A wannan sashe za mu bincika labaran Littafi Mai Tsarki da suka tabbatar da ikon Jehovah na halitta, na halakarwa, da kārewa, da kuma na maidowa. Fahimtar yadda Jehovah Allah, wanda “Mai-karfi cikin iko” ne, yake amfani da “girman ikonsa,” zai cika zukatanmu da ban tsoro.—Ishaya 40:26.