ƙofofin hankali da za su taimake mu mu ga ayyukansu kuma mu yi farin ciki. (Zabura 139:14) Ka yi tunanin yanayi da aka kwatanta a farkon wannan sura. Menene da ake gani ke kawo farin ciki a irin waɗannan lokatai? Yaro mai farin ciki domin ƙoshin lafiya. Yadda ruwa ke zubowa bisa gonaki. Launi ja, ruwan zinariya, da kuma ruɗa kuyangi. An tsara idon ɗan Adam ya bambance launuka dabam dabam fiye da 300,000! Kuma ƙofar hankalinmu ta ji tana bambance ƙarfin sauti a murya da muke ƙauna ƙwarai, raɗa ta iska a kunnen itatuwa, dariyar farin ciki ta jariri. Me ya sa muke iya ji da kuma gani? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kunne mai-ji, da ido mai-gani, Ubangiji ne ya yi duka biyunsu.” (Misalai 20:12) Amma waɗannan ƙofofi ne biyu kawai na hankali.

11 Ƙofar hankali ta jin ƙamshi wata tabbaci ce ta nagartar Jehovah. Hancin ɗan Adam zai iya ya bambance ƙamshi da wari dabam dabam 10,000. Ka yi tunanin ’yan kaɗan kawai: ƙamshin abinci da ka fi so, furanni, na ganye, warin hayaƙin wuta. Ƙofar hankali ta ji a jiki tana sa ka ji iska tana shafar fuskarka, runguma ta tabbaci ta wadda kake ƙauna, da kuma santsin ’ya’yan itace a cikin tafin hannunka. Idan ka kafa masa haƙori, ƙofar hankali ta ɗanɗano ta samu aiki. Sai ka ji ɗanɗano daga ruwan ’ya’yan itacen, kana jin daɗin  abin da ke ƙunshe cikin ’ya’yan itacen. Hakika, muna da dalilai na cewa game da Jehovah: “Ina misalin girman alherinka, wanda ka ajiye ma waɗanda ke tsoronka!” (Zabura 31:19) Ta yaya Jehovah ya “ajiye” alheri ga waɗanda suke da tsoron Allah?

Nagarta Mai Madawwamiyar Fa’ida

12. Waɗanne tanadi ne na Jehovah suka fi muhimmanci, kuma me ya sa?

12 Yesu ya ce: “An rubuta, Ba da abinci kaɗai ba mutum za ya rayu, amma da kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.” (Matta 4:4) Hakika, tanadin Jehovah na ruhaniya za su amfane mu fiye ma da na zahiri, domin za su kai zuwa rai madawwami. A Babi na 8 na wannan littafin, mun lura cewa Jehovah ya yi amfani da ikonsa na maidowa a lokatan nan na zamanin ƙarshe ya kawo aljanna ta ruhaniya. Muhimmiyar aba ta wannan aljannar ita ce abinci mai yawa na ruhaniya.

13, 14. (a) Menene annabi Ezekiel ya gani a wahayi, da wace ma’ana a gare mu a yau? (b) Wane tanadi ne na ruhaniya Jehovah ya yi wa bayinsa masu aminci?

13 A cikin annabce-annabce masu girma na Littafi Mai Tsarki, an ba wa annabi Ezekiel wahayi na haikali mai girma da aka maido da shi. Daga cikin haikalin ruwa ya malalo, yana daɗa faɗi kuma yana zurfi yayin da yake tafiya har sai da ya zama ‘kogi ninki biyu.’ Duk inda ya bi, kogin zai kawo albarka. A bakin kogin da akwai itatuwa masu ba da ’ya’ya don abinci da kuma warkarwa. Kogin har ma ya ba da rai da kuma amfani ga kogi marar rai, mai gishiri, Mataccen Kogi! (Ezekiel 47:1-12) Menene wannan duka yake nufi?

14 Wahayin yana nufin cewa Jehovah zai maido da tsarin bautarsa ta gaskiya, kamar yadda haikalin da Ezekiel ya gani ya alamta. Kamar wannan kogin na wahayi, tanadin Allah na rayuwa zai malalo a yalwace ƙwarai ga mutanensa.  Tun da aka maido da bauta ta gaskiya a shekara ta 1919, Jehovah ya albarkaci mutanensa da tanadi mai ba da rai. Ta yaya? Littafi Mai Tsarki, littattafai na Littafi Mai Tsarki, taro, da kuma taron gunduma dukansu suna kawo muhimmiyar gaskiya ga miliyoyi. Ta wannan hanyar Jehovah ya koya wa mutanensa game da tanadi mafi muhimmanci don rai—hadayar fansa ta Kristi, wadda take kawo matsayi mai tsabta a gaban Jehovah da kuma begen rai madawwami ga dukan waɗanda suke ƙaunar kuma ke tsoron Allah da gaske. * Saboda haka, a cikin dukan wannan kwanaki na ƙarshe, yayin da duniya tana fama da ƙarancin abinci na ruhaniya, mutanen Jehovah suna more dina na ruhaniya.—Ishaya 65:13.

15. A wace hanya ce nagartar Jehovah za ta malalo zuwa ga mutane masu aminci a lokacin Sarautar Kristi ta Alif?

15 Amma kogin wahayi na Ezekiel bai daina malalowa ba sa’anda wannan tsohon zamani ya zo ƙarshensa. Akasarin haka, zai malalo ma fiye da haka a lokacin Sarautar Kristi ta Alif. Sai ta wajen Mulkin Almasihu, Jehovah zai yi amfani cikakke da tamanin hadayar Yesu, a hankali a ɗaukaka mutane masu aminci zuwa kamilci. Lallai sa’an nan za mu ɗaukaka nagartar Jehovah!

Ƙarin Ɓangarori na Nagartar Jehovah

16. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa nagartar Jehovah ta haɗa da wasu halaye, kuma waɗanne ne wasu a cikinsu?

16 Nagartar Jehovah ta ƙunshi fiye da karimanci. Allah ya gaya wa Musa: “Zan sa dukan nagartata ta gibta a gabanka, in yi shelar sunan Ubangiji a gabanka.” Labarin ya ci gaba da cewa: “Ubangiji ya gibta a gabansa, ya furta kuma, Ubangiji, Ubangiji, Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya.”  (Fitowa 33:19; 34:6) Saboda haka nagartar Jehovah ta haɗa da wasu halaye masu kyau. Bari mu bincika biyu kawai cikinsu.

17. Menene alheri, kuma yaya Jehovah ya nuna ta ga mutane turɓaya, ajizai?

17 “Mai-alheri.” Wannan halin ya gaya mana game da yadda Jehovah yake bi da halittunsa. Maimakon ya kasance babu taushi, marar tausayi ko kuma azzalumi, kamar yadda yake sau da yawa da masu iko, Jehovah yana da kamewa da kuma kirki. Alal misali, Jehovah ya gaya wa Abram: “[Ina roƙonka] ka tada idanunka yanzu, daga wurin da ka ke kuma ka duba arewa da kudu da gabas da yamma.” (Farawa 13:14) Fassara da yawa sun cire kalmar nan na nuna ‘roƙo.’ Amma manazartan Littafi Mai Tsarki sun lura cewa kalmomin asali na Ibranancin sun haɗa da kalma da ta canja furcin daga umurni zuwa roƙo. Da akwai wasu yanayi masu kama da haka. (Farawa 31:12; Ezekiel 8:5) Ka yi tunani, Mamallakin dukan halitta ya ce ‘ina roƙo’ ga mutum turɓaya! A duniyar da mugunta, baƙar magana, da rashin hankali suka zama ruwan dare, ba ya wartsakarwa ne mu yi bimbinin alherin Allahnmu, Jehovah?

18. A wace hanya ce Jehovah “mai-yalwar . . . gaskiya,” kuma me ya sa waɗannan kalmomin suke ba da tabbaci?

18 “Mai-yalwar . . . gaskiya.” Rashin gaskiya ya zama hanyar rayuwa a duniya ta yau. Amma Littafi Mai Tsarki ya tuna mana cewa: “Allah ba mutum ba ne da za ya yi ƙarya.” (Litafin Lissafi 23:19) Alhali ma, Titus 1:2 ta ce: “Allah, . . . ba shi iya yin ƙarya.” (Tafiyar tsutsa tamu ce.) Nagartarsa ba za ta ƙyale shi ba ya yi ƙarya. Saboda haka, alkawuran Jehovah tabbatattu ne ƙwarai; maganarsa, kullum a tabbace take, za ta cika. An kira Jehovah ma “Allah na gaskiya.” (Zabura 31:5) Ba kawai ba ya ƙarya ba amma kuma yana ba da gaskiya mai yawa. Ba a rufe yake ba, ko kuma ya ɓoye saƙo, ko kuma asirce; maimakon haka, yana faɗakar da  bayinsa masu aminci daga ma’ajin hikimarsa marar iyaka. * Har yana koya musu yadda za su rayu cikin gaskiya da yake bayarwa saboda su je su ci gaba da “tafiya cikin gaskiya.” (3 Yohanna 3) Galibi, yaya ya kamata nagartar Jehovah ta shafe kowannenmu?

‘Ka Yi Annuri Saboda Nagartar Ubangiji’

19, 20. (a) Ta yaya Shaiɗan ya nemi ya yi wa dogarar Hauwa’u ga nagartar Jehovah zangon ƙasa, kuma menene sakamakon haka? (b) Yaya nagartar Jehovah ya kamata ta shafe mu, kuma me ya sa?

19 Sa’ad da Shaiɗan ya jarabci Hauwa’u a lambun Adnin, ya fara a hankali wajen yi wa dogararta ga nagartar Jehovah zangon ƙasa. Jehovah ya gaya wa Adamu: “An yarda maka ka ci daga kowane itacen gona a sāke.” A dukan dubban itatuwa da wataƙila suke lambun, ɗaya ne kurum Jehovah ya saka wa mutum taƙunƙumi a kai. Duk da haka, ka lura da yadda Shaiɗan ya yi tambayarsa: “Ashe, ko Allah ya ce, ba za ku ci daga dukan itatuwa na gona ba?” (Farawa 2:9, 16; 3:1) Shaiɗan ya murɗe kalmomin Allah ya sa Hauwa’u ta yi tunanin cewa Jehovah yana hana su wani abu mai kyau. Abin baƙin ciki, kissar ta yi nasara? Hauwa’u, kamar mutane da yawa maza da mata daga bayan ta, ta fara shakkar nagartar Allah, wanda ya ba ta dukan abin da take da su.

20 Mun san zurfin baƙin ciki da azaba da wannan shakkar ta jawo. Saboda haka bari mu riƙe a zuciyarmu kalmomin Irmiya 31:12: ‘Za su yi annuri saboda nagartar Ubangiji.’ Ya kamata nagartar Jehovah ta samu farin ciki da annuri. Bai kamata mu yi shakkar Allahnmu ba, wanda yake cike da nagarta. Za mu iya dogara gare shi ƙwarai, domin dukan abin da yake nema nagari ne ga waɗanda suke ƙaunarsa.

21, 22. (a) Waɗanne hanyoyi ne za mu so mu yi na’am ga nagartar Jehovah? (b) Wane hali ne za a tattauna a babi na gaba, kuma ta yaya ya bambanta da nagarta?

 21 Ƙari ga haka, sa’ad da muka samu zarafi mu yi magana da wasu game da nagartar Allah, mu yi farin ciki a yin haka. Game da mutanen Jehovah, Zabura 145:7 ta ce: “Za su furta zancen alherinka mai-girma, su raira adalcinka.” Kowacce rana da muke raye, muna amfana a wata hanya daga nagartar Jehovah. Me ya sa ba za ka yi ƙoƙari ka riƙa yi wa Jehovah godiya kowacce rana domin nagartarsa, ka faɗi takamammun abubuwa? Ka yi tunanin wannan halin, ka riƙa godiya ga Jehovah kowacce rana, kuma ka gaya wa wasu game da ita za ta taimake mu mu yi koyi da Allahnmu nagari. Yayin da muke neman hanyoyin da za mu yi nagarta, kamar yadda Jehovah yake yi, mu kusace shi sosai. Tsoho manzo Yohanna ya rubuta: “Ƙaunatacena, kada ka bi mugun gurbi, sai mai-kyau. Wanda ya ke aika nagarta na Allah ne.”—3 Yohanna 11.

22 Nagartar Jehovah an danganta ta da wasu halaye. Alal misali, Allah “mai-yalwar jinƙai” ne, ko kuma ƙauna ta aminci. (Fitowa 34:6) Wannan halin ba kamar nagarta ba, takamaimai ne, domin Jehovah yana nuna shi musamman ga bayinsa masu aminci. A babi na gaba za mu koyi yadda yake yin haka.

^ sakin layi na 14 Babu wani misali na nagartar Jehovah mafi girma fiye da na fansa. Dukan yawan miliyoyin halittu na ruhu da zai zaɓa daga ciki, Jehovah ya zaɓi Ɗansa makaɗaici wanda yake ƙauna, ya mutu dominmu.

^ sakin layi na 18 Ya dace da Littafi Mai Tsarki ya danganta haske da gaskiya. “Ka aiko da haskenka da gaskiyarka,” yadda mai Zabura ya rera ke nan. (Zabura 43:3) Jehovah yana ba da haske na ruhaniya mai yawa ga waɗanda suke a shirye a koyar da su, ko kuma ya faɗakar da su.—2 Korinthiyawa 4:6; 1 Yohanna 1:5.