Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Ka Kusaci Jehovah

 Babi Na 9

“Kristi Ikon Allah”

“Kristi Ikon Allah”

1-3. (a) Wane abu mai razanarwa almajiran suka fuskanta a cikin Tekun Galili, kuma menene Yesu ya yi? (b) Me ya sa aka kira Yesu yadda ya dace, “Kristi ikon Allah”?

ALMAJIRAN sun razana. Suna ketare Tekun Galili sai hadari ya dauro farat daya. Babu shakka sun saba da hadari a wannan tekun da ma—ban da haka ma, wasu cikin mutanen kwararru ne wajen sū. * (Matta 4:18, 19) Amma wannan “babban hadari kuwa na iska,” nan da nan ya ta da rakuman ruwa ya sa ruwan ya fusata. Mutanen suka yi aiki tukuru domin su rike jirgin amma ina, hadarin ya fi karfinsu. Rakuman ruwa suna “bubbuga har cikin jirgi,” wanda ruwa ya fara cika shi. Duk da rikicewar, Yesu yana barci mai zurfi a bayan jirgin, domin gajiya daga koyar da taro a ranar. Da suka tsorata domin rayukansu, sai almajiran suka ta da shi, suna roko: “Ubangiji, ka yi ceto; muna halaka.”—Markus 4:35-38; Matta 8:23-25.

2 Yesu bai tsorata ba. Da cikakken tabbaci, ya tsauta wa iskar da kuma tekun: “Ka natsu, ka yi shuru.” Nan da nan, iskar da tekun suka yi biyayya—hadarin ya watse, rakuman ruwan suka baje, sai “babbar natsuwa ta samu.” Sai wani irin tsoro ya kama almajiran. Suka ce wa junansu “wanene wannan fa?” Hakika, wane irin mutum ne wannan da ya tsauta wa iska da kuma teku kamar yana yi wa yaro mai taurin kai tsawa?—Markus 4:39-41; Matta 8:26, 27.

3 Amma Yesu ba mutum ba ne kawai. Ikon Jehovah yana  aiki cikinsa a hanyoyi na ban mamaki. Manzo Bulus da aka hure, daidai kuwa ya ce game da shi “Kristi ikon Allah.” (1 Korinthiyawa 1:24) A wace hanya ce ikon Allah ya bayyana wajen Yesu? Kuma wace rinjaya, yadda Yesu ya yi amfani da ikonsa za ta yi a rayukanmu?

Ikon Dan Allah Makadaici

4, 5. (a) Jehovah ya ba wa Dansa makadaici wane irin iko? (b) Ta yaya aka shirya Dan domin ya yi nufe-nufen Ubansa wajen halitta?

4 Ka yi la’akari da ikon da Yesu yake da shi lokacin rayuwarsa a sama kafin ya zama mutum. Jehovah ya nuna “ikonsa madawwami” sa’ad da ya halicci Dansa makadaici, wanda ya zo duniya aka san shi da Yesu Kristi. (Romawa 1:20; Kolossiyawa 1:15) Daga baya, Jehovah ya ba wa Dansa iko mai girma, ya sa shi ya yi nufe-nufensa na halitta. Game da Dan, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ta wurinsa aka yi dukan abu; ba a yi kome ba cikin abin da an yi, sai ta wurinsa.”—Yohanna 1:3.

5 Za mu iya fahimtar girman wannan aiki kadan ne kawai. Ka yi tunanin ikon da ake bukata don a sa miliyoyin mala’iku masu karfi su rayu, wannan sararin samaniya da biliyoyin dami damin taurarinta, da kuma duniya da iri-irin rayukanta masu yawa. Domin ya cim ma wadannan ayyuka, makadaicin Dan yana da iko mafi karfi a dukan sararin samaniya a hannunsa—ruhu mai tsarki na Allah. Dansa ya yi farin ciki kwarai da ya kasance Gwanin Aiki, da Jehovah ya yi amfani da shi wajen halittar dukan abu.—Misalai 8:22-31.

6. Bayan mutuwarsa a duniya da tashinsa daga matattu, wane iko aka ba wa Yesu?

6 Shin makadaicin Dan zai samu karin iko ne? Bayan mutuwarsa a duniya da kuma tashinsa daga matattu, ya ce: “Dukan hukunci a cikin sama da kasa an bayar gareni.” (Matta 28:18) Hakika, an ba wa Yesu iyawa da kuma  damar nuna iko a dukan sararin samaniya. An ba wa “Sarkin sarakuna, da Ubangijin iyayengiji,” ikon ya “kawarda dukan hukunci, da dukan sarauta, da dukan iko”—wanda ake gani da wanda ba a gani—da ke yin gaba da Ubansa. (Ru’ya ta Yohanna 19:16; 1 Korinthiyawa 15:24-26) Allah “ba ya rage kome ke nan da ba karkashin” Yesu ba—watau, ban da Jehovah kansa.—Ibraniyawa 2:8; 1 Korinthiyawa 15:27.

7. Me ya sa za mu tabbata cewa Yesu ba zai taba yin barna da ikon da Jehovah ya saka cikin hannunsa ba?

7 Muna bukatar mu damu ne cewa Yesu watakila ya yi barna da ikonsa? Ko kadan! Yesu yana kaunar Ubansa da gaske kuma ba zai taba yin wani abin da zai bata masa rai ba. (Yohanna 8:29; 14:31) Yesu ya sani cewa Jehovah ba ya barna da ikonsa mafi girma. Yesu ya lura da kansa cewa Jehovah yana neman zarafi “domin ya bayyana kansa mai karfi sabili da wadanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.” (2 Labarbaru 16:9) Hakika, Yesu yana da irin kaunar Ubansa ga ’yan Adam, saboda haka, za mu iya tabbata cewa Yesu zai yi amfani da ikonsa a nagarin hanya. (Yohanna 13:1) Yesu ya kafa tarihi marar aibi a wannan batun. Bari mu bincika ikon da yake da shi lokacin da yake duniya da kuma yadda ya motsa ya yi amfani da shi.

“Mai-Iko Cikin . . . Magana”

8. Bayan an shafe shi, menene aka ba wa Yesu ikon ya yi, kuma yaya ya yi amfani da ikonsa?

8 Babu shakka cewa Yesu bai yi mu’ujiza ba sa’ad da yake yaro yake girma a Nazarat. Amma wannan ya canja bayan da ya yi baftisma a shekara ta 29 A.Z., yana dan shekara 30. (Luka 3:21-23) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Allah ya zuba masa Ruhu Mai-Tsarki da iko: ya yi yawo yana aikin alheri, yana warkadda dukan wadanda Shaidan ke wahalda su.” (Ayukan Manzanni 10:38) “Aikin alheri”—wannan bai nuna ba cewa Yesu ya yi amfani da ikonsa a hanya mai  kyau? Bayan an shafe shi, ya zama “annabi mai-iko cikin aiki duk da magana.”—Luka 24:19.

9-11. (a) A ina Yesu ya yi yawancin koyarwarsa, kuma wane kalubale ya fuskanta? (b) Me ya sa taron suka yi mamakin koyarwar Yesu?

9 Ta yaya Yesu ya kasance mai iko cikin magana? Ya koyar sau da yawa a fili—a bakin kogi da kuma gefen duwatsu har ma da tituna da kuma kasuwoyi. (Markus 6:53-56; Luka 5:1-3; 13:26) Da a ce maganarsa ba ta ba masu sauraronsa sha’awa ba da sai su yi tafiyarsu. A zamanin da babu littattafai da aka buga, masu sauraro da suka dauki koyarwarsa da muhimmanci dole ne su rike maganarsa cikin zuciyarsu. Saboda haka, koyarwar Yesu dole ne ta kasance da ban sha’awa kwarai, a bayyane sarai, kuma ta kasance ba ta da wuyar tunawa. Amma wannan kalubalen bai kasance matsala ba ga Yesu. Alal misali, ka yi la’akari da Hudubarsa a kan Dutse.

10 Wata safiya a farkon shekara ta 31 A.Z., jama’a sun taru a gefen dutse kusa da Tekun Galili. Wasu sun zo daga Yahudiya da kuma Urushalima, tafiyar mil 60 ko 70. Wasu sun zo daga iyakar Tyre da Sidon kusa da teku, ta arewa. Majiyata da yawa suka matso kusa da Yesu su taba shi, kuma ya warkar da dukansu. Sa’ad da babu ko daya cikinsu da yake ciwo, sai ya fara koyar da su. (Luka 6:17-19) Sa’ad da ya gama magana bayan dan lokaci, dukansu suka yi mamakin abin da suka ji. Me ya sa?

11 Bayan wasu shekaru, wani da ya saurari hudubar ya rubuta: “Taron mutane suka yi mamaki da koyarwarsa: gama ya koya musu kamar mai-hukunci.” (Matta 7:28, 29) Yesu ya yi magana da iko da suka so. Ya yi magana a madadin Allah kuma ya tabbatar da koyarwarsa da ikon Kalmar Allah. (Yohanna 7:16) Furcin Yesu sun fita sarai, gargadinsa suna motsawa, maganarsa ta fi gaban a musanta.  Maganarsa tana taba cibiyar batu da kuma zuciyar masu sauraronsa. Ya koya musu yadda za su sami farin ciki, yadda za su yi addu’a, da kuma yadda za su gina rayuwa mai kwanciyar rai a nan gaba. (Matta 5:3–7:27) Kalmominsa sun taba zukatan wadanda suke neman gaskiya da kuma adalci. Irin wadannan mutane suna shirye su ‘ki’ kansu su bar kome domin su bi shi. (Matta 16:24; Luka 5:10, 11) Wannan shaida ce ga iko cikin maganar Yesu!

“Mai-Iko Cikin Aiki”

12, 13. A wace hanya ce Yesu yake da “iko cikin aiki,” kuma mu’ujizojinsa wane irin bambanci ne suke da shi?

12 Yesu yana da iko kuma “cikin aiki.” (Luka 24:19) Lingila ta ba da rahotannin ayyukan mu’ujiza takamammu guda 30 da ya yi—duka cikin “ikon Ubangiji.” * (Luka 5:17) Mu’ujizojin Yesu sun taba rayukan dubban mutane. Mu’ujizoji biyu kawai—ya ciyar da maza 5,000 daga baya maza 4,000, “banda mata da yara”—watakila taron ya kai mutane 20,000!—Matta 14:13-21; 15:32-38.

Yesu yana tafiya a kan Tekun Galili sa’ad da ake hadari da dare

13 Mu’ujizojin Yesu iri-iri ne. Yana da iko bisa aljanu, yana fitar da su da sauki. (Luka 9:37-43) Yana da iko bisa abubuwa na zahiri, ya juya ruwa ya zama giya. (Yohanna 2:1-11) Ga mamakin almajiransa, ya yi tafiya a kan Tekun Galili da iska ke hurawa kwarai. (Yohanna 6:18, 19) Ya yi iko bisa cuta, ya warkar da nakasa, ciwo mai tsanani, da kuma cututtuka masu razana rai. (Markus 3:1-5; Yohanna 4:46-54) Ya yi irin wannan warkarwa a hanyoyi dabam dabam. An warkar da wasu daga nesa, wasu kuma Yesu ya taba su. (Matta 8:2, 3, 5-13) Wasu sun warke a take, wasu kuma sannu a hankali.—Markus 8:22-25; Luka 8:43, 44.

14. A cikin wadanne yanayi ne Yesu ya nuna yana da iko ya sa a daina mutuwa?

 14 Mafifici ma, Yesu yana da ikon sa a daina mutuwa. A lokaci uku dabam dabam da aka rubuta, ya ta da matattu, ya mayar da yarinya ’yar shekara 12 ga iyayenta, dan tilo ga uwarsa gwauruwa, kuma kaunatacce ga kannensa mata. (Luka 7:11-15; 8:49-56; Yohanna 11:38-44) Ba yanayi da ya gagari Yesu. Ya ta da ’yar shekara 12 daga gado bayan ta mutu ba da dadewa ba. Ya ta da dan gwauruwa daga kan makara, a ranar da ya mutu. Kuma ya ta da Li’azaru daga kabari bayan ya mutu da kwana hudu.

Amfani da Iko Cikin Rashin Son Kai, Cikin Fahimi, da Kuma La’akari

15, 16. Wane tabbaci ne ake da shi cewa Yesu ba shi da son kai wajen amfani da ikonsa?

15 Za ka yi tunanin alamun yin barna da iko da a ce ikon Yesu yana hannun masarauta ajizai? Amma Yesu ba shi da zunubi. (1 Bitrus 2:22) Bai kyale son kai da dogon buri su lalata shi ba, da kuma hadama da take tura mutane ajizai su yi amfani da ikonsu su zalunci wasu.

16 Yesu bai nuna son kai ba wajen amfani da ikonsa, bai taba amfani da ikonsa ba domin ya amfani kansa. Sa’ad da yake jin yunwa, ya ki ya mai da duwatsu su zama burodi wa kansa. (Matta 4:1-4) Dan abin da yake da shi tabbaci ne cewa bai amfana ba da abin duniya ta wajen amfani da ikonsa. (Matta 8:20) Da akwai karin tabbaci cewa ayyukansa na iko ya yi ne ba da son kai ba. Sa’ad da ya yi mu’ujizoji, yana yin haka domin sadaukarwa. Sa’ad da ya warkar da marasa lafiya, iko yana fita a jikinsa. Yana jin fitar ikonsa, har a lokacin warkar da mutum guda kawai. (Markus 5:25-34) Duk da haka, ya kyale taron mutane su taba shi, kuma sukan samu lafiya. (Luka 6:19) Hakika kuwa sadaukarwa ce!

17. Ta yaya Yesu ya nuna cewa yana da fahimi wajen amfani da ikonsa?

 17 Yesu yana da fahimi wajen amfani da ikonsa. Bai taba yin mu’ujiza ba kawai domin ya nuna iko ko kuma yi wasan banza ba. (Matta 4:5-7) Bai yarda ya ba da alamu ba domin ya gamsar da muradin da bai dace ba na Hirudus. (Luka 23:8, 9) Maimakon ya sanar da ikonsa, Yesu sau da yawa ya umurci wadanda ya warkar kada su gaya wa kowa. (Markus 5:43; 7:36) Ba ya so mutane su zo ga kammala game da shi kawai bisa jita-jita.—Matta 12:15-19.

18-20. (a) Menene ya rinjayi yadda Yesu ya yi amfani da ikonsa? (b) Yaya kake ji game da yadda Yesu ya warkar da wani kurma?

18 Wannan mutum mai iko Yesu, ya bambanta kwarai daga sarakuna wadanda suke nuna iko cikin rashin la’akari da bukatu da kuma wahalar wasu. Yesu yana kaunar mutane. Ganin wadanda suke wahala yana taba shi kwarai kuma yana motsa shi ya taimake su. (Matta 14:14) Yana la’akari da yadda suke ji da kuma bukatunsu, kuma kaunarsa tana rinjayar yadda yake amfani da ikonsa. Akwai misali mai sosa zuciya a Markus 7:31-37.

19 A wannan lokacin, taro mai girma sun samu Yesu kuma sun kawo masa marasa lafiya da yawa, kuma ya warkar da duka. (Matta 15:29, 30) Amma Yesu ya fitar da mutum daya domin taimako na musamman. Mutumin kurma ne kuma baya iya magana. Watakila ya lura da tozartuwar wannan mutumin. Yesu ya fid da mutumin gefe—ya fitar da shi daga cikin jama’ar—zuwa wajen da babu kowa. Sai Yesu ya yi amfani da bebenci ya gaya wa mutumin abin da yake so ya yi. Ya “sa yatsotsinsa a cikin kunnuwansa, ya tofa yau, ya taba harshensa.” * (Markus  7:33) Sai Yesu ya duba sama ya yi addu’a. Wadannan ayyuka za su ce wa mutumin, ‘Abin da nake so na yi maka da ikon Allah ne.’ A karshe Yesu ya ce: “Ka bude.” (Markus 7:34) Sai mutumin ya samu kunne kuma yana magana daidai.

20 Lalle yana sosa zuciya a yi tunani cewa har sa’ad da yake amfani da ikon da Allah ya ba shi ya warkar da mawahalta, Yesu ya nuna juyayi ga yadda suke ji! Ba ya ba da tabbaci ne mu san cewa Jehovah ya saka Mulkin Almasihu cikin hannun irin wannan Masarauci mai kauna da la’akari?

Annabcin Abubuwa da Suke Zuwa

21, 22. (a) Menene mu’ujizojin Yesu suke annabtawa? (b) Domin Yesu yana da iko bisa yanayi, me za mu yi tsammaninsa a karkashin Mulkinsa?

21 Mu’ujizojin da Yesu ya yi a duniya alama ce kawai ta albarka mai girma da take zuwa a karkashin sarautarsa ta kirki. A sabuwar duniya ta Allah, Yesu zai sake yin mu’ujizoji—amma a dukan duniya! Ka yi la’akari da abubuwa masu ban sha’awa da suke zuwa a nan gaba.

22 Yesu zai mai da yanayin duniya cikakke. Ka tuna cewa ya nuna iko ta wajen sa hadari ya lafa. Hakika, a karkashin Mulkin Kristi, ’yan Adam ba za su bukaci su tsorata cewa hadari na wajajen tekun Sin, girgizar kasa, gobarar dutse, ko wasu bala’i za su yi musu lahani ba. Tun da Yesu shi ne Gwanin Aiki, wanda Jehovah ya yi amfani da shi wajen halittar duniya da dukan rai da ke bisanta, yana da cikakken sanin yanayin duniya. Ya san yadda zai iya amfani da arzikinta yadda ya dace. A karkashin mulkinsa, dukan duniya za a juya ta zuwa Aljanna.—Luka 23:43.

23. Tun da Sarki ne, ta yaya Yesu zai biya bukatun ’yan Adam?

23 Yaya game da bukatu na ’yan Adam? Da yake Yesu ya iya ciyar da dubbai sosai, ta wajen amfani da abubuwa  kadan, ya tabbatar mana cewa sarautarsa za ta kawo ’yanci daga yunwa. Hakika, abinci da yawa, idan aka raba shi daidai, zai kawo karshen yunwa har abada. (Zabura 72:16) Ikonsa bisa ciwo da cuta ya nuna mana cewa marasa lafiya, makafi, kurame, nakasassu, da kuma guragu za su warke—gabaki daya kuma na dindindin. (Ishaya 33:24; 35:5, 6) Iyawarsa na ta da matattu kuma ya tabbatar da cewa girmansa na Sarkin sama ya hada da ikonsa ya ta da miliyoyin mutane babu iyaka da Ubansa zai yi farin cikin tunawa da su.—Yohanna 5:28, 29.

24. Yayin da muke bimbini bisa ikon Yesu, menene ya kamata mu tuna da shi, kuma me ya sa?

24 Yayin da muke bimbini bisa ikon Yesu, bari mu tuna cewa wannan Dan ya yi kamiltaccen koyi da Ubansa. (Yohanna 14:9) Amfani da iko na Yesu ya bayyana sarai yadda Jehovah yake yin amfani da iko. Alal misali, ka yi tunanin hanya ta kauna da Yesu ya warkar da wani kuturu. Ya ji tausayinsa, ya taba mutumin ya ce: “Na yarda.” (Markus 1:40-42) Ta wajen tarihi irin wannan, Jehovah yana cewa ne, ‘Haka nake amfani da ikona!’ Ba ka motsa ba ka yaba wa Allah mai girma kuma ka yi masa godiya domin yana amfani da ikonsa a hanya ta kauna?

^ sakin layi na 1 Tasowar hadari ba labari abin yau da kullum ne a Tekun Galili. Domin tekun ta yi kasa ainu (wajen kafa 700 kasa da bakin teku), iska ya fi zafi a wurin fiye da wuraren da suke kewaye, kuma wannan yana jawo hadari. Iska mai karfi takan sauko daga Kwarin Urdun na Dutsen Hermon, da yake arewaci. In wuri ya yi shuru yanzu an jima hadari ya fara.

^ sakin layi na 12 Bugu da kari, Lingila a wani lokaci tana tara mu’ujizoji da yawa a karkashin kwatanci guda. Alal misali, a wani lokaci “birni duka” suka zo su gan shi, kuma ya warkar da masu ciwo “dayawa.”—Markus 1:32-34.

^ sakin layi na 19 Tofar da yau alama ce ta warkarwa da Yahudawa da kuma ’Yan Al’umma suka yarda da ita, kuma yin amfani da yau wajen magani an ba da rahoton haka a rubuce-rubucen malaman Yahudawa. Watakila Yesu ya tofar da yau ne ya gaya wa mutumin cewa ya kusa ya warke. Ko yaya dai, Yesu ba amfani ya yi da yaunsa wajen magani ba.