1, 2. Ta yaya rana ta kwatanta ikon Jehovah na halitta?

KA TABA zama a bakin wuta a lokacin sanyin dare? Watakila ka ajiye hannayenka a daidai inda ya dace daga wutar domin ka ji dadin duminta. Idan ka zo kusa da wutar sosai, zafin zai yi yawa. Idan kuma ka yi baya sosai, iska za ta busa, kuma za ka ji sanyi.

2 Da akwai “wuta” da take dimama fatarmu da rana. Wannan “wutar” tana ci ne daga wajen mil miliyan 93 daga inda muke! * Lallai rana tana da karfi sosai, shi ya sa kake jin zafinta daga nisa irin wannan! Duk da haka, duniya tana zagaya wannan tanderu a daidai inda ya dace. Idan duniya tana kusa da rana, ruwa na duniya zai zama tiriri; idan kuma duniya tana nesa zai daskare ya zama kankara. Kowanne cikin yanayi biyun ba zai sa rayuwa ta yiwu a duniya ba. Domin rayuwa ta yiwu a duniya dole ne hasken rana ya kasance da tsabta marar lahani, a bar zancen dadinsa ma.—Mai-Wa’azi 11:7.

Jehovah ya “shirya haske, har da rana”

3. Rana tana ba da tabbaci game da wace muhimmiyar gaskiya ce?

3 Amma, mutane da yawa ba su dauki rana da muhimmanci ba ko da yake rayuwarsu ta dangana ne bisanta. Shi ya sa, ba su iya koyon abin da rana za ta koya mana ba. Littafi Mai Tsarki ya ce game da Jehovah: “Kai ne . . . ka shirya haske da rana.” (Zabura 74:16) Hakika, rana tana kawo daukaka ga Jehovah, “Mai-halittan sama da kasa.” (Zabura 19:1; 146:6) Daya ne kawai daga cikin halittu na sama da babu iyaka da suke koya mana game da ikon Jehovah marar  iyaka na halitta. Bari mu bincika wasu cikin wadannan sosai kuma mu mai da hankalinmu ga duniya da kuma rai da ke raye cikinta.

“Ku Tada Idanunku Sama, Ku Duba”

4, 5. Yaya karfin rana da kuma girmanta suke, duk da haka yaya take idan aka gwada ta da wasu taurari?

4 Kamar yadda watakila ka sani, rana tauraruwa ce. Ta bayyana da girma fiye da taurari da muke gani daddare domin, idan aka gwada su, rana ta fi kusa da mu. Yaya karfinta yake? A tsakiyarta, rana tana da zafin da ya kai kusan awo 27,000,000. Idan za ka iya daukan dan mitsitsi kamar kan allura na rana ka ajiye a nan duniya, ba za ka iya tsayawa ba daga nisan mil 90 ba tare da ka yi rauni ba don wannan dan kankanin tushen zafi! Kowacce dakika, rana tana fid da zafi da ya yi daidai da darurruwan miliyoyin bom na nukiliya.

5 Rana tana da girma sosai da duniyarmu za ta iya shiga cikinta sau 1,300,000. Ita rana tauraruwa ce da ta fi girma? A’a, masana taurari suna kiranta wadar rawaya. Manzo  Bulus ya rubuta cewa ‘tauraro ya bambanta da tauraro ga daraja.’ (1 Korinthiyawa 15:41) Ba zai san gaskiyar wadannan hurarrun kalmomi ba. Akwai tauraro mai girma da idan aka ajiye shi a wurin da rana take, duniya za ta kasance a cikinsa. Wani tauraro mai bala’in girma idan aka ajiye shi a wannan wurin zai kai har Satun—ko da yake wannan duniyar tana da nisa kwarai da duniyarmu, zai dauki jirgin sama shekara hudu kafin ya kai, idan yana gudun da ya fi na harshashi da aka harba da karamin bindiga sau 40!

6. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa adadin taurari yana da yawa a idanun ’yan Adam?

6 Abin ban mamaki ba girman taurarin ba ne amma yawansu. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya ce taurari kusan ba su da iyaka, da wuyar kirgawa kamar “yashi a teku.” (Irmiya  33:22) Wannan furcin yana nufin cewa akwai taurari da yawa da idanunmu ba za su iya gani ba. Hakika, idan marubucin Littafi Mai Tsarki kamar Irmiya ya daga idanunsa cikin dare kuma ya yi kokarin ya kirga taurari da yake gani, zai iya kirga dubu uku ne kawai, iyakar abin da idanun ’yan Adam ba tare da taimako ba za su iya gani cikin dare ke nan. Wannan adadin za a iya gwada shi da adadin kwayoyin yashi da ke cike cikin hannu. Hakika, adadin taurari wane mutum, kamar yashi a teku suke. * Wanene zai iya kirga wannan adadin?

“Yana kiransu duka da sunansu”

7. (a) Kamar taurari nawa damin taurari namu na Kwalkwada ya kunsa, kuma yaya yawan wannan adadin? (b) Me ya sa yake da muhimmanci cewa masana taurari ba su san adadin damin taurari ba, kuma menene wannan ya koya mana game da ikon halitta na Jehovah?

7 Ishaya 40:26 ta ba da amsa: “Ku tada idanunku sama, ku duba ko wanene ya halicci wadannan, wanda ya kawo rundunarsu bisa ga lissafinsu: yana kiransu duka da sunansu.” Zabura 147:4 ta ce: “Yana kididigan yawan taurari.” Nawa ne ‘adadin taurarin’? Wannan ba tambaya ba ce mai sauki. Masana taurari sun kimanta cewa a cikin damin taurari na Kwalkwada tamu kawai da akwai taurari fiye da biliyan 100. * Amma namu daya ne cikin damin taurari masu yawa, kuma da yawa cikin wadannan suna da taurari da suka ma fi yawa. Damin taurari nawa ake da su? Wasu masana taurari sun kimanta cewa akwai biliyan 50. Wasu sun yi zaton cewa sun kai biliyan 125. Mutum ba zai iya tabbata adadin damin taurari ba, ballantana a ce  ainihin biliyoyin taurari da suke cikinsu. Duk da haka, Jehovah ya san wannan adadin. Bugu da kari, ya bai wa kowanne tauraro sunansa!

8. (a) Ta yaya za ka yi bayanin girman damin taurari na Kwalkwada? (b) Ta wace hanya ce Jehovah ya kafa dokar tafiyar wadannan halittun sama?

8 Ibadarmu sai dai ta karu idan muka yi tunanin girman damin taurari. Kwalkwadan taurari namu an lissafa zai dauki gudun haske shekaru 100,000 kafin ya ketare. Haske yana tafiya da saurin bala’i na mil 186,000 kowacce dakika. Cikin wannan tafiyar, haske na daukan shekara 100,000 ya ketare damin taurari da muke ciki! Wasu damin taurari girmansu ya fi namu sau da yawa. Littafi Mai Tsarki ya ce Jehovah yana “shimfida” sammai mai fadi kamar zani. (Zabura 104:2) Kuma shi ya kafa tafiyar wadannan halittun. Daga kwaya mitsitsi ta kura zuwa damin taurari mai girman bala’i, duka suna tafiya ne bisa dokoki na zahiri da Allah ya kafa kuma ya sa su aiki. (Ayuba 38:31-33) Saboda haka, masana kimiyya suka kamanta daidaicin tafiyar wadannan halittun sama da rawa! To, ka yi tunanin Wanda ya halicci wadannan abubuwa. Ba ka tsoron Allahn da yake da irin wannan iko na halitta?

‘Mahaliccin Duniya da Ikonsa’

9, 10. Ta yaya ikon Jehovah ya bayyana game da wurin da ya kafa rana, Jufita, duniya, da kuma wata?

9 Ikon Jehovah na halitta yana bayyane a mazauninmu, duniya. Ya kafa duniya a waje mai kyau cikin sararin samaniya mai girma. Wasu masana kimiyya sun gaskata cewa yawancin damin taurari ba za su kasance wurare da suka dace ba ga rayuwa cikinta kamar ta duniya tamu. Yawancin sashe cikin damin taurari na Kwalkwada da muke ciki babu shakka ba a shirya shi masaukin rai ba. Tsakiyar damin taurari tana cunkushe da taurari. Zafi yana da yawa, kuma taurari suna kusan gogar juna wannan yana faruwa da yawa.  Baki bakin damin taurarin ba shi da abubuwa da suke tallafa wa rayuwa. Rana da duniyarmu suna tsakanin wadannan yanayi biyu.

10 Duniya tana amfana daga kāriyar duniya mai girma da take nesa—duniyar Jufita. Ta fi Duniyarmu girma fiye da sau dubu, Jufita tana da rinjaya mai karfi na maganadiso. Sakamakon haka fa? Tana ja ko kuma kawar da abubuwa da suke gudu cikin sarari. Masana kimiyya sun ce idan ba domin Jufita ba, fadowan abubuwa masu yawa a duniya zai fi haka sau 10,000 fiye da yadda yake a yanzu. A kusa da gida, an albarkaci duniyarmu da kumbo na musamman—wata. Ba kawai abu ba ne mai kyau mai ba da “haske daddare” ba, wata yana taimakawa wajen jirkice duniya daidai. Wannan jirkicewar ce take ba wa duniya fasalinta na kullum, da za a iya tsammani—wata albarka ga rayuwa.

11. Ta yaya iska ta duniya an tsara ta kamar garkuwa?

11 Ikon halitta na Jehovah ya bayyana a dukan bangarori na zanen duniya. Ka yi la’akari da yanayi na mazauni, wanda yake aikin kāre duniya. Rana tana fid da tsirkiya mai amfani da kuma mai kisa. Sa’ad da tsirkiya mai kisa ta sauko bisa yanayin duniya ta sama sama, yana sa iska da muke sheka ta juya ta zama iskar ozone. Wadda ta zama shimfidar ozone, ita kuma, sai ta tsotse yawancin tsirkiyar. Watau, duniyarmu an zana ta ne da laima mai kāre ta!

12. Ta yaya kewayar ruwa ta yanayin iskar duniya ta kwatanta ikon halitta na Jehovah?

12 Wannan bangare daya ne kawai na yanayin duniyarmu, gauraya ce ta iskar gas dabam dabam da suka dace domin su tallafa wa halittu da suke rayuwa a duniya ko kuma kusa da fuskar duniya. Cikin abubuwa na mamaki na yanayin duniyarmu ita ce kewayar ruwa. Kowacce shekara rana tana daga fiye da ruwa mil 100,000 daga teku zuwa sama ta tiriri. Ruwan su zama gajimare, wanda iskar duniya take busa su zuwa ko’ina. Wannan ruwan da ya zama tacacce kuma  mai tsabta, ya sauko ta ruwan sama, dusar kankara, da kuma kankara, ya cika tushen samun ruwa. Kamar yadda Mai-Wa’azi 1:7 ta ce: “Dukan rafufuka suna gudu zuwa teku, duk da haka teku ba ya cika ba; wurinda rafufuka su ke nufa, can za su sake nufa.” Jehovah kadai ne ya iya halittar irin wannan tsarin kewayar.

13. Wane tabbaci ne na ikon Mahalicci muka gani a tsire-tsire na duniya da kuma kasarta?

13 Duk sa’ad da muka ga rai, mun ga tabbaci na ikon Mahalicci. Daga manyan itatuwa da suke da tsawon bene mai hawa 30 zuwa tsiro da suke tsira a teku kuma suke ba da yawancin iskar da muke sheka, ikon halitta na Jehovah yana bayyane ciki. Kasa kanta tana dauke da abubuwa masu rai—tsutsotsi, naman gwari, kwayoyin cuta, duka suna aiki tare a hanya mai girma wajen taimakon tsiro su yi girma. Daidai kuma, Littafi Mai Tsarki ya yi maganar kasa cewa tana da iko.—Farawa 4:12.

14. Wane karfi ne yake cikin kwayar atam ’yar mitsitsi?

14 Babu wani shakka, Jehovah ne “ta wurin ikonsa ya yi duniya.” (Irmiya 10:12) Ikon Allah ya tabbata har cikin kankanin halittarsa. Alal misali, idan kwayoyin atam miliyan suka taru ba za su kai kwarin gashin mutum ba. Kuma idan aka mike kwayar atam har sai ta kai tsawon bene mai hawa 14, cibiyarta ba za ta fi kwayar gishiri ba da za a iya gani a hawa na bakwai. Duk da haka, wannan cibiyar ’yar mitsitsi ita ce tushen karfi mai ban tsoro da ke fashewa a bom na nukiliya!

‘Kowanne Abu Mai Numfashi’

15. Ta wajen tattauna batun bisashe dabam dabam, menene Jehovah yake so ya koya wa Ayuba?

15 Wani tabbaci na ikon halitta na Jehovah yana wajen dabbobi da yawa da ke duniya. Zabura ta 148 ta lissafa abubuwa da yawa da suke yabon Jehovah, kuma aya ta 10 ta hada da “dabbobi da dukan bisashe.” Ya nuna abin da ya sa  mutum ya kamata ya ji tsoron Mahalicci, Jehovah ya taba magana da Ayuba game da irin wadannan dabbobi, kamar su zaki, jakin daji, bauna, dorina, da kuma kada. Menene nufinsa? Idan mutum yana tsoron wadannan manyan dabbobi, masu ban tsoro, da ba a iya rike su, yaya ya kamata ya ji game da Mahaliccinsu?—Ayuba, surori 38-41.

16. Me ya burge ka game da wasu tsuntsaye da Jehovah ya halitta?

16 Zabura 148:10 ta ambaci “tsuntsaye masu-fukafukai.” Ka yi tunanin irinsu dabam dabam! Jehovah ya gaya wa Ayuba game da jimina, wadda take “raina doki da mahayinsa.” Wannan tsuntsuwa mai tsawon kafa takwas ko da yake ba ta iya tashiwa, amma tana iya gudun mil 40 a awa guda, in ta yi taku daya, tana kai wa kafa 15! (Ayuba 39:13, 18) A wani bangare kuma, tsuntsu albatross yana yawancin rayuwarsa a bakin teku. Marar fiffika, wannan tsuntsun fadin fukafukinsa ya kai kafa 11. Zai iya tashi na awoyi yana mike ba tare da fiffika ba. Akasin haka, tsuntsu dangin marai shi ne tsuntsu mafi kankanta a duniya tsawonsa inci biyu ne kawai. Yana fiffika wajen sau 80 cikin dakika daya! Tsuntsu dangin marai yana walkiya kamar lu’u lu’ai, zai iya tsayawa wuri daya kamar jirgin sama mai saukar ungulu.

17. Yaya girman babbar dabbar teku yake, kuma yaya ya kamata mu kammala bayan mun bincika dabbobin da Jehovah ya halitta?

17 Zabura 148:7 ta ce har “dodoni na ruwa” suna yabon Jehovah. Ka yi la’akari da dabbar da yawanci suka gaskata cewa ita ce dabba mafi girma a wannan duniyar, babbar dabban ruwa. Wannan “dodo” da ke zama cikin teku zai kai tsawon kafa 100 ko ma fiye da haka. Nauyinsa zai kai na manyan giwaye 30. Harshensa kawai ya kai nauyin giwa guda. Zuciyarsa ta kai girman karamar mota. Wannan babbar aba tana bugu sau 9 ne kawai a minti guda—akasin wannan zuciyar tsuntsu dangin marai tana bugu wajen sau 1,200 a minti guda. Akalla daya cikin hanyoyin jini na katuwar dabbar teku tana da girma sosai da yaro zai iya rarrafe  a ciki. Hakika zuciyarmu ta motsa mu mu furta yabo da ya rufe littafin Zabura: “Abin da yake da numfashi duka shi yi yabon Ubangiji.”—Zabura 150:6.

Koyo Daga Ikon Halitta na Jehovah

18, 19. Yaya bambancin abin da Jehovah ya halitta yake a wannan duniya, kuma menene halitta yake koya mana game da ikon mallakarsa?

18 Menene muka koya daga yadda Jehovah yake amfani da ikonsa na halitta? Mun tsorata domin halittu iri-iri. Wani mai Zabura ya ce: “Ya Ubangiji, ayyukanka ina misalin yawansu! . . . duniya cike ta ke da wadatarka.” (Zabura 104:24) Kwarai kuwa! Masana kwayoyin rai sun gano iri-irin abubuwa masu rai a duniya fiye da miliyan; duk da haka, ra’ayoyinsu sun bambanta, wasu sun ce watakila akwai wajen miliyan 10, miliyan 30 ko ma fiye da haka. Mai zane, wani lokaci sai ya ga iyawarsa ta kare. Akasin haka, iyawar Jehovah—ikon ya halicci sabo da kuma abubuwa iri-iri—lallai ba ya karewa.

19 Amfani da Jehovah yake yi da ikonsa na halitta yana koya mana game da ikon mallakarsa. Kalmar nan “Mahalicci” ta bambanta Jehovah daga dukan abubuwa na cikin sararin samaniya, dukan wadannan “halittu” ne. Har Dan Jehovah makadaici, wanda “gwanin mai-aiki ne” a lokacin  halitta, ba a taba kiransa Mahalicci ba ko kuma aboki Mahalicci wajen halitta a cikin Littafi Mai Tsarki. (Misalai 8:30; Matta 19:4) Maimakon haka, shi “dan fari ne gaban dukan halitta.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Kolossiyawa 1:15) Matsayin Jehovah na Mahalicci ya ba shi cikakken dama ya yi iko bisa dukan halitta.—Romawa 1:20; Ru’ya ta Yohanna 4:11.

20. A wace hanya ce Jehovah ya huta tun da ya gama halittarsa ta duniya?

20 Jehovah ya daina amfani da ikonsa na halitta ne? To, Littafi Mai Tsarki ya ce sa’ad da Jehovah ya gama ayyukansa na halitta a rana ta shida ta halitta, sai “ya huta fa a kan rana ta bakwai daga dukan aikinsa da ya yi.” (Farawa 2:2) Manzo Bulus ya nuna cewa wannan “rana” ta bakwai shekaru dubbai ne, domin har yanzu tana ci gaba. (Ibraniyawa 4:3-6) Amma ‘hutu’ yana nufi ne cewa Jehovah ya daina aiki gabaki daya? A’a, Jehovah bai daina aiki ba. (Yohanna 5:17) Hutunsa, watau, yana nufi ne cewa ya dakata daga aikin halitta ta zahiri game da duniya. Aikin cika nufinsa kam, ya ci gaba ba tare da dakatawa ba. Irin wannan aikin ya hada da hure Nassosi Masu Tsarki. Aikinsa ya hada da kawo “sabon halitta,” da za mu tattauna a Babi na 19.—2 Korinthiyawa 5:17.

21. Ta yaya ikon halitta na Jehovah zai shafi mutane amintattu har abada abadin?

21 Lokacin da ranar hutu ta Jehovah ta kare, zai iya cewa dukan ayyuka a duniya “yana da kyau kwarai,” kamar yadda ya ce a karshen kwanaki shida na halitta. (Farawa 1:31) Yadda zai zabi ya nuna ikonsa na halitta daga baya, ba a sani ba tukuna. Ko yaya dai, za mu tabbata cewa amfani da ikonsa na halitta zai ci gaba da burge mu. Za mu koya game da Jehovah ta wajen halittunsa har abada abadin. (Mai-Wa’azi 3:11) Da zarar mun samu karin sani game da shi, hakanan kuma tsoronmu na ibada zai zurfafa—kuma hakanan za mu kusaci Mahaliccinmu Mai Girma.

^ sakin layi na 2 Domin ka fahimci wannan zango mai nisa, ka yi tunanin wannan: Don ka yi tafiya mai nisan nan da mota—kana gudun mil 100 a awa, awoyi 24 a rana—zai dauke ka fiye da shekara dari!

^ sakin layi na 6 Wasu suna tunanin cewa mutanen dā a lokatan Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da madubin kawo nesa kusa irin na dā. Idan ba haka ba, suka ci gaba, yaya mutanen wancan lokacin suka san cewa adadin taurari yana da yawa, marar iyaka, ga mutum? Irin wadannan kame-kame marasa tushe ba su daraja Jehovah ba, Mawallafin Littafi Mai Tsarki.—2 Timothawus 3:16.

^ sakin layi na 7 Ka yi la’akari da lokacin da zai dauke ka ka kirga taurari biliyan 100 kawai. Idan za ka iya kirga tauraro daya kowacce dakika—kuma ka ci gaba awoyi 24 a rana—zai dauke ka shekaru 3,171!